Showing 1 words to 3000 words out of 23188 words
Chapter 1 - KAI NE GATANA BOOK COMPLETE DOCUMENT BY FIDDAUSI SODANGI .txt
[12/5, 3:54 PM] +234 813 502 2313: 🍃KAINE GATANA 🍃
1⃣
NA
FIDDAUSI SODANGI
©TASKAR MARUBUTA📝
"Yarinyace matashiyar budurwa wacce bazata wuce shekara sha hudu ba,s "sanye take da wata kod'add'iyar atamfa riga daban zani ma daban, kanta d'aure da d'ank'wali irin mai santsin nan d'uk'un d'uk'un take kayan sunyi Bala'in daud'a sai tsami ne ke tashi ajikin ta, bak'ace sosai, tanada tsawo amman ba sosai ba. Kanta d'auke da bokiti da alamar ruwa ta d'ibo, sai sauri takeyi ruwan cikin bokitin na zubowa yana jik'a mata jiki,
"Sannu da aiki goggo" Dan uwarki sai yanzu kikaga damar dawowo?" tunyaushe kika tafi d'ibo ruwan kinje kin tsaya yawon iskancin naki shine zaki wani shugo kina min sannu!" aikece da sannu bani ba dan kece agajiye, anya kuwa kausar kina tsoron yanda k'arshan ki zai zama kuwa?" ace yarinya k'arama dake amman kinsan ki ringa bin maza!?" kai ni talatu wannan jaraba dayawa take wannan wani irin bala'i ne haka, kai!!" Allah yasauwaka maki. Shegiya munafuka kallo na kika tsaya yi bazaki sauke ruwan ba saikin kwaro minshi ajiki dawannan sanyin iyyee!!"
"Dasauri tafara k'ok'arin sauke ruwan akanta aiko nan bokitin ya subuce yafad'o k'asa dama bokitin roba ne nan ruwan ya malale ak'asa. Ciki da masifa goggo ta mike ta shak'e kausar ta had'a ta da bango tashiga jibga saikace tana bugun k'ato, "dan Allah gaggo kiyi hakuri wallahi bada gangan nayiba fad'owa yayi kiyi hakuri" saida taga jini nafitar mata hanci da baki sannnan ta k'yaleta haka nan taci gaba da d'ura mata ashar, kuka kawai kausar keyi, fice min daga gidannan karki sake ki shigo batare da sabon bokiti naba yar'iska kawai, haka kawai yarinya kinzame min jaraba babu dangin iya babu na baba kullum ina ciyar dake ina shayar dake amman ke kullum burinki ki bakanta min rai kiringa jawo min asara!" to wallahi bazan k'ara yarda ba duk sanda kika min asara saikin biyani wallahi nagaji da adashin da babu k'wasa zaki fice kosai na shake ki kin mutu!" bakar banza da wofi kawai wacce tayi gadon mugun hali, "dagudu kausar ta fice tana kuka abin gwanin ban tausayi.....................
Fido sodangi❣
Dedicated to
KAUSAR M HASSAN (kausar luv)
[12/5, 3:55 PM] +234 813 502 2313: 🍃🍃KAINE GATANA🍃🍃
2⃣
NA FIDDAUSI SODANGI❣
©TASKAR MARUBUTA📝
"Tana fita taci karo da malan mamman mak'ocinsu, yace subuhanalillahi kausar lafiya?" meke faruwa haka naganki a wannan yanayi?" cikin kuka sosai tayi masa baya nin abinda ke faruwa,yace assha!" wai meyasa talatu take irin haka ne?" anya kuwa talatu, anya! " shige muje ciki inji, ta girgiza kai ta mak'ure jikin bango, Ya girgiza kai kawai ya shiga k'wad'a sallama, goggo naji amman tayi shuru ta k'yale, saida yayi sallama wajan sau hud'u sannan taga damar amsawa tafito tana sababin waye ne yake ta doka mata sallama haka baiji anata amsawa bane!" tafito taga malan mamman tsaye ga kausar rakube, nan danan ta d'aure fuska tace lafiya malan da sassafen nan!" yace lafiyar ce takawo haka, nandai yashiga bata hakuri akan ta k'yale kausar tashiga cikin gidan, amman sam ta runtse ido taita bala'i daga k'arshe harsai daya biyata kud'in bokitin sannan ta hakura tabari tashige ciki, malan maman nata Allah wadai da ita acikin zuciyar sa sannan ya kad'a kansa yai gaba.
"A hankali wasu zafafan hawaye suka cigaba da bin kumatunta, tana shieshikar kuka. A hankali2, har tagajie da kukan ta tashi ta share hawayen dake zuba mata a ido ta dubie cikin dakin, da duk yayi datti, ga wasu kaya gefe an ajiye sai wari sukeyi, zaune tai kan tabarman da ita dayace mallakinta a gidan, ta dubie fatan jikinta, a hnkli cikin zuciyanta ta fara magana "yaushe wannan azaba da nake ciki zata barni"? Wace irin rayuwa ce nake hka"? Shin ni dayace a duniya dake shan wahala? Wata zuciyar ke cewa a'a Kausara! Ai komai halin dake tsinci kanki a cikinta to ki tabbata akwai wanda yafiki wahala a cikinshi".
Tana cikin wannan tunanin tajie ana sallama wanda wnnn ba kowa bace face kawanta mai suna Rahane, kai tsaye rahane ta dushie dakin da kausar take ciki, dasauri kausar ta mike tana fad'in inazaki haka rahane naga kinsha kwalliya kinyi kyau!" rahane ta washe baki cikin jin dadin kausar tace tayi kyau tace ai burni zamu wuce yanzu nida salame da uwani, uwani ce tasama mana gidan dazamuyi aiki ana biyan mu duk wata, takara washe baki kamar gonar auduga, kausar ta zare ido tace da gaske rahane?" Dan Allah kuje dani zan biku dan allah?" rahana ta dafe kirji tace ke kausar babu ruwana ai duk wanda yatafi dake yajawo wa kansa bala'i dan goggonki ba kirki gareta ba kinsani kausar ta d'uk'a ta rik'e k'afar rahane tashiga kuka sosai tana rok'onta dan girman allah sutafi da ita batare da goggon tasani ba.........
Fido sodangi❣
Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
( kausar luv)
[12/5, 3:55 PM] +234 813 502 2313: 🍃🍃KAINE GATANA🍃🍃
3⃣
NA FIDDAUSI SODANGI🍃
©TASKAR MARUBUTA📝
"Rahane taja ajiyar zuciya tace to shikenan kausar karki damu zamu tafi dake amma sai naje nagaya ma uwani tukun idan ta yarda kinji? Kai kawai kausar ta d'aga mata alamar taji, rahane tafice abinta kausar tabi bayanta da kallo kawai tana hawaye,
"Rahane nashiga gidansu babarta tafara yimata fadan danme zataje ta dade ana jiranta,nan ta shiga warware masu abinda ke faruwa aikuwa uwani tafara washe baki ta kalli babar rahane tace to ai mu adadin mu kinga kawai tafiya da ita zanyi idan anfara biyanta albashi sai mu rabe shi tunda dai ai batare da sanin goggon nata zataba kinga shikenan mu adadinmu gara da akai haka koya kikace? Jinjina kai kawai babar rahane tayi tace to uwani ai kinfini dabara nikam banida tacewa yanda kikace ai haka za ayi, uwani ta kalli rahane tace ke maza tashi jeki taho min da ita inganta danni bama sanin ta nayi ba, jiki asanyaye rahane ta dubi uwani tace to ai goggon nata nacan takasa ta tsare a tsakar gidan ina tsoron inkoma ta koroni kinsan bataso anazuwa wajan kausar, tokenan bakiso atafi da ita birnin kenan? Cewar uwani, dasauri rahane tace inaso mana uwani aikinsa kausar itace babbar kawata aduk fadin kauyan nan banda wacce tafita, babarta ta dubeta cikin fada fada tace to tashi mana ki taho da ita lokaci na tafiya , dasauri ta tashi tafice.
"kausar na zaune a d'akin kamar yanda rahane tabarta sai raba ido take taga ta inda rahanan zata bullo, aikuwa sai sallamar rahane taji daga tsakar gida, goggo na zaune a tsakar gidan tanata yan wak'okinta, a fusace ta kalli rahane tace wai yau uwar mekuke k'ullawa ne kiketa sintiri a gidan nan tunda safe!" ke nifa banason kicihi da iyayi! Idan ke bakida aikin yi to ita tana dashi fice kiban waje kafin inmike in fasa maki kai! Dagudu tayi hanyar waje, goggo taci gaba da fada cikin kumfar baki, candai datayi tagaji ta k'wallama kausar kira kee dan uwarki zonan in aike ki gidan lanto saura kuma daganan kitafi niman mazan dakikasaka agaba shegiya jarababbiyar yarinya mai fuskar munafukai kawai, da gudu kausar tafito dan abin nima ne yasamu dama, kicema lanto wai sai yaushe za a hada min k'udin adashi nane tun jiya fa yakamata in kwasa amman dan iskanci har yau shuru! Tokice mata nace hakuri na yagama k'arewa! Kuma wallahi kikaje kika zauna wallahi sainayi k'ulunk'ulun kubura dake acikin gidan nan dan wallahi jikin kine zai gaya maki, wuce kibani waje bak'ar banza mai kama da uwarta!
"Da gudu kausar ta fice tana murna kai tsaye gidansu rahane tashiga nan ta taddasu tsatsaye sunyi cirko cirko tamkar marasa gaskiya, kausar na shugowa rahane tahau washe baki yauwa uwani kingantanan tazo kausar ya akai goggonki tabarki kika fito? Uwani tace ke rahane yanzu dai ba lokacin tsayawa ayi surutu bane dan haka mukama hanya kawai mutafi dan munsoma mu makara, nandai sukayi ma babar rahane sallama suka tafi da d'an k'ullin kayan rahane a d'an k'wali,
"kausar wacce take d'uk'un d'uk'un sai tashin wari take tamkar wacce ta fad'a k'wata hak'oran nan nata sunyi jawur dasu tawani washesu tana jin dadin yau zata burni, ta dubi rahane tace kee kikace min harda salame zamu burnin toya bangan taba kefa hanne kincika k'arya alk'ur'an, ke dallacan gidansu zamu mu d'auko ta, uwani ta dubi kausar tace to ke kausara bayan gidan su salame zaki jira mu dan banaso asan dake zamu tafi kar aje agayawa goggonki ta d'agama babar rahane hankali tunda ance ita haka halinta yake, dasauri kausar tace Eh ai babu komi uwani hakan ma yayi ai Allah ya amfana........
Fido sodangi🍃
Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(kausar luv)
[12/5, 3:55 PM] +234 813 502 2313: 🍃KAINE GATANA🍃
4⃣&5⃣
NA FIDDAUSI SODANGI
©TASKAR MARUBUTA📝
Haka Kausar taita tsayuwa a wajan har zuwa lokacin dasu uwani suka dawo suda salamen, "izuwa lokacin duk ta kosa da tsayuwar jiransu awajan, gani take tamkar wani zai ganta yaje ya fada ma goggon ta tazo ta tasa k'eyarta zuwa gida, "sai lokacin data hango su sun karyo kwanar inda take sannan hankalin ta yadan k'wanta, cike da d'oki ta washe jajayan hak'oranta tana fad'in to uwani ai yakamata muyi gaba haka nan kar muyi rana ko? Kokuwa birnin babu nisa a mota ne? Amman kuma ai daga nan zuwa tasha akwai nisa sosai! "Duk wannan tambayoyin dataketa jerowa uwani basu riga sun iso inda take ba amman ka rantse da Allah kusa da ita take,
" Tafiya sukeyi sunata zabga sauri kowannansu da d'an k'ullin kayan sa bisa kai k'afafuwan nan nasu sunyi butu butu kasancewar tashan nada dan tazara da inda suke, "A lokacin dasuka isa zuwa tashar mota daya ce jal tarage bata cika ba saidai wajan mutum uku kacal yarage, nan uwani ta dubi kausar wacce idanuwanta harsun cika taf da hawaye taga samu zataga rashi, kanta tasoma girgizawa da karfi tana fadin dan Allah uwani karkice in koma dan girman Allah, "k'wandastan motar ne yayi saurin cewa A'a yanmata menene abin kuka ga bayan motar nan basai ki shiga ba idan zaki iya?amman fa zakisha zafi kuma ga uban lodin kaya, dasauri kausar tace wallahi zan iya mezai haka nidai inza atai birni dani ai babu matsala ko a saman motar zan iya zama ai, gaba dayan su suka kwashe da dariya uwani tace eh lallai y'arnan kina kaunar zuwa birni!
"Tafiyar awa biyu ce takaisu cikin garin katsina inda suka d'ira a sabuwar tasha, dak'yar kausar ta iya ajiye k'afarta a kasa saboda tsabagen tsamin dayayi, duk tayi wani zuru zuru sai zare ido takeyi saikace wacce tayi karya, kallo daya uwani taimata ta fashe da wani mugun dariya saikace wata gardi, " fuska a yamutse kausar ta dubeta tace wallahi uwani fitsari nakeji kamar zanyi a wando nakeji, tafadi tana rike zaninta da hannu, k'ullin kayan dake bisa kanta uwani ta karba tare da nuna mata wani waje nisa dasu tace da kin karya waccan kwanar zakiga kewaye a wajan taciro wata yamu tsatsiyar naira goma ta mika mata tace inkinje saiki basu wannan zasu barki ki shiga mu bari mu jiraki daga nan gefe, dasauri kausar tayi gaba harda dan hadawa da gudunta dan kuwa fitsarin kiris yarage yafara zubowa,
"A lokacin data fito daga k'ewayan sai taga gaba daya hanyar ya canza mata kasancewar ya kasu kashi uku tarasa ta wacce ta biyo zuwa wajan dan lokacin datazo a rude take fitsari ya sha mata kai, nanfa ta shiga rud'u " A rikice ta dubi dattijon dake can gefe a zaune tace dan Allah baba ta ina na biyo nazo nan? Wani irin duba yai mata yace yarinya tayaya zanyi insan ta inda kika biyo? Tace wallahi baba hanyar ce ta rikice min naganta har uku, yace to ai duk wacce kika bi aciki zata kaiki har cikin tashar duk daya ne, ya kauda kansa gefe tamkar bashi yai maganar ba, jiki a sanyaye kausar ta dubeshi tace to baba nagode, daga haka bata kuma cewa komi ba ta nufi daya daga cikin kwanar wacce tana tunanin itace hanyar data biyo..............
Fido sodangi🍃
Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 3:56 PM] +234 813 502 2313: [7/5, 11:53 AM] fiddausi sodangi💅: 🍃KAINE GATANA🍃
5⃣to1⃣0⃣
NA FIDDAUSI SODANGI
©TASKAR MARUBUTA📝
*********BARKA DA SALLAH******
Dafatan kunyi sallah lfy ubangiji Allah ya maimaita mana Ameen, Allah ya sa ibadarmu karb'abbiya ce Ameen,
"Nagode da sak'onnin gaisuwarku danaketa samu ubangiji Allah yabar kauna SODANGI tana kaunar masoyanta tana kuma baraba dasu akoda yaushe😘
***************************
" Wai kai Aliyu sai yaushe zakaima kanka fada ne! Ace wai kayi aure amman kullum saikazo ka matsa min dazancan abinci? Kuma dan tsiya kace kai bazakaci na yan aiki ba sai wanda na girkawa abban ku shizakaxo ka saki jiki ka cinye! To ka bude kunnuwanka kaji ingaya maka daga yau sai yau kar ka kuma zuwa ka hau dinning table dinnan dasunan cin abinci ka ringa tsayawa can gidan ka kana cin na matar ka kaji nagaya maka! "Abincinsa kawai yake ci cikin natsuwa batare daya ce mata kala ba, inda sabo yasaba da gorin da mahaifiyar tasa ke masa akan abinci Amman shikam bai iya yin zuciya, " Dariyar da Umar Faruq yake ta rikewa tuntuni ne ta subuce masa yaringa yi yana karawa, wani irin mugun kallo Aliyu ya watsa masa hade da kara tamke fuska ba shiri ya hade dariyar tasa dan yasan halin yayan nasa, " murmushi kawai abban nasu yakeyi yana duban kowa d'ai d'ai,
"Adai dai lokacin da mai gadi Malan iliya ya danni kararrawar falon inda daya daga cikin yan aikin gidan taje kofar ta bude suka gaisa da Malan iliya yace hajiya na kusa kuwa? Tace eh bari ai mata magana, ta koma cikin falon cikin natsuwa ta isa gaban hajiyar tadan duka tace hajiya Malan iliya ne ke magana, cike da murmushi tace to kice masa ya shigo, dasauri ta koma ta gaya masa, shugowa yayi hade da doka sallama, ya dan d'uk'a ya gaida su kansa a d'uke yace hajiya wata yarinya ce a waje take niman taimako yarinya ce karama da alama bacewa tayi sai kuka take tayi gwanin ban tausayi shine nace bari in gaya maku ko za a iyayin wani abu akai, cike da tausayi hajiyar ta dubesa tace jeka ka shigo da ita, dasauri ya mike yafice, takai dubanta kan fuskar abban wanda shima dubanta yakeyi, cikin fuskar tausayi tayi masa magana da ido dasauri ya kawar da fuskar sa yana duban wani waje daban,
"Sallamar malan iliya ya katse masu abinda suke gaba dayan su suka kai dubansu wajan, wani irin bala'in wari ne ya dume falon kausar wacce hawaye da majina yayi dabe dabe bisa fuskar ta saboda tsabagen kukan datasha, a firgice Aliyu da umar suka mike lokaci daya suna toshe hancin su kakarin amai Umar Faruq yasoma da gudu yayi hanyar wata yar k'wana saikace wani dan yaro karami, ido suka bisa dashi dukkan su, jiki a sanyaye Aliyu ya koma ya zauna, haryanzu hannunsa d'aya na nan toshe da hancinsa fuskar nan tasa tamkar wanda aka aikowa da mutuwa,
" Abban ne yace shikenan Malan iliya jeka abinka, godiya yayi ya fice yana maiyimasu saida safe, tasowa hajiyar tayi ta kamo kausar dukda tsananin warin dake fita a jikinta hakan baihana ta rungumar taba tana dan bubbuga mata bayanta alamar lallashi, ajiyar zuciya kawai kausar keyi saboda kukan data sha koma ince take kansha, baki kawai Aliyu ya bude yana bin mahaifiyar tasa da kallo abin na bashi mamaki wannan wani irin tausayi keda mahaifiyar tasa? Ganin babu mai basa amsa yasashi mikewa toshe da hanci yana fadin saida safen ku abba nina tafi, abban ne kawai ya amsa masa banda mahaifiyar tasa wacce gaba daya hankalinta nakan kausar,
"A hankali ta dago kan kausar tace yasunan ki? Sunana kausar, "wow suna mai dadi kausar! Nikuma sunana hajiya nafisa amman yarana suna kirana da mummy inafata kema zaki ringa kirana da hakan? Kai kawai kausar ta daga tana kallon mummy, abba ne yace yau naga ikon Allah nafisa daga ganin sarkin fawa kawai sai miya yayi zak'i ikon Allah sai kallo hararar wasa mummy ta watsa masa hade da fadin kaidai kasa ido kai kallo Allah ne yakawo min y'a har cikin gida na nikam Allah yatayani rik'o "wai ke nafisa wace iri ce ke daganin yarinya ance ta bace kawai ke bakya tunanin a nimo inda iyayanta suke a hadasu da y'arsu kawai saikice wani wai kinyi y'a ina kika taba ganin anyi haka? Adan zafafe yake maganar, "haba abban su wai meyasa kake haka ne? Hmm! Yayi k'wafa kawai ya nufi hanyar zuwa d'akinsa abinsa, ido kawai mummy tabishi dashi har ya bacewa ganinta,"a hankali ta maido dubanta kan kausar wacce itama tabi abban da ido dukda bata fahimci abinda yake fada ba saboda gaba daya magan ganun dasukeyi da turanci sukeyi ita kuwa kausar baji takeba balle ta fahimta, mummy tajawo hannunta tanufi d'akin ta da ita........
Fido sodangi🍃
Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
HAPPY SALLAH😘
[12/5, 3:56 PM] +234 813 502 2313: [7/6, 8:17 AM] fiddausi sodangi💅: 🍃KAINE GATANA🍃
1⃣0⃣to1⃣5⃣
NA FIDDAUSI SODANGI
©TASKAR MARUBUTA📝
"Alhaji Muhammad Sadiq K'urfi shahararran d'an siyasan nan wanda ahalin yanzu shine mataimakin governor katsina, mutumin kiirki ne wanda duk tarin dukiyar sa baisa yazama mai girman kai ba, yana da tsananin tausayin talaka kuma sam bai yarda da cutaba yana iyakar kokarinsa wajan ganin ba a tauyewa kowa hakkin saba, mutum ne mai imani da tsoron Allah kowa yabonsa yakeyi shiyasa akoda yaushe k'ofar gidansa ba a rabashi da jama'a yan niman taimako, "yanada matar auran sa guda d'aya tal wacce tazame mashi uwar y'ayansa maza guda biyu watau Umar Faruq dakuma Aliyu gadanga kusar yaki!
"Matar sa nafisa mutuniyar kirkice wacce saboda tsananin tausayin ta dakuma kyautatawa y'an uwan mijin nata yasa suke bala'in kaunar ta tamkar su lashe ta, shiyasa mijin nata