Showing 198001 words to 201000 words out of 235479 words

Chapter 67 - Gidanmu Book Complete Document hausa Novels by Janafty .txt

18 Jan 2025

18208

dai Tana Gidan Amarya sai an juma Zata dawo.
Su suka Hadu suka kara gyara Gidan suka Share suka Turare gidan Turaran Wuta masu kamshi da Sanyaya rai Wanda Maman Nasara tazo ma da Inteesar da yawa kala kala bayan na Jiki harda na Daki dana Turara gida..
Sai gabda mangariba suka yi Shirin Tafiya Fareesatu sun fasa Tafiya suma sai Gobe Mazajen nasu suka zo Daukansu zuwa Gidan Abba abar Amarya Ta Huta kafin Ango ya Shigo.
Inteesar da Farko bata Damu ba sai da Taga Tafiyar zasu yi da gaske kana ta Fara Kuka Tana Rike Munari Duk Dauriyan Munari Sai da tayi kukan Sabo hawaye shabe shabe aka Bambare su Daga Jikin juna aka yo Waje da Munari Hafsah ma da Tasleem da Nasara sai kuka, Harda Umaima itama Haka suka Shiga Mota suna Sharan Hawaye Inteesar kuma Ta Kudundune kan Gadonta Tana ta kuka kukan da kowacce mace take yinsa Ranar da aka Kaita Gidan Mijinta Za"a Tafi a barta.
Gashi kuma suna da Jarabawa Allah yasa Munari ta Dauko mata Wasu Li ttafai da Zata Bukata Ba mganar Amarci mganace ta Karatu kawai ba kama Hannun yaro,Sagir ma yazo Daukan su Hafsah aMotan Imran din Tunda ya iya Tuki Imran ya koya masa,Dukkansu agidan Abba sukayi Sallar mangariba aka Zauna anata Labarin Biki da maida yadda abubuwa suka Kasance Imran na Cikin Dakinsa ya kasa Tabuka komai Kewa yake jin kewa zai yi nesa da Abba da Ya Yusuf da Gidansu Daya Saba Dashi Fiye da ko"ina zai Tafi yau ya Kwana ainda bazai ji Motsin Abba ba Rauninsa yaso ya Tabasa Raunin Tuna Anni a wajensa Yau yayi aure zai Tare a Gidansa ammh Anni bata Wannan Duniya yana Tuna kalamanta Imran Duk Ranar da kayi aure ni da kaina Zan Rakaka Dakin Matarka ba Kai ne Zan bama Hakurin Zama da ita ba kai zan bata amanarka na kumace Tayi Hakuri Domin ba karamar Jaruma bace Macen da ta yadda ta aureka..
Alokacin Tabe baki kadai yake yi baya Mgana ammh yau sai da Zafafan Hawaye suka Zubomai acikin Kwarmin Idanuwansa ya Hade kansa da Gwiwa yana ta kuka kukan mai Cinrai da kewa da kaunar Uwa acikin Ransa.
Abba ne yake ta Cigiyansa kan abar Inteesar ita kadai achan Gida Sagir aka Kira kosuna Tare yace shima Nemansa yake yana ta Kiransa bai Dauka ba Yusuf ne yasan ba inda Za"a Gansa sai Cikin Dakinsa Halin Daya Samesa ne yasa ya Kira Abba Shi kanshi Abba sai da ya Fitar da kwallah Shima yayi kuka a irin wannan Ranar Allah ya jikan Zuwaira da Sauran ya"yanta Allah yasa suna Cikin Aljannah
Haka Abba ya Rungume Zaratan ya"yan nashi yana Sharan kwallah yana Lallashinsu sun yi ma yan"uwansu da Mahaifiyarsu addu"an Dacewa da Fatan Allah ya jikansu da Rahma.
Yusuf shi ya Hadama Imran Kayansa da Zai Bukata Tunda bai Dauki Hutu ba Mr Tunde da Mr Sulaiman sun yi Dashi ya Dauki Hutu yace bazai Dauka ba Duka Duka yaushe ya Fara aikin Da wannan kuma don wannan Dole suka kyalesa Har Khalil ma yamai mgana shima wannan Hujjar ya kawomai kuma shima ya yarda yace ya bari sai nan gaba sai ya Dauka sai susha Honey moon Cikin Natsuwa Lokacin itama Intee ta gama Jarabawarta ba Streess na makaranta.
Duk yadda Imran yaso kada Rauninsa ya bayyana kasawa yayi yau Rana ta Farko da kowa yaga yana kuka Ya Rumgume Abba kamar Wata Mace ba wanda bai Tsausayamai ba Abba ya Buga Kafadarsa yana Fadin"Ka Daina kuka..Jarumai kamar ka da Juriya aka sansu ba kuka ba..Kaje Ga.Matarka Allah yayi maka albarka ka Riketa Amana Kanwa take gareka Ta Kowani bangare ta Chanchanci Kulawarka..Sannan Rokona na Karshe ka Rage Zafin Rai don Allah Imran kuma ina Rokon Allah yasa wannan auran ne Sanadiyar Dukkan Wasu alherai Allah ya Zaunar daku Lafiya!
Gabadaya aka amsa da Ameen Ameen Sagir ne zai Tukasa zuwa Gidan bayan an gama Saka kayan nashi a Mota ya Shiga Gidan Gaba Sagir yayi Riverse ya Fice Daga gidan su Abba na Dagamai Hannu Yusuf bai san yana Kwallah ba sai da yaji Abba ya Saka Hannu ya Sharemai ko da Imu ya kasance bamai Hayaniya da shiga Mutane ba Akwai Shakuwa Tsakaninsu Sosai Kuma shi Sabo ai ake yima kuka Su Sa"id suna ta bama Yusuf baki suna Fadin suma fa Tare koda yaushe suka so zasu ga juna ba"a Rabu ba Har Abada.
Shi kanshi Sagir Jikinsa ya Mutu da yanayin Imran din kuma shima wannan kewar na Damunsa Bai fi Shekara uku Dayasan Imran ba Ammh Sun yi Sharing din kauna da Shakuwa a Tsakaninsu suyi Fada su Shirya ammh kuma basa iya Rabuwa da juna Ammh yau aure yakai Imran wani Mtsyin da zai bar anguwan Gabadaya sai dai Waya ko kuma in ya Lekosu shima Tuni jikinsa yayi sanyi Har suka kai Gidan ba wanda yayi ma Dan"uwansa mgana..
Gidan bamai gadi Imran ya Sauka ya Bude Get din Sagir ya Shigo Ciki Shi ya Tayasa suka Kwashe kayan zuwa Cikin Gidan Har Cikin Dayan Bedroom din da zai zama mallakin na Imran ne.
Sagir ya zauna Saman Daya Daga Cikin kujeran Falon yana Fadin"Ango ba Kazan Amarci haka zaka shigarma Amaryan taka Hannun Rabbana..!
Imran na Tsaye yana kallon Wani Barayin ya Karkace kai Idanuwansa sun kala yace"Uhm..!
Daga haka bai kara cewa komai ba Sagir ma sai bai kara cewa komai ba yana Bin Falon da kallo yace"Baffa Kabiru yayi Kokari..Allah ya Biyasa..!
Imran na Jinsa bai ce komai ba Tunaninsa ya Tafi yadda Rayuwa Zata Juyamai na Rayuwa shi da Inteesar a Inuwa Daya a mtsayin mata da Miji.
Anya zai iya Daukan wannan Nauyin..?shifa ba Daya yake da kowa ba Kansa ma bai Damu dashi ba ballatana Nauyin wata..?wata zuciyar tace mai ai ita Zatta kula Dakai kaima ai Zaka kula da ita Tunda itace kadai Zuciyarka bata manta da ita ba..!
Yana Cikin wannan Tunanin Sagir yace"kamar Tashin kuka fa nake ji aciki..?ko Inteesar ne bata Daina kukan Rabuwa dasu Munarin ba..?
Sai alokacin Imran yaji dan Tashin kuka Kofar Bedroom din Dayake Kyautata Zaton tana ciki ya sakama Ido Itama Tana kuka ne..?
Shi tasan meya sa yake kuka..?saboda yau zai kwana inda ba Yusuf ba Abba ba Munari wadanan sune Ahalinsa da baida Kamarsu duk Duniya ko"ina Yaje ya dawo Su din kamar wasu Garkuwa ne a garesa yana kukan yau ya bar Gidansu Wata Rayuwa ta kawosa Wata gabar da bai Taba Hasashe ba ko Fatanta nan kusa ba bai Taba ji aransa zai iya aure nan kusa ba sai gashi shigowar Inteesar Rayuwarsa ta sauya komai.
Sagir ne ya Katsesa Yana Fadin"Bari na Tafi..Tunda naga anko kuka kai da Amaryan taka kai kuka ita kuka..Kawai ka shiga Ciki ne ku Hada kai kuyi ta Rafzan kuka sai gobe da asuba sai ku Dakata..!
Yafada Lokaci Daya yana Mikewa Tsaye Imran ya Murmusa Lokaci Daya ya saka Kafa ya Daki Kafar Sagir yayi Gaba da Sauri yana Fadin"Bakomai na yafe Maka duk cikin Nishadin Ango ne..!
Yafada yana jin wani kewa na kamaaa sa bayaso ya waigo Hawayen Dayake ta Rikewa ya bayyana Imran ya Taka ya Bisa yana Fadin"bazaka Tsaya mu yi Sallama ba..!?
Sagir na Ficewa yana Fadin"Wani Sallama.?bayan wacce mukayi..Sai da Safe a gaida Amarya sai an kwana Biyu indawo cin Girkinta ka Fadamata tayi Hakuri haka auran yake kaima Allah ya baka Hakuri Imran Allah ya baku Zaman lafiya..!
Yafada Lokaci Daya yana Dauke Hawayen da suka Cikomai ido
Imran ya Tsaya Cak yana kallonsa juyowa yayi yana Mikamai key din Motarsa yana Fadin"Sai da safe..!
Imran ya saka Hannu ya karba yana Fadin"Zaka Samu abun hawa kuwa..?
Sagir ya Gyada kai yana Fadin"Insha Allahu..!
Imran yayi gaba yana Fadin"Muje na Taka maka!
Yafada yana Tusa Key din Motar Cikin Aljihun yadin Boyel din da Sagir yayi musu wanda suka sanya yau din Yana jin Wani abu Daga Karkashin Ransa
Sagir yabiyosa suka jera kowa na Sauke Ajiyar rai Imran acikin Ransa yana Fadin Waye Sagir a wajena..?
Sagir Dan"uwa ne kuma Abokina aminina wanda bani da kamarsa acikin Wannan Duniyan ya Zauna Dani Da Dadi ba Dadi duk abunda na Zama yau ko na Taka da Gudummuwarsa Abokina Wanda Samun Irinsa sai an Tona Inda Haka abokai suke kamar Sagir da Mutane da Dadama sun ji Dadin abota bazai Kirasa aboki ba ya Zama Bangaran Dan"uwansa da Kokarinsa akaina bazan Taba mantawa ba.
Sagir kuma Tuna Alheran Imran yake a garesa Duk da yana da Murdaddun Halaye ammh shi ya Fi kowa Fahimtarsa yana da kyakyawan Zuciya da Tunani mai kyau mai Kirki ne kuma mai Nagarta ne bai Taba Haduwa da aboki kamarsa ba ya wuce aboki ya wuce amini Shi din Dan"uwane a Wajensa
Suna wannan Sake saken suka isa Bakin Titi Cikin Sa"a Sagir ya samu mai adaidaita sai ya juya ya mikama Imran hannu sukayi musabaha yana Fadin"Ka koma ka bar Min kanwata ita kadai..Kuma Mallam ka Sauke wannan Ego din naka da wani Kukan ka agefe in ka koma ka Lallasheta Ta Daina kuka Haka ango kema kowacce Amarya sannan Tell Her sorry Kazanta Tabini Bashi Khalil gabadaya Nauyin ni ya Doramawa kuma yana kaina Zan Biya bashi..!
Imran kallonsa kawai yake bai ce komai ba sai da ya gama yace"Shirme..!
Yafada yana wani Dakuna Fuska,Sagir ya Daki Kafadarsa yana Fadin"Ko da yake na Tuna..Ranar Lallashin bata zo bane ko Imran..?
Yafada cikin Dariya Shima Imran din Dariya yake suka Rumgume juna Kowa na Dauke Hawayensa Imran ya Dago yana Jinjina Hannun Sagir lokaci Daya yana Fadin"Tanque....Nagode kwarai..Bansan da wani baki Zan gode maka ba..!
Sagir yace"Ni bana Bukatar Godiyarka mallam abu Daya zakamin..?
Imran ya Kallesa yana Fadin'menene shi..?
Sagir yace"Ka so kanwata..Ka bata Kulawa kuma don Allah kada ka bari wannan Girman kan naka ya Bata Wahala..!
Yafada yana Dunguremai kai Dariya suka saka gabadaya yana Fadin"Insha Allahu zan taimaka muku.!
Mai adaidaita ne ya gaji da jira yayi hon kana suka kara Sallama Sagir ya shiga Imram na Dagamai hannu suka Wuce kowa na Dauke kwallarsa.
Jiki ba Laka Imran ya Taka ya dawo Gidan sa yana Kallo da nazarin anguwan da kansa ya Rufe get din Kana ya taka zuwa Cikin gidan ya Kulle Kofar Falom a aransa yana Fadib"Lalle na yarda nabar gida..Imran na kulle gida..?
Sai da ya Murmusa Har zai shiga Dakinsa ya fasa ya Tunkari Dakin Da Inteesar take ya Tura a Hankali sai ta Bude bai Shiga ba kansa ya Leka ya Hangota Tsakiyar gado Cikin mayafi ta Dungule Tana Ta kuka sai ta Bashi Tsausayi sai ya Bude Kofar gabadaya ya Shigo Kafafunsa suna Taka Italian Cafet din Daya malale Bedroom din
Bataji Takun sa ba ballatana Bude Kofarsa,Tadaiji mganar su Shida Sagir a Falo da Farko har Tsorata ma tayi kafin ta gane sune kawai taji Muryansa a saman kanta.
"Kinsan bana son yaawan kuka ko..!?
Haka ya fada yana Tsaye Gaban gadon hannayensa Zube Cikin Aljihun Wandon Kayan Dake jikinsa ya Zuba Mata Idanuwansa yana kallonta da Duk Zuciyarsa.
Dagowa tayi ahankali jajayen Idanuwanta da suka tasa saboda kuka suka Shiga Cikin nasa gabadayansu sai da Zuciyarsu ta amsa Shi yayi Saurin kauda kai yana Fadin"Subahanallah Maryam kuka haka..?
Mamakin yadda ya Kira sunanta taji yasa Hawayenta suka karo ta Runtse ido kafin ta Bude akansa Karisowa yayi gabanta yana Fadin"Look nifa kinga ban iya Lallashi ba..Kuma kowa yace na Kula Dake ban iya da wannan Shagwabar taki Intee kiyima Girman Allah ki Daina kukan nan kin ji ko..?
Kallonsa Take yi Cikin so da kaunarsa Mganarsa tana kara sakata Dariya Sai dai bata Daran ba Idanuwansa ta kallah Taga sun sauya shima kamar yayi kuka yasa tace"Kai ma kayi kuka ne..?
Tafada Tana lamgwabe mai kai Cikin Dabi"arta Daya zame mata jiki
Saurin Kauda kai yayi yana Fadin"Kuka..! Ni ban yi kuka ba..!
Yafada Lokaci Daya yana Dakuna Fuska Mirmishi Tayi tana Hawaye tace"Nasani..Kayi kukan Rabuwa da Abba da ya yusuf da Munari ko..?
Nafada tana kallonsa Shima kallonta yake da Dukkan Zuciyarsa
Kai ya girgizamata yana Fadin"Anni..Anni na Tuna..!
Inteesar taji kaunarsa ya kara kamata da Tsausayinsa Bataasan Sadda tace"Allah ya jikanta da gafara..da Sauran duka musulmai nima ina jin Zafin Dakake ji Ya Imran..!
Nima ina ta kuka da zan Rabu da Umma da Daddy na da Ya basheer..Ina ta kuka..,!
Ta fada Lokaci Daya Tana Fashewa da kuka Imran ya Dafe kai yarasa Mafita ganin Tana ta kuka yasa ya Zauna gefenta batare da Tunanin komai ba ya jata Jikinsa ya Rumgumeta kamkam yana Fadin"Intee plz..Ki bar wannan kukan ni ban iya Lallashi ba..Bansan ta ina zan fara ba..!
Ya Fada Muryansa na karyewa kamar Zai yi kuka shi ya karama Inteesar Rauni Ta kamkamesa shima suka Hade Waje Daya suna Jin Bugun Zyciyar Juna Imran yana Shakan kamshinta yana jinsa kamar yana Wata Duniya kanta yake ta Shafawa alamun Lallashi.
Yana Fadin"kiyi Shuru..!
Dole tayi Shuru Dolenta ta karbi Wannan Lallashin da Imran ya Tattaro Duka Karfin Halinsa yanayi mata Sai daga yaga Tayi shuru kana ya Rabata da Jikinsa yana kallon Fuskarta yace"Kin yi sallah..?
Kai ta girgizamai kafin tace"La"asar kadai nayi..Ban yi mangariba da isha"i ba..!
Tafada Tana kallonsa Shima kallomta yake yi kafin yace"Ni kuma nayi mangariba Tare da su Abba Isha"i ne ban yi ba..bari najr nayi wannka In Dauro alwala kema ki tashi kiyi wanka kiyi alwala kiyi mangariba sai nazo mu yi jam"i muyi Sallar Isha"i Tare ko baki so..?
Inteesar tace"Ina so mana..Ai bamu da kowa anan sai mu kadai ko.?
Mirmishi yayi yana Lakuce mata Hanci bai ce komai ba ya Mike ya Fice ta Bisa da kallon Kauna yana Fita ta Mike Daman Less din Jikinta ya Dameta Tiolet ta Fada daman Tun kafin Fitan su Anty Safiya sukace tayi wanka Kukan data Fara ne ya mantar da ita komai.
Tayo wanka tazo ta Shafa lotion da Turare,kayan barcin ta acikin na Gida ta saka wata riga doguwa mai Taushi Saboda kayan suna cikin akwati kuma bazata iya Bude su ba Allah yasa Munari Duk ta Hado mata kayanta Taji Dadin ganin Harda Littafan Karatunta gobe karfe 8:00am na Safe suke da Jarabawa ga Gajiyan Biki Da Zirga Zirga bata gama Sakinta ba


Ta idar da Sallar mangariban kenan sai ga shi ya shigo Cikin Jallabiya Sabuwa mai Ruwan Madara Ruwa na Diga ajikinsa Mikewa tayi Hijabi ne ajikinta suna kallon junansu kamar wasu masu warkewar makanta.
Ganin Ruwa na Diga Daga wuyansa ne Tace"Ya Imu baka Shafa mai bane..?
Yana yin gaba Wajen Darduman yace"Ni bai Dameni ba..Taho muyi Sallar..!
Yana gaba tana bayansa ya Tada Salla Sai da sukayi isha"in suka idar kana Sukayi Sallar Raka"a Hudu na Godiya ga Allah bayan sun Idar Imran ya Daga Hannu yayi ta addu"a Duka Rabin addu"ansa na Allah ya Jikansu Anni ne har Sai da ya kusa kara saka Inteeesar kuka,Sannan ya Rufe da addu"an zaman lafiya a tsakaninsu.
Sanda suka Shafa addu"an ya juyo yana kallonta Wayarsa yadan Danna yana so yaga Lokaci 10 ta wuce na Dare yana kallonta yace"Kina jin yunwa..?
Kai ta girgirzamai alamun A"a ajiyar rai ya sauke yana fadin"Kinsan me..?ni fa imran na Dabam ne shiyasa ko Irin kazan nan da ake siyoma amare bansani ba Sagir ne ya san irin abubuwanan ni Shirme na Daukesu yace a gayamiki zai kawo miki..!
Kanta na kasa tace"Bakomai..Ni na yafe..!
Imran kallonta kawai yake yi yana jin wani Salama kafin yace"Gobe zaku Fara Jarabawa ko..?
Ta gyadamai kai kafin ya cigaba da Fadin"Nima gobe zani wajen aiki Karfe nawa ne sai na Fara ijiyeki kafin na wuce..!
Tana kallonsa tace"8:00am na Safe ne..!
Kansa ya gyada kafin ya Mike yana Fadin"Is ok..Ki kwanta Kiyi Barci and Don"t Stress ur self kice zaki karatu kin ji ko..?nasan ai baki da wasa Insha Allahu komai zai zo da sauki..!
Gyadamai kai Tayi tana Mikewa Idonta yayi Raurai ita kadai Zata kwana.!?
Bata samu bakin mgana ba Har ya Fice Lokaci Daya yana Fadin"Kiyi addu"a...!
Daga haka ya jawomata Kofar ya Nufi Dakinsa yana Sauke Numfashi.
Shifa bai iya kwana da Mutum a Daki ba Ko Namji ne ballatana Mace baisan ta ina zai fara ba..!
Bama haka ba ai in taga yanayin kwanciyarsa sai ta Rainasa.
Inteesar kuwa haka ta kwanta a Darare tana jin Tsoro ba batajin Motsin kowa ko agida Watarana Ita da Umma Take kwana,yau dai taji kewa sosai haka ta Dungule ita kadai Tana Jin Tsoro gata a sabon Wajen da bata Saba ba ita kadai Saboda gajiyan Biki Da suka sha yasa Barci ya kwasheta bata sani ba barci mai nauyi kamar yadda ya sace Imran yana Tsaka da Duba wani aikin da zai bama Manager Mr Sulaiman gobe.














*Shakira..*
3/28/22, 18:35 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�25*


*Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488*


Barci ne suka yi na gajiya Wanda yasa suka makara basu sani ba Kuma Dayake Kusa da gidan ba Masallaci Sai Dagachan nesa ne,Shiyasa har akayi Sallar asuba aka idar Imran bai ji ballatana Inteesar Datake baje Tana Barcinta Bilhakki da gaskiya..
Allah ne ya Tada Imran da Misalin Karfe 6:30am na Safe Koda ya Farka ya Duba agogon Wayarsa sai ya Zaro ido ya Mike Zaune da Sauri Lokaci Daya yana Dirowa Daga kan gadon laptop dinsa ya Tattara wacce barci ya Kwasheshi yana aiki akanta ya Fada Tiolet ya makara shiyasa bai Fara yin wanka ba ya Dauro alwala ya Fito Tunani yake yi ko Inteesar ta tashi..?
Ko Itama bata tashi ba..!
Agurguje ya Saka Jallabiya ya Fita Zuwa Dakin Inteesar Knoking ya fara yi mata yana Kiran sunanta a Hankali bai ji ta amsa ba yasa ya Tura Kofar ya Shiga..
Yanayin Kwanciyarta Kadai ya tabbatar mai da itama Barcin Gajiya n e ajikinta yadda ta Karkace kai gefe ko Filo bata Nema ba ko kuma Zamewa yayi bai sani ba.
Kusa da ita ya isa yana Kokarin Tashinta din Gefen katifar yake Duka Kadan kadan yana kiran sunanta Kamar a mafarki haka taji Kiran nata Sama sama yasa ta Bude Idanuwanta Cike da Barci akansa Da Sauri yace Mata"Ki tashi mun makara fa..!
Mikewa Tayi Zaune a Hankali Tana gyara Wuyan Rigarta Daya Zame Imran kansa ya kauda yana Kokarin Daidaita Natsuwarsa baya so idonsa ya kara kaiwa kanta Zata Sa ya rasa Duka Natsuwarsa da Jarumtarsa.
Da Sauri yace mata"Ki tashi kiyo alwala muyi sallah ina Jiran ki..!
Cikin Kasala

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login