Showing 3001 words to 6000 words out of 35354 words
Chapter 2 - KAINE SANADI BOOK COMPLETE (1 to End) By Sodangi & Khalisat .pdf
dai har ta gama, ta sanya wata had'add'iyar doguwar
riga, ta fice daga d'akin kanta ko d'an k'wali babu sai wata y'ar k'aramar waya mai k'yau a
hannun ta. Palo ta shiga ta kame a d'aya daga cikin had'addun kujerun dake cikin palon, tana lallatsa
wayar,
Teena ce tafito tace "ranki ya dad'e har kin fito?"
Kai kawai ta d'aga mata kafin tace "kije kice ma musa yatafi makaranta yajira Khadija idan ta
gama ya maido ta gida"
"to ranki ya dad'e"
Da sauri Teena ta fice dan isar da sak'on uwar d'akin ta...........
*DEDICATED TO*
*KUBRA USMAN BALA*
[4/11, 6:47 AM] +234 703 962 5239: *KAINE SANADI*5⃣to1⃣0⃣
*WRITTEN BY*
*FIDDAUSI SODANGI*
*STORY BY*
*KHALISAT HAYDAR*
*EDITTED BY*
*SANAH S, ISMA'IL MATAZU*
*®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)*
_ina matuk'ar jin dad'in yabawar ku agareni tare da k'arfafa min guiwa, nogode sosai da k'aunar
ku agare ni domin duk mai son abin ka to kai yake so._
_Fatyma Izland_
_Ummi Hambali_
_Fatima Aliyu Garba_
_Zara Bukkar_
_Humaira Bashir Melody_
Wani irin mugun kallo yake mata ko k'yaftawa baya yi, jikin sa gaba d'aya rawa yake yi
idanuwansa sun kad'a sunyi jawur kamar gauta.
A sanyaye tasaki hannun nasa tare dayin baya kad'an, matsowa yasoma yi inda take cikin wani
irin taku, zuciyar ta ce tayi wani irin bugawa nan da nan kamannin ta ya canza alamar tsoro
yad'an baiyya na a fuskar ta amman cikin dakiya irin tata ta dake saidai tasoma yin baya kad'an
kad'an, binta yaciga dayi har ta kurema bango, tamkar zai shige cikin jikin ta yaja ya tsaya yai
mata runfa da makeken k'irjin sa.
Yafita tsawo nesa ba kusa ba da ace wani zai shigo a lokacin sam bazai yi nasarar ganin taba
domin kuwa gaba d'aya _Aliyu Rasheed Ganduje_ ya lullube ta da tsawon sa dakuma fad'in sa.
Bud'e bakinsa yayi zai mata magana wani irin had'add'an k'amshi had'e dawani irin huci mai
zafin gaske yabigi fuskar ta, nan da nan y'an hanjin ta suka kad'a zuciyar ta ta yanke ta fad'i
rass!! Rass!!
Manyan idanuwan ta ta zaro tana duban sa tsoro k'arara shimfid'e a fuskar tata.
Cikin wani irin kakkausar murya yashi ga fad'in "meyasa kika rainani dayawa har kike
tunanin zaki iya siyan _Aliyu Rasheed Ganduje?"_
"me kike tak'ama dashi?"
"wacece ke mekike da shi?"
"kinyi babban kuskure dakika shiga gonar _Aliyu Rasheed Ganduje_ kin tafka babban kuskure
da kika shigo rayuwar Aliyu".
"Da ace zaki nimawa kanki gata dakin tattara tsummo karanki kin bar k'asar nan dan zamanki
baida wani amfani, kina zaman kashe wando ne zaman dazai sa ki koma abin tausayi abin
k'watance acikin makarantar nan!".
"ina jin dad'in wannan game d'in damuke bugawa nida ke! Dan haka Allah yabawa mai rabo
sa'a ,kina iya ficewa daga _office_ d'ina Kafin in rufe idona in bud'e, idan kuwa ba haka ba na
rantse da Allah saina illata ki anan yanzu ba anjima ba idan kuma k'aramar k'wak'walwar ki
yabaki k'arya nakeyi ki tsaya in bud'e ido baki fice ba kigani."
Tsaki taja tare da fad'in "zamu had'u ne zakasha mamaki wallahi wallahi!".
Dasauri ta d'au jakarta tafice.
Tana fituwa suka gwabza karo ita da _Muhammad Hussein D'anbatta_ d'auke yake dawasu
littafai a hannun sa, yayinda itama take rik'e da jakar ta, littafan nashi ne suka watse a gaban
ta, yayin da itama jak'ar nata ya fad'i k'asa daf da littafan.
Gaba d'ayan su suka d'uk'a lokaci d'aya kowanne ya d'auki nasa.
Tana d'agowa bud'an bakin ta tace "shishigi da niman suna! To uban me kuma kazo yi a
_office_ d'innan?"
"Dad'i na da d'an talaka wallahi bai iya samun waje ba!, mutum shi ba d'an kowa ba, asalima
d'an scholarship, amman sai iyayin tsiya da fi'ili."
"yanzu in banda jahilci da duhun kai irin na d'an k'auye ina kai ina bangaza ta, _Hussein
D'anbatta_ kake ko uban wa?"
"To bari ingaya maka ninan daka ganni bana yafiya!, bana mantuwa!, haka nan kuma bana
mance ranar d'aukar fansa!"
"Dan haka kazauna cikin shiri wannan lallausar jikin daka bangaza bazai wuce a banza ba
saina nuna maka kuran ka!"
Taja wani mugun tsaki da k'wafa tamkar harshan ta zai bar bakin ta tayi gaba guy's d'in ta suka
rufa mata baya.
Mamakin kalaman ta suka sa shi sakin baki yana duban ta, lallai yarinyar nan y'ar rainin hankali
ce yafad'i a fili, hmm! Adai guji zuwa rafi.....
Khadija ce ta dube ta bayan ta zauna tace "to ya kukayi da mutumin naki?"
Iska ta furzar cikin bacin rai tace "ai kin san komi akai da jakki sai yaci kara!"
Nayi iya k'ok'ari na amman abin ya faskara,
Kinsan shi taurin kai gare shi da girman kai kamar shaid'an.
Dariya Khadija ta k'washe dashi harda tuntsurawa.
"To Amatullah yanzu yaza mu bullo masa ne"
"amman kinsan me nifa wallahi guy d'in burge ni yake yi dan ya iya d'aukar wanka k'arshe
wallahi."
Wani irin mugun kallo Amatullah tayi mata cikin daka tsawa tace "kar ki k'ara batan rai dan
Allah!"
"meye abin burgewa ajikin wannan d'an matsiyatan?"
Kisa ido kigani muna nan za a zo a damk'i shege dan da ganin kayan daya ke sawa yana fafa
dasu da turaran dayake amfani kinsan katon barawo ne! Dan haka ina nan ina addu'a ina
kaiwa Allah kuka na Allah ya kawo k'arshan sa watau watan cin uban sa ya kama a damk'i
matsiyacin mai kama da k'osan rogo.
Hmm! Amatullahi kenan inaso inga ranan da wannan kiyayya taku zata k'are, koda yake shima
guy d'in ne d'an rainin wayau Allah!.
**************
Bayan sati d'aya yauma kamar kullum Amatullah taki ta shirya da wuri dan sanin cewa yau
lecture d'in farko ta _Aliyu Ganduje_ ce, tana ji tana gani Khadija ta shirya ta wuce abin ta, ita
kuwa sai bayan minti arba'in da yafiyar ta sannan ta shirya ta Shiga makarantar ita da guy's d'in
ta. Kai tsaye tashiga cikin ajin tana takun ta ta tak'ama, gaba d'aya k'amshin ta ya bad'e ko ina.
Cingum take tauna abin ta cike da yanga,
Sosai ya bud'e murya yace "karki k'araso nan! Koma inda kika fito,"
Ko kalma d'aya bata furta ba asali ma ko tsakin bata yi ba yau, ta juye tayi waje tana wani
jujjuya jiki.
Cikin bacin rai yaci gaba da koyar da darasin sa.
Kai tsaye _office_ d'in shugaban makarantar ta nufa kanta tsaye ta fad'a _office_ d'in.
Zaune yake shida wasu manyan makarantar suna d'an tattaunawa.
Cike da fara'a gaba d'ayan su suka mik'e suka tare ta saikace ita ce shgabar k'asar.
Cikin fara'a shugaban makarantar yasoma fad'in "ranki ya dad'e da kanki da sassafen nan lafiya
dai ko?"
Kuka ta fashe dashi sosai tana fad'in su kira Abban ta su shaida masa bazasu iya d'aukar
amanar daya basu ba nata, wanda harda mak'udan kud'ad'e ya had'a masu dan dai kurum su
kular masa da ita....... Da sauri shugaban makarantar ya katseta a rud'e da fad'in me akai mata?
Cikin kuka da shasshek'a tasoma magana.
_Aliyu Rasheed Ganduje ya tsane ni acikin makarantar nan, sam baya son ci gaba na, baya
son farincikina da k'wanciyar hankali na.
Kullum burin shi shine yatakurawa rayuwata.
Nashigo makaranta _last two weeks_ ya kore ni daga ajin sa, yaba da test bani, yace duk
wanda baiyi test d'in shi ba bazai ci jarabawar saba.
Nabishi _office_ d'in sa nabashi hakuri yace sai dai in siya test d'in da kud'i, na bashi kud'i
masu yawa yace shikenan magana ta k'are.
_last week_ yakira ni _office_ d'in sa bayan naje yake cemin shi ya janye zancan kud'i saidai
inbashi kaina, tak'ara fashewa da kuka mai cin rai duk wanda yagan ta a lokacin sai ya tausaya
mata."
"ina son karatuna sosai saboda burin mahaifinane insamu ilimi sosai kuma kun sani, wannan
dalili yasa nabawa _Aliyu Rasheed Ganduje kai na saboda kawai yadai bani test d'in nan kada
infad'i jarabawar sa."
"A bin mamaki yau ya tare ni dazancan saidai in k'ara bashi kaina saboda test d'in nan ba abu
bane mai sauk'i dazai iya bani shi haka a bagas."
"na nuna masa sam ban yarda ba tunda abin nasa rainin hankali ne shine wai dan nashiga
lecture d'in shi yanzu ya koreni daga ajin, tak'ara fashewa da wani irin kuka tamkar zata
shid'e...........
*DEDICATED TO*
*KUBRA USMAN BALA*
[4/11, 6:47 AM] +234 703 962 5239: *KAINE SANADI* 1⃣0⃣to1⃣5⃣
*WRITTEN BY:*
*FIDDAUSI SODANGI*
*STORY BY:*
*KHALISAT HAYDAR*
*EDITTED BY:*
*SANAH S, ISMA'IL MATAZU*
*®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)*
_wannan page d'in nakune_
_Anty Sadiya Jegal_
_Safreenah Annour_
_Abeeda_
A fusace shugaban makarantar yace _"what!_ dama duk cikin turan ci suke maganar,
yaci gaba da fad'in _Aliyu Rasheed Ganduje_ ne ya aikata wannan mummunar..... D'aya daga
cikin wa'yan da yake tare dasu ne ya katse shi da fad'in karkayi mamaki zai aikata fiye da
hakan! Ai d'an iskan yarone ak'wai yarinyar data taba kawo min k'arar sa nida kaina naja masa
kunni aka rufe maganar to kaga yanzu yakuma maimaitawa inda bazamu taba k'yale shiba!,
_(kai jama'a kuji k'arya k'iri-k'iri)_
Cikin muryar kuka tace "idan ma baku yarda da zance naba muje ajin a tambaye su, domin
kuwa su shaida ne, suna kallo ya kore ni rannan yayi test, yau ma suna kallo yakore ni, har
marina yayi rannan duk agaban kowa akayi nasan zasu fad'i gaskiya, sannan kuma
_Muhammad Hussein D'anbatta_ shaida nane, domin kuwa yaga fito wata daga _office_ d'in
_Aliyu Rasheed Ganduje_ ranan dana kai masa kud'i.
A fusace shugabar makarantar ya tasata gaba ita da sauran malaman suka nufi _department_
d'in nasu, kai tsaye ajin suka nufa ,
Yana ta koyar wa abin shi cikin k'wanciyar hankali da k'warewa.
Koda ya hango su baisa ya tsaya daga abinda yake ba illama k'ara sautin shi dayayi wajan
baya nin daya keyi.
Saida suka k'araso har gaban ajin sannan Aliyu yayi shuru yana duban su.
Shugaban makarantar ne yafara magana a fusace bayan ya fuskan ci y'an ajin, "yau shene
kukayi test d'in _Aliyu Ganduje?"_ yayi tambayar cikin dakakkiyar murya da harshan turanci.
Gaba d'aya suka had'a baki suka sanar dashi.
Kai ya gwad'a kafin yace "kunsan wanna?" yanuna Amatullah, suka bashi amsa dacewa nan
ajin take, yace "a ranan da Aliyu yayi test d'in sa ya kori Amatullah kokuwa?"
Suka sake bashi amsa da tabbas anyi haka, yakore ta sannan daga baya yarubuta masu test.
Yasake cewa "yau tashigo ajin nan kobata shigo ba?"
Suka sake bashi amsa dacewa tashigo yakore ta saboda dama shi k'a'idar sa indai yariga ka
shigowa to koran ka zaiyi.
_"where is Muhammad Hussein D'anbatta?"_
Mik'ewa yayi tare da fad'in _"am here sir!"_
"inaso in tambaye ka tsakanin ka da Allah zaka gaya min, idan ka boye min kokari min k'arya
baza ka boyewa Allah ba saboda yana kallon ka!".
Kai _Muhammad Hussein D'anbatta_ ya d'aga masa alamar zai fad'i gaskiya.
"kataba ganin wannan y'ar ajin taku tafito daga _office_ d'in _Aliyu Ganduje_ ko za ta shiga?"
Shuru Muhammad yayi tsawon wani lokaci shidai bai san make faruwa ba amman tabbas dai
yasan ya taba ganin ta tafito harma ta gaggaya masa bak'ak'en maganganu, wanda har gobe
sunai masa ciwo matuk'a.
Dan haka yace "k'warai kuwa idan ban manta ba anyi sati d'aya kenan dana ganta tafito daga
_office_ d'in _Aliyu Ganduje_
_"good"_
Shugaban makarantar ya furta da k'arfi, sannan ya dubi Aliyu wanda yayi sororo yana kallon sa,
zuciyar sa yana tafasa meyake shirin gani haka yau?
Kamar shi shi _Aliyu Rasheed Ganduje_ za a wulak'anta a cikin yara k'anana! Way'anda suke
ganin girman sa da mutuncin sa!?
Lallai yarinyar nan ta d'auko ruwan dafa kanta yau!
Wani mugun kallo shugaban makarantar yayi masa kafin yafara magana cikin masifa, "dama
nasan cewa baza ta yi maka k'arya ba, domin d'an babban gida baya k'arya!, kawai nazo ne
dan in fita hakkin ka ayi komi a gaban ka kana gani dan kar kace anyima sharri ko k'azafi!.
Ya kalli Amatullahi yace "ranki ya dad'e maimata abinda ya had'aku agaban sa yaji dan yasan
komi ya iso kunnin mu, kuma dama yasan dokar makarantar nan dan haka sai ya yankewa
kansa hukunci da kansa.
Babu kunya babu tsoron Allah Amatullah ta maimaita abinda tace masu babu ragi babu k'ari.
Shugaban makarantar ya dubi Aliyu yace "meza ka iya cewa akan abinda ta fad'a?"
Bud'an bakin Aliyu sai cewa yayi gaskiya ta fad'a anyi haka.
"murmush Amatullah tayi tace ai bai isa ya k'aryata ba tunda yasan cewa tabbas ya aikata.
Wani irin kallo Aliyu yake mata cikin ido mai wuyar fassarawa, gira ta d'aga masa ta kashe
masa ido d'aya.
"to Aliyu Ganduje kana iya zuwa _office_ d'ina domin ka amshi takardar sallama, domin kaima
kasani wannan shine hukun cin duk wanda aka kama da irin laifin ka.
Daga haka suka fice gaba d'ayan su har Amatullah tabi su tana karkad'a mazaunai.
Kaf miyan bakin Aliyu ya kafi da k'yar ya iya tattaro numfashin sa gu d'aya har ya saisai ta
kansa.
Idanuwan sa sam babu k'yawun gani.
Cikin wani irin tafiya mai kama dana bijimin sa yafice daga cikin ajin.
Gaba d'aya d'aliban jikin su yayi sanyi da ace sun san wannan ne dalilin da yasa akai masu
tambayoyi ai da basu fad'i komi ba sun rufa masa asiri domin kuwa koba komi suna gane
lectures d'in sa.
Khadija kuwa hawaye ne taji yana gudu bisa fuskar ta wanda ita kan ta batasan dalilin saukar
suba.
*******
Bayan awa biyar, Amatullah ce ta k'ure k'arar radio tana shan sauti tana tik'ar rawa daga ita sai
wata yar _vest_ da guntun wando.
Rawa take hankalin ta k'wance dagani kasan tana cikin nishad'i, wani irin rawa take tamkar
zata karye, sai kace wata bebin roba.
Khadija ce tayi sallama tashigo amman sam Amatullah bata san da shigowar taba.
Khadija tafi minti biyar da shigowa amman sam Amatullah tayi nisa a sharholiyar ta.
Wani irin juyi tayi cikin rawar ta kawai sukai ido hud'u da aminiyar ta Khadija.
Dasauri ta kashe radio d'in cikin ihun murna ta rungume Khadija tana fad'in _i am the winner of
the game_ sis kitayani murna, nagama da _Aliyu Rasheed Ganduje_ nagama dashi wallahi.
"Yau ina cikin farin ciki mara misaltuwa, Allah nagode maka daka bani sa'a akan mak'iyina."
"Khadija na dad'e banyi farinciki irin na yau ba wallahi,"
Na maida Aliyu abin kwatan ce a duniya,
"yace wai in tattara tsummokarana in koma k'asata."
"to gashi nan kafin ni in koma matsiyacin ya riga ni."
"hmm!! Ai duk wanda yaci tuwo dani wallahi Allah miya yasha!"
"in banda _Aliyu Rasheed Ganduje_ ina shi ina ja da d'iyar manya!"
"ai bigi sai big! Babban goro sai magogin k'arfe!"
"Hmm!! _Aliyu Rasheed Ganduje_ *KAINE SANADI*
amman sam bahaka Amatullah take ba, kaine ka canza ni nazama haka.
Sai a lokacin ta lura da yanda Aminiyar tata ta tsaya mata cak tamkar wata gunki bata taya ta
farin ciki.
Jiki a sanyaye ta sake ta tanai mata kallon tuhuma.
"Khadija lafiyar ki kuwa?"
Cikin muryar kuka Khadija tasoma magana, "Amatullah sam banji dad'in abinda kikai ma Aliyu
ba! Sam baki k'yauta ba."
"ina so ki sani Allah ya jarabceni da k'aunar _Aliyu Rasheed Ganduje_ tun daga ranan dana
soma ganin sa!"
"ina son Aliyu ina k'aunar sa ina kuma burin in mallake sa, sai gashi cikin k'ank'anin lokaci kin
rusa min lissafi na! Amatullah bakiyi min adalci ba kin ma rayuwata illa babba!, yanzu ta ina
zani niman Aliyu ina zanbi ingan sa, dawani ido zan dube sa?" tafashe dawani irin kuka mai
taba zuciyar mai saurare.
Wani irin kallo Amatullah keyi mata ko k'yaftawa batayi, kafin tafara magana cikin rashin
mutunci mai cike da masifa.
"Khadija ashe bakida mutunci bansani ba! Ashe zaune nake da makiyiya ta bansani ba?"
"haba! Tabbas biri yayi kama da mutum."
"lallai d'an adam butulu ne"
"to bud'e kunnuwan ki kiji ni da k'yau! Daga yau sai yau, bani baki! Ke ko a hanya kika ganni
kika nuna kinsan ni Allah ya isa ban yafe maki ba! Kuma ki tattara kayan ki kibar min gida na
yan zunnan bada bata lokaci ba"
"banza mara zuciya! Inbanda Kare ya cinye zuciyar ki ina ke ina Aliyu Ganduje?"
"mutumin daya tsane mu nida ke baya k'aunar ya bud'e ido yagan mu a duniya! Wai shi kike
k'auna! To ki k'arawa motar ki mai kibi Aliyu Ganduje gidan matsiyacin uban sa yayi maki wajan
k'wana acan."
Taja tsaki tanimi kujera ta kame tana ci gaba da masifa.........
*DEDICATED TO*
*KUBRA USMAN BALA*
[4/11, 6:47 AM] +234 703 962 5239: *KAINE SANADI* 1⃣6⃣
*WRITTEN BY*
*FIDDAUSI SODANGI*
*STORY BY*
*KHALISAT HAYDAR*
*EDITTED BY*
*SANAH S, ISMA'IL MATAZU*
*®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)*
_kuyi hakuri da wannan ina fama da ciwon ido, ina barar addu'ar ku pls_
Sororo Khadija tayi tana kallon Amatullah tana jinjina irin rashin mutuncin ta, sam bata zaci