Showing 6001 words to 6974 words out of 6974 words
Chapter 3 - JAMI'IN SIRRI C'I'D BOOK NA MUJAHEEDAH MATAR MALAM AMMYN KHAUSAR .txt
muma A taro Daddy Damu,"
"To Muje" Aje kayan tayi suka fad'ama Ammaaa sannan suka fito,
"Bara nacema Yazo muje"
Nocking k'ofar Tayi tad'an Jima Kafin ya bud'e murmushi suka sakarwa juna, Tace"jirgin Daddy ya sauka Yanzu Zamuje Airport ne kazo muje,"
"Kai haba Daddy ya sauko, Masha Allah, Yanzu kinsan me bazan Sami zuwa ba Zan k'ara kintsa kainane Kafin ya iso sai mu had'u,"
"Kintsawar me kuma saikace yau Za'a d'aura Auren,"?
"Nainaaa Kenan bazaki ganeba ne nidai kuje kawai sai kundawo yanzu bara nashiga wanka idan kundawo sai mu gaisa dashi,"
"Shikenan tinda kace haka sai mundawo,"
"To Allah ya tsare"
"Ameen"
Wucewa Sukayi
Yakoma d'akinsa yau farinciki yakeji Sosai Ransa Fess domin daf yake da cinma Burinsa, waya Yafara nidai bansan meyake fad'a ba Kawai Naga ya tsuke fuska Yana Magana k'asa k'asa ne,
Koda suka Isa jirgin Daddy ya sauka Yana saukowa Kan jirgin da gudu Nainaaa da Hairat suka rungumeshi suna murna, Hakama mommy duk wani Bak'in halinta ga Nainaaa b'oye shi tayi
Suka rankaya mota suka nufe gida,
Jin k'arar shigowarsu yasa ya lek'o ta window yana ganin fitowar su murmushi Kawai yake ya koma Yana Shirinsa Cikin Bak'in suit,
Kai tsaye palourn daddy suka Wuce,
Yace"Yato Yanzu kubari nayi wanka idan nafito sai kowa yazo muyi fira,"
Hakan kuwa sukayi Saida Yayi wanka Yashirya tsaf Cikin had'ad'd'iyar jallabiyarsa Yafito palourn Ancika Masa daining da Abinci tare Suka zauna suna CI suna fira gwanin Sha'awa Saida suka Gama suka dawo tsakiyar palourn Suka cigaba da fira,
"Yawwa mamana kije kizo da bak'on naki na ganshi yanzu ya kamata mugana Ai,"
Cikin Jin Kunya tamik'e tana Fad'in"to Daddy"
Nocking tamasa ya bud'e k'ura Masa Ido Tayi Ganin ya shirya cikin suit Bak'i Amma fa yayi kyau ba kad'an ba,
"Ya Abbas Irin Wannan Shirin Haka saikace zaka wani Aikin,"?
Murmushi Yayi Yace"Daddy yace nazo ba, kidai muje Kawai ai yau Rana ta musamman ce Yau zanyi surprise D'INKU duka,"
"Allah ko to bani Nasha ko kad'an ne,"?
"Habadai Ina Kika tab'a gani ko ji Ai Saidai Acan muje kawai,"
Jerawa Sukayi suna fira har Suka Isa palourn yashiga komawa tayi d'ayan kujerar ta zauna shikuma ya zauna k'asa Yana gaida Daddy
"Ansawa Daddy Yayi Cikin fara'a yace Sannu Ai naji Labarin ka Sosai Kawai sai yanzu Allah Yayi zamu had'u,"
"Eh Daddy Hakane Sannu da zuwa ya Hanya,"
"Alhamdulillah,"
Fira suka hau tadashi A sace yake tab'a Wayarsa Yana gamawa ya Tura ta Aljihu,
Mik'a masa Hannu Daddy Yayi Yace"kazo mu gaisa Mana ai Yanzu mun Zama d'aya Abbas tinda har Y'ata take sonka,"
Cikin Jin kunya ya mik'e tsaye Yanufe sa Yana Isa inda yake yasa Hannu bayan wandonsa saiga Bindiga Yaciro ya d'aurawa Daddy Agoshi tareda cewa
"you are Under Arreste Alhaji Salman"
Dukansu cikin tsananin mamaki Suka mik'e tsaye Banda Nainaaa da idanuwa Kawai ta zuba masa
Cikin k'arfin hali Daddy yace"Arrested for what,"
"Idan mukaje zakaji, kanayin wani motsi wllh saina fasa kanka da Bindiga,"
Yana Danna wani madanni take d'akin Yacika da sojoji ko wanne Cikin bak'ak'en Kaya kuma d'auke da k'atuwar bindiga,
"Zo kasaka Mai Handcuffs mutafi,"
Ganin Za'a sawa Daddy handcuffs d'in yasa ta mik'e Cikin Yanayin mamaki tsoro fargaba tace," Are you out of your Sense Abbas mahaifina zaka kama mahaifina zaka sawa Handcuffs kodai kasha giya n,....,"
"Ke Yarinya ki iya bakinki kisan da wa kike magana Ogerh ne gabanki yafi Gaban Raini, yanzu saina fasa kanki da bindiga,"
"A'a dakata better tasan Komai A Yanzu,"
"Ni ba Abbas Sunana ba, Na'if sale Mai gold shine Cikakken sunana, nazo ne daga cikakken sashen bincike na Farin Kaya wato C.i.d in shout Ni *JAMI'IN SIRRI C~I~D* ne daga Babbar Headquarter dake Abuja, kawai Aikina yakawo Ni Rayuwarki Domin Kama wannnan Azzulamin Uban naki,"
"Abbas kasan me kake fad'a kuwa,? Hatsari Zama Asibiti loosing memory Soyayyata Duka cikin Aikinka ne Kenan,"
"K'warai kuwa Nainaaa, Duka nayi Amfani dake ne dama Sauran likitan dakika sani Ni sukewa Aiki saboda Ni doctor San Yakoma wannnan Asibitin taku Ni lafiya nake bana tare da komai,"
Wasu zafafan Hawaye suka Soma gudana daga idanuwanta Tace,"Meyasa zakayi Amfani da Ni gurin kassara rayuwata,? Me mahaifina yamuku,"
"Laifinsa Mai girman ne domin Ni kaina ya cutar da Ahlina Kuma ya sace dukiyar mu Kuma mun kamashi da safarar miyagun kwayoyi musamman Cookie hodar iblis, Kaisa mishi handcuffs d'in muje,"
"Okay Sir,"
Saka mishi handcuffs d'in yayi suka jashi zasu fita Cikin sauri ta Shiga gabanshi
Hawaye kezuba daga idanuwanta Tace"kacutar Dani cuta mafi Muni karabani da Sauran farinciki na Natsane ka Na'if wllh Allah bazai Barka ba Kuma Sainayi Shari'a dakai wannnan b'acin Sunan da Kama mahaifina bazai tafi Abanza ba, kayi Amfani da Raunina da Soyayyata ka rabamu da farincikinmu Allah ya Isa tsakanina dakai,"
Sosai kalamanta suka masa zafi Amma ya daure fuska d'aure suka fita da Daddy Cikin Gidan,
"Shikenan shegiyar yarinya takawo Annoba da kanki kinkawo K'arshen mahaifinki hasararriya kamar dai uwarta," Mommy tafad'a cikin kuka da barin d'akin
Durk'ushewa k'asa Tayi tana kuka Mai ban Tausayi tana Fad'in"Kenan harda soyayya ta Duka Shirice Wai Abbas ne ya yaudare ni,? Ammanaaa ku tayar Dani daga wannnan mugun mafalkin danake,"........................................
*Kash gashidai MUNKORO Amma Saidai Kash laifin Dad'i k'arewa, Anan Free page YAK'ARE idan kina Kana so kabiya 300 Kawai ka MALLAKE naka,*
_SHIN YA ZATA KAYA KUNA SANE CEWA YANZU WASAN YA D'AUKI ZAFI KUWA? HUNMMMM YANZU ZAMU FARA LABARIN, SHIN DADDY ZAI KUB'UTA KUWA? SHIN DA GASKE ANKAMASHI DA SAFARAR MIYAGUN KWAYOYI? SHIN INA LABARIN MAHAIFIYAR NAINAAAHH ZASU HAD'U KUWA? WACE TARBA NAINAAA ZATAWA MAHAIFIYAR TA? SHIN NA'IF ZAI GANO NAINAAA ITACE YAR AUNTYN SA KUWA? WANE HALI ZAI SHIGA IDAN YAGANO CEWAR NAINAAA Y'AR UWARSA CE? SHIN SOYAYYAR SU TACIGABA ZASUYI AURE KUWA? WANE IRIN MATAKI NAINAAA ZATA D'AUKA??????? TO DOMIN SANI MU KASACE CIKIN NEXT PAGE KUMA DA 300 D'IN KU KADA KIBARI KADA KABARI WANNNAN K'ASAITACCEN LABARIN YA WUCEKA.............. JAMI'IN SIRRI C~I~D.... HUNMMM RIGIJI GABJI WANI KAYA SAI A MALE.........._
_KUTAYANI ADDU'A ZANYI EXAM KUMIN FATAN NASARA FANSSS,_
_BASEEERATA ITACE ARZIKINA😍_
WhatsApp number 07064904617