Showing 30001 words to 30317 words out of 30317 words
Chapter 11 - CANJIN RAYUWA Book 1 Complete Hausa Novels by Halima Abdullahi K Mashi.txt
masa kar ya damu, mimi ta zama ta shi don na bashi.
nan Alh akilu ya hau godiya cikin murna, Abbas cikin murna ya rungume mahaifin sa.
Alh bashir ya kosa ya iso gida don yayi Albishir ga mimi da momi nafisa, lallai burin shi zai cika.
Alh lawal ya kalle direban shi, yarin yar nan ba zata bamu hadin kai ba, dan haka kayi min sallama da maman ta.
haka kuwa ya rangada sallama, kaninta ya leko ya ce, yauwa ka ce Alh yana sallama da maman ku, yaron yace inannar mu...?
ya ce, eh, ka ce inji Alh lawal.
ba da jimawa ba, innar su zainabu ta fito, tamkar marokiya, haka take tayiwa Alh barka da zuwan ka ka iso lafiya, sannu sannu.
ya fito ta durkusa bari a yi shin fida a zaure, ta mike ta koma cikin gida da gudu.
daga gani Alh wanan yar raka yarima ce a sha kida, suka yi dariya tamkar ba direba da uban gida ba.
to direba za a kirashi ko kawali, tunda shi ne me kawo ma Alh mata.
suna zaune a kan tabarma a zaure, Alh ya ce, inna na zone akan maganar aure, zainabu taki bani hadinkai in turo manya ns, sai fada min take tana da wanda zata aura.
inna ta cefke zancen da cewa, karya ne bata da shi, ka turo kawai, ya ce, to na gode.
ya ajeye daurin yan dari biyar-biyar, inna ga wanan kyaci goro, kuma zan turo manya na gobe, bana son bikin ya wuce sati uku.
ta ce, ai kuma lokacin bamu shirya ba, Alh kasan sai min nemi na gado.
ya ce, ina da ko mai inna, mata na ce ina so, kuma ita za a bani ba tarkacen kaya ba.
ta ce, to shike nan, in gobe kake so a daura bare nan da sati uku.
tirkashi!!! ku biyuni a kashi na biyu don jin yadda zata kaya.
taku halima k/mashi.
ina sauraran ku,08081165107
dan shawara ko kuma korafi na gode....""