Showing 3001 words to 4715 words out of 4715 words

Chapter 2 - HASSAN DA HUSSAINI BOOK BY HAJ MARYAM.pdf

16 Mar 2025

1052

wa'azi nace kamin ba idan ba zaka taya ni ba ka bar
ni".


Isata hol din taro yayi taro qawayen ango suntaru inda na hango Muhammadu Shafi'u babban
abokin ango tare da Nazifi yarima, a gefe guda kuma Yan group din MSHELIYAS sunyi gungun
su daban Aisha humaira sai surutu take kamar akun kuturu😜.

Fannin amarya ko qawayen ta kowa yayi shiga ta alfarma,su Aisha maman nawal su hajara Aj
ina daga kaina na hango Asmau ban yi mamaki ba dan naga yan group din MATA MASU
AJI,gefe daya kuma MATAN GIRMA nagani su Aisha Ibrahim su ummu Hasina.

Muryar mc naji" za mu bude taron mu da suna Allah Yanzun muna so muga amarya da ango".


Isowar amarya da ango a kan filin ke da wuya wutar hal din ta dauke gabadaya .

Dede lokacin da aka kunna wutar wajen Hussaini nagani yakwace sifika ahannun m c budar
bakin Hussaini yace.....


Yanzu gam zai fara🤪🤪🤪

Kubiyoni a page nagaba muga mai Hussaini zai yi, zai cika burin shi ne na ganin ya wulaqanta
Maryam ko kuwa🤪🤪



Haj Maryam takuce
💋💋💋💋💋💋
*HASSAN DA HUSSAINI*
💋💋💋💋💋💋

By haj Maryam


Page 15 to 20

Bismillahirahmanirahim


Karbe sifikar Hussaini yayi yace "ni sunana Hussaini wanda ku ka fi sani da 80k,

Nariga nayi Alqawarin Hassan ba zai ta6a auren Maryam ba ,

Amman tunda ta dake seda ta aure shi to wlh tallahi ba zata samu zaman lafiyaba,

Kuma nayi Alqawarin...."wuf naji an amshi sifika a hannun shi ko da nakai kallona gefen wata
tsaleliyar yarinya matashi mai kyau.


Tace "ni sunana chamsiya nice wacce keson Hassan kuma nayi Alqawarin Sai na aure shi ko ta
wane hali" ta fada tare da miqawa takusa da ita .



"Ni kuma sunana Aisha humaira nice babbar qawar Chamsiya kuma munyi alqawarin bata
goyon baya dari bisa dari",nan sauran qawayenta suka amsa duk suka gabatar da kansu sunna
gamawa Hussaini yace" ina umartar kowa yabar wajen nan".,

Nan wata babbar qawar amarya ta miqe" babu mezuwa ko Ina kuma ku kunyi kadan ku lalata
mana biki"ba ta ida rufe baki ba naji tass Hussaini ya watsa mata mari daga hannu tayi zata
rama chamsiya tariqe ta "ke wawuya karki saki ki mari qanin mijina"


Budar bakin Aisha maman nawal tace" shi bai ji kunyar marina ina matar aure ba sai ni zanji
kunyar ramawa?".



Nan dambe yabarke tsakanin qawayen chamsiya da Maryam anyi kacakaca da hol duk an kori
jama'a , chamsiya ta dauki cake tawatsawa Hassan afuska ganin haka amarya taa tashi ta
nufeta.


"Wallahi zan dau komi
amma bazan yarda awula qanta Hassan ba "


Nadanbe yakachame tsakanin amarya Maryam da chamsiya .

Mai martaba na zaune a fada wani bafade ya fado da dugudu Allah yaba ka yawan Rai balafiya
Nan yagaya mashi duk Abunda ke faru.


Anan mai martaba yayi umarni da fadawa suje wajjen .

Koda fadawa suka iso anyiwa amarya kacakaca shi ko Hassan tunda ya daskare guri daya
komotsi bai yi ba sai shigowar fadawan ne ya dawo daga dogon suman zaunen da yayi.


Nan fadawa suka kori kowa a kamaida amarya gida.


Tunda amarya ta isa gida take kuka tana danasanin auren Hassan bata taba sanin qiyayyar
dangin miji haka take ba sai yau .

Jama'a suka shirya aka kai amarya,abokan ango na watsewa sai ga su Hussaini suna shigowa
Hussaini yafara watsawa Maryam mari "wlh tunda kika aure dan uwana wallahi kinta rarwakan
ki
wahala "

Bai gama rufe baki ba sai chamsiya da qawayen ta suna shigowa Hussaini yace duk kayan da
ke gidan Nan kufarfasa shi ai ba daga gidan ubanta tazo da suba.


Nandanan komi ya hargitse suka fara buge_buge .

Show glass da kayan kallo duk seda suka fasa seda suka tabbatar sun fasa komi sunba amarya
kashi.

Har ango da yazo dakartar dashi dede lokacin Aisha humaira tacillon plet se agoshin Hassan

Nan jini yabarke
Ko da suka bar gidan daqyar Hassan ya iya daga waya yakira momy su
.
Momy nazaune kiran Hassan yashigo Yana mata bayani najitace "innalillahi wa Inna ilaihi Raji
un "


Kode Hussaini so ya ke ya kashe ni ne nan takwashi fadawa sunna Isa suka iske Maryam
asume ,aka kwashe su se asibity suna shiga nurses suka dauketa zuwa Emargency tun da
suka shiga ake ba maryam taimako amma har yanzun bata farfado ba........

Haj Maryam takuce
💋💋💋💋💋💋
HASSAN DA HUSSAINI
💋💋💋💋💋💋

Duka littafin Nan nasadaukar dashine gareka uban gidana Hassan ATK




By haj maryam

Fage 20 to 25
End

Wannan fage dinnakine Anty Aisha my sweet sister



Bismillahirahmanirahim


Tunda aka Kai Maryam asibity Bata farfadoba haryan zun

Tunkoma war momy su gida

Tayi ma mahaifinsu magana akan tanaso adaura auren Hussaini da zainab



Mai martaba yace insha Allah ranar juma a za a daura


Auren shi da zainab zamu gani inshi yahaifemu

Satin maryam daya cif a asibity sannan ta farfado washe gari aka sallame su suka koma gida

Sede me martaba yasa angyara mata gida Kuma yasiya mata sabbinkaya Nan Hassan da
Maryam aka bude sabon rayuwa mecikike da soyayya da qauna

Sukaci amarcin su hankali kwance yauta takama ranar alhamis


Dady su yazaunar da Hussaini yayi maina siha inde harni na haifeka banyarda kaqara shiga
Sha a nin rayuwar auren Dan uwankaba


Kuma gobe insha Allah za a daura auren ka da zainab cewar dady su



To Hussaini yace Yana turo baki gaba

Washe ga Ana idar da sallar juma a aka daura auren Hussaini da zainab


Gidan su zainab sunyi taro sunyi biki sosai sabanin gidan ango


Inda Hussaini bema San anayiba kwata kwata bema shigo gidan ba tunda suka fara Sha ani


Anyi taro anwatse ankai amarya dakin mijinta


Saide tunda aka Kai amarya ango be wai wayetaba kullum se dai yaje gidan abokan shi
yakwana


Akwana atashi yau watan zainab uku Amma ango betaba zu gidan amarya ba


Yauda wowar Nana daga gidan take gayawa momy komi


Nan momy takishi

Wallah Hussaini zansaba ma cewar momy Kuma wallahi daga yau inaso karunqa zuwa gurin
matarka


To najiyo Hussaini yace canqasan maqoshi

Yanatashi be zarce ko inaba se part dinshi

Yana shiga wani dadda Dan kamshine yadaki hancinshi

Kallo gefen shida yayi zainab yahanga

zaune tana cin abinci wani hadiyar miyo yayi sakamakon ganinta da yayi cikin lafiyayyun kayan
bacci masu daukar Hankali


Dagokai zainab tayi sukayi ido biyu da Hussaini


Cikin rawar murya tace sannu da zuwa

Yauwa ya amsa mata atakaice yawuce bed room dinshi tunda yadaura idon shi akan zainab
yauce


Rana tafarko daya farajin wani Abu akanta

tunda yashiga daki yakasa rintsawa Yana rufe ido surarta yakegani

Semamaki yakeyi Ashe haka take

Kullum baya iya barci yau satin su biyu kenan suna zaune ahaka


Hussaini na hango Kwance yanata juyi Amma barci yaga gara kawai



Yauze yasame ta ayita ta qare zainab nakwance adakinta tana chat jitayi anbude qofa Adan
razane tamiqe ganin


Hussaini tayi tsaye akanta budar bakinta malam yafiya

Lafiyarce takawo haka cewar Hussaini nazo inkabi haqina

A danrazane zainab tamiqe bangane mekake nufiba

Zaki gane cewar Hussaini danmatsawa yayi kusa da ita ka Dan


Ban ankaraba naji zainab tadiro akan gado

Duk iya qoqarin da Hussaini zeyi Dan yashawo kan zainab

Yayi Amman taqi

Yagaji daroqo dama giya yakoma yimata wa azi


Nadai daqyar yashawo kan zainab

Nikuma inagani sun sulhunta nagashe musu wuta naja musu qofa na urufe


Washe gari da sassafe nahango Hussaini nagyaran gida yayi wanke wanke da shara hargoge
goge fuskar nantashi cike da annuri


Faran ciki yabayyana afuskarshi Yana gama hada mata break fast

Yazauna yayi ta gumi Yana tunani asha haka aure keda Dadi Aida nasan haka yake


Datuni nabari an hada Dana Hassan

Gaskiya nayi kuskure da nake shiga tsakanin masoya




Akwana atashi bawuya agurin Allah yau sheka biyarkenan da auren
Hassan da
maryam


Nan hango wasu yara yandu Gul dugul guda uku


Macen ce tasheqo da gudu Abba Abba kaga kanzillahi ko

Budar baki abban nasu yace zo Nan Afra kaima kanzillahi zona bana Hana kufa ba affan yace
Abba wallahi afrace bataji


Abban Yan uku wallahi bakwa gajiya da shirme ce war maryam


Hassan Naga yataso Ina zan gaji tunda yauma inaso aqara samomin Yan uku Nan
yariungumeta yanawa Allah godiya

Umma umma cewar
Yasmin zainab na hango akici tanace wa karku shigo minnan kuwuce gunbaban ku Hussaini na
hango Yana cewa kuzo yayan baba



Haba abban Minal wallah nina gaji kullum abudaya komi Kai Minal wallah banso kasha gwabata

Cewar chamsiya

Budarbakin abban Minal yace bari insha gwaba abuta

Tunda Hussaini yayi aure chamsiya matayi aure Da nafiu Nana ko ta auri Dan abokin abbansu

Kuma suna zaune lafiya



Alhamdulillah anan nakawo qarshe labarina inagodiya ga Allah dayabani

Ikon kammala wannan labari

Ina godiya ga Anty chamsiya

Masuce wa inkwatanta a dallaci tsakanin Hassan da husaini Dan nafison Hassan

Wlh da Hassan da husaini duk daya suke awaje bawanda yafi wani

Kuma duk inason su irin so na addinin musulunci

Wannan littafin nasadaukar dashine

Gabadaya gareka uban gidana Hassan ATK Allah yajamana kwananka

Se mun hadu Alittafi nagaba

Haj Maryam takuce

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login