Showing 1 words to 3000 words out of 35354 words
Chapter 1 - KAINE SANADI BOOK COMPLETE (1 to End) By Sodangi & Khalisat .pdf
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen2⃣)
WHATSAPP NO:
+2347039625239
[4/11, 6:47 AM] +234 703 962 5239: [3/6, 11:13 AM] Fdaus Sodangi: *KAINE SANADI!* 1⃣
*WRITTEN BY*:
*FIDDAUSI SODANGI*
*STORY BY:*
*KHALISAT HAYDAR*
*EDITTED BY*
*SANAH S ISMA'IL MATAZU*
*®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)*
_Bismillahirrahmanirrahim_
_Godiya ga ubangijin mu Allah daya bani ikon fara rubutun nan lafiya, ina rokon Allah yasa
inkare lafiya batare dawata matsala ba Ameen, wannan labarin kirkirarrene banyi shi dan cin
zarafin wani ba kowata, idan yayi shige da labarin rayuwar ki ko naka ina niman afuwa hasashe
ne dakuma aikin alkalami wanda yafi na takobi.
D'akin d'aukar karatun a cike yake taf babu masaka tsinke, duk inda ka waiga babu alamar
zaka iya samun wajan zama domin kuwa d'alibai ne tako ina, duka-duka k'arfe takwas ne na
safiya amman kuwani d'alibi ya halarci lecture d'in kasan cewar sam mallamin babu wasa bare
d'aga k'afa a tattare dashi, gashi yau d'in nan suna saka ran zaimasu test, duk kuwa da bawai
ya fad'a cewa zaiyin bane, amman da dukkan alamu suna saka ran zaiyi d'in, dan shi haka yake
badai yace zaiyi abu ba, saidai ya shammace ku yayi d'in.
Hayaniyar d'aliban ne yacika d'akin karatun, wasu na hira, wasu na karatu wasu na bacci,
yayinda wasu keta faman cece kuce.
Lokaci d'aya d'akin ya d'auki shuru, tsit kakeji tamkar ba sune keta hayaniyar nan ba, masu
bacci tuni sun tashi, kowa ya kama kansa yashiga taitayin sa.
Matashin malamin ne yashigo, wanda k'amshin turaransa ya sanar wa d'aliban nasa ya iso.
K'yakk'yawan matashi ne wanda shekarun sa na haihuwa bazasu haura 30 ba, wankan
tarwad'a ne dogo sosai ga fad'i, yanada manyan idanuwa had'e da yalwataccan gashin gira
dana ido, ga wani had'add'an sajensa wanda yak'ara fitowa da k'yawun da Allah yai masa,
hancin sa dogo mai k'yawun gaske. Sanye yake cikin k'ananan kaya, bak'in wandon Jeans ne had'e da wata jar riga mai
azababben k'yau, rigar ta d'an matse shi kad'an saita k'ara fiddo shi, k'afar sa sanye cikin wasu
had'add'un takalma na maza, dagani kasan masu tsata ne, wani dank'areran agogo ne d'aure a
tsintsiyar hannun sa mai kalan bak'i sai wani shek'i yakeyi tamkar daimon.
*ALIYU RASHEED GANDUJE* kenan, matashin malamin dake lokacin sa a jami'ar ta
*CATHOLIC UNIVERSITY OF AMERICA*, cikin takunsa ta k'asaita ya isa gaban d'akin
karatun, inda ya k'arasa sama inda ya dace ya tsaya d'in, tsawon minti uku ya d'auka a tsaye
yana k'arewa d'aliban nasa kallo d'aya bayan d'aya, idanuwan sa suka fad'a gun zamanta inda
yaga wayam batazo ba, illa k'awar tata mai suna, *KHADIJA MUHAMMAD DALA* murmushi
yasaki wanda ya tsaya a fatar bakin sa, gaba d'aya d'aliban nasa sunyi mamakin ganin
murmushin nasa dan sabon abu ne agare su, wannan ne yasa kowa yak'ara shiga taitayin sa,
dan acewar su murmushin mugunta ne wannan *ALIYU RASHEED GANDUJE* yayi, cikin
k'warewa yashiga koyar dasu daki-daki, gaba d'aya hankulan su nakan sa ko motsi mai k'arfi
babu maiyi acikin su, tsawon minti talatin yanai masu darasin.
K'was!! K'was!! K'was!! K'arar takalmin nata ke bada sauti, kasancewar wajan yayi shuru
shiyasa k'arar ya karad'e ko ina, shi kansa *ALIYU RASHEED GANDUJE* cak ya tsaya daga
bayanin sa yana kallon ikon Allah, shidai yasan cewa babu d'alibin daya isa yashigo mashi aji
bayan shi d'in yashigo, dan wannan rainin wayau ne babba acewar sa.
Hankalin ta k'wance taci gaba da takunta tana k'arasowa cikin d'akin karatun, tafiya take cikin
yanga da tak'ama, kallo d'aya zakai mata ka tabbatar dacewar babbar yarinya ce kuma d'iyar
wani babban mai mulki da sarauta, zaka gane hakan ne ta yanayin shigar ta dakuma yanayin
yanda take tafiyar tamkar bazata taka k'asar ba, k'yakk'yawa ce ajin farko, tsayawa in k'watanta
maku k'yawunta k'arin bata lokaci ne gara kawai inbarku ku k'watan tota da kanku masu karatu,
*AMATULLAHI AHMAD FAGE* kenan matashiyar budurwar da babu kamar ta acikin jami'ar,
wajan k'yau da tak'ama dakuma nuna isar cewar ita d'in fa d'iyar shugaban k'asa ce, wohoho.....
*DEDICATED TO*
*KUBRA USMAN BALA*
[3/6, 2:36 PM] Fdaus Sodangi: *KAINE SANADI*2⃣
*WRITTEN BY*:
*FIDDAUSI SODANGI*
*STORY BY:*
*KHALISAT HAYDAR*
*EDITTED BY:*
*SANAH S ISMA'IL MATAZU*
*®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)*
_Yawan comments d'inku shi zai k'ara k'arfafa min gwuiwa, insan lbrn nada masoya indage
wajan yin typing dasauri_
Tafiya take ko ina na jikin ta na k'adawa duk da doguwar riga ce ajikin ta amman saboda
kayan datake d'auke dashi wanda Allah ya halicce ta dashi, dole ne jikin nata ya kad'a abin
gwanin ban Sha'awa, gaba d'aya kallo yakoma kanta, itakuwa tafiyar ta take hankali k'wance
tamkar ita d'aya ce a duka filin d'akin haka take ji, tana k'ok'arin zama bisa kujerar daya zame
tamkar dan su aka yishi ita da k'awar tata wacce duk sanda tariga ta shigowa sai ta aje mata
gu, kai koma duka basu zo dawuri ba babu mai hurumin zama a kujerar dan kuwa kowa yasan
wacece *Amatullahi Ahmad Fage* da k'awar ta *Khadija Muhammad Dala*, wani wawan tsawa
yadaka mata, cikin harshan turanci yasoma magana, "You are very stupid wacece ke dazaki
shugo min aji yanzu har kike k'ok'arin zama dan bakida kunya bayan kin d'aukewa kowa hankali
daga sauraron abu mai mahimman ci!"
"will you get out before I slap your dirty face!"
Cak taja ta tsaya tana masa wani k'ask'antaccan kallo, kafin taja wani dogon tsaki da k'wafa
tamkar harshan ta zai fita, ta doka masa wata uwar harara da manyan idanuwan ta tamkar zasu
fad'o k'asa, tafice a d'akin karatun cikin wannan tafiyar tata mai d'aukar hankali, harta bace
daga cikin d'akin baibar kallon inda tabi ba, zuciyar sa tamkar ta fasa k'irjin sa tafito, lallai
yazama dole yayi maganin yarinyar nan, aduk fad'in jami'ar nan ita k'adai ce ke taka shi son
ranta, but lokaci yayi daya kamata yanuna mata iya karta yanuna mata ita d'in fa ba kowa bace!,
Hankalinsa ya maida kan abinda yakeyi, gaba d'aya ajin kowa yasha jinin jikin sa dangane da
abinda yafaru yanzu,
Awa d'aya ya bata yana koyar dasu kafin yabasu test, hankalin Khadija ne yayi bala'in tashi
dan ganin k'awar tata bata nan yabada test d'in, takuma san da gangan yayi hakan saboda
wannan shine test d'in shi na k'arshe yace, har nanata masu yayi duk wanda yarasa wannan
test d'in to kada yasaka ran zaici jarabawar sa, nan danan idanuwan Khadija suka kad'a sukai
jawur dan bacin rai, "wai shi wannan d'an talakawan me yake tak'ama dashi ne?" waye shi
dayake taka _Amatullahi_ haka? Gaskiya dole suyi maganin gayan nan dan isar shi tayi yawa
yanaso yawuce gona da iri.
Minti ashirin kacal sukayi yasa a k'arbar masa, ana gama had'awa ya fice abinsa, zaune ya
iske ta akan wani had'add'an Capet mai kama da jikin damisa sai d'aukar ido yake, guys d'in ta
zagaye da ita kowanne ya d'od'e ido cikin bakin tabarau kallo d'aya zakai masu ka tabbatar
basuda mutunci zasu iya aikata komi akan aikin su.
Manyan idanuwan ta ta watsa akan sa tare daja masa tsaki, kallo d'aya yaimata ya d'auke
kansa daga barin kallon ta, yawuce abinsa, d'aya daga cikin guy's d'in nata yayi k'ok'arin binsa
saboda tsakin dayayi, ta dakatar dashi da fad'in "barshi ba Yanzu ba akwai sauran lokaci!".
D'aliban ne suka suma fitowa daga d'akin karatun kowanne na surutu akan test d'in da _Aliyu
Rasheed Ganduje_ yayi.
Khadija ce tafito rannan nata a had'e ta zauna kusa da k'awar tata tana labar tamata abinfa
Aliyu Ganduje yayi, tsaki Amatullah tayi tace "karki damu k'awata indai kud'i suna aiki a duniya
zan saye Aliyu Ganduje dashi da y'an gidansu gaba d'aya, dan haka ki barni dashi shi ai
k'aramin d'an iska ne!". Murmushi Khadija tayi ta bata hannu suka kashe, tace har naji sanyi a zuciya ta wallahi gayen
baida mutunci, hira suka ci gaba dayi abinsu cikin k'wanciyar hankali harsanda wani malamin
yashiga ajin kafin suka mik'e suka shiga suma.
Tsawon wani lokaci malamin nayi masu darasi kafin yafara watso masu tambayoyi, tsit ajin
yayi dan kuwa tambayar tad'an yimasu wuya, tsawon minti uku babu mai alamar mik'ewa,
tambayar malamin yak'ara nanatawa cikin bacin rai amman tsit kake ji, ajin yad'auki shuru
dayawa, can wani had'add'an gaye daga baya ya mik'e cikin turancin sa mai dad'in saurare
yasoma watso amsar tambayoyin, *MUHAMMAD HUSSAIN D'ANBATTA*
kenan Yaro mai tarin baseera da hazak'a.
Wani dogon tsaki Amatullah taja tare da fad'in banza d'an scholarship kawai!, mutum sai
iyayin tsiya kowa yayi shuru amman shi yawani mik'e da banzan turancin sa saikace d'an
koyo.........
*DEDICATED TO*
*KUBRA USMAN BALA*
[3/6, 5:14 PM] Fdaus Sodangi: *KAINE SANADI*3⃣
*WRITTEN BY:*
*FIDDAUSI SODANGI*
*STORY BY:*
*KHALISAT HAYDAR*
*EDITTED BY:*
*SANAH S ISMA'IL MATAZU*
*®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)*
Gaba d'aya kowa yabita da kallo dan da k'arfi tayi maganar, kuma da harshan turanci,
shuru gayen yayi yana kallon ta da mamakin kalaman ta, shidai a iya sanin dayayi mata tsawon
shekara biyu kenan suna tare a aji d'aya amman yasan takk'wala ce ta k'arshe, sam bata gane
karatu da k'yar da sid'in goshi take wucewa kowace semester, dan haka ranshi bak'aramin baci
yayi ba, ko uban wama yace mata da scholarship yazo makarantar oho mata, lallai zaiyi
maganin ta kuwa.
Sam malamin baidamu da maganar datayi ba illa iyaka yace ma _Muhammad Hussein
D'anbatta_ yaci gaba da maganar sa shi suke sauraro, a k'uffule yaci gaba da koro bayani
tamkar zai fashe da kuka.
Haka sukaci gaba da d'aukar darasin har lokacin fitar shi yayi.
****
Yauma course d'in _Aliyu Rasheed Ganduje_ gare su, kamar koda yaushe d'akin karatun
yacika ya batse, jiran shigowar sa kawai suke yi, Khadija ce ta dubi Amatullah tace, "yakama ta
kije kiga Ganduje akan maganar test d'in ki,"
"eh yau d'in nan nake so inje daya fita zani,"
Basu k'arasa maganar ba, k'amshin sa ya tabbatar basu cewar ya iso, a hankali Amatullah ta
furta, "barawon banza kawai!, wannan turaran dayake kuri dashi dagani kinsan satowa yayi
kokuma maula yayi aka bashi!, dan wannan turaran yafi k'arfin albashin sa wallahi!," ta k'arasa
maganar cike da takai ci, k"aramar dariya Khadija tasaki wanda yasata had'a ido da Aliyu
wanda ya k'araso dai-dai gefen su dan hayewa sama.
Basarwa yayi ya haye sama dankuwa yau d'in nan saiya wulak'anta yarinyar nan acikin d'alibai
y'an uwanta tunda ita batada mutunci, yasani sarai bata san komi ba inbanda gigiwan tsiya da
rawar kai, dan haka yashiga yin abinda yakawo sa ajin.
Sanye yake cikin manyan kaya yayi bala'in yin k'yau tamkar asace a ruga, cikin k'warewa
sosai yakeyi masu darasin, gaba d'aya Sun natsu suna sauraran sa.
Tsawon awa d'aya yana koyar dasu, kafin yashiga watso tambayoyi yana nuna wanda yakeso
ya amsa, _Muhammad Hussein D'anbatta_ yasoma tadawa, nan ya bashi amsa ko gargada
babu, dama yanasa ran hakan, yakuma yin wata tambayar ya nuna wata d'iyar turawa, itama ta
mik'e ta bashi amsa kamar yanda ya buk'ata, daga k'arshe yayi wata tambayar ya nuna
Amatullah wacce sam hankalin tama baya kansa yana kan wayar ta datake ta latse latse a ciki,
Khadija nata d'an taba ta, amman ina hankalin ta yayi nisa, da k'arfi yakira sunan ta,
_Amatullahi Ahmad Fage!_
Dasauri ta d'ago manyan idanuwan ta tana kallon sa, irin kallon ne mai d'auke da harara,
mamakin yanda akai yasan sunan ta take, lallai ma gayen nan d'an rainin wayau ne!, sunana
dana uba na yake kira haka kamar wata sa'ar shi? K'wafa taja dai-dai sanda yak'ara kiran
sunan ta had'e da k'ara jefo mata tambayar tasa, tsaye ta mik'e kai tsaye tace "ban sani ba!,
angaya maka ni k'aramar yarinyar ce daza ka tadani gaban y'ay'an talakawa kace in amsa wata
banzan tambayar ka?"
"to wallahi Allah hawainiyar ka ta kiyayi rama ta!"
"ai dama tsiyar y'ay'an talakawa kenan, ni banma san meyasa aka d'auke ka aiki a wannan
jami'ar ba, naga dai tuk turawa ne malaman amman kai bak'ikkirin k'azami dakai aka"....... Wani
irin gigitaccan mari yasakar mata da hannunsa gaba da baya, sam batasan sakkowar shi ba,
kawai saukar marin taji, bata gama watsakewa waba yakuma kai mata wani had'e da shak'eta
yana fad'in "nine kazamin!?" hannunta yashiga ja da k'arfi yana k'ok'arin yin waje da ita sai
tirjewa takeyi, a haka suka fito waje yana jaye da ita, nan danan guy's d'in ta suka yanyame shi
kowanne d'auke da bindigar sa suka hayayyak'o masa tamkar zasu cinye shi..............
*DEDICATED TO*
*KUBRA USMAN BALA*
[3/7, 11:14 AM] Fdaus Sodangi: *KAINE SANADI*4⃣
*WRITTEN BY:*
*FIDDAUSI SODANGI*
*STORY BY:*
*KHALISAT HAYDAR*
*EDITTED BY:*
*SANAH S. ISMA'IL MATAZU*
*®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)*
Fisge hannun ta tayi cikin na sa da k'arfi tana kallon yanda wajan yayi jawur, murmushin
takai ci ta yi sannan ta watsa masa manyan idanuwan ta, tace _"Aliyu Rasheed Ganduje"_
Kayi k'ok'ari matuk'a! Madallah da wannan k'arfi hali naka! Da har ka iya d'aga k'azamin
hannun ka kasauke shi bisa wannan k'yak'yawan fuska tawa mai matuk'ar tsada! To ka bud'e
manyan kunnuwan ka masu kama dana zomo ka saurare ni, wallahi wallahi wallahi Aliyu
katabo ma kanka da y'an gidan ku kai da duka dangin ku bala'i da masifa, wanda wallahi nayi
maka alk'awarin cewa zaman 9ja sai ya gagare ku, sai dai ku tafi can nijar dan da alama dama
cirani yakawo ku 9ja dan da ganin wannan mummunar fuskar taka ansan y'an bararoji ne ku!
Saboda haka ka zauna da shirin ka, "hmm! Inma banda k'addarar data hau kan ka ina kai ina
taba _Amatullahi Ahmad fage!"_
"gaskiya ne kam d'an talaka bai iya samun waje ba, sai ya wuce gona da iri!"
Guy's d'in ta ne suka rufar masa ta d'aga masu hannu, cikin gadara da isa tace "ku k'yale shi,
ak'wai sauran lokaci bayan zuba", wani k'ask'antaccan kallo tayi masa ta tofa masa miyau tace
"kasaurare ni anjima inada magana da kai!, daga haka ta juya abin ta tai gaba, guy's d'in nata
su ka rufa mata baya, sororo Aliyu yayi yabisu da manyan idanuwansa da su ka kad'a jawur
dasu, zuciyar sa wani irin k'una yake yi, jikin sa sai k'yar ma yake dan tsananin bacin rai, lallai
yarinyar nan batasan _Aliyu Rasheed Ganduje_ ba! Kamar shi wannan k'wailar yarinyar zata
wulak'an ta haka?
Lallai watan cin uban ta ya tsaya, tunda iyayan nata basu yi mata tarbiyyar k'warai ba, "yazama
dole in nuna mata ak'wai banbanci tsakanin mace da na miji!"
K'wafa yayi ya tafi yana tad'in zuci.
Wasu had'add'un motoci ne kuda hud'u masu azabar k'yau bak'ak'e wuluk dasu, kowace
mota a bayan ta an rubuta _Amatullah_ suna isa gun motocin da sauri aka bud'e mata baya,
tashiga ta kame tana daddan na wayar ta, d'aya ya shiga yaja motar yayin da sauran suka raba
kansu, mota d'aya ce a gaba sai wanda take ciki a baya, sai sauran biyun suka biyo su a baya
da k'arfi suka fisgi motocin suka fice daga makarantar, yau kam Amatullah ta hakura da dukkan
lectures d'in,
Kai tsaye gidan ta suka nufa wanda ke awajan makarantar, tsakanin makarantar ma da gidan
nata yakai kilomita 5, wani d'an k'aramin gida ne mai azababban k'yau, ya tsaru iya tsaruwa,
taga ita sai k'awar ta _Khadija Muhammad Dala_ ke zama a cikin gidan sai kuwa tarin y'an aiki,
harabar gidan cike yake da motoci iri iri, da sauri suka bud'e mata k'ofar motar ta fito, cikin
tafiyar ta ta tak'ama tashiga cikin gidan, da sauri y'ar aikin ta mai suna Teena ta iso gaban ta
tare da zubewa tana k'wasar gaisuwa, da murmushi a fuskar ta ta amsa tana fad'in "babu
matsala dai ko?"
"babu ranki ya dad'e, meza a kawo maki?"
"bana buk'atar komi Teena, jeki abinki wanka ma zanyi yanzu,"
"to ranki ya dad'e bari inje inhad'a maki ruwan wankan,"
"ohh ohh Teena nace kibar shi kinaso kita saka ni magana" _sorry_ ranki ya dad'e,
D'uka da harshan turanci suke maganar kasancewar Teena baturiya ce babu hausa a bakin ta.
D'aki tashiga kai tsaye ta wuce toilet ta watsa ruwa tafito d'aure da tawul, gaban dressing mirror
ta wuce, ta yi tsaye tana k'arewa surar ta kallo, iska ta shak'a cike da farin ciki, wani irin nishad'i
takeji yanda ta gasa wa _Aliyu Ganduje_ magana cikin ruwan sanyi, murmush tayi wanda
yak'ara fitowa da k'yawun fuskar ta, a hankali ta furta "saina ga iyakar ka Aliyu Ganduje" "ka tsokalowa kan ka tsuliyar dodo!"
Tafi minti sha biyar gaban madubin tana ta kalailaita, tashafa wannan ta murza wancan ta
fesa wannan ta gurza wancan, ahaka