Showing 9001 words to 12000 words out of 19786 words
Chapter 4 - BABY ZUMA BOOK COMPLETE PDF BY Maryam Muhammad.txt
idanuwanshi, tsaki ya saki mtssww, sannan ya samu yai wankanshi, ya fito yana goge jikinshi da towel.
Gani ya yi Safnah tana ta bacci har lokacin, gaban mirror yaje ya gyara kanshi, sannan ya nufa wardrobe d'inshi ya duba wasu k'ananun kayan ya saka, yai kyau sosai.
K'aramin letter ya rubuta ma Safnah ta damin kud'in, ya ije mata, sannan ya d'auki key d'in motanshi ya fita a d'akin.
_________
Nadrah bayan ta idar da sallah ne ta zauna tana ta addu'oi har lokacin kukan be tsaya mata ba, Maman Shahid ne ta shigo hannunta d'auke da plate d'in abinci.
Da sauri tasa hannu ta share hawayen fuskanta, Murmushi ta sakar mata ta ce "Kin idar da sallah ne"? Gyad'a kai ta yi, Maman Shahid ta ce "Zoga abinci kici kinji" Nadrah ya mutse fuska ta yi tana girgiza mata kai, Maman Shahid ta d'an had'e fuskarta ta ce "Nace miki kizo kici abinci, idan bazaki ci ba to zanyi fushi dake", ta fad'a tana ije plate d'in abinci fuskanta a had'e, Nadrah gani ta yi bata kyauta mata tasan tunda suke a rayuwarsu ba wanda yasan damuwansu ko suna kuka ya lallashe su itace kawai suka sami kulawanta a wannan lokacin da suke neman mai kulawa dasu, tasan cewa Mommansu baza ta b'ata kulasu ba ko kwana d'ari zasuyi basuci abinci ba kanta kawai ta sani.
Ganin zata fita a d'akin ne da sauri ta ce "Toh zanci abincin", jin haka Maman Shahid ta jiyo fuskanta d'auke da murmushi sannan ta d'auko plate d'in abinci taje kusa da ita ta zauna ta fara bata a baki, bud'e bakin ta yi ta amsa ta faraci, duk da jin abincin ta yi yana mata d'acin magani haka take amsa bata saton ta sab'a ma Maman Shahid ne kawai yasa take ci.
Yana isa gidan ya shiga parlorn yaci sa'a kuwan ba kowa a Parlorn da sauri ya haura Upstairs zuwa part d'inshi.
Yana shiga ya zube a kan bed rufda ciki yanajin wani sha'awan na k'ara taso mishi jusa kanshi ya yi a pillow yana jujjuya kanshi kaman zautacce gashi ya kasa mantawa da suran Nadrah shidai yasan ba sonta yake ba, bata da abinda zaiso a jikinta, yasan a yanzun duk duniyar nan, ba wanda ya tsana kamarta, ga jarababben sha'awanta dake damun shi yarasa mai yasa yake jin haka akanta, nishi ya sauke a zuciyarshi ya ce "Dama banganta ba, gashi tazamomin fitina", dafe maranshi ya yi yaji tauri kaman dutse, runtse idonshi yayi gaba d'aya tak'i b'ace mishi a fuskanshi, ya yi k'ok'arin mancewa da ita amman ina kaman k'ara tuna mishi ita a keyi.
Da sauri ya mik'e, yaje Parlornshi, ya bud'e fridge ya d'auko k'an k'ara, yasan shine kawai zaisa yaji sauk'in abinda ya keji, yana d'auka ya kwanta a kujeran Parlorn, ya d'aura k'ank'aran a maranshi, yana yawo dashi a hankali, nishi ya sauke tare da fitar da iska a bakinshi, jin sauk'in da maranshi ya fara mishi.
_______
K'aran ringing d'in wayarshi ne ya tashe shi daga baccin da ya fara d'aukanshi, a hankali ya mik'e, Alhamdulillah maran nashi ya fad'a mishi, sai dai Ayabarshi bata gama kwanciya ba, tashi ya yi a hankali ya shiga bedroom d'inshi, ya d'auki wayarshi dake ta faman ringing, Amminah ya gani a screen d'in wayartashi, da sauri ya d'auka, cikin wayar akace, "Son wai har yanzun baka dawo bane"? A hankali ya ce "Ammi na dawo bara na sauko, bai jira mai Ammi zata ce ba ya kashe wayar.
Sai da yai wurin minti 10 sannan ya sauko downstairs sai baza k'amshi ya keyi.
A dinning table ya samu mesu dukansu harda Daddy, amman banda Granny domin ita ta fison akai mata abincinta part d'inta, Daddy yana ganinshi ya bud'e hannunshi yana "Oyoyo my son", Murmushi Areef ya sakar ma Daddy sannan yaje yai hugging d'inshi, yana gaidashi, shafa kanshi ya yi sannan ya amsa gaisuwar yana tambayan ya na lafiya koh?, Gyad'a mishi kai Areef ya yi yaja d'aya daga cikin kujeran dinning d'in ya zauna.
Jan kumatun Iftee ya yi ya ce "My little girl naga kin k'ara kuma tune"? Iftee ta ce "Oushhhh Ammi Yaya Areef zai ciremin kuma tuna", Ammi ta ce "My son saketa karka cire mata kumatu", dariya ya yi yana sakin mata kumatun, ya ce "Ammi kinga idan nacire mata kumatun sai asamata na mage ko"? Da sauri Iftee ta ce "Ya Areef ni banso please", tai kaman zatai kuka don Iftee batasan mage ko kad'an.
Areef ya ce "To sorry my sweet girl, "Daddy ka bata hak'uri pls" Murmushi Daddy ya yi ya ce "Ai kunfi kusa kai Babynnaka".
Dariya su kayi dukansu sannan suka fara dinner kowa fuskanshi d'auke da fara a.
_________
Bayan sun gama ne Areef ya wuce part d'in Granny.
Wata kyakyawar farar tsohuwa ce zaune a kan sallayar tana jan calbi, ta tsufa amman akwai kawunta tsantsa a fuskanta, kamansu ya b'aci da Daddy.
Ko sallama baye ba ya shigo d'akin ya zauna a kujera yana "Aushhh na gaji".
Kallonshi ta yi ta tsuk'e fuskanta ta ce "Kai d'an bazan yaro fita kaimin sallama ko ubanka bazai shigomin d'akin ba tare da izini na ba, balle kai jika ka shigo min kai tsaye abin takai cin ma ko sallama bakai ba".
Banza da ita ya yi ya lumshe idonshi, kamar ma besan tana magana ba a wurin.
Granny tashi ta yi da jikin tsufanta taje gabanshi, ta zula mishi calbin hannunta a cinyanshi, da k'arfi Areef ya ce "Aushhhh Granny meye haka"? Ya fad'a yana sosa inda ta zuba mishi calbin.
Granny had'e fuska ta yi ta ce "Uban kane, bani ka maida mahaukaciya ba tashi ka fita kaimin sallama, ko na k'ara zuba maka a shegen kannan naka da ko aski ba kayi", Areef yasan zata aika kuwan, ya tashi yana mata k'unkunai.
Ciki ciki yai sallaman kaman bazai motsa labb'anshi ba, amsawa ta yi tana "Da kar kayi mana da kaga aiki da cikawa kuwan".
Zama ya yi cikin had'e fuska ya ce "Ina wuni"? Shima ciki ciki, Granny ta ce "Da ban wuni ba ai baza ka ganni haka ba, ni zaka ka gaidar cike da miskilanci, wannan iskanci naka sai matar ka ai".
Marairai fuska Granny ta yi ta rik'o hannunshi ta ce "Don Allah wai yaushe zakai aure ne na k'osa naga matar ka muga yadda zata zauna dakai da wannan miskilanci naka".
Areef ya ce "Wai waya fad'a miki zanyi aure ne ni"? Granny ta ce "Haba jikalle na baka so naga matar kace kafin na mutu, ko saina mutu sannan zakai auren"? Dariya Areef ya yi ya ce "Granny karki damu ko kin mutu zan sa akai miki hoton matana har ka barinki, Granny ta tumke fuskanta ta ce "Kaci Ubanka Areefu niza kai ma isgilanci"?
"Kawai dan nadamu da kayi aure, inason naga matarka da tattab'a kunne na" Dariya Areef ya yi ya ce "Granny zanyi aure amman sai da sharad'i".
Granny ta yashe tsofen hak'ora yenta ta ce "Fad'in sharand'in Areefu ina jinka".
Areef ya ce "Saikin fad'amin idan anyi auren mai akeyi a cikin aure.
Dariya Granny ta yi ta ce "Abu mai sauk'i, zata dinga kulawa dakai kaima kana kulawa da ita, sannan kuna kyautata ma junansu kusan darajar kanku sannan ku......
Saurin da katar da ita ya yi ya ce "Granny nifa ba wannan nake miki magana ba nasan wa'ina, kawai inason ki fad'amin, ranar da aka kai maka mata bayan kunyi sallah kunci abincin, to mai akeyi a gado har kaji ana cewa mace tasamu ciki"?
Granny tsuk'e baki ta yi ganin tambayar rainin wayan da yake mata, ta ce "Ban gane ba", Murmushi Areef ya yi ya ce "Shikenan tunda baki sani ba kinga ba maganar auren kenan tunda baza ki iya fad'amin abinda a keyi ba nasani koda nayi aure nima nayi asamu cikin harta aifa miki tattab'a kunne da kike magana ba".....
[3/7, 9:41 AM] +234 803 231 7531: _Page 11&12_
Granny d'aska mishi duka ta yi a banyanshi ta ce "Areefu baka da mutunci wllh kaje ka tambayi uwarka Fatima ko Ubanka Wazreeu, bani zaka zo kana wa wannan tambayar ba", Areef dariya ya yi ya tashi yana ce wa"Tom nizan tafi duk lokacin da kika shirya fad'amin abinda akeyi idan anyi aure nayi auren kuma ke nake son ki fad'amin ba wani ba, tunda ke kika matsa akan nai auren, yanzun kuwan bazanyi aure ba sai na banzan sun..... Shiru ya yi ba tare da ya k'arisa zancen bakin nashi ba, yai hanya fita a d'akin yana dariya k'asa k'asa.
Granny sakin baki ta yi tana kallon Areef, cike da mamakin rashin kunyarshi, , cikin d'aga murya ta ce "Bara Wazreeun yazo anjima wllh saina fad'a mishi rashin kunyar da kake min, kuma zansa ya nemo maka matar aure da kanshi koma wacce irice ita, Areef shima ya ce "Wllh ko kin fad'a ma Daddy bazai tab'a yarda ba, kuma idan kina shakku ki fad'a mishi abinda nace miki, kuma maganar zaki sa a nemomin mata tazo tagani Wllh da k'afarta zata gudu ma.
Yana fad'in haka ya fice a d'akin yabar Granny da sakin baki.
Granny ta ce "Oh ni Maryam Allah ya had'ani da jika mara kunya"
Areef d'akin shi ya wuce don maganar nan da yai da Granny har ya farajin ciwon kai wllh, shi inba dole ba bayason magana mai tsaho, da itace daman kawai yake iya dogan magana, itama saboda surutunta akan yai aure ne.
_________
Yau ne ukun Abba, Alhamdulillah yanzun Nadrah ta fara dawowa yadda take, amman kullun wayarta a kashe yake, Yasir kullun sai ya kira amman wayar a kashe gashi be masan gidansu ba ya shiga damuwa da tashin hankalin ina zai ganta, don Nadrah kaf samarinta ba wanda tabari yasan gidansu.
Kullun Maman Shahid saita shigo da yake ga gida ga gida ne, Nadrah kuma ta fara sabawa da ita duk da itad'in bamai son mutane bane, amman harga Allah Maman Shahid ta shiga ranta, gashi a haife ta haifeta amman sun zama kamar k'awaye.
---------
Areef kuwan tun ranar idan ya kira Safnah bata d'aukar wayarshi.
Safnah a ranar kuwan tunda ta farka daga baccin wahalan daya d'auketa, ta kwashe kayanta ta saka ta d'auki kud'in da ya ije mata tabar gidan don ta ce duk sonda take ma Areef ta hak'ura dashi, daya kasheta da ranta gwanda ta rabu dashi gaba d'aya ita kad'ai tasan wahalan data sha a hannunshi.
Areef kuwan sha'awa ya sashi gaba, da daddare da k'er yake iya bacci ga tunanin nonuwan Nadrah sunki fita a idanunshi, gashi bai masan ina zai ganta ba, balle ya huce haushinta da ya keji dako da k'arfine wllh sai ya cita, tunda ta hanani sukuni a rayuwarshi gaba d'aya, tunda ya ganta komai nashi ya rikice mishi ga b'acin ranta duk yai mishi yawa, jiyake da zai ganta kasheta ne kawai bazaiyi ba, da irin cin da zai mata, ga Safnah bata d'aukar wayarshi balle ya rage zafi.
Ammi tana zaune a Parlorn, akai knocking k'ofan Parlorn, izini ta bada aka shigo, Salisu ne bodyguard d'in Areef, gaida ita ya yi sannan ya ce "Hajiya nasamo asalin wacce yarinyar da address d'in gidansu.
Ammi da sauri ta ce "Salisu da gaske"? Salisu ya ce "Eh Hajiya", Ammi ta ce "Yar wacece kuma a ina take, Salisu ya d'an ya mutse fuska sannan ya ce "Hajiya yarinyar fa, ba yar kowa bace asalima mutane da yawa sunce basu masan daga ina suke ba, sunce basu wuce 2 years da dawowa unguwar ba, ba wanda yasan asalinsu, don sunce min yarinyar ma kamar maza take bi, sunanta Nadrah Babanta ya rasu yau ake ukunshi, kuma bamasu kud'i bane kawai suna zaune a k'aramin gidane mai ciki uku da bayi biyu a ciki, kuma ita take biyan kud'in hayan gidan ma.
Ammi cikin had'e fuska ta ce "Ita harta ma isa tai ma son d'ina haka, daman matsiyaciya ce ma"? Salisu ya ce "Haka ne Hajiya tsiyatar ma harda karuwanci ta keyi".
Ammi ta ce "Salisu jira ni na d'auka Veil d'ina a upstairs, muje ka kaini gidan wllh yau sai ta yi kwanan cell ba ruwana da yau ne ukun Babanta.
Dad'i ne ya lullub'e Salisu koba komai zata gane kurenta kodan marin da tai mishi, Ya ce "To Hajiya a fito lafiya, Ammi ta haura upstairs da sauri.
Areef yana kwance a bed d'inshi, wayarshi ta fara ringing, dubawa ya yi yaga number abokinshi ne Yasir, d'auka ya yi ya ce "Sorry Yas", Yasir Murmushi ya yi wanda sautinshi ya fito har wayar sannan ya ce "Haba my Friend yau 3 days kana Abuja ko ne mana ba kai ba Ko"? Areef ya ce "Yasir nace maka sorry" Yasir ya ce "It's okay, yanzun kana inane"? Areef ya ce "ina gida", Yasir ya ce "Baka da lafiya ne kodai abunne ya motsa naji muryan so slowly"?, Ajiyar zuciya ya sauke "Eh" kawai ya ce "Yasir ya ce "Oh God, ina Safnah ko ba kayi waya bane da ita"? Areef ya tab'e baki kaman yana ganinshi ya ce "Itama ta gudu", Yasir ya ce "kaman ya itama ta gudu, How comes"?
Areef ya ce "Yas Kai kasan ba macen da take iya jurewa dani wurin sex, damun fara zakaga suna min kukan na kyalesu su sungaji, kuma baza ka k'ara ganin su ba, Safnah ce kawai take ita d'auka na to itama tun randa nadawo muka had'u yanzun bata d'aukan wayana, kuma kasan bazan iya kad'an ba na kyale ba abinda zai min.
Yasir ya ce "Ohh my friend sorry, yanzun meye solution akan wannan matsalan"? Areef ya d'aga ka fad'a kaman yana ganinshi, Kaman yasan abinda ya yi kenan ya ce "My guy akwai wata BABY ZUMA ina son ya yarinyar nan kaman raina, wllh ta iya harka sosai kuma bata tab'a gajiya idan kunayi ita kad'ai ce zata iya d'aukanka nasani, domin Baby zuma jaruma ce sosai gata da d'an k'aran dad'i Areef wllh ka d'an d'ana zumanta baza ka tab'a iya rabuwa da ita b.... Areef ya da katar dashi don baya son surutu ya ce "Ya take ya yanayi k'iran jikinta ya ke"?
Yasir yasan bayason mace mara k'iba sai katuwar mace.
Ya ce "Eh tana da k'ira mai kyau tana da manyan nonuwa kuma tana da manyan d'uwaiwuka sosai, sai dai bata da k'iba ne sosai, kuma gaskiya yarinya ce, baza ta wuce 18 years ba, amman tana da kayan alatu da kake so a jikin mace".
Yasir yasan yana ma Nadrah son gaskiya ne, amman yadda ya keson Areef ko matarshi ne ya gani ya ce yana so, wllh zai iya bashi ya cita muddin zai sashi farin ciki.
Tsaki Areef yaja mai k'arfi mtswwww, Sannan ya ce "Yas amman baka da hankali ko kad'an, manya mata wanda su keji da kansu sun kasa d'auka na sai kwailace zata d'auke ni"? Kar kasa na balla musu yarinyar mutanen, kuma ni kasan bani da ra'ayin mace mai irin shekarunta da k'iranta, inason mace katuwa ce mai manyan mala malai ba jarirai ba".
Yasir ya ce"Aboki wllh da gaske nake BABY ZUMA zata iya maka komai duk abinda kake so zatai maka, itama tana da su fa, ka gwada ka gani zaka ban labari".
Areef ya ce "Pls Yas mubar maganar nan, kawai nidai kasa momin irin wacce nake so don Allah, wllh a matse nake yau idan banyi ba akwai matsala".
Yas ya ce "Shikenan zan samo maka, bara na kira jamcy baby ko tana gari.
Kashe wayar Areef ya yi ba tare da ya ce komai ba.
__________
Ammi kuwan sai da suka biya police station don taho da motan yan sanda, zuwa gidan su Nadrah.
Address d'in da aka ba Salisu su kaje wato gidan su Nadrah, koda suka isa k'ofar gidan yan gaisuwa na fitowa daga gidan, ga jiniyar motan yan sanda ya cika ugunwar da k'ara ji kake wiwiii wiwiii.
Yan sanda fitowa sukayi daga motan, suka zagaye k'ofar get d'in gidan da bindigu, kamar sunje kama b'arawo.
Nadrah suna zaune a Parlorn suna amsan gaisuwan uku, su kaji jiniyar motan yan sanda a k'ofar gidan.
Da sauri suka fito har bakin get d'in, cike da mamakin me ya kawo yan sanda k'ofar gidan, Salisu ya na ganin Nadrah ya ganeta, duk da tasha hijab d'inta har k'asa ya ce "Ranka ya dad'e gata nan ya fad'a yana nuna Nadrah, Nadrah da mamaki ta kalli Salisu tana son ta tuna inda tasan fuska amman ta manta, cikin sanyin murya ta ce "Me nayi kuma da ake nunani"?.
D'aya daga cikin police d'in ne ya ce "Sai munje police station tukun zakiji abinda ki kayi".
Momma ta ce "Wllh baku isa ba ba inda zaku tafin min da y'ata meta yi to zaka ku tafi da ita har police station?".
Ammi ta ce "Ki tambayi munafuk'ar y'arki ita tasan abinda ta yi ai" ta fad'a tana cewa "Ku jata muje da ita ni suna b'ata min lokaci ma anan wurin".
Aikon janta sukayi har cikin motan tasu suka sata a ciki.
Nadrah gaba d'aya kanta ya kulle ita tasan ba abinda ta yi da har za azo tafi da ita wai har police station, Nafisa cikin kuka ta