Showing 78001 words to 81000 words out of 110552 words

Chapter 27 - GABA GADI book Complete by Jamila Umar Tanko JUT.txt

saka ni na sake yin imani, na yi godiya ga Allah mahallicina da a zahiri bai dora min talauci ba. Na sake tausayawa talaka na yi alkawari zan ci gaba da taimakonsa a duk lokacin da na ga alamar yana neman taimako." Nihal ta fada yayin da hawaye ya sirnano daga idanuwanta. Tabbas ta tuna wulaqancin da ta gani.
"ki koma duniyarku ki fita daga cikinmu toh. Ke ba alkhairi ba ce a gare mu." In ji Bash.
"sai ga shi na saba da ku ba zan iya barinku ba, na zame mu ku qadangaren bakin tulu." In ji Nihal a lokacin da suka kara takubbansu.
"Ka matsa ka bani hanya zan wuce duk wannan abinda ka ke yi na riga da na gama jin saqonka na kuma gane da kaina cewar ka na sona ne, wataqila dan ba na kula ka ne shine damuwarka."
Ya matsa ya bata hanya, Nihal ta wuce ta je ta hau kan raquminta ta tafi yayin da Bash ya bi ta da kallo a fusace shima ya haye kan dokinsa ya wuce.
" cuuuuut." In ji Abbas yayin da ya fara tafi yana daga hannu yana jinjina. Sai 'yan wajen gaba daya su ka hau tafi da ihu.
Tabbas sin din nan ya yi masa kyau gaba daya an canja kalamansa amma kuma am fito da sakonnin da ake so a isar ba tare da Abbas ya san abinda suke nufi da junansu ba, domin su na da manufarsu a wannan maganar ta su . Aisa ta fahimci akwai alamar tamabaya a cikin kalamansu sai ta sake fusata.
Bayan an yi sallar la'asar aka koma bakin aiki anan ne Nihal za ta kara da Aisa buzuwa.
" sarkin garinku ma bawanmu ne dan haka ke ba kowa ba ce illa baiwata wacce ta fito daga tsatson da basu da asali. Ba ki isa ki ja da Gimbiya Nihal ba."
Aisa Buzuwa ta tunzura ta ce " Darakta daman haka ka ce ta fada? Na dauka cewa ka yi ta ce "asalin sarkin garinku ma bawanmu ne."
Abbas ya yi dariya ya ce "tunda aka ce sarkin garinku ma bawansu ne, kin ga kenan ke ma baiwarsu ce."
Aka kwashe da dariya aka kowa ya ce Hausar Nihal ta daidai, dukka abu daya yake nufi.
A haka dai dakyar aka qara sin din kamar fada kamar wasa. Dare ya kawo kai don haka aka fara shirin tashi. Garin Maradi zasu koma masaukinsu na jiya sai gobe zaa dawo.



Talla!! Talla!! Talla!!!


Katafaren wajen cin abinci mai suna a qasa:


'JAYROUQ CAFE'

Ana daf da bude shi.
Akan titin Court Road opp kotun Nafi'u.


Abincin zamani irin su:
Chinese fried Rice
Fried rice
Coconut rice
Jellop rice.


Source:
Chiken in sweet and sour source.
Stewed Fish
Chicken soup


Salad:
Macaroni salad
Chicken Salad
Les vagas barbecue chicken salad.
Potato salad.


Pastries:
Shawarma.
Burger.


Cakes:
Birthday cakes
Chocolate cake
Vanilla cup cakes
Red valvet cake


Mocktail:
Virgin mojito
Melonade
Lemonade


Contact no. 08065283822
11/14/21, 7:19 AM - MY MTN 2: Na kudi ne 馃グ


GABA GADI


NA


JAMILA UMAR TANKO
(JUT)


Su Nihal sun nufi wajen doguwar motarsu Bus da ta kawo su za su shiga sai ta hango Abbas ya na yi ma ta dan kira daga lungu, da alama baya so kowa ya gan shi. Ta ce da su Hashim su jira ta bari ta je wajen Darakta ya na kiranta, ta isa wajensa cike da mamaki.
Abbas ya ce "ban baki shawara akan ku koma masaukinku zaa iya samun matsala ko su dake ku ko su zage ku. Zan canja muku masauki ku dukka ukun. Yanzu ku yi dubara ko Hashim ya je ya dauko mu ku kayanku daga cikin bus ku kawo motata in sun tafi sai mu tafi. Yanzu kin fita daban da su,kin zama celebrity." Su ka yi dariya ita da shi.
Nihal ta kira Hashim da Najaatu gefe ta fada musu saqon Abbas, tabbas ya fadi gaskiya babu abinda zai hana a yi fada yadda kowa ya ke jin haushinsu. Hashim ya tafi da sauri ya fadawa direba cewar ya bude masa but zai dauki kayansu za su canja mota. Ana budewa aka yi yiwa Hashim caaa akai wai kada ya sake ya sace musu wani abu, dan haka duk abinda ya bata shi ne.
Mata da maza wasu a waje wasu a cikin mota sai caccakarsa a ke yi, ba komai ba ne illa haushinsu da ake ji sun samu daukaka. Bai kula su ba ya jawo akwatunansu guda uku ya tafi.
Anan aka gane cewar an canja musu matsayi sun bar cikinsu sun koma cikin super stars sai ran kowa ya sake baci, Abbas ya na shan zagi daidai gwargwado.
Dukka motocin su ka ja suka tafi, Bash ya dauki Aisa su ka tafi. Abbas ne da su Nihal su ka rage, Abbas ya na can su na lissafi da masu raquma ya sallame su.
Motarsa ya ce su shiga su tafi, Hashim ya shiga gidan gaba yayin da Nihal da Najaatu suka zauna a baya. Abin mamaki sai ya ga buza daya ya shigo cikin motar. Abbas ya zabura ya tambaya Nihal ta ce ita ce ta ce ya zo su je akwai tattaunawar da za su yi, ta na so ta koyi yaren ko da kadan ne kafin a gama fim din.
Abbas ya ji dadi sosai domin akwai hikima a yin hakan. Ya na son Nihal dan komai na ta kamar da gaske take yi ana son actor ya zama haka.
Buzu ya na jin Hausa kadan-kadan tun a cikin mota ya fara koya musu ita da Najaatu. Da suka isa Maradi hotel din da aka sauke su Bilal nan ya kai su Nihal da Najaatu ya kama musu daki mai daraja irin na su Bilal. Kai! duniya abar tsoro ce in kai ba kowa ba ne za ka ga wulaqanci. Wato Abbas ko kunya babu har ya daukaka darajarsu. Ya ce Hashim ya zo su je wani gida.
Kafin ya bar hotel din sai da Abbas ya wuce dakin Bilal kai tsaye ya je ya duba jikinsa, Aisa ta raka Abbas dakin Halima ya duba ta itama, jikin na su da sauki amma fa za su dauki lokaci mai tsayi kafin su warke gaba daya. Ya shaida musu gobe zaa samo wanda zai tuqa su ya kai su gida. Daga dukkan alamu har yanzu labari bai iske su cewar Nihal ta haye gurbin su ba. Dan a maganganunsu ya ji su na cewa idan su ka warke sai a dawo a yi fim din.
Murmushi Darakta yayi a zuciyarsa ya ce " kun makara ai, a wani fim din ma ba zan sake yi da ku balle wannan. Ni da nake da Nihal me zan yi da ku kuma?"
Nihal Nuren ce sanye da riga da Wando na Jeans ta na zaune akan kujera a wajen shaqatawa na hotel din tare da bature da buzu su na tattaunawa.
Ta bude komfoyutar bature ta na daddannawa email din ta ta shiga ta na karantawa, ta sami dubbunnan sakonni daga masoya da daraktoci turawa da kuma kamfanoni daban daban, ana zawarcinta data zo ta yi musu fim. Da alama an saki wasu daga cikin finafinan da ta yi, duniya gaba daya ta dauka da alama ta karbu. Farin ciki ya ya kama ta sosai musamman da ta ci karo da ruwan alerts zunzutun kudaden da ta samu abin ya firgita ta, ya tsorata ta. Har ta fara tunanin ko mafarki take yi ne, miliyoyin kudin da aka qarasa biyanta ne na fim din data yi, tabbas idan su ka zama naira tana daya daga cikin matasa masu kudin Africa.
Nihal ta yi murna sosai tallar da wannan baturen ya gayyace ta kamfanin sun tura mata mail cewa sun dauke ta, domin sun yi bincike akanta sun gano ko ita wacece dan haka za ta yi musu talla akan macemacen mata masu ciki da masu mutuwa a wajen haihuwa a afrika. Za ta yi musu da Hausa da turanci da faransanci. Tashin farko ma miliyan biyar su ka biya ta in ta gama za su cika mata.
Ashe meeting din da suka dinga yi kenan da turawa har su Bilal su ka ganta suka zaci ba ita bace. Shi kuwa wannan buzu ya zo ne dan ya karbi kudi, Nihal ta ce gobe su hayo ma ta raquma guda dari da mahaya guda dari da takubba guda dari haka a taho da kayan yaqi guda hamsin-hamsin lallai zaa sha gumirzun yaqi. Da kudinta ta biya ba ta buqatar Abbas ya sani.
Bayan bature ya bata takarda ta saka hannu sai ya bata zunzurutun cefa ta miliyan biyu, a ciki ta warewa buzu na sa maqudan kudi ne masu yawa, murna ta rufe shi yana ta godiya.
Bilal ne a zaune a gefensu ya na sanye da gajeren wando da riga shimi kasancewar ko ina bandeji ne a jikinsa, sai da ta waiwayo su ka hada ido ta fuskanci ya razana matuqa da ganinta. Ta yi kamar bata ganshi ba, ita da bature da Buzu suka gama kowa ya kama gabansa. Ya bi ta da kallo har ta qure.
Abin mamaki bayan ta tafi babu jimawa sai Bilal ya ga Nihal sanye da abaya ita da Najaatu da Bash Auta sun fito su na nemansa. Bash ne a gaba su na biye da shi. Sallama Nihal ta yi masa gami da gaishe shi haka ma Najaatu. Bilal ya saki baki ya na kallon Nihal sama da qasa tabbas yarinyar nan ta na so ta zautar da shi fa. Ya shiga tunani "ashe ba ita ya gani yanzu ta na meeting da bature da Buzu ba kenan?:
"Yaya Bilal yaya jikinka? Allah Ya sa kaffara?" In ji Nihal a lokacin da ta katse masa tunanin da ya tsunduma.
"da sauki." Ya amsa a fusace gami da kawar da kai gefe da alama baya son ganinta."
Da Najaatu ta ga haka sai ta shafawa kanta ruwa, ba ta ma yi magana ba dan ta san ba zai amsa ba.
Cikin fara'a Nihal ta dubi Bash ta ce " mu zamu shiga gari wataqila mu shiga cikin wannan qaton wajen cin abincin nan mai tsada na masu kudi, mu sake yin irin na jiya mu ci ko da ba mu da kudin biya Allah Zai fitar da mu, mun ji dadin abincinsu. Ko qawata Najaatu?"
Najaatu ta gyada kai ta ce " kwarai kuwa."
Su ka juya suka tafi ba tare da sun jira amsa ba. Bash da Bilal suka bi su da kallo har suka qure.
Zazzafan tunani ya kece a cikin zuqatan Bilal da Bash sai Bash ya lalubo kujera a kusa da Bilal ya zauna suka ci gaba da kallon masu wanka a cikin swimming pool.
Billal yayi a ajiyar zuciya ya ce "ban yarda da Nihal ba, ina zargin fusks biyu ce. Yanzu na ga wannan yarinyar mai kama da ita din nan, ta zauna a wadancan kujerun sun yi meeting da baturen nan da muke ganinsu tare har da daya daga cikin buzayen cikin fim din Abbas. Na gane kayan dan na gansu a hotuna tun kafin mu zo Abbas ya nuna min su. Ta bude laptop ta yi rubutu sosai, da ta shiga ciki sai ta fito sanye da tsohuwar abaya. Anya ba ita ce ba kuwa, take yi mana wasa da hankali ba kuwa?"
Bash ya bude baki yana kallonsa ya kasa magana dan kansa a kulle yake.
Can ya yi ajiyar zuciya ya ce " ai ta bani amsa a cikin wani sin da muka yi tare da ita dazu. Na ce ta fada da bakinta ita wacece? sai ta ce ita attajira ce mai ilimi, 'yar gata, 'yar sarauta, ta shigo duniyarmu ne dan ta gane masu qaunarta na gaske da maqiyanta na gaskiya."
Bilal ya zabura har sai da ya fama ciwonsa.
Bash ya riqe shi ya ce "ka da ka tashi tsaye zaka gurde."
Bilal ya ce " kada fa a ce Princess last born ce da gaske? Amma ba ka ganin maganarta tana cikin abinda Darakta ya ce ta fada ne?"
Bash ya ce " kwarai yana ciki amma ba yadda aka ce ta fada ba ne. Ni dai kaina a daure yake ina mamakinta fa."
"Tukunna ma wanne fim ka ke magana, an fara shooting din Gimbiya Rima ne na Abbas?"
Bash ya fada cike da gadara " kwarai kuwa mai zai hana an fara. Nihal ce a matsayin Halima Jabir ta sake karbar ragamarta. Kai in takaice maka ma fim ya canja suna ya tashi daga Gimniya Rima ya koma Gimbiya Nihal."
Tashin hankali ya kai qololuwa a cikin zuciyar Bilal, sai ya kasa magana.
Aisa da Halima ne suka qaraso, Halima tana ta dingishi su ka sami kujeru suka zauna.
Bash ya yi zubur ya miqe kamar an muntsine shi, ya ce " zan shiga gari zan ga abokaina."
Ya yi gaba ba tare da ya jira amsarsu ba.
Bilal ya dago da jajayen idanuwansa ya dubi Aisa cikin fushi ya ce " yau me ya faru a wajen shooting? Labarin da Bash ya bani gaske ne ko dan ya bani haushi ne ya fada?"
Aisa ta tabe baki ta ce " bana so in fada muku ne dan kada ranku ya baci, shiyasa ban yi niyyar fada muku ba amma yau kam an yi wani abu wai shi rufa ido. Idanuwan Abbas ya rufe baya ganin kowa sai Nihal, ba ya jin maganar kowa sai ta Nihal da wadannan qazama 'yan korarta."
Halima ta zabura ta ce " kina nufin su Nihal ne suka maye gurbinmu?"
" sunan fim din ma ya koma sunanta qarewa ma."
Sai Halima da Bilal su ka ji hankalinsu ya tashi. Tabbas sun san laifinsu ne, su su ka bawa maqiayar su qofa ta shige.
Aisa ta ci gaba da basu labarin wanda tamkar tana caka musu wuqa a zuciya ne.
Ta ce " babu labarin da yake trending a social media sai labarin Nihal, ta daukaka kowa ya santa yanzu kuma mu da hannunmu muka tallata ta. Abinda nake gudu kenan, na san idan Nihal ta falle ta shigo aka santa zamu zama 'yan kallo. Dan wayoyinku sun kwankwatse ne ai da kun shiga kun gani, na san ana ta nemanku a waya zaa fada muku wannan labari."
Cikin dare bacci ya gagari idanuwan su Bilal, sai juyi kowannensu yake yi saboda hassada da fargaba da nemo mafita yadda zasu dakushe Nihal, har gari ya waye.
Abbas ya samo motar da zaa kai su Kano domin ta su ta kwankwatse, wannan kyakkyawar motar da Nihal ta yi ta santi sabuwa fil ita ce ta ragargaje. Allah kenan me yadda Ya so. Sun sha mamaki da su ka ga Nijal da Najaatu sun fito su ma daga cikin hotel, ashe anan suma suka sauka. Wato an daga darajarsu Nihal kenan kafada da kafada suke yi da su. Nihal ta gaishe su ta yi musu sannu babu wanda ya amsa ma ta.
Abbas ya ce "yauwa Nihal ku jira ni in sallame su zaa mayar da su Kano ne sai mu tafi da ku a motata."
Fuskokinsu Nihal ta kalla tabbas ta san zaa rina wai an saci zanin mahaukaciya tanar sallah, lallai tana shan harara.
Ta yi murmushi ta ce "gaskiya ne, su na buqatar su je gida su huta."
Maganar nan data yi tabbas harshen damo ce, baqar magana ta fada a takaice amma Bilal ya sha alwashin zai gyara mata zama nan gaba. Kamar wasu awaki haka aka ciccibi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login