Showing 18001 words to 21000 words out of 23188 words
Chapter 7 - KAI NE GATANA BOOK COMPLETE DOCUMENT BY FIDDAUSI SODANGI .txt
kwalarsa yana fadin nizaka tozarta Ali! Irin tarbiyyar danabaka kenan Aliyu?" Kai ranan Aliyu yasha mari da zagi na fitar hankali daga karshe mummy ta karbe tayi tayi itama tamkar zata ari baki, fuskar sa duk ta kumbura da mari, kausar kuwa dadi tamkar ya kashe ta ita aganintama wannan ai yayima Ali kadan, batasan me zatayi masa a duniya ta huce ba amman tasha alwashin cewa saita rama kota halin k'ak'a!
"Umar Faruq dai sai binsu da ido yakeyi shikam wannan abu na matukar d'aure masa kai ya matsu yaji meya sameshi haka ne?" A daya bangaran na zuciyar sa kuma yana tunanin k'anwar sa da baban sa!
"Bayan komi ya lafa ne abba ya dubi Umar Faruq yace ka gafarce ni d'ana yanzu zakaji abinda yafaru,
"Shakara goma sha biyar data wuce a wata safiyar jama'a a hanyata ta zuwa k'urfi nida d'ana Aliyu muka sami hatsarin mota a hanya idan baka manta ba kaida mahaifin kane a cikin motar yana tuki kai kuma kana gaba to inajin motar ce ta k'wace masa daidai lokacin nikuma na taho da gudu to idan Allah yakawo tsautsayi babu yanda za ayi, Allah yariga ya hukunta, nasami karaya a k'afata da hannuna inda d'ana Aliyu kuma hannunsa na dama ne ya k'arye, mahaifin ka kuma Allah yayi masa rasuwa kai kuma kasami juyewar k'wak'walwa inda likita yasanar mana cewa ka mance da duk wani abu daya faru dakai a baya illa sabuwar rayuwa dazaka fuskanta, saidai akwai yuwuwar dawowar hankalin ka zuwa wasu shekaru masu yawa wanda shi kansa bazai ce gasu ba,
"To bayan ka war ware ne na d'auko nadawo dakai gida na ina rike dakai har zuwa yanzu bayan mun saka maka suna da Umar Faruq! Munyi iya binciken mu dan gano dangin ka amman wallahi sam hakan bai samu ba bamu taba jin wanda yace yasan kaba, gaba daya dai abba yafada masa komi bai boye masa ba harda abinda Ali yai masa bai rage ba!
"Nanfa Umar Faruq yashiga kuka wiwi suna lallashinsa,dakyar suka samu yai shuru inda shima yasoma basu labarin sa kamar haka,
" Mahaifiyata Allah yayi mata rasuwa a wajan haihuwar k'anwata wacce tazamemin "SANYIN IDANIYATA! "muntaso nida kanwata a hannun matar baban mu wacce takasance mace ce mai son zuciya! Sam bama jin dadin zama da ita musamman ma k'anwata wacce takasance yar shekara hud'u a lokacin, ina tsananin kaunar yar'uwata dakuma tausayinta, haka matar baban nan tawa take azabtar damu gashi baban mu bashi da tacewa akanta sai abinda tace, ahaka dai har na kammala karatun secondary school dina anan cikin garin dutsanma din inda nasamu admission a umaru Musa yar'adua university, to a lokacin da hatsarin nan ya afku muna kan hanyar mu ne nazuwa can makarantar domin infara registration, munbar matar babana a gida tare da k'anwata gashi kuma Allah yayima baba rasuwa ya fashe da kuka mai tsuma zuciyar mai saurare, hakuri d'uka suke ta bashi tare dayima iyayan nasa addu'a,
" kausar wacce taji tausayinsa ya bala'in kamata atake tasoma kuka tana tuna rayuwar ta itama dayanda ta bar goggon ta itama a garin dutsanma, nan tace yaya Umar Faruq ashema garinmu daya nan yayi mamakin ashe basu abba suka haifetaba, abba ne yabashi labarin ta itama ya tausaya mata matuka sai tunanin k'anwar sa yadawo masa d'anye yana tuna ko a wani hali take yanzu a hannun wannan azzalumar matar oho! Nanda nan hankalin sa yayi garin dutsanma yanaso yaje yaga a wani hali k'anwar sa take,
"Atake ya shaida ma abba k'udirinsa tare dayi masa godiya bisa d'awainiyar dasukayi dashi har yazama wani a yau! " abba yace kayi hakuri umar ka kara warwarewa sai mutafi gaba dayanmu mudubasu ina gani hakan zaifi, nanfa umar yace shifa alanbaran bazai iya kara k'wana batare dayaga k'anwar saba gaskiya! "A dole suka shirya gaba dayansu cikin k'atuwar motar abba suka d'au hanyar dutsanma........
Fido sodangi🍃
Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 5:44 PM] +234 813 502 2313: 🍃KAINE GATANA🍃
1⃣2⃣5⃣to1⃣3⃣0⃣
NA FIDDAUSI SODANGI
©TASKAR MARUBUTA📝
"Sunshiga cikin garin dutsanma da misalin k'arfe sha biyu da rabi na rana, nan danan hankalin kausar yai bala'in tashi zuciyar ta tahau bugawa tana tunanin haduwar ta da goggonta dan kuwa abba yace har can gidan zasu domin su sadu da dangin kausar din, " har abada kamannin garin nasu bazai taba sauya mata ba, duk da ci gaban da aka samu na karin gine gine dawasu sauye sauye, zuciyata bugawa kawai yake tamkar zai fado k'asa,
"Shi kuwa Umar Faruq wani irin farinciki ne ya lullube masa zuciya, awani bangaran kuma yana danjin faduwar gaba dan bai san a halin dazai tarar da kanwar tasaba,
"Shike zaune a gaba da abba dan haka shike nuna masa hanya, "mamaki ne yakama kausar ganin sun tsaya cak a k'ofar gidan su, ido ta zaro itakam tsoron shiga gidan nan take, towaima ya akai ya Faruq yasan gidan su?" Tambayar datakeyiwa kanta kenan, mamaki bai gama kamata ba sai da dukkansu suka sauko daga motar taga ya Faruq ya nufi k'ofar gidan yana doka sallama, hannun mummy ta matse da k'arfe cikin nata tana sauke ajiyar zuciya,
"Muryar goggo sukaji cikin fada tana fadin waye haka yake doka min sallama kamar naci masa bashi ban biya ba!" Gaban kausar ne yayi bala'in faduwa jin muryar goggo, shi kuwa Umar Faruq zuciyar sace ta tsinke yana fadin haryanzu dai tananan da bakin halinta!
"Goggo ce ta karaso tana kallonsu d'aya bayan daya,kafin ta tsada idonta akan Umar Faruq, cikin wani irin kid'ima da rawar murya take furta kalamar nasuruuu!!!!!!!!!!!! " A tsorace take ja baya tana nuna Umar Faruq, "dama kana raye baka mutuba?" To ina mallan yake?" Wayyo ni talatu naga ta kaina dama kuna raye tsawon wannan lokacin kuka yada ni?! Sai kuma tasaki kuka mai k'arfi tana ihu, "ganin zata tara masu jama'a ne Umar Faruq yace abba mu shiga daga ciki, gaba dayansu suka shiga banda kausar data saki hannun mummy ta kame a bakin k'ofa, mummy tace muje mana hawaye na bin idonta ta girgiza ma mummy kai alamar bazata ba, wata kod'add'iyar tabarma goggo ta shimfid'a masu tana fadin bisimillan ku, d'uka mazan suka zauna akai abba ne yakai dubansa kan mummy dake ta fama da kausar yace nafisa meke faruwa ne?" Abban su kausar ce taki shigowa wai ita tsoro takeyi ni narasa tsoron me takeyi haka ji yanda jikinta ke rawa fa, abba dakansa ya mike ya kamo hannun Kausar suka shigo ciki, ido goggo ta tsare kausar dashi sai dai sam bata ganeta ba kamace kawai acewar ta, kai nasiru ina Malan?" Ina kabaro shi ne?! "A hankali Umar Faruq yace Allah yayima Malan rasuwa nan dai yabata dukkan labarin da abba ya bashi, aikuwa atake goggo tasaka ihu tana fadin shikenan tashiga uku ta lalace sai kace wata arniya, aikuwa nanfa mata suka fara cika gidan ana tambayar ta ko lafiya?" Kuka take tana fadin Ashe Malan mutuwa yayi Allah yayiwa malan rasu hatsarin mota sukayi Ashe shida nasiru ga nasirun nan yanzu suka iso shida mutanannan yake fada mani, tasake sakin wani sabon kukan tana jan hanci,
"Nandai akaita jajanta mata saikace a lokacin abin ya faru, " babar rahane kawar kausar wacce suka tafi birni atare idan baku manta ba tace ohhh! Allah mai iko to kuma ina shi nasirun ya gano kausar ko ba ita bace wannan ne dannaga wannan y'ar gayuce dukda dai shima nasirun yazama d'an gayu dakyar na shaida shi?" Goggo tasake kallon kausar wacce gaba daya jikinta k'yarma yakeyi tace A'a ba ita bace kamace kawai waccan y'ar iskar ai izuwa yanzu nasan ta mutu tunda yawon karuwanci tasaka agaba! Yanzu kuwa wannan ciwo na zamani ai baya k'yale tsinannu la'anannu fasikai! Ubansu yakece aini wallahi nagode wa Allah kullum godiya nake agaresa!
"Cikin muryar kuka kausar tace wallahi nice goggo wallahi ba yawon karuwanci najeba! Tafada tana mai fashewa da kuka mai ban tausayi, ido goggo ta zaro tare da mikewa ta k'arasa inda Kausar take kafin mummy ta ankare harta shake kausar tana jibga duk kuwa data tsufa duk wahala ya mokad'ar da ita, dasauri mummy ta shiga tsakaninsu tana mai mamakin meke samun tsohuwar nan ne?"
"Izuwa yanzu k'wak'walwar Umar Faruq na niman rikicewa wai meke shirin faruwa ne haka?! Yana fata dai ba k'anwar sa bace wannan?" Mikewa tsaye yayi domin ya k'ara tabbatarwa yace goggo talatu ina k'anwata kausar take?!
"Gatanan kuwa kana gani a gabanka tashiga yawan duniya gatanan tazama bak'ar baturiya ai duk wanda yaga wannan yasan babbar yar bariki ce! " aishi Allah ba azzalumin bayinsa bane saidai Wanda ya zalinci kansa! Sakaiyace da hakkina ke bibiyarta! Ki fice kibar min gidana kada kisaka min d'aud'a a cikin gida!
"Basu ankara ba kawai ganin Umar Faruq sukayi ya yanke jiki ya fadi, gaba daya su abba suka Mike suma a rikice dan izuwa yanzu suma sun fahimci abinda ke faruwa, tofa! Ana wata gawata kenan, ..........
Fido sodangi🍃
Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un! Zanyi amfani dawannan damar domin in mik'a sakon ta'aziiyata ga iyalan marigayi Alhaji Ibrahim Kaduna! Da rashin d'ansu Nasir dasukayi, ubangiji Allah yajikansa yasa ya huta, Allah yayi masa rahama yasa mutuwa yazamo hutu agaresa, Ameen! Allah yakara mana hakuri da dangana Ameen!😭
[12/5, 5:44 PM] +234 813 502 2313: 🍃KAINE GATANA🍃
1⃣3⃣0⃣to1⃣3⃣5⃣
NA FIDDAUSI SODANGI
©TASKAR MARUBUTA📝
"Basu ankara ba kawai ganin Umar Faruq sukayi ya yanke jiki ya fadi, gaba daya su abba suka mike a rikice dan uzuwa yanzu suma sun fahimci abinda ke faruwa. " innalillahi wa'inna ilaihirraju'un! Kalmar da abba ke furtawa kenan, a rikice Aliyu yayu kansa wanda tun zuwansu yaketawani yatsine fuska yana cin magani dakyar ya zauna akan tabarmar dama shi ala dole d'an gayu bayaso ya bata jiki, shikam badan abba ya matsa ba aida baiga abinda zaikawoshi wannan k'auye ba acewar sa kenan.
"Ruwa aka dibo masa adan kofi ya dan diba ya yaiyafa masa a fuskar sa nandanan yai ajiyar zuciya sannan ya fashe da kuka yana fadin wannan wace irin rayuwa ce ace mutum ya auri k'anwar sa ta jini baisani ba! Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un! Allah nagode maka dakasa kausar bata tare a gida naba Allah kaine abin godiya,
" kausar wacce ke kuka tamkar ranta zai fita ta fada jikin umar Faruq tana fadin Ashe banyi karya ba danake cewa KAINE GATANA! ashe da gaske kai gatan nawa ne! Allah nagode maka daka kara hadani da d'an uwana a karo na biyu, a hankali yake bubbuga bayanta alamar rarrashi,
"Goggo ce taja wani mugun tsaki tana fadin aikin banza aikin wofi anje angama tambadewa za a wani fake da zancan dababu gaira ba dalili! "Alhaji da hajiya dan Allah Ku tashi kubar min gidana dan ina ganin d'an mutuncinku tun wuri gara ku fice kafin rashin mutunci na yatashi! " kafin ma ta rufe baki mak'otanta dasuka cika gidan kowa ya fara ficewa d'aya bayan d'aya dan sun riga sunsan halinta tunda ta furta hakan,
"Umar Faruq zaiyi magana abba ya d'aga masa hannu alamar dakatarwa, nan sukayi ma goggo sallama suka tafi abinsu tace yadai fiye maku inga dan shegen dazai kuma dawo min gida! Kuje can ku karaci gantalinku mutanan banza da wofi kawai! " taci gaba da masifar ta tamkar suna wajan,
"Haka su abba suka tafi da mamakin halin goggo, Umar Faruq yace ai abba wannan kad'an ne daga halin ta! Mummy tace to umar wai bakuda wasu yan uwa ne kuma?" Ina nufin dangin baban ku kona maman Ku?"
"Ajiyar zuciya kawai yayi idanuwansa cike da hawaye yace mummy bamuda sauran dangin mu wayanda suka rage, dama baban mu su biyu ne shida Yayan sa, kuma a shekarar dana gama makaranta Allah yayi masa rasuwa, ita kuma maman mu dama ita d'aya iyayanta suka haifa kuma Allah yayi masu rasuwa tun tana raye, " cike da tausayawa mummy ta kara jawo Kausar a jikinta,
"Aliyu dai bazan iya cewa ga yanayinsa ba wayar sa kawai yaketa latsawa, tamkar babu shi a cikin motar, (miskili kafi kare ban haushi, Aliyu Haydar kenan,Ali Jan zaki, Ali Jan rina ba nama ba, Ali gadanga k'usar yaki!)
"BAYAN K'WANA BIYU"
**************************
"Aliyu nizaka maida mutumin banza! To wallahi tallahi baka isa ba! Kayi kadan ka wulakantani wajan mutanan dake ganin mutunci na da kimataba! Yarinya tsawon wata biyu ka korata gida batare dawani daliliba?" Sannan ubanta yanata kiranka kaki kaje balle yaji me kake ciki game da y'arsa! Waikai Ali sai yaushe zakayi hankali ne ace kullum kana girma amman iskancinka karuwa yake amaimakon ya ragu to wallahi nabaka nan dazuwa anjima kaje ka maida matar ka idan ba haka ba zaka gamu da bacin raina! Kaji na gaya maka kenan wuce kabani waje mutumin banza kawai!
"Dasauri ya kalli abba yana kokarin yimasa bayani amman ina abba ya daka masa tsawa fice kabar min gida nace!!! Jiki a sanyaye Aliyu ya fice wai shi dan Allah meyasa yanzu abba sam bayayi masa uzirine?" tunsanda ya kashema Kausar aure abba yake nuna masa halin ko inkula, shi anashin ganin aima shahada yayi tunda badan yayi haka ba kila da yanzu kausar din nacan da cikin yayanta ajikinta, shikam ai godiya ma yaci aimasa bawai aringa nuna masa tsana da tsangwama ba haka! Shikam dole ma ya auri kausar kodan yakawo shiri tsakaninsa da iyayan sa!..........
Fido sodangi🍃
Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 5:45 PM] +234 813 502 2313: 🍃KAINE GATANA🍃
1⃣3⃣5⃣to1⃣4⃣0⃣
NA FIDDAUSI SODANGI
©TASKAR MARUBUTA📝
"BAYAN WATA UKU"
Kausar ce ke kuka tamkar ranta zai fita, tsugunne take a gaban Umar Faruq wanda ya hade rai tamkar baitaba dariya ba, "yaya dan Allah kayi hakuri bazan kara k'watanta hakan ba, amman wallahi yaya harga Allah banason ya Aliyu zuciyata kwata kwata babu kaunar sa aciki! Idan aure kake bukatar inyi yaya kabani nan da wani d'an lokaci wallahi zan fiddo dawanda nake so amman nikam bana son ya Aliyu!
"Cikin kakkausar murya ya kira sunanta kausar!!! Kalleni! " a sanyaye ta d'ago kanta tana kallon cikin idonsa, ba shawarar ki nake nima ba! Bakuma ra'ayinki nakeson jiba! Haka kuma ba zabi nabaki ba! Bakuma so nake inji kina sonsa ko baki sonsa ba no! Niba haka nakeba! Niba butulu bane! Bankuma iya son zuciya ba!
"Ke yanzu ba abin kunya da takaici bane ki iya duban tsabagen idon mummy da Abba kice wai ke baki son d'ansu ba! Ai ko basu fada ba dole zasuji zuciyar su babu dadi ace duk halarcin dasuka yi maki ki guji jininsu, kokuwa dan kinga sunayi maki haka saikiyi tunanin son Aliyu ne ke basuyi?" Wallahi ko d'aya suna tsananin son d'ansu da kaunar shi kawai dai suna mana alkunya da kara ne! Dan haka idan mafarki kikeyi maza ki farka kuma yanzu bada bata lokaci ba inaso kije maza ki basu hakuri kuma ki gaya masu cewa kin amince da auran Aliyu idan bahaka ba Wallahi wallahi sainayi bala'in saba maki! Tashi kibani waje sakarya kawai!
"Jiki a sanyaye tamike zata fice, zonan! Ok zaki je masu kina kuka kenan saboda magana ta bata shiga kunnin kiba ko?" Dasauri ta goge idonta ta saisaita kanta kafin ta fice, yabita da kallon tausayi shikam bada son ransa yaimata fada ba kawai dai hakan yakeso tayi domin kuwa basuda abinda zasu sakawa wayannan bayin allan dashi.
"A cikin wata ukun nan sunyi bala'in shakuwa shida k'anwar tasa shakuwa irinta jini sam baya son bacin ranta yanzuma dan ya zamar masa dole shiyasa kawai yayi mata haka dan yanata lallashinta tana wani botsarewa, yasani sarai Aliyu bai kyauta ba to amman yaza ayi da ikon Allah hakan ai shine alkairi agaresu baki d'aya,
"Mummy da abba ne zaune a cikin falon abba din, yayinda Aliyu yake zaune akasa yawani sunkuyar dakai kamar wani munafuki, da alama fada ake masa, " dai dai lokacin kausar tayi sallama ta shigo gaidasu tayi sannan taje kusa da Abba ta zauna kanta na a k'asa, Aliyu ne ya harareta tare da fadin ke ni bazaki gaidani ba?! Ga sa'an ki ko?" Saida ta fakaici idon su mummy sannan ta hararesa tare da murgud'a masa baki tace ina k'wana ya Haydar?" Shuru yayi mata tareda yin k'wafa, wannan ai rashin kyautatawa ne Aliyu yaya kace yarinya bata gaida kaba kuma ta juya ta gaidakan kaimata banza waikai wani irin tsiya ne akanka ne k'wanannan ne?" Fad'an fa damuke yi maka kenan fa yanzu! Hmm! Nafisa wannan d'an naki saike aidama ke ce kika sangartashi! Murmushi kawai mummy tayi,
"Abba yace y'ata ya akayine naga kamar akwai magana a bakin ki ko?" K'ara sunkuyar da kai k'asa tayi tace Abba dama nazo inbaku hakuri ne kuma in shaida maku cewa na amince da auran ya Aliyu kuma kumaku yafe masa dan girman Allah!
"Farinciki mara misaltuwa ne yakamasu har suka kasa boyewa, mummy tajawo kausar jikinta tana fadin Allah yayi maki albarka y'ata shima abba addu'a yaketa yi mata yana saka mata albarka, " shi kuwa gogan sai wani murmushi yake yana wani kallonta k'asa k'asa,
***************************
"Tofa biki kam ya kankama shagali akeyi babu kama hannun yaro, duk wani abu dayakamata mummy tayi tayishi itace uwar Amarya itace ta ango, shima Abba hakan ne ya kasance, shi kuwa Umar Faruq daya zama babban abokin ango kuma wan Amarya ai abin ba a cewa komi hidima kawai yakeyi sai kaiwa da kawowa yake tayi bashi nan bashi can!
" Amarya kuwa fuskarta babu yabo babu fallasa, tashirya duk irin zaman da mai gidan da matar sa suka zaba suyi da ita, a shirye take data taka duk wanda ya toneta, bazata ragawa kowaba! Haka taketa fada a zuciyar ta,
"Tayi kyau harta gaji tasha gyara yanda yakamata, mummy ta gyara y'arta tsaf dan tace sam babu wasa tunda gidan kishiya za a kai mata y'a gara taje da shirinta, dan bazata yarda y'arta tazama bora ba!........
Fido sodangi🍃
Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 5:45 PM] +234 813 502 2313: 🍃KAINE GATANA🍃
1⃣4⃣0⃣to1⃣4⃣5⃣
NA FIDDAUSI SODANGI
©TASKAR MARUBUTA📝
"Yau ya kasance ranan jama'a ranan d'aurin aure, bayan an sauko masallaci ne jama'a suka shaida d'aurin auran kausar da Aliyu Haydar, akan sadaki naira dubu ashirin, Umar Faruq ne yazamo waliyin amarya yayinda abba yazamo na ango, bayan an tashi d'aurin auran ne aka gudanar da walima