Showing 3001 words to 3972 words out of 3972 words

Chapter 2 - JARUMAN DUNIYA Book 1 Complete littafin yaki Document by Sarkin Marubutan Yaki .txt

Shi kuwa yarima sai ya kura kyakkyawar budurwar idanu batare da yayi yunƙurin komai ba, kawai sai a ka ga budurwar ta tsaya cak sannan ta waigo tare da yiwa junan su lallausan murmushi a lokaci guda su duka biyun su kaji sun kamu da matuƙar soyayyar junan su.
kyakkyawar budurwar ta ɗauke dubanta daga na yarima su ka ci gaba da tafiya sai dai su yarima su ka daina hango su.
jiki a sanyaye yarima ya je ya kama linzamin dokinshi yayi gaba, Sauran dakarun su ka mara ma shi baya suna masu zaburar dawakansu.
Tun da aka fara wannan tafiya har aka iso gidan sarauta yarima bai ce kalaba.


*****


Fada ce ƙasaitacciya da aka ƙawata ta da kayan alatun jin dadin rayuwar duniya, Duk isar BASARAKE ko attajiri idan ya tsinci kanshi a cikin wannan fada dola ne ya zamo cikekken ɗan kauye kuma ya rai na kanshi.
Zaune a bisa karagar mulkin, sarki Baddadul-arus ne.
Sarki Baddadul-arus yakasance garjejen kato mai kama da giwa yana da ɗan mitsitsin kai da katon ciki tamkar an kifa ƙwarya a habarshi yana da ɗan mitsitsin gemu fari rol! da tsawon shi bai huce kamu ɗaya ba.
A gefen hannunshi na dama gimbiya uzaima ce, zaune a bisa wata kayatacciyar kujera ta alfarma ta na sanye da tsaleliyar alkyabba mai fatsi-fatsi, shigar tayi matukar fito da kyawun surar jikin ta.
Haƙiƙa duk inda kyawu yake gimbiya uzaima ta cika kyakkyawa domin ko gasar kyau Za ayi zata iya zamowa ta daya.
A wannan lokaci gaba ɗaya mutanen fadar babu abinda su ke kallo face satar kallon gimbiya uzaima, kai bama maza hatta 'yan uwanta mata idan su kayi arba da ita sai kaga sun wan game bakunan su suna dalalar da yawu, saboda yadda kyawun ta ya burgesu.
Gaba ɗaya fadar tayi tsit! tamkar mutuwa ta gifta, Daga can sai gimbiya ta katse shirun daya wanzu ta dubi mahaifinta sannan ta buɗi baki cikin zazzaƙar murya mai daɗi tamkar sarewa tace
"ya Abbana wai yaushe ne zamu tafiya nemo abubuwa guda uku domin mallakar TAKOBIN SIHIRI ?, Tabbas na ƙagu naga anyi wannan tafiya domin na sake yin ido biyu da abokin gaba ta yarima muzaifar domin ayi ta takare.
Koda jin wannan tambaya daga bakin uzaima sai sarki Baddadul-arus ya bushe da dariyar mugunta har da kyakyatawa sannan daga bisani ya dubi uzaima yace
"ya yata mafi soyuwa agareni kiyi sani cewa bakomai ne ya hanamu tafiya nemo abubuwa uku ba domin mallakar TAKOBIN SIHIRI ba sai domin akwai wani sauran birni guda daya da nake so na cinye shi da yaƙi, dazarar na kammala zamu fara shirye -shiryen tafiya, ina fatan kin gamsu da wannan bayani. Uzaima ta gyaɗa kai alamar gamsuwa sannan ta buɗi baki a karo na biyu tace,
"ya Abbana a sanina babu wata ƙasa da tarage a yankinmu da bamu cinye ta da yaki ba.
kafin uzaima ta ƙarashe maganar ta sarki Baddadul-Arus ya tari numfashin ta yace.
"wannan birni dazan kai farmaki baya iyaka da ƙasata na gano boyayyen birnin ne a lokacin da nake gudanar da bincike bisa halarar tsafi na.
Gama fadin hakan keda wuya sai sarki Baddadul-arus ya haɗe hannayenshu biyu ya karanto wadansu dalasiman tsafi jim kadan sai ga hoton wani kasaitaccen birni ya bayyana akan tafukan nashi.
Gine-ginen birnin sun kasancce cikin tsari, hatta tufafin su abin sha'awa ne.
Nan take uzaima taji birnin ya burge ta sannu A hankali hoton yana canza launi har ya bayyana hoton wani kyakkyawan saurayi yana sanye da kayan ado na sarauta.
Tun da gimbiya uzaima tazo duniya ba ta taɓa gani ko jin labarin da namijin da yakai saurayin kyawu ba.
Nan fa uzaima ta ƙurawa saurayin idanu tana nazarin shi, koda sarki Baddadul-Arus ya lura da halin 'yar tashi shiga sai ya karanto ɗalasiman tsafi ya tofa akan hannunshi, Faruwar hakan keda wuya sai hoton ya bace bat!,
Tamkar bai taɓa wanzuwa ba.
A sannanne uzaima ta dawo hayyacinta tana mai sauke ajiyar zuciya,
sarki Baddadul-arus yayi gyaran murya ya dubi uzaima yace"wannan birni dazan kai farmaki ana kiransa da suna JARUL-IMAN.
Yaushe ne zamu kai MAMAYAR BAZATO birnin?.
Uzaima ta tambaya a kagauce.
Baddadul-arus ya bushe da dariya sannan yace "Haba 'yata mai ki ke ci na baka na zuba ai saura kwanaki kaɗan mu kai wannan farmaki, ke dai kawai ki yi tanadi kafin ranar.
Ko da jin wannan batu sai uzaima ta cika da matukar farin ciki maral-musaltuwa.
koda gama fadin hakan sai sarki Baddadul-arus ya rike hannunta suka miƙe tsaye daga kan kujerunsu su ka nufi wata yar siririyar hanya dazata sadasu da gidan sarauta.



Mu haɗu a littafi na biyu domin jin cigaban wannan kayataccen littafi
Daga mai ɗebe muku kewa a kullum da koyaushe.
Mansur Usman Sufi
08137237071

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login