Showing 9001 words to 12000 words out of 38761 words
isa gareshi da hanzari yakama hannun ta suka koma ciki, bassam tasamu a zaune shida general cikin office din dasuka shiga haryanzu a daure yake da anchor jiki a sabule tazauna gefen Abban nasu kanta yana kasa, yace.
"Mimi haryanzu kicigaba da kallon bassam a matsayin wanda zaki aura wannan abun daya faru bazesa najanye kudiri naba"
cikin wani irin firgici mimi tamike hannuwa biyu tazube a kirji tadafe shi saboda irin bugawar dayake yi mata,se hawaye shar!
Ganin hakanne yasa bassam yataso izuwa gareta cikin wani irin yanayi yake kallonta kana yace.
"Mimi idan nahakura da aurenki nabarwa mujaheed ke zaki yafe min? kitemaka kiyafe min mimi" yana maganar shima yana hawaye,
Kallonshi tayi na dan lokaci san nan tadaga masa kai, juyawa yayi ya tsugunna gaban Abbansu cikin sanyin murya yace.
"Abbah ina neman al farma a gareka"
"Ina saurarenka bassam"
Seda yasauke ajiyan zuciya yace." nahakura da mimi Abbah tunda batasona nahakura alfar mar danake nema kuma Abbah kate maka kabawa mimi wanda takeso idan kayi min hakan kagama min komai a rayuwa,hakan shine zebawa mimi farin ciki har a bada idan takasan ce da masoyin ta, idan na aureta na tauye mata farin ciki mujaheed yana tsananin kaunar mimi shima saboda ganina ne yasashi boye nashi son,kayarda dani Abbah idan kayi haka nasan mimi zata yafemin abin da namata katemaka Abbah, kada kaji tsoron bawa kado auren 'yarka saboda kafini sanin halin dattakonsu sunada amana kada abinda yafaru damu yasa kayi tunanin duka haka suke, kai Allah yaha daka da mutane nagari,"
Tunda yafara maganar Abbah shiru kawai yayi yazuba masa idanu yana tausayin bassam yasan karfin haline kawai yakeyi don shikadai yasan abinda yakeji a zuciyansa dafashi yayi yace,
"Shikenan bassam tunda kahakura dakanka babu komai, alfarmar dakane ma kuma insha Allah zanyi maka ita," hannunsa bassam yarike yace.
"Abbah inason ganin wan nan dauren auren kafin natafi katemaka Abbah kada ka ce a ah hakanne zebani karfin gwiwan yin rayuwa cikin salama a prison"
Kallonshi Abbah yayi dakyau san nan yace.
"Indai sun amince zasubi al'adarmu bassam meze hana"
Mikewa general yayi yace .
"Aminta kamar sunyita ne sungama kada kadamu da wan nan bassam a yau din nan zamuyi maka abinda kakeso,yau insha Allah za ah daura auren mimi kuma za ah hada dayarona yousep dakuma 'yar gidan Alhj.Abubakar"
Zuwa yanzu mamaki yahana mimi yin kukanma binsu kawai takeyi da idanu tarasa wani hali kuma take ciki,tana zaune akakira su Daddy da Daddyn mujaheed,lokacinma su su muhammad suntafi basusan wainai da ake toya musuba, cikin Dan kan kanin lokaci su Daddy suka gama tattaunawa mimi nazaune kunyar duniya ta isheta tana ganin abin kamar a film wai yau za ah mata aure,
Cikin Awa daya me karatu idan kaga taron da aka hada a gidan fulani zakayi mamaki ga 'yan jaridu tako ina an gayyato su saboda wanda besamu halatta ba yagani a kafafen sadarwa,
General ne yakira mujaheed da yousep yasanar musu abinda ke faruwa yasasu a gaba yana zaune kowa ya shirya yana jiransu, tangazo keyarsu yayi kamar yara 😅😅 suka tafi masalla cin gidan fulani inda za ah daura aure,can sukasamu muhammad wanda in banda dariya babu abinda yakeyi shima yaci ado kamar yaune nashi auren,Abbansu mimi yana kallon muhammad don Daddy yagaya masa batun auren sa da meenal, sam beji wani dar a zuciyan saba hasali ma muhammad burgeshi yakeyi.
Kallonda general yakewa yousep ne yahanashi yin kwak kwaran motsi don yasan sarai halin mahaifin nashi babu sauki,
Bisa sadaki mafi daraja aka daura auren Mujaheed Jafar,dakuma safiyya Aliyu fulani,
Se Yousep A adamawa,dakuma nana fatima Abubakar Bauchi,
ko ina gidan radio yadauka da TV ana shelan wan nan auren ana kuma nunawa,
{Tome karatu shifa aure dama haka yake,idan kaga bakayi bah to lokacinka ne beyi bah,inlokaci yayi kuma kobaka shiryaba sekayi shi, rana tsaka dai yanzu mujaheed an zama ango da yousupah}
Inty ce kwance a parlour tana kallon abin mamaki harda rike baki takira mom itama ta tayata kallon abin mamaki,wayarta ta daga takira sameer tace.
"Ya sameer maza ka kunna TV idan kana gida kaga abin mamaki dakuma daure kai," cikin zakuwa sameef yace.
"Mene ne yafaru? dakika tashi hankalin ki haka"
"Wai ya mujaheed ne ya auri 'yar gidan mate makin gwamna na adamawa"
Bata kare maganar ba yasaki kawai yaje ya kunna kayan kallon dama yana gida ganin hakan ne yasa salma biyoshi itama taga abinda ze kalla,itada da dan baby boy dinsu a hannu,tashoshi yaketa canzawa har yakamo wadda ake nuna auren nasu mujaheed gashi ( live ) yanzu ake gudanar da daurin auren, har ankarema anata jin tabakin iyayen amare,
Cikin tsananin mamaki sameer yaje yadauki wayarsa yasoma kiran mujaheed harta tsinke be dagaba, yakuma kiranshi to ana biyunne yaciro wayan a al jihunsa time din kiranma yakusa tsinkewa,mujaheed koda yaga mekiransa besan sanda murmushi ya subuce masaba ya maida wayan al jihu,
Kai yadafe yace.
"Wlh wannan mujaheed ne seyanzu na yarda tome kaishi adama wa kuma ko ince meya kaisu don naga harda muhammad da Daddyn su, to meyake faruwane haka"
TAKU A KULLUM NANA BMB.
08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: ❣️RABON KWADO....!!
BOOK 3
NA NANA BMB
GARKUWA WRITTER'S ASSOCIATION
{Marubuta masu garkuwa da al kalami domin fadakar da al'ummah}
page 19 - 20
Cikin zubar hawaye bassam yace.
"wlh mamy kin cuceni bazan iya yafe miki cutar dakikayi minba se allah yasakamin da wannan torancin da kikajamin"
Cikin kuka itama asiya tasoma cewa.
"kayi hakuri bassam nima bayin kaina bane mahaifiyatace nima tasakani itace ta cucemu"
Alokacin kuma mahaifin bassam yataso yasoma dannawa asiya Allah ya isa, dagashi se Alhj.Sulaiman shima yataso yasoma tsinewa halin balaraba,
" wlh balaraba kinyi asarar hali aduniya mara mutumci mugun iri gara da Allah yatoni asirinki yanzu me bakar zuciya" yana maganar yanajin kamar yashaketa a gurin ta mutu, cikin kuka gwaggo ta mike ta iso garesu tana takarkarawa dakyar tasoma magana cikin yarensu na fillo cewa.
Sulaimanu kaine kaja mana duk wannan abun yafaru kaje ka auro mana mugun iri cikin zuri'armu gashi yanzu bakin halinta yanata bimin jikoki Allah ya isanmu balaraba kuma yau Allah yakawo karshenki a gidan nan, kado! kado! kaji tsoron halinsu bakowa yasan hallaciba"
Tana magana tana sharar kwalla,to Abbansu mimi dai mamaki ya hanashi magana da jimami kallon bassam kawai yake mutumin daya dau yardar duniya yabashi ashe shine maka shinsa besaniba,ummi in banda hamdala babu abinda takeyi da Allah yasa bassam berigada ya aurar mata 'ya ba asirinsa ya tonu,
Sosai kukan mimi ya tsananta saboda komai daya shiga dawo mata cikin kai, a ranar dazasu fita hana hasana yayi tafisu koda sukaje gurin siyan icecream hanata fitowa yayi daga mota yatafi shikadai kafin yadawo anyi gaba da ita ashe da abinda ya taka,haka sunata koke koke aka tarkatasu aka tafi dasu gida yakara hautsinewa koke koke yayi yawa
Tome karatu lamarin auntie se du'ah ei, haryanzu tanacan kwance kamar matatta nana ce a tare da ita tana kula da ita sosai take tausayin mahaifiyar tata don tabbas kuwa takawo kanta gidan dafa kanta.
Kwana biyu da fara shari ar su bassam sega ganeral shida 'ya'yan sa yousep da nadiya,se matarsa a gidan fulani abin kamar a al mara, domin tafe suke da Abbansu mimi,yadda yousep ya rame inka ganshi seya baka tausayi saboda duk abinda yake faruwa nana tasanarwa nadiya hatta da zuwansu nan, ita kuwa nadiya farin ciki ya isheta zasu hadu da meenal aminiyar ta mom dinsu kuwa 'yar kauye ta koma tasau baki tanata bin gidan da ido tun farkon zaman aurenta da ganeral a nan yola takejin labarin gidan fulani harzuwa sanda suka koma kano dazama bata tama sanin yadda yakeba seyau, direct part dinsa yawuce dasu nan danan aka cikasu da kayen ciye ciye, babu kowa a gidan se ummi kadai wanda zuwan nasu dama ya hanata binsu hasana suje gurin su meenal,seda sukaci suka koshi sannan Abbansu mimi da ganeral suka fara yiwa ummi bayanin abinda yake tafe dasu,
Batune a kan bassam sam bashida laifi yaudarar shi mahaifiyarsa tayi sam besan cutarda mimi za ayiba sedaga baya,wan nan dalilin ne yasa yakira ganeral yasanar masa da duk abinda yake faruwa dakuma gurinda suka boye mimi,badon shiba kam da tabbas mimi bazata dawo da raiba ko ince meenal,
Allah sarki ummi tausayin bassam ne yakamata matuka saboda tasan beyi dacen uwaba ne yasa irin haka yake faruwa dashi,
auntie bata juma da farkawaba nana takira su daddy tana shaida musu auntie tafarka kamar zautatta saboda ta tubure setabar wanan gida sam bazata iya zamansa ba,a parlour su daddy sukaci karo da ita tana shirin yowa waje su mummy nariketa don masifa irin nata tana tafe tana tangadi amma taki saduda, muhammad yadda yaga auntie tagama firgicewa da rudewa yasa dariya takamashi daurewa kawae yakeyi duk yasan saboda ummi take wannan haukan da borin kunya,
Hannun ta daddy kawai yarike suka koma cikin bedroom, sosai yake daurewa don shima dariyar yake sonyi daurewa yayi yabata fuska yasoma cewa
"Haba maryam menene haka kikeyi ne? kinson tonawa kanki asiri dakanki,yanzu idan sukaga kina wannan borin kunyar naki ba tuhumarki za ah cigaba dayiba gaba daya kinfice a hayyacinki kamar bakida hankali sam ba safiyya bace kika gani yakamata kinutsu haka, 'yar uwartace ba ita bace bah, nan ne asalin safiyya yakamata kisan mekikeyi fah! kikama kanki,yawwa kinga yanzu ina amfanin mugun hali idan da abun azziki kikayiwa safiyya bazaki shiga wannan halinba a yanzu,kullum ina nusar dake ina fahimtar dake kikayi watsi da maganata, yanzu ga sakamako kinso magani kinga asalin safiyya koh, tafiki asali idan kudin kike takama kingani dai tafiki azziki tafiki matsayi babu abinda zaki nuna mata, sedai dake zuciyanki tayi nisa idanunki sun rufe, kisani kusan saboda ke na aurawa muhammad meenal,saboda zarginda kikeyi na meenal 'ya tace, zuwa yanzu kuma nasan duk wani zargi dake zuciyanki yafita koh sekuma kiyi shirin girbar abinda kika shuka"
Duk maganar dayakeyi auntie kuka takeyi meban tausayi tana jimama wannan lamarin kaico duniya kaico! ganin abin take kamar a tatsuniya wai yau itace a cikin family din safiyya haka,
To fitowan daddy kenan sega su yousep sunshigo shida nadiya suna gaba,se mom dinsu da ummi abaya, Ya Allah! meenal koda tayi arba da abin kaunarta mancewa tayi da komai tamike cikin tsananin farin ciki tanufesu, zuciyan muhammad tamkar zata fado saboda harbawan data somayi,
"Ya yousep!" tazo zata rumgumeshi saboda murna da farin ciki, cikin mamaki matuka yayi baya yana kallonta, harda rike baki yace.
"Ke meye haka zakiyi kinmanta kinada aure ko yaya"
"Nashiga uku!"
Meenal tafada tana dafe girjinta da hannu biyu saboda tsananin firgicin data shiga,tace.
"Wani makaryacinne yagaya maka? wlh kowaye karya yakeyi"
Nadiya batasan sanda dariya ta kwace mataba tarike mata hannu tace.
Yanzu meenal kina nufin baki saniba? ko kuwa a tunaninki bazamu jiba,duk wan nan gyaran dakika sha kinata kyalli ga kunshi kinsha amma yatashi a banza"tuni kwalla tacikawa meenal ido jiki a sanyaye tace. "wlh bestie ba bikina za ayiba na sister nane kune baku saniba"
Yousep kallon inda su muhammad suke zaune yayi yana son sanin cikin shida mujaheed waye mijin na meenal, to drama din datake faruwane yasa mujaheed darawa sosai yakewa muhammad dariya jin furucinda meenal takeyi,dukda yana cikin damuwa hakan behanashi darawaba,mimi kuwa ganin hakanne yasata sakin ajiyan zuciya tana hamdala ganin sahibin nata yasoma saukowa, rabonta daganin fara arshi tun a kano lokacinda sukayi selfie, cukurkude fuska da muhammad yayine yasa yousep tunanin shine mijin nata,
Kallon nadiya yayi yace. "Sister shige muje tunda bata saniba to ko baza aji mutuwar sarki a bakina bah"
Cikin rashin fahimta meenal taje gurin daddy tazauna gefensa cikin wani irin yanayi tace.
"Daddy kaji abinda suke cewa kagaya musu gaskiya nibanida aure"
Murmushi kawai yayi yashafi kanta yace.
"Yata takaina kinada aure mana,nayi miki aure tuntuni, amma inason kibar maganar semun koma gida"
cikeda tsoro meenal take kallonsa dakuma jin kamar yana mata ta tsuniya, kura mata idanu kawai muhammad yayi yanason ganin yanayin dazata shiga, cikin muryar kuka meenal tace Daddy waka auramin?
Kallon takaitaccen lokaci yamata sannan yace. "Itama wannan maganar kibarta semun koma gida"
Kai kawai meenal ta iya jinjina masa tamike dakyar tabar parlour din batare da takuma kallon su nadiya bah,nana kuwa kana kallonta zakaga zallar farin cikin datake ciki tagode Allah yanzu tasamu 'yan cinda zata mallaki yousep,
Kuka meenal take meban tausayi ta kulle kanta adaki saboda zafinda zuciyarta keyi mata meyasa Daddy zeyi mata haka bayan ga wanda takeso ita,
Har dare bata fitoba saboda ankule su meenal bakuma wanda yaje inda take bare ya rarrashe ta har muhammad kuwa, duka an hadu a parlour anata hira cikin farin ciki dajin dadi banda ita banda auntie,
Se bayan ishah Abban su mimi da ganeral suka dawo gidan suna dakinsa nasaukar baki suna tattaunawa yakira yousep awaya yasanar masa yazo yasamesu,
Ana cikin hira yousep yamike yafita wanda kamar jira nana takeyi dama, takuwa mike tabishi itama ko kunya🤔,
Sarai yaga nana tabiyoshi wannan dalilinne yasa shi karawa tafiyan sa sauri, cikin tafiyarsa ta takama yay mata nisa hakanne yasata saka gudu, itama tacimmasa don harya kusa isa inda zashima, batareda shakkar komaiba nana tariko masa hannu, hakanne yasa yajuyo a fusace yana kallonta ganin bata da niyyar magana ne yasa yafisge hannunsa yace.
"Sakeni tunda bakida abin cewa ni inada abinyi"
Ya juya zecigaba da tafiyarsa nana takuma rikesa idanunta nata ambaliyan hawaye cikin maida numfashi tace.
"Narokeka katsaya ka fahimceni kada kayimin haka katema ki rayuwata kasoni koyaya,kaine kadai zuciyata take kauna a duniyar nan kada kayi min haka, Allah yayi nice rabonka ba meenal bah"
Tana maganar tana kara shigewa jikinshi kamar zatayi kuka, cikin takaici kuwa yousep ya fisgeta daga jikinshi haryana huci yanuna ta yace.
"Nana kada kiyaudari kankifa! don narasa meenal hakan bayana nufin nasoki bane kingane koh! saboda haka kikama kanki kisan mekikeyi nibazan taba sonkiba kada kikara tabani koda wasa nagaya miki"
Cikin shashekar kuka nana tace.
"Narokeka kada kajuyamin baya wlh bansan yadda rayuwata zata kasanceba kate makamin nizan maka abinda meenal btayi makaba ka yarda dani"
Tsaki kawae yousep yayi yajuya,caraf suka hada idanu da Dad dinshi, da Abban su mimi suna tsaye suna kallonsu,zuciyansa kuwa tasoma bugu yana addu an Allah yasa basuji abinda yafaruba....
TAKU A KULLUM NANA BMB.
08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: ❣️RABON KWADO....!!
BOOK 3
NA NANA BMB
GARKUWA WRITTER'S ASSOCIATION
{Marubuta masu garkuwa da alkalami domin fadakar da al' ummah}
page 17 - 18
Cikin zubar hawaye meenal takarasa ga mujaheed,tace.
"Shin ya mujaheed meyasa zakayiwa 'yar uwata haka?menene laifinta anan ko kana jah da kudira ta ubangiji ne?mimi fah alheri ce a garemu, itace sanadin dana gano ko wacece ni, saboda tana kaunarka shine zakayi mata haka,kasani gatace a gareka domin idan da nika furtawa SO sam bazan amin taba, saboda inada wanda nakeso"
Kallon muhammad mujaheed yay dajin furucin meenal cewar tanada wanda takeso,sauke ajiyan zuciya yayi sannan yace.
"Meenal kidena wannan maganar mana sam batada amfani saura kwana uku fa adaura mata aure,"
Zuwa lokacin muhammad yagama hassala da iskanci irinna mujaheed,yakaraso cikin takaici yace.
"Wai meyasa bakada hankali ne mujaheed? meyasa kakeson karyata zuciyanka karya kake kace bakason mimi karma ka yaudari zuciyanka don zakayi nadama babba"
"Banasonta! wai anaso dolane? kukyaleni mana"
Mujaheed yafada cikin daga murya dajin haushi, harara muhammad ya antaya masa yace.
"Zoka kalli kwayar idanunta kace bakasonta idan ka isa, asan nan zamu tabbatar da hakan"
Mujaheed batare daya kalleshiba yasa kai yay gaba yasoma sauka daga steps din cikin sauri, shima muhammad yarufa masa baya yanata ruwan bala i,
Mimi najikin mummy inbanda kuka babu abinda takeyi sosai take tausaya wa rayuwar ta haka hasana mah jikinta yayi sanyi matuka haka taja twins suka nufi ban garensu
Bassam yana zaune shikadai a garden yanata kuka tamkar karamin yaro,yana surutai meyasa mimi zatayi masa wan nan sakayyar meyay mata arayuwa haka dabata kaunarsa ko kadan,yana cikin wannan halin ne yaji an dafashi,koda yadago idanunshi dana hasana suka sarke nadan sakanni, kana ta matso tazauna gefenshi dukda irin tsanar data masa yau a yanayin data sameshi seda yabata tausayi,cikin muryan tausayawa tace.
"kayi hakuri ya bassam"
Share hawayen fuskansa yayi yana fitar da huce daga bakinsa mezafi yajuyo yakalleta yace.
"Hakurin mezanyi hasana? kinason nahakura nafasa auren yayarki,ta auri wanda baya sonta bayason ganinta,wai meyasa yayarki zatayimin haka? taso wanda besan darajartaba"
"Bayin kanta bane ya bassam" hasana tayi maganar idonta tafda kwallah, murmushin takaici yayi yace.
"Banyi mamakin jin furucinki ba hasana, saboda nasan yadda bakya kaunar na rabi yayarki, kina yimin kallon dan iska koh"
Sam kasa magana tayi illah idanu data zuba masa,
"Niba Dan iska bane hasana sam koda wasa bantaba kusan tar zinaba ,amma zeyi wuya kifahimceni koki yarda dani,"
Cikin zubar hawaye tace.
"Nayarda dakai ya bassam"
Da mamaki yadago yazuba mata manyan eyes dinsa dasukayi jah saboda kuka,hakanne yasata sunkuyar dakanta tana kallon zara zaran yatsun hannayen ta tace.
"Dama Abban mune yake nemanka, yace gobe insha Allah za ah fadi wanda sukeda sa hannu akan sace yayar mu da akayi"
Wani irin kara cikin bassam yabayar,wanda seda hasana ta dago ta kallesa, hakanne yasashi saita nutsuwarshi yace mata taje tanasanr yana zuwa, tamike kuwa tashige ciki tabarsa anan yadauki wayansa yayi kiranda seda yakwashi time sosai sannan yagama wayan,yamike yashiga ciki shima
WASHE GARI
Karfe 9 kowa ya hallara a gurin meeting anata cece kuce kowa da abinda yake furtawa akan suwa za ah kama yanzu,sam bassam baya cikin nutsuwarsa hatta abban su hasana yafuskan ci haka,isowar su (DPO) dinne yakara hautsina gurin saboda ko isowarsu bassam aka fara arrest dinsa akasa masa anchor,san nan aka kira sunan mahaifiyar sama wato asiya haka ta taso tana gun sheken kuka koda tafito itama sukace ina mahaifiyarta? zuwa lokacin bakajin komi se sallallami namutanen su kaji fulatanci kaji hausa harda turanci, hajiya balaraba tana zaune tayi sharkaf da gumi kunyar duniya ta isheta tsamo tsamo ta taso kuwa bakunya ba tsoron Allah kiri kirk aka daureta itama,se a lokacin (DPO) yayi magana yana kallon Abban