Showing 1 words to 3000 words out of 4715 words

Chapter 1 - HASSAN DA HUSSAINI BOOK BY HAJ MARYAM.pdf

16 Mar 2025

1049


*HASSAN DA HUSSAINI*


By

Haj Maryam

Page 1

Wasu kyawawan samari na hango a wani katafaren gida dan da ka gani kasan gidan sarauta ne
.

Wata mata ce kyakyawa ajin farko yar gajera fara sol da ita humm Maryam kenan macce mai ji
da izza da son iko.

Maryam ji take tafi kowa a duniya saboda kawai tana auren dan sarkin Kaduna wato Hassan.

Yauma kamar kullum Hussaini nahango abakin wata bushirya mangwaro yana kuka yana
gayawa abukanan sa tunda Hassan yayi aure ya juya mashi baya.

Daya daga cikin aboken mai suna Yusuf yace "haba Hussaini kaima kayi aure kadena sawa dan
uwanka".

Budar bakin Hussaini sai cewa yayi " abokina baka gane bane dama ni tun farko nbason
Maryam dan batayi mani ba"ya karashe fada tare da jan tsuki mtwsss.

Dariya Yusuf yayi"to wa kakeso ya aura?"ya tambaye shi yana dan duban shi cike da mamaki.

"Ga Chamsiya nan ko ita ba macce ce ba ai tafi Maryam komi"ya fada cikin dan gaga murya.

" A ganinka ba shi dai Maryam din ya ke so"Yusuf ya fada tare da tashi ya nufi inda ya aje motar
shi.

Maryam ce zaune ita da masoyin ta Hassan suna hira cike da so da kauna da kuma shaukin
juna.

Hussaini ya shigo falon direct inda suke ya nufo,Hassan ya kura mashi ido yana kallon shi ganin
duk ya rame hasken fatar shi ya kara fitowa sai yayi wani fayau.

"Good morning!ya fada tare da zaunawa a kujera mai facing din su,amsawa sukayi cike da
kulawa,Maryam kuma ta tashi ta shiga kitchen.

Abinci ta shiga jerawa a dan karamin table ta turo gaban Hussaini ture table din yayi abinci ya
zube ji kake rugugugu duk kwanonin sun zube a kasa.

A hasale Hassan ya mike ya nufo......

Your comment please in yayi maku zan cigaba

Taku ce Haj Maryam

*HASSAN DA HUSSAINI*


By

Haj Maryam

Bismillahirahmanirahim

Page 2

A hassale Hassan ya miqe har ya daga
hannu kuma ya sauke, "Hussaini ka ga dai kai dan uwana ne, inason ka ina k'aunar ka amman
soyayyar da ni ke maka ba zata bari in tsaya ina gani kana wulaqantamin matata ba,ka sani
Maryam matata ce amanar ta aka bani kuma inason ta bantaba sanin dadin soyayya ba sai
akanta kuma wlh zan iya sa6awa da kowa akanta saboda haka inason daga yau karunqa
girmamata ka dauketa amatsayin anty ka mudin kana so mu zauna lafiya".

Tinda ya fara zuba Hussaini ya daskare wuri guda yana kallon Hassan cike da mamaki.

"Har bada Maryam ba anty na ba ce kuma batada darajar da zan girmamata" Hussaini ya fada
tare da nufar hanyar fita.

Yana isa gida ya samu momy a main falo tana kallon TV.


"Hussaini zo nan" momy ta fada tare da nuna mashi wuri kusa da ita.

zuwa yayi ya zauna y'a sunne kai,murya ta na tsinkayo tana cewa" wai kai Hussaini yaushe
zaka girma? kullum kana girma kana cin qasa"dagowa yayi yana kallon ta kafin ya ce "momy mi
nayi Kuma?".

" Rufe min baki ai kafi kowa sanin abinda kayi,to abinda zan gaya maka ka fita da matar aure
tunkafin ranka ya bace,in kuma kaqi zan hada ka da yar qawata zainab atiku yarinya mai ankali

ga nutsuwa,"

"Gaskiya ni momy babu mai mani auren doli".

" Shine kuma kake matsa ma dan uwanka ya auri wadda bai so,to wlh bari Alhaji ya dawo mu
tsara yadda za ayi in ya so ka korota in an kai maka ita tashi kabani wuri".

Fuuu ya tashi yana gunguni direct part din shi ya wuce nan ya hau kuka"ni mi zanyi da zainab
wallah babu mai mani auren doli".

Asalin labarin....

Maryam Salis shine cikaken sunanta, asalin su yan zanfara ne suna zaune a unguwar gada
biyu.

Mahaifan Maryam talakawa ne,sai dai ita Maryam Bata aje kanta kusa ba yar karya ce ba ta aje
komi ba sai girman kai ga son a ce ita wata ce.

Cikin qarya da Maryam ta sa ma kanta har da k'in makaranta gwamnati ita ala doli sai privé ta
ya'ayan masu kudi,ganin mahaifan ta basuda hali ta tatara karatun ta watsar.

Yanzu babu abinda take sai abkin tara samari kuma akasarin su duk t yayan masu kudi ne
amman abinda bata sani ba duk cikin babu mai sonta da aure........

Taku ce Haj Maryam Aliyu Yahya

*HASSAN DA HUSSAINI*


By


Haj Maryam


Page 3

Bismillahirahmanirahim

Suwa ye Hassan da Hussaini????


asalinsu suyan kaduna ne,mahaifinsu Alhaji Muhammadu cikakkun yan sarauta ne masarautar

su ta dauko asali ne tun daga kakan su alhaji Ayuba dattijon arziki gason talakawa azamanin
mulkin shi.

Talakawa suna son shi saboda yanada tausayi,ga babu kyarmar na kasa dashi.


Ya auri mata shi mai suwaiba inda zaman auren ya kasance cike da soyayya da kaunar juna,
sai da suka kwashe sama da sheka goma Allah bai basu haihuwaba.


Tin hankalin su bai tashi har dai suka bazama neman magani inda har takai da sunyi neman
magani har sun gaji suka zuba ma saurauta allah ido.


Rahama ubangiji bata yankewa,rana daya Suwaiba ta tashi da zazzabi hankalin Alhaji Ayuba
ya tashi sosai.

Suna zuwa asibiti a gwajin farko aka gano Suwaiba nadauke da ciki na tsawon wata biyu

Zo kuga murna wajan alhaji Ayuba,dan tsabar murna sai da ya bidi zaucewa dan yaji dadi sosai
wanda bai milsaltuwa.

Ko da suka dawo gida sukaci gaba da renon cikin su,akwana atashi harcikin Suwaiba yashiga
watan haihuwar.

Wata ranar litinin suwaiba ta tashi danaquda,tin tana daurewa har ta kasa ta gayama mijinta.

Zuwansu asibity babu wuya s ta haifi danta mai kyau mai kama da mahaifin shi.

Ranar suna akasawa yaro suna Muhammadu.

Tin lokacin da aka haife shi bai sans wani abu rishi ba,ya taso cikin gata da so da kauna wanda
iyayen shi nuna mashi.

A kwana a tashi babu wuya wurin allah Mahammadu yayi karatu secondary na school nan
Alhaji yatura Shi qasar waje dan cigaba da karatun shi.

A can America ma Muhammadu ya maida hankalin shi akan karatunshi inda ya karanci aikin
likitanci.

Tin kan ya dawo mahaifin shi ya gina mashi katuwar asibiti a nan gida Nigeria yabude mai suna
Muhammadu clinic Hospital agarin kaduna.

Yau kama kamar kullum yadowo daga aiki ya iske mahaifinshi falow zaune Yana huta ya duqa
har kasa yace" baba sannu da hutawa"dagowa mahaifin nashi yayi yace "yauwa son" ya fada
yana dan murmushi.

Gyaran murya alhaji Ayuba yayi "alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah daya nuna mani
wanan rana da ka gama karatun ka lafiya yanzu abinda yarage shine kafitar da matar aure".

Dan sadda kai kasa yayi kafin yace " to baba insha Allah"........




Haj Maryam takuce

*HASSANA DA HUSSAINI*


By

Haj Maryam


Page 4


Wannan fage din nakane Hussaini 80k bawan mata


Bismillahirahmanirahim

Muhammad yace "to
To baba insh allah zanyi qoqari infitar da matar aure ciki yan kwanakin nan"," allah yayi maka
albarka"shine abinda mahaifin shi yace.


Muhammad ne ke shiri a gagauce domin zuwa asibiti.

Tuki yake ahankali can ya hangi wata kyakyawa tana tafiya cikin nutsuwa, tunda yagan ta yaji ta
shiga ran shi.


Dan matsawa yayi kadan yayi parking motar shi daf da ita ya sauke gilas yace"Assalamu
alaikum",dan tsayawa tayi tace" wa alaikassalamu".

"Dan allah in ba zaki damu ba ina son sanin sunan ki" dan kallon shi tayi alamun shi ya fara
gaya mata nashi mana,
" ni sunana Muhammad to ke fa?" tace nikuma "hauwa'u" ,"nice name!amman ina zuwa
haka?".

"Makaranta zani".

" ok ki shigo in rage maki hanya mana".

"A'a na gode babu matsala zan samu adaidaita".

"haba malam hauwa ki daure ki shigo mana"

Nan dai ta shiga,"malama hauwa'u zan iyasanin gidanku?"

"Eh Mana, a malali gidan mu ya ke ",a nan ya anshi number ta ya wuce asibity.


Bayan haduwarsu dakwana biyu ya shirya zuwa unguwar malali ya nazuwa ya kira number da
ta bashi tana dagawa tayi mashi kwatance.

Yana Isa qofar gidan su ya iske mahaifinta zaune a kan tabarma yana shan iska,zuwa yayi ya
duqa har qasa ya gaishe shi.

Bayan sun gaisa cikin mutunci Mahaifinta yace "sai dai ban gane ka ba yaro" yace "eh nazo gun
hauwa'u ne" ya fada yana susar keya.

Yace "Masha Allah daga ina ?"

"ni dan gidan sarki Alhaji Ayuba ne kuma da niya auren ta nazo".

Mahaifinta yace " ba matsala in dai tana son ka"ya fada tare ta tashi shiga gida ya turo mashi
hauwa'u.

Tana fita ta tarar dashi suka gaisa tare da yin hirara ta masoya.

Yana isa gida bai wuce ko ina ba sai wajen mahaifin sa anan yakwashe duk yadda suka da
baban hauwa'u ya gaya mashi.

Mahaifinsa yaji Dadi sosai yace" insha Allah gobe za aje gidansu ayi magana"

Washe gari takama ranar laraba qanin mahaifin shi suka je gidan su hauwa'u kasancewar
baqananan mutane ba anan aka tsai da maganar aure wata biyu.

Akwana atashi wata 2 kamar yauce agurin Allah yau juma a aka daura auren Muhammadu da
hauwa'u.

Anyi biki nagani nafada anci an sha a ngama lafiya a ka kai amarya dakinta.

Bayan aure dashe Kara biyu hauwa'u ta haifi yaran ta yanbiyu Hassan da Hussaini kyawawa
farare tasss .

Haka su ka tashi cikin so da kaunar junansu sai dai ko wane da nashi hali, Hassan yatashi da
haquri Hussaini yatashi da fada ga kishin dan uwanshi.

Komi tare ake masu ba a banban tasu Amma kullum Hussaini gani yake anfison Hassan sun
tashi cikin gata dakulawa bawajen kakanniba Baga iyaye ba dayan uwakowa sonsu ya keyi.

Sai da suka kwashe wajan shekara goma a duniya sanan hawa'u ta kara samun wani ciki......



Ta kuce Haj Maryam

*HASSAN DA HUSSAINI*


By haj Maryam


Wannan page din na kine Nafissa Laouali Rabo

Page 5 to 10


Bismillahirahmanirahim

Sai da suka kwashe shekara goma a duniya sannan mahaifiyar su ta qara samun ciki.



Samun wannan cikin ba karamin farin ciki familyn su kayi ba,dan murnar su bai musaltuwa.

A kwana a tashi yau cikin momyn su ya cika wata takwas nan mahaifin su ya kwashe su zuwa
India a can mahaifiyar su ta haifi yarinyar ta mai kyau, ranar suna yarinya taci sunan Nana a
nace mata Hamdala.


Su kuma Hassan da Hussaini suka cigaba da karatunsu a can.


Tunda a ka haifi Nana dukannin su suna nuna mata soyayya dan ba karamin so suke mata ba.


Bayan shekara goma sha biyar kakan su ya kamu da rashin lafiya,shi yayi sanadiyar dawowar
su Nigeria.

Inda yanzu su twins suna da shekara 25,Nana Kuma tanada shekara 15 .


Bayan dawowar su da sati biyu Allah yayi wa kakan su Alhaji Ayuba rasuwa.

Jama'a da dama sunyi kukan mutuwar me martaba musamman ma talakawa,familyn shi kuma
ba a magana.

A kwana a tashi yau
Alhaji Ayuba ya cika shekara daya darasuwa inda a ka nada mahaifin su a ka bashi sarautar
kakan su.


Yau ta kama ranar asabar Hassan da Hussani sun shirya zasu gida abokin su Nafi'u.

Suna kan hanyar suta tafiya Hassan yayi saurin taka birki "kuuuut!"wanda yasa Hussaini ya
firgita tare da cewa"ya dai lafiya zaka tsaida mu kan titi?".

Hassan kasa cewa komi sai nuni da yayi mashi da dan yatsan shi ,hurin da ya nuna yabi da
kallo wata kyakyawar matashiya na hango gajeruwa fara sol da ita sai sheqi take.


Marfin motar ya bude ya qarasa wurinta tare da yi mata sallama,cikin yanga da jan aji ta amsa
mashi tare da yin shiru hakan ya bashi damar cigaba da cewa "my name is Hassan,you fah?".


cikin yauqi tace"ni kuma Maryam", dan murmusawa yayi yace" nice name ,daga wacce unguwa
kike ?"

"Ni ba yar nan garin ba ce
bikin qawata ne ya kawo ni", " ah ok ina kuke bikin?inji Hassan,kai tsaye ta bashi amsa da
"unguwar dosa GRA ".

"Masha Allah
zan iya samun number ki?" ta daga mashi kai alamun eh nan ta karanto mashi.


Duk abinda suke Hussaini na tsinkayan su ta glass din mota tunda ya ganta yaji yatsaneta shi
haka kawai bata burge shi ba...


Tunda Hassan ya koma gida bai da magana sai ta Maryam ko hira ya ke sai yasa Maryam daga
ya fara Hussaini ke barin wajen kwatakwata baya qaunarta .


Yau ta kama Monday an gama biki Maryam ta koma gida,kullum Hassan sai ya kira wayar
ta,yauma da sukayi waya ya mata alqawari zai je gidan su.

Haka ko akayi ranar juma'a ya shirya ya tafi gusau inda ya samu tarbar arziki,sun sha hirar
soyayya da qauna a nan ya tabbatar mata da aure ya ke sonta bai sha wuya ba wajen
amincewar ta ba saboda burin Maryam har kullum bai wuce ta auri me kudi ba balle ta samu
dan sarki kullum sai girman kai daji da kai....



Taku ce haj Maryam

*HASSAN DA HUSSAINI*


By haj Maryam



Wannan page din na ki ne Chamsiya Laouali Rabo

Bismillahirahmanirahim

Page 12 to 15


Bayan maganar su da kwana biyu dadyn su ya kira Hussaini "ina umartar ka da kayi gagawar
fitar da matar aure dan a hada ka da dan uwanka" cewar dady ya fada tare da tamke fuska
alamun babu wasa.

Budar bakin Hussaini sai cewa yayi" gaskiya ni dady ban shirya aure yanzu ba".

Dady yace "rufemin baki sakarai,wlh indai zakaci gaba dawanan halin kanada tashi ka bani
waje".


Yauma kamar kullum mahaifiyar zainab ce na hango zaune kusa da momy su Hassan ,tana
cewa "ya maganar auren Hussaini da zainab dan magana ce ta kkawo ni,
zainab nanan ko abincin kirki bataci saboda Hussaini kullum kuka takeyi Dan Allah hajiya mai
zai hana ayi auren su da wuri a huta?"


"Hmmm"cewar hajiya " wlh qawata yaron ne ka haifeshi baka haifi halin shin ba,na rasa ya
zanyi da yaron nan kullum taurin kanshi qaruwa yake,amma dan Allah ki bani lokaci zamu san
yanda zamuyi"

"Toh" kawai maman Zainab tace.



Yau a kaje a ka nema ma Hassan auren Maryam kuma sun samu,daman mahaifin Maryam
abinda ya ke so kenan ya kawar da ita kafin ta jawo mashi abun kunya.



Hassan da Maryam ko wata shaquwa da qauna ke qaruwa a zuciyoyin su kullum Hassan
natarairayar Maryam duk da halinta nakwadayi daroqo amma Hassan bai ganin aibun ta.


A kwana a tashi har an fara shirye_shiyen auren Maryam da Hassan komi shi yayi mata,yayi
mata lefe nagani nafada harta da kayan daki yace zai yi mmata komi,wannan ya kara hura
hutar qiyayar ta a zuciya Hussaini dan shi ya tsani macce mara kamun kai wadda batada aikin
yi sai roqon samari.
Maryam ko ta je ta samu mahaifiyar ta da zancen Hassan yayi mata Alqawarin zai mata komi.

Mahaifiyar ta tace "ban yarda ba,ba zan saida maki da darajar ki ba a gun dangin mijin ki ba,duk
da muna talakawa zamuyi komi na mu daidai gwargwado".


Budar bakin Maryam sai cewa tayi " gaskiya ni bana so saboda ko za a yi mani baza amin
wanda yakai shiba,gaskiya ai ina zuwa gida qawayena ina ganin nasu so kike yi suzo su mani
dariya ga Hajara Aj anyi mata kaya mai tsada ga Aisha maman nawal nan itama haka sai ni
gaskiya ni abari yayi mani"Maryam ta fada tana turo baki gaba.

Babu yadda mamata batayi ba dan ta fahimtar da Maryam illar hakan amman taqi.


An fara shiye_shiyen biki ammar ya ta sha gyara inda ango ya bude mata bakin aljihu.


Yau ta kama ranar kamu qawayen amarya duk sun hadu amarya tasha kyau domin ango ya
kawo mata mai kwalliya Lina gwanar iya kwalliya ce.



Anci an sha galgale ansha inda qawayen amarya suka zage dan tsewa Jen rawa


Abun dai baki bai iya misalta shi har ta da yan uwan Hassan sun zo sun ga amarya ta zage
damtse tana kwasar shoki abun bai wani ba su haushiba tinda su yan boko ne in ka fida
Hussaini da ya dauki hakan rashin kunya.


Anyi taro lafiya an watse lafiya.


Yau ta kama ranar lahadi,ranan kuma a ka daura auren Hassan da Maryam akan sadaki dubu
dari

Maryam amarya na gani tana shirin zuwa reception bayan miti ishirin sai ga motar ango ya zo
daukar Maryam.


Wucewar su keda wuya Hussaini na hango da abukanan shi yana cewa "wallahi baza ayi taron
an lafiya ba tunda tace kwadayi ne aikin ta,to ni ku sai na lalata masu wannan taron".

Muryar Yusuf na tsinkayo yana "haba Hussaini kai da yaci ace ka taya dan uwanka farinciki
amman kai ne zaka batamai taro?"


Budar bakin Hussaini cewa yayi "malam ba

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login