Showing 15001 words to 18000 words out of 47407 words
Chapter 6 - GONAR SHARRI BOOK 1 COMPLETE by Billy S Fari And Hajja ce.pdf
yi musu special abinci ba sai
sunci jagwalgwalen Jauhar ba. Murmushi kawai Mommy ta sakar mata taci gaba da aikin kafin
Suhaila data dawo daga school tafito ta sameta aciki,
"Sannu Mommy, Wai yau meke damunki ne?" Sai da Hajja Maimoon ta juye kayan miyanta a
blender da zata markaÉ—a ta kunna sannan ta kalli Suhaila data ciro crackers daga cikin loka É—in
dake kitchen É—in ta haye carbinant tana ci tace,
"Ba lafiya kam Suhaila, gold É—ina na nema acikin gidannan na rasa!"
"What!" Suhaila tafaÉ—a tana zaro idanuwa, sai data tura crackers É—in acikin bakinta sannan ta
sake cewa,
"Mommy are joking? Toh waye zai É—aukar maki gold har cikin dakinki?"
"Tambayar da nayiwa kaina kenan Suhaila saboda Jauhar tace ba ita ta É—auka ba, kuma kinga
ita kaÉ—ai ke shiga É—akin nawa."
"Maganar banza, wallahi ita ta É—auka Mommy kawai tafito miki da abunki ko taci ubanta acikin
gidan nan, dama da ɓarauniya muke zaune Mommy?"
"Abunda nake tunani kenan, shiyasa na rufeta cikin É—aki har sai ta gaji ta fito min da abuna."
Hajja Maimoon tafaÉ—a tana kashe blender É—in dan kayan miyan sun markaÉ—u, da haka kuma
Mommy ta kammala aikin suna tayata fira. Tana gamawa tasa suka kwashe abincin suka kai
kan dining ita kuma ta gyara kitchen É—in sannan ta haye sama, wanka tayi tai sallar magriba
sannan ta sakko ta samu yaran a palour zaune suna kallo, Jannat ce ta É—ago kai tana cewa.
"Mommy wai gold É—inki aka É—auke?" Shafa kanta kawai Mommy tayi haÉ—e da neman kujera ta
zauna don gaba ɗaya ƙarfin halin yin komai takeyi, ɓatan gold ɗin ba ƙaramin tashin hankali ya
sakata aciki ba daurewa kawai takeyi tana yin abubuwa. Kusa da ita Jannat ta koma ta zauna
tare da É—ago kanta tana kallon fuskar Hajja Maimoon tace,
"Mommy sorry, Jauhar ce ta É—auke miki ko?"
Kafin ta tankata sai ga Daddy ya shigo, da gudu tamiƙe ta nufi wajensa tana yi masa oyoyo ya
rike hannunta suka ƙaraso ciki, sannu da zuwa Suhana da Suhaila suka yi masa ya amsa cike
da farin ciki kafin yakai kallonsa ga Hajja Maimoon dake yi masa sannu da zuwa yana cewa,
"Yawwa Mommyn Jannat, yau nasan nayi laifi ayimun afuwa." Ya faÉ—i hakan saboda rashin
dawowa gida dawuri da baiyi ba dan ba irin wannan lokacin yake dawowa ba, kullum ana gama
sallar la'asar yake dawowa gida amma yau wani aiki ya riƙesa bai dawo ba sai yanzu. Murmushi
ta sakar masa kafin tamiƙe ta nufi sashensa, tana jin Jannat na faɗa masa cewa Jauhar ta
É—aukewa Mommy gold, bata dawo baya ba tayi gaba abunta. Bai bi takan zancen ba har sai
bayan ta haÉ—a masa ruwa yayi wanka ya saka doguwar jalabiya ya wuce masallaci yayo sallar
isha'i ya dawo sun zauna cin abinci sannan ya kalli Jannat yana cewa,
"Jannat kika ce me? Me Jauhar tayi?"
"Gold É—in Mommy ta É—auke." Juyowa yai ya kalli Mommy dake É—an tsakurar abincin dake
gabanta dan ba da É—insa take ji ba yace,
"Mommyn Jannat wai da gaske ne?" Ajiyar zuciya ta sauke haÉ—e da cewa,
"To na nemesa na rasa Habiby, waye zai É—auka idan ba ita ba tunda ita kadai ke shiga É—akin?"
"Kin duba da kyau kuwa? kuma kin tambayeta ko ta sauya mishi wajen zama ne data je gyaran
ɗakin?." Ranta a ɗan ɓace take magana,
"Na duba ko'ina fa Ya Habiby, na kuma tambayeta amma ta tsaya tana yi min musu wai bata
É—auka ba, dan haka wallahi ko mutuwa zatayi a gidan nan sai ta fito min da gold É—ina kafin na
sake barinta ta shaƙi iskar wajen nan." Hannunsa ya miƙa ya ɗora saman nata ganin yadda
ɓacin rai ya taso mata lokaci ɗaya haɗe da cewa.
"Calmdown Mommyn Jannat, Jauhar É—in tana ina yanzu?" Sai data haÉ—iye wasu yawun bakin
ciki da tun ɗazu suka tsaya mata a maƙoshi hawaye na sakko mata tunawa da makudan kuɗin
data saka ta sayi gold ɗin da tsada dan shiga tsara amma wai ace yanzu ya ɓata sannan tace,
"Tana É—akinta na rufe ta dan babu inda zata je ban sani ba kota haÉ—a kai da wani taje ta bayar a
sayar min da abu."
"Kamar ya? Wai tun yaushe hakan tafaru ban sani ba?" YafaÉ—a cike da mamaki jin wai ta rufeta
a É—aki sai kace wata dabba,
"Tun da kafita." Ta bashi amsa a takaice tana wani turo baki,
"Subhanallahi shine kuma kika rufeta? Haba Mommyn Jannat mutunce fa kuma ki tuna muna
da Æ´aÆ´a, zaki ji daÉ—i idan aka yiwa Jannat, ko Suhana ko Suhaila hakan? Look koma meye kiyi
hakuri ki buÉ—eta abi abun a hankali kada azo a samu matsala yarinyar mutane tazo ta mutu a
hannun mu." Kuka Hajja Maimoon ta saka tare da miƙewa tana cewa,
"Wallahi ni bazan buÉ—eta ba sai tafito min da gold É—ina, kasan nawa nasa na siyashi?" Goshinsa
ya dafe haÉ—e da cewa,
"Oh my God! Kije ki buÉ—eta nace zamu yi magana daga baya Maimoon." Yadda yai maganar ya
alamta mata cewa ransa ya ɓaci, ba dan ranta ya so ba ta shiga kitchen ta ɗakko key ɗin taje ta
buÉ—e É—akin Jauhar tana barin wajen aguje tana kuka. Da idanuwa Alhaji Sha'aban Sada ya bita
yana kallo kafin ya maido kallonsa wajansu Suhana da ransu ya ɓaci ganin Mommyn na kuka
yana cewa,
"Suhaila je ki kira yarinyar." YafaÉ—a cike da damuwa shima. Wani kallon wulakanci Suhaila
tayiwa Jauhar da tana jin motsin buÉ—e kofar a tsorace ta tashi ta takure waje É—aya tana
ƙanƙame jikinta acan kusuwar ɗakin,
"Munafuka, ki taso Dady nakira kuma sai kin fitowa da Mommyn mu gold É—inta ko bakya so
ɓarauniya kawai."
Jiki ba ƙwari Jauhar tamiƙe wani irin jiri na ɗibarta saboda yunwa da halin da take ciki tafito tana
rabewa ajikin bango, tausayinta ne ya rufe Alhaji Sha'aban ganin yadda ta koma yace,
"Ƙaraso nan Jauhar." Sai data dudduba palourn taga Hajja Maimoon bata nan sannan ta saki
jikinta ta iya ƙarasawa wajen ta duƙa ƙasa yaran sai harara suke aika mata da ita tamkar
idanunsu zai faÉ—o. Cikin sigar rarrashi Alhaji Sha'aban yace da ita,
"A ina kika ajiyewa Mommynku gold É—inta har tayita nema bata gani ba?" Ba tare data É—ago
kanta ba tace,
"Ban ganshi ba Dady kuma wallahi bani na ɗaukar mata ba." Taƙarasa zancen hawaye na
sakko mata akan fuskarta.
"A'a Jauhar kiyi tunani tunda kinga ke kaÉ—ai ke shiga É—akin yi mata gyara ko kin gansa kin
sauya masa waje?." Sai alokacin ta É—ago kai tana kallon Dady har lokacin hawaye basu daina
sakkowa akan koÉ—aÉ—iyar fuskar tata ba da gaba É—aya tayi kama kalar aljanu saboda rashin
kulawa duk ta dushe in ba ga wanda ya santa ba tun farko tana cewa.
"Allah Dady ban ganshi ba, za'a iya sake cajeni agani ko a sake duba É—akina, wallahi ko kashe
ni idan za'ayi Dady bansan inda Mommy ke ajiye gold É—inta ba idan ba nagani a wuyanta ta
saka ba."
"Shikenan, tashi kije." Dady yafaɗa tare da miƙewa ya nufi sama wajen Hajja Maimoon ɗin.
Wani irin mugun ranƙwashi Jauhar taji Suhaila ta sakar mata da zata wuce akai tana cewa,
"Barauniya kin dai ji kunya wallahi." Suhana ta bangajeta ita kuma daga inda take ta faÉ—i tare da
wucewa abin ta. Jannat na zuwa itama tasa kafa ta takata ta wuce tana cewa,
"Beranya.."
Zuwa yanzu hawayen Jauhar sun fara ƙarewa, haka ma zuciyarta ta bushe da sam babu sanyin
dazai sata tausasa har taba idanuwan nata damar zubo da ƙwalla, hakan yasa ta miƙe ta wuce
É—akinta ta rufo tana addu'ar Allah ya kawo mata mafitar barin gidan kota samu Æ´ancin rayuwa
data rasa tun tana ƙarama.
Alhaji Sha'aban Sada kuwa a hankali ya tura ƙofar ɗakin Mommy ya shiga, tana zaune gefen
gado ya ƙarasa ciki tare da tsayawa agaban madubi ya ɗan jingina yana kallonta yake cewa.
"Yanzu meye abun kuka Maimoon da har zaki bari waÉ—annan tsadaddun hawayen naki su zuba
kuma agaban Æ´aÆ´an ki? Ina gold ne dai ko? Toh kibari zan siya miki wani, kiyi hakuri kibi abun a
hankali tare da saka mata idanuwa, idan har yana wajenta na tabbata zaki ganoshi amma to me
I don't think yarinyar nan ita ta É—aukar miki abu saboda na sake tambayarta ta tabbatar min da
batasan ma inda kike ajiyewa ba, a yanda kuma nasan kina daraja duk abinda kike so bana
tunanin zaki ajiyesa inda zata iya ganinsa." ÆŠago kai tayi tana tsaresa da idanuwa kafin tace.
"Me kake nufi? kenan kana goya mata baya kenan ko? bayan ni da kai da kowa ma na gidan
nan munsan ita kadai ce zata iya É—aukarsa. Jannat, Suhana da Suhaila duka nasan wannan ba
halinsu bane, be side ba abunda suka rasa daga wajen mahaifinsu balle suyi negative thinking
irin wannan, but Jauhar fa? I don't trust her at all, bana tunanin zata wadata da abinda take
dashi tunda ba tada gata irin nasu, asali ma da ita da babu duka É—aya ne a wajen mahaifanta
me zai hana tafara tunanin É—auke-É—auke." Iska Alhaji Sha'aban Sada ya ja ya furzar ta baki
haÉ—e da cewa,
"Ba goyon bayanta nakeyi ba, nasan itama baki taɓa cewa kin nemi abunki kin rasa acikin gidan
nan ba, zancen gata da kikeyi Allah fa shike gatanta wanda yaso, koda wannan É—abi'ar ta
Jauhar ce zan so ki ajiye duk abinda kike ji a zuciyarki da iyayenta suka yi ba dai-dai ba, ki
janyota ajikinki tamkar Æ´arki ki gatanta itama, hakan zai iya sa ta sauya kuma ta amfaneki nan
gaba ta hanyar mayar da alkhairi agareki akan sharrin da iyayenta sukayi miki, ƙaramar yarinya
ce ita Maimoon, mai yiyuwa bata masan abinda sukayi miki ba amma kina sauke fushinki
akanta which is wrong, very very wrong." Wani kallo take jifan Alhaji Sha'aban É—in dashi haÉ—e
da miƙewa tana kallonsa.
"Over my died body Habiby bazan taɓa ɗaukar Jauhar a matsayin ƴa ba a wajena balle har na
gatanta, yadda na tsani mutuwata haka na tsaneta da duk wani abu daya shafi rayuwarta,
halinta kuwa idan zaifi haka muni Allah ya tabbatar mata dashi ya sake lunka mata da wanda
yafisa, ni kuma akwai nau'ukan azaba kala-kala da zan tanadar mata har zuwa lokacin da zata
gudu da kanta tafice cikin rayuwata nima na huta." A yanzu ko kaÉ—an Alhaji Sha'aban Sada
baya mamakin duk wasu munanan kalamai da zasu fito daga bakin Hajja Maimoon akan
Jauhar, wanda hakan ke tabbatar masa da koma meye tsakaninta da iyayen yarinyar to
baƙaramin abu bane, sai dai hakan bazai zama hujjar da zata sa ta ɗauki fansa akanta ba.
"Shikenan, what ever dai wannan damuwar ta wuce please in sha Allah gobe zamu je na siya
miki wani gold ɗin kiyi hakuri kin ji ko?" Ya faɗa yana ƙarasawa yariƙota tare da janyota zuwa
jikinsa...
#A heart touching story
#Gonar Sharri..
#Hajja ce
#Billy s Fari
#Ƴan Tagwaye
*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
*GONAR SHARRI*
Billy S Fari & Hajja ce
*IDANIYAR RUWA*
(Mai wuyar toshewa)
Ayusher Muhd & Jeeddah Aliyu
*WATA ALAƘA*
Zee Bawa & Stylish bch
*BISHIYAR TSIYA*
(Wanda bai jiba bai gani ba ke girbar ki)
Umm Ashgar & Sadiya Dan.
*TSARIN ALLAH*
(Ba mai iya canzawa)
Asmy b Aliyu & Nana Diso
*ZAI IYA BIYAN*
GUDA 1 akan 500
GUDA 2 akan 800
GUDA 3 akan 1200
GUDA 4 akan 1600
GUDA 5 akan 2000
*BANK ACCOUNT*
8098456130
Opay digital services
Shaidar biya 08098456130
*KATIN MTN*
07065283730
Shaidar biya ta lambar.
[8/1, 9:34 PM] Billy S Fari: *GONAR SHARRI...!*
*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
   (Batch C)
NA
*BILLY S FARI*í ½í²Ž
Da
*HAJJA CE*í ½í±ˆ
Arewabooks@billysfari
*BOJUWA HERBAL'S & SCENTS*
*Suna kawo Saiwowin sanyi da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.*
*Haka nan akwai dafaffen maganin ga wanda tafi son ready made.*
*Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah*
*Saiwowin tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru*
*Saiwowin matsi gangariya*
*Original gadalin mata*
*Ƴaƴan gadali na asali*
*Original gumba*
*Tsumin Saiwowi*
*Tsumin kwakwa da Dabino*
*Igiyar alkairi*
*Zumar goran tula*
*Hakkin daka na musamman na asali*
*Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*.
*Akwai bridal package*
*Mai jego package*
*Ƴar gata package*.
*Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.*
*A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne*
*Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi*
*08032773332*
*Iyah Basiru na gaisuwa*í ½í¸…
Page 7..
Tabbacin data samu akan zai sai mata wani gold É—in yasa zuciyarta yin wani irin sanyi, da haka
ya riƙo hannunta suka sakko suna hira tamkar ba itace ta gama kuka ba har yana tsokanarta
wai itama zata koma kamar Baby Jannat tafara saka mashi ciwon kai da rigimarta. Su Suhana
dama sun wuce É—akin su, kallonta yai tare da cewa,
"Muje kici abincin ki dan na lura baki ci komai ba."
"Na ƙoshi, bari nayi mata magana kawai tazo ta gyara wajen." Ta ƙarasa zancen tana nufar
ɗakin Jauhar ɗin. Kwance ta hangota wani baƙin ciki ya sake tokareta na ganinta kaɗai da tayi
kwance, gani tayi tamkar jin daÉ—i ne yasa ta kwanciyar saboda idan son samunta ne kawai ta
buÉ—e idanuwa taga Jauhar cikin wahala da kuma aikin bauta da babu ranar tsayawa a huta
aciki,
"Ki tashi kije ki gyara wurin can, amma ki sani bawai na kyaleki bane, inhar banga zinarina ba
bazan taɓa bari kihutawa rayuwarki ba acikin gidan nan, saboda na dinga jefaki a masifa
kala-kala har sai kin gaji kin fito dashi, nonesense!"
Daga haka ta wuce part É—in Alhaji Sha'aban tana tunanin kalar ukubar da zata tanadar mata
gobe. Jauhar kuwa miƙewa tayi da kyar tafito palourn don dama wata irin masifaffiyar yunwa
take ji ta kwashe kayan takai kitchen ta dawo ta gyara wajen, abincin da aka rage ta tattara ta
hau ci har sai data canyesu tas sannan ta wanke kayan ta gyara kitchen É—in, tana fitowa Suhaila
na sakkowa, tana ganinta tace,
"Ke.!" Lokacin Jauhar na ƙoƙarin shiga ɗakinta ta juyo tana kallonta ba tare data amsa ba,
"Ki haÉ—o min coffee ki kawo mun." Jauhar da jikinta ke tsami taji kamar ta fashe da kuka amma
ba damar yin hakan sai kawai ta amsa mata da,
"Toh." Tana juyawa tare da komawa cikin kitchen É—in ita kuma Suhaila ta juya takoma É—akinsu.
bayan mintuna biyar Jauhar ta kammala haÉ—a coffee É—in ta nufi É—akinsu ta kai mata, har zata
juya tafita Suhana tace,
"Ki shiga toilet akwai undies ɗina cikin washing machine ki ƙara wankemun ki shanya." Jauhar
ta amsa mata da,
"Toh." Tana sake É—an tattaro karfin jikinta ta nufi toilet É—in ta shiga wankin undies É—in Suhana. Ba
ita ta gama ba sai kusan ƙarfe sha biyu ta wanke toilet ɗin tas sannan tafito ta wuce ɗakinta,
wanka ta shiga tafara yi ko jikinta zai saki sannan tasha ragowar maganin da Uncle Irfaan ya
taɓa bata daga nan ta kwanta, kamar jira akeyi ta kwanta wani irin zazzaɓi ya taso ya rufeta,
take tafara rawar sanyi ta ja zannuwanta duka ta lulluɓa hawaye na sakko mata, bata san
lokacin data fara kuka ba tana kiran sunan Abbanta ba dako kasheta za ayi bata san inda yake
ba yanzu, kuma bata san duniyar da zata shiga wajen nemansa ba.
Yadda taga dare haka taga safiya ba tare data runtsa ba saboda yadda zazzaɓi ya rufeta. Tun
tana jurewa har takasa tafara kuka ƙasa-ƙasa, duniya ta sake yi mata zafi wacce dama ba wai
ta taɓa yi mata bane, haka ta taso bata san wani abu farin ciki ba ko kaɗan. Alhaji Sha'aban
Sada ne da asuba daya fito zai tafi masallaci yaji kukan nata can ƙasa-ƙasa amma da yake har
an tada sallah bai tsaya bi takai ba ya wuce masallaci, da kuma ya dawo sai ya manta ya shige
part É—insa ba tare da ya tuna cewa yaji kuka kafin ya fita ba. Hajja Maimoon na zaune ta idar da
sallah tana duba wasu kaya a wayarta da take son fara business É—in su, kai ta É—ago ta gaishe
shi ya amsa yana faÉ—in,
"Yau da wuri nake son fita saboda akwai bakin da zan gani ƙarfe bakwai, saboda haka ina
tunanin bazan tsaya karyawa ba kawai haÉ—a min ruwan wanka dan bana so asamu matsala,
mutanene masu muhimmanci da nake sakaran idan Allah ya daidaita tsakaninmu zan cika miki
alkawarinki a cikin satin nan."
"Kamar kasan kayan da nake son fara business É—in sune nake dubawa a wani group dana
shiga na masu campany, duba kaga kalar designers ɗinsu." Ta miƙa masa wayar haɗe da tashi
ta shiga toilet ta haɗa masa ruwan wankan tafito. Wayarta ya bata sannan ya miƙe yana cewa,
"Kayan sunyi kyau sosai idan har naga business ɗin ya karɓeki to nima zan saka hannun jari
aciki sai na buɗe miki shago." Tana murmushi ta karɓi wayar tare da cewa,
"Zai ma karbeni in sha Allah, ai sana'ar kayan yara da turarukka da jakunkuna da kake gani ba
ƙaramin samu akeyi ba, matsalar kawai idan mutum baida kuɗi da kuma isasshen jari, hala ka
manta a cikin harkar ka ganni ka ƙyasa?" Ta kasara maganar cike da zolaya. Ya yi murmushi
yana cewa.
"To ki É—auka ba kida wannan matsalar gimbiya