Showing 66001 words to 69000 words out of 74305 words
Chapter 23 - MUJARRABI BOOK ONE BY SAYYADA BARRISTER.txt
auren suka zo idan suka ji wannan labarin basan dole ransu ya ɓaci suga kamar anɓata musu time ne. Ɗazu mu kayi waya da Ammie take sanar dani cewa ƴan rakiya suna jirana kuma ta gama haɗa min kayayyakina na tafiya sannan kuma yaushe ne zamu tafin na ce da ita gobe ba tare da nayi tunanin komai ba yanzu kuma na rasa mafita shine na kira muyi shawara ya zanyi da gobe da na ce da ita nasan zuwa goben dole ne su kaimin kayana inda zan zauna, shine nayi nazari na ce ko kaje ka sanar dasu cewa anan garin Maiduguri zan zauna zuwa wani lokaci sai na koma Abuja, sbd Alhaji Sama'ila ne ya sauya tunani yace na zai kamamin gida. In yaso gobe sai ka biyo tanan ka sanar dani yadda ku kayi sai kasa a bincika min flat house sai akaimin kayana cen a jera min su kaga daga nan sai mu zauna mu tsara muga yadda abin zayyu sai na sanar dasu halin da nake ciki.
Ta sauke numfashi bayan ta kora masa dogon jawabin tana kallon yadda yake karɓan shawarar. Sauke numfashi yayi yayi shiru yana nazarin maganganun ta a hankali ya sauke ajiyar zuciya ya ce
"To naji Hamrah amma why not mu sanar da Daddy komai in yaso sai bayan an watse sai a zauna a tattauna kan batun kinga komai zaizo da sauki"
A'a Ammar in muka sanar dashi yanzu zai shiga tashin hankali sosai kuma kasan Daddy ba zai ɓoye bacin ranba sai kowa ya sani, kawai kayi yadda nace in shaa Allahu zamu sami mafita.
"To ba komai a daren yau ɗin nan zan saka a nemo min dillali zuwa gobe komai zai yi kamar yadda ki keso, shikenan hakan yayi miki"
Kai ta gyaɗa ganin lokacin ya tafi kusan 10:00pm yasa ta ce ya tafi da ƙyar Ammar ya tafi, ta sanyawa ɗakin key ta dawo ta kwanta tana ta tunanin ko ya su Daddy zasu ɗauki wannan lamarin har bacci ya ɗauketa.
_WASHEGARI_
A hankali ta buɗe idanuwanta da sukayi mata nawi da zafi sbd kukan da tasha, bin ɗakin da kallo tayi tasa hannu ta janyo wayarta ganin lokacin sallah asubah tayi yasa ta sauko da ƙyar ta iya kai kanta toilet jiri ne ke neman ɗibanta sbd yunwa da damuwar da take ciki ta ɗaura alwala ta fito ta idar da sallah anan kan dardumar sallah ta kwanta bacci ya sake yin awun gaba da ita.....
Cikin bacci taji alamun ana tashinta jim kaɗan tayi ta buɗe idanuwan ta ganin Ammar sugunne kanta duk ya tashi hankalin sa yasa ta tashi ta zauna tare da sauke numfashi ta ce
Ammar yaushe ka shigo?.
Ajiyar zuciya yayi da karfi ganin ta buɗe idanuwanta ya ce
"Kin matukar bani tsoro, tun ina gida nake ta kiran number ki amma baki ɗaukawa har na iso bayan nazo ne na tadda kofar a kulle nayi tunanin wani abu ne ya sameki shine na koma na sanar da ma'aikatan wajen suka zo suka buɗe ganin ki anan nayi tunanin baki numfashi wallahi na tsorata"
Ta sauke numfashi, a hankali ta ce
Bacci ne ya ɗibeni. Ya ku kayi?.
A hankali ya janyo ledar dake kusa dashi ya ajiye gabanta tare da wani cup mai murfi ya buɗe haɗaɗɗen tea ne mai kauri ya ajiye gabanta tare da buɗe ledar ya ajiye mata gashashiyar kaza ce da kuma cheaps sai egg souce ya ce
"Ki ci sai na faɗa miki yadda mu kayi"
Kai t girgiza masa tana jin yunwa amma bata sha'awar komi, ganin bata da niyyar ci yasa ya sake cewa
"To shikenan zanje na sanar dasu Daddy gaskiyar lamarin indai zaki hukunta kanki da yunwa"
Tasan sarai zai aikata, kuma in bata ci ba zai tayi mata rigima yasa ta sanya hannu tana ci kaɗan kaɗan ci take yi amma bata jin ɗanɗanon komai ɗaci ma take ji cikin makokaronta da ƙyar take iya haɗiye ya zuba mata idanu kamar wata karamar yarinya sai da ta ci mai ɗan yawa sannan ya sauke numfashi, ya ce
"Jiya ina shiga gida na tadda Daddy a farfajiyan gida, na sanar dashi abin da ki kace na faɗa ya ce bakomai zai sanar da Ammie to kinsan gidan da jama'a har na fito bamu haɗu da Ammie ba amma na haɗu da Daddy ya ce inji Ammie in an samu a sanar dasu, shine na biya ta wajen abokaina nayi ta cigiyar gida sun haɗani da wani dillali yanzu dai mun gama a cen new GRA mun sami gidan kuma ya haɗu sai dai yayi kuɗi kuma bansan iya kwanakin da zaki zauna aciki ba shine na ce bari na zo muyi shawara"
Alhamdulillah.
Shine abin da ta furta taji sanyi cikin ranta shikenan komai zaizo cikin sauki ta ce
Thank you Ammar Allah ya baka mace ta gari ka gama min komai. Tunda ka ce gidan na da kyau ba sai an tsaya jayayya ba ko nawa ne zan bada amma nasan baza su karɓa kuɗin kwanaki ko sati ba sai watanni zan kama na 1yrs a faɗi kenan in komai ya daidaita a wannan watan ma falillahil hamdu sai na koma gida kai kuma ka zauna acen na wani lokaci sai mu sake ko ya ka gani.
Murmushi kawai tayi yabi ra'ayinta ne kawai dan yaga tana cikin damuwa kuma baya so ta tashi hankalinta ne amma bayan an watse zai sanar da iyayensu sbd a samu mafita. Ciro wayarsa yayi ya kira wannan mutumin bugu ɗaya ya ɗauka ya sanar mashi cewa za a bada kuɗin nan suka gama su kayi sallama. Ya dawo da kallon shi kanta ya ce
"Sai kuma menene ya rage yanzu?"
Ta sauke numfashi ta ce
"Let me inform Ammie about the house, sai zuwa yamma in yaso akai kayan"
Yana kallon cikin tausayawa wai yaushe Hamrah zata sami farin cikin ne kullum cikin damuwa, kuka, tashin hankali. Ɗauko wayar tayi ta kira Ammie ta ɗauka tare da gaidata
Ina kwana Ammie.
"Lafiya Hamrah, yauwa naji komai daga bakin Daddynku ya sanar dani, kuma hakan ma yafi duk ƴan'uwanki na nesa suga ɗakinki su sanya miki albarka"
Uhm. Ammie an sami gidan ma cewa ma yayi za'a tura motar da zata kwashi kayan sai aje gidan a jira.
"Ah to madalla babu damuwa mu ai mun haɗa komai a shirye yake sai sunzo kawai"
To.
Ka katse wayar ta fashe da kuka, da ƙyar Ammar ya rarrasheta tayi shuru ta ce dashi
Ina zamu sami motar da zaikai kaya da kuma mutane anjima da wanda zai kaini.
Kamar yayi kuka ya ce
"Barmin komai a hannuna"
Ammar ya fice ya bar Hamrah zaune jigum kamar wacce akayiwa mutuwa ko da shike babu maraba da mutuwar hawaye ke fitowa babu kuka ita dai ganin abin take tamkar a mafarki. Ta ɗau waya ta kira Shatu bugu ɗaya ta ɗauka cikin zolaya ta ce
"Amarya ran gida, amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida"
Haɗiye damuwarta tayi ta ce
Shatu ya gajiyanki naso kiranki tun jiya amma ban samu damar kiran ba, yauwa ki je gidanmu ki tadda Ayshe da Zeenat za a kai kayana a jera kin san mun sauya shawara zan zauna anan zuwa wasu watanni sai na koma Abuja da zama.
"Kai ƙawata nayi matukar farin ciki dajin wannan batu daman ina ta jimamin tafiyanki tun jiya kamar mara lafiya nake, aiko yanzu zan shirya na tafi cen gidanku"
Uhm nagode bestie.
"Ba komai"
Su kayi sallama. Ta kira Ayshe da Zeenat suke ta shawara da juna har Ammar ya samu babbar motar da ta kwashe kayan Hamrah aka kai wunin ranar kam a cen akayi duk an jikkata, sun shirya mata gida. Shatu da Ayshe suka kawo mata kayan da zata saka har cikin hotel ɗin suna ta sokanar ta wai tayi kyau a kwana biyu ita dai dariyar yake kawai take yi har Ammar ya hayo mutanen da zasu zo a matsayin abokan Alhaji Sama'ila suka ɗauki Hamrah bayan tayiwa manager hotel ɗin godiya ba tare da Shatu da Ayshe sun fahimci komai ba. Sai da aka biya ta gidansu aka kwashi ƴan rakiya sannan aka wuce gidan amarya, a lokacin da suka iso kofar gidan su kamar ta ruga da gudu ta shiga haka take ji tayi ta kuka har suka iso gidanta.
_________________________
Abin da ya samu kenan a yau, ina fita aiki shiyasa bana samun isasshen lokacin yin typing kun san sha'anin aiki ga kuma hidimar gida. Amma in shaa Allahu a weekend zanyi readmore fiye da haka.
Godiya gareki A'isha Allah ya bar ƙauna 🥰
Comments and share
*MUJARRABI*
By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA
09021706569
PG 47 & 48
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
__________ Da isowarsu unguwar new GRA suka yi parking a gaban katafaren gida mai ɗauke da babban gate milk color, sun ɗan yi jim kaɗan da yin parking ɗin aka buɗe gate ɗin, wani dattijo ne ya buɗe musu ganin haka dukkanin su suka dunguma cikin gidan a farfajiyar gidan su kayi parking aka fara fitowa. Tun daga farfajiyar gidan suke yaba gidan har suka shige ciki a nan babban palourn duka yada zango. Hamrah dake zaune cikin motar ta rabka uban tagumi ta zubawa sarautar Allah ido dan ta miƙa masa dukkanin al'amuranta, duk sai tayi sanyi ganin abin take tamkar a mafarki sai al'ajabin abin dake faruwa da ita take yi ace yau ake rakiyarta ɗakin aurenta amma babu miji, bata taɓa kawo irin wannan ranar zata risketa ba. Ganin yanda ƴan'uwanta ke farin cikin rakota da suke yi ne ma yasa ta ɗan ji sanyi cikin ranta ko ba komai ta faranta musu, musamman ma Ammie. Tana cikin wannan tunanin ne taji muryar babarsu dake zaune a gefenta ta ce da ita
"To mun iso menene kuma abin kin fitowa"
A hankali ta sauke numfashi dan ita tayi nesa cikin tunanin zuci bata ma san anayi mata magana ba, ganin an buɗe ƙofar motar da suke cikin ne babarta da kuma Innarta sun fice yasa ta saka kafa ta fito, suna rike da ita har cikin palour nan ko sai guɗa ake ita dai tayi shuru bata ce komai ba, har aka shigar da ita ɗakinta. Kaya kam Masha Allah Daddy yayi mata dan kaf gidansu ta fiso kyaun kaya tun daga na palour, ɗaki zuwa kitchen ba abin da aka saya da farashi mai sauki duk kayan masu sadane. A bakin bed ta zauna tana jin yadda suke yaba gidan suna ta sanyawa Alhaji Sama'ila albarka suna ta musu fatan alkhairi har lokacin tafiyarsu yayi. Nan ko Hamrah sabon kuka ita tama rasa na menene na tafiyarsu ne ko na bakin cikin da take ciki ne da ƙyar Ayshe da Shatu suka yi ta rarrashin ta tayi shuru har suka fice. Ta rabka tagumi a karo na biyu, oh yanzu kuma ko wacce iriyar rayuwa za tayi ita kaɗai a wannan kata faren gidan dan tasan kan ta sanar dasu Daddy sai an dau tsawon wasu watanni dan zuwa wancan lokacin babu sun mance komai hankalin su ya kwanta sai ta sanar dasu.
Ta miƙe tsaye tare da yaye gyallen dake jikinta tana bin ɗakin da kallo ganin set na ɗakinta wanda yaji uban kuɗi da kuma kyau sbd ba a Nigeria Daddy ya siya ba order sa akayi a lokacin da za a shigo masa da kayayyakin business na sa. Sauke numfashi tayi gashi anyi mata hidima kuma ace suji wannan mummunar labarin ai dole hankalinsu ya tashi, ta fito ta wuce palour nan ma haka ya matukar haɗuwa da kuma tsaruwa musamman Dining area ya matukar kayatu, ga standard fridge nata haɗaɗɗe da kuma babban plasma. Hawaye ne take ya wanke mata fuskar sai a lokacin taji wani irin kuka ya taho mata nan take ta zube a wajen ta saki kukan tana jujjuya kanta tana kuma tausayawa rayuwarta shikenan ta rabu da farin ciki na har abada kuma ta ɗaukarwa kanta alkawarin babu ita babu aure har aba kawai za tayi ta bautawa Ubangiji in ta kama ma ta zauna a wannan gidan ta karashi rayuwarta.....
Jin an taɓata ne yasa ta ɗago a hankali tana sauke idanuwanta kan Ammar dake zaune kusa da ita ya dafata yana girgiza mata kansa alamun ta daina kuka sai dai kuma ina shi kansa ya kasa jurewa nan hawaye suka zubo masa, ji yake da yana da halin ɗaukewa Hamrah damuwar da take ciki da ko ya ɗauke mata ya dawo kansa. Hamrah ganin Ammar na ƙwalla yasa ta tsagaita nata kukan tare da share hawayenta cikin sanyin murya ta ce
You have to go back Ammar, dare ya soma yi babu daɗi kana waje kuma...
Hannun sa yasa ya riƙe nata da ƙyar ya buɗe baki yayi magana dan zuciyarsa nayi masa tsuya da raɗaɗi ga kuma tausayinta da yake ji a hankali ya ce
"Do you think, i can go and leave you hear?. No, I can't"
Uhm Ammar, ni ce ya zame mun dole na zauna ana cos i don't have a choice amma kai ba zayyu ka bar gida ba, kuma nasan Daddy zai nemeka.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da miƙewa ya ɗauko ledar da ya shigo da ita wacce bata ma san da ita ba ya ajiye gabanta shima ya zauna kamar yadda take zaune bisa ƙafafuwanta ya ce
"Kin manta lokacin da muke yara in zaki kwana bikin kawarki in Daddy ya hanaki Ammie kuma ta barki sai mu haɗa plan sai Daddy ya shigo na taimaka miki ta saman garu ki fice a tunanin Daddy kina gida to irinsa nayi yau ma. Ya shigo mun gaisa mu kayiwa juna sai da safe shine na biyo ta baya na hawo garu na wuce nayi miki siyayya dan nasan tun abin da ki ka saka a baki tun safe baki ci komai ba"
Murmushi tayi duk da yanayin da take ciki sai taji zuciyarta tayi mata sanyi, tuno mata da rayuwar kuruciyarta da Ammar yayi ne yasa tayi murmushi. Ganin tayi murmushi yasa ya buɗe ledar ya fiddo da roasted fish and chicken with souce ya matso dashi kusa da ita ya buɗe mata fresh milk mai sanyi ya ce
"To kici abinci ba a fushi da abinci"
Uhm Ammar i don't feel to eat anything at all this time....
"Ki daure ki ce kin cin da ki keyi shine ki ke jin kamar baki da lafiya shi wanda ya jefaki cikin wannan halin fah yana cen yana wantayawarsa ko a jikinsa to ke meyasa zaki tashi hankalinki, ki daure ki"
A hankali take yanka tana ci kamar ta amayar take ji amma ta daure gaskiya ne bai kamata ta na fushi da ƙaddararta ba, duk da akwai ciwo amma ya zama dole ta yarda da ƙaddarar da ta sameta. Ba laifi ta ɗan sha fresh milk ta koma da baya ta jingine jinjina kujera tana sauke numfashi...
"Ga magungunan ki nan ki sha sai ki kwanta"
Da mamaki ta kallesa ita ta ma manta tana kan magangana an ɗaurata akan su shiyasa ma ta mance bata dauka ba to amma yaushe Ammar ya ɗauko bata sani ba. Ba tare da ta ce komai ba ta buɗe su ta haɗiye ya mika mata wani sachet ɗin ya ce tasha ba tare da tasan na menene ba ta karɓa ta haɗiye sa, nan da nan ta fara jin bacci ta miƙe ta shige ciki sabar baccin yayi nawi da kayan jikinta ta faɗa kan bed nan take ta bacci yayi awun gaba da ita.
_WASHEGARI_
Buɗe idanuwanta tayi ta ƙurawa roba slink, ganin haske ya gauraye ɗakin yasa tayi mamaki wane irin bacci ne tayi har gari yayi haske bata farka ba, a hankali ta sauke ajiyar zuciya, ta tashi ta zauna tare da karanta addu'ar tashi daga bacci. Tayi miƙa ta sauko daga kan bed ta shige toilet ta haɗa ruwan ɗumi ta watsa sannan ta fito ta shirya cikin doguwar riga ta atamfa ta shimfiɗa dardumar sallah ta gabatar da sallah asubah duk da ta makara amma ta jima tana ta addu'oin. Jin ana nocking kuma tasan Ammar ne sbd babu kowa cikin gidan bayan ita sai shi yasa ta miƙe ta buɗe. Murmushi ya sakar mata ya ce
"The breakfast is ready"
Sauke numfashi tayi tare da cewa
Uhm sai zuwa anjima zanci kaci naka.
"Kin manta ne kina kan shan magunguna kuma ba zaiyu ki shasu ba tare da kinci abinci ba, kuma ai ya kamata kimin kara ko dan tashi da wuri da nayi na haɗa miki delicious"
Fitowa tayi ta wuce Dining area tare da cewa
To muje na gani.
Ya bi bayanta, ya matukar sharya Dining table ɗin ya matukar burgeta harda wasu flower's da light a jiki suna kawowa su kuma ɗauke tayi murmushi Allah sarki Ammar a dole yana son ta mance komai. Ta iso ta zauna shima ya iso a nutse ya soma buɗe rufaffun plate ɗin da ya jerosu kan Dining ɗin yana nuna mata, murmushi tayi a kan ko wanne plate yayi decorating da abincin wani aresh ne wani kuma fried yam sai kuma ma ɗauke da souce na hanta. Abu dai kala daban daban kuma ba masu yawa ba, ko wanne ya ɗiba ya zuba mata kan plate dake gabanta ya haɗa mata hot tea mai kauri ya bata sannan ya zuba ma kanta. Ta ɗan dauko spoun tana ci kaɗan kaɗan ba laifi ta ɗan ci ya bata magungunan ta ma tasha sai kuma bacci a nan palour kan kujera ta kwanta tayi bacci ganin haka ya fice ya koma gida. Kusan wunin ranar tayi tane a kwance sbd bacci da ta dinga yi babu tantama Ammar maganin bacci ya bata tasha. Bayan ta idar da sallah la'asar ne taji tsayuwar motar ta leka Ammar ne da wani mutum a tsaye ta fito sbd ganin da sabuwar motar ta wacce Alhaji Sama'ila ya siya mata shi ya taho. Tana nan tsaye ya sallami mutumin ya iso inda take ya ce
"Ga mukullin motar ki Daddy ya ce na taho muki dashi yana kuma gaidaku"
Uhm Ammar, na bar maka motar in ma saida ita za kayi kaje kayi ni bana sonta.
Murmushi yayi ganin ta juya ta shige ciki ba tare da ta karɓi kin motar ba, yabi bayanta, ya taddata zaune kan 1sitter shima ya zauna daga gefe ya ce
"Babbar yaya fushi ba naki bane sbd duk wannan abin tafe yake