Showing 1 words to 3000 words out of 21093 words
Chapter 1 - TA DABAN BOOK COMPLETE By AMMEY LAYLERH.pdf
https://chat.whatsapp.com/DGIo9iiSjlgJPPqFHNtddH
*♡SPECIAL☆*
_Ta daban_
ِ
مْسِب_* ِ
هَّللا ِنٰ
َمْحَّرلا *_ميِحَّرلا
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
~Na Maryam Naseer Mirrah~
_AMMEY LAYLERH_
Page 1&2
_ƊAN ƊANO_
*NA'EEMA SULAIMAN SARAUTA*. _NIMCY LUV_ Ban manta kalan gudun mawar da kika
ringa bani ba a littafi na na baya wato MIKIYA. TO haka za wannan ma da Salonta labarin ze
fara SEY MA SHA ALLAH.Na sadaukar miki da wanan littafin, this novel is for you my humi
darling, my Mummy'na, my support system, my role model, i love you_ *_Special Thanks to:_*
Masoya masu bibiyana ina alfahari daku a ko ina a kowacce duniya kuke
Love you all
♡♡♡♡♡♡♡
The official trailer for *SPECIAL* {Ta daban} (2025) introduces Novelist to a chilling,
suspense-filled Power Romance thriller set in an isolated, post world. Directed by MARYAM
NASEER MIRRAH *AMMEYLAYLERH* SHEIKH JURAIJ THABIT JT follows.
*♡SPECIAL☆*must evade capture while uncovering hidden truths about her past and her
connection to the cult’s terrifying leader. The trailer teases
In a world where trust is a luxury and survival is the only rule.
Alhamdulillah masoya na Asali am back dawo muku da wani fitacce kuma ƙayatacce
ƙasaitaccen labarin dazai ƙayatar daku, Bazan iya misalta muku meya ƙunsa ba sai inhar
kun biyo alƙalamin AMMEY LAYLERHbAnan ne kaɗai zaku fashimta inane alqamin ya dosa,
fatar baku manta da ƙayatattun littatafan nan nata ba irin su. *MIKIYA*
*KAREN BANA*
*JALAAL AREEF*
*ƘAUNA BIYU*
*SANYI YA HAIFA WUTA*
And Ongoing
*♡SPECIAL☆*
Fatan baku manta da yadda kuke nishanɗan tuwa da duka littatafaina na baya ba. Iyaka
waɗan da suka karanta littafinta na MIKIYA to kuwa sune zasu fi kowa bada yadda waccen
tafiyar ya kaya. Se dai wannan ma is not free book shima yazo ne a paid amma kafin nan
akwai free page da zan ba *MASOYA* Masu bibiyana.
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
*_KADUNA MARAFA_*
~012 Alongside films shot~
Cike ƙaton hall ɗin yake da mutane babu ko masakar tsinke.kowa ka kalla zakaga fuskansa na
ɗauke da annurine. Dan kuwa kalla ɗaya zaka ma fuskokin nasu ka gane lallai suna cikin farin
ciki ne matuƙa. Se dai wasu tsirari daga cikin jama'ar dake cike tab da hall ɗin suka soma kallar
wrist watch ɗin dake ɗaure da hannayensu suna jan tsuƙa can ciki ciki. Wasu kuwa suna a cikin
yanayi ne na shiru fuskansa suma yana fara sanjawa zuwa na damuwa. Domin kuwa idan har
akace yauma Babbar jarumi kuma fitacciyar ƴar wasan Hausan nan wato *DIAMOND
MEESHERH* ba zata samu halartar wannan shooting trailers ɗin ba Lallai kuwa da akwai
babbar damuwa. duka mutanen dake zaune a hall ɗin zaka kalla lallai yakai ya kawo ya kuma
taka wani matsayine tabbas, ko daga yanayin murjewan jikkunansu da kuma uwa uba tsarin da
hall yake da.
Wani shahararren tallane na ADD companies Wanda manyan ƙusoshi suka haɗaka wajen
gina shi, Tsaye tsammm shi kansa shugaba a companies ɗin ya miƙe ganin wasu har ransu ya
soma ɓaci. Ehhhh lallai tabbas kuwa da haushi ace yau har kimanin kwanaki uku kullum a jere
suna taruwa iwar haka amma haka suke bajewa ba tare da an gudanar da TRAILER na ADD
companies ɗin ba.
A dai-dai loƙacin ne kuma wata farar mota samfurin ƙirar Toyota Highlander ta yi parking a
harabar hall ɗin. Cikin yanayi na sauri² wata farar matashiya amma ba can ba ta fito daga cikin
motar tana sanye cikin wani baƙar
pleate skirt sai farar oxford shirt wadda ta ɗora maroon suit a kai,wuyanta saƙale da tie se
silver band ɗin dake kanta, gashin kanta wanda ya ji gyara an ɗaureshi cikin pony rail ya zubo
har gadon bayanta. ƙafafunta sanye cikin baƙaƙen sneakers. A kuma daidai loƙacinne hall ɗin
ya ɗauka wani kalan ihu na tarin masoyanta, har wasu na tsalle wanda suke daga waje basa da
ikon shiga ainihin inda za'a gudanar da Trailer ɗin.Hotuna wasu suka fara ɗaukanta wasu na
aikin video wasu na ɗaga takardu masu ɗauke da sunanta me haɗi da tallar ADD
companies.ɗaya daga cikin security female ɗin dake zagaye da wurin ne tayi saurin isa ga
DIAMOND MEESHERH tana saƙala mata Symbol na tallar da zata gudanar.
Cike da mutsuwa take tafiya Fuskarta rufe da mask, ta rufe fuskar ne kuma saboda bata son
takurawar jama'a, duk da kasancewarta mutum me nuna so da ƙauna ga masoyanta, Fuskanta
da kai tsaye ba'a gani ta zare mask ɗin dake kan fuskan nata ganin ta faranta wa masoyanta
Rai. Wani twisting na ihun murna mutanen suka sake saki suna jin ƙaunarta na sake ratsasu.
A natse cikin wannan ɗan banzar izza da mulkin da duk wani ahali daya kasance ɗaya daga
cikin ahali na *JEDAANS POWER MENTION* to kuwa kowa yasan *_Respect and peace_*
ake ƙiran duk wanda ya fito daga wannan Ahalin. Tafiya taci gaba dayi harta dangana da kan
stage na hall ɗin. Tun kamin ta kai ga shigar manyan mara masu gwara kan nera yaran ajebor
suka ɗauka wani kalan ihu suma harda ma waɗan da suka ɗan manyan ta bi ma'ana dattijai
masu rukunin ADD companies kenan. Microphone ɗin da wannan macen security ta farko ta
sake maƙale mata ne ya sanya sakin kyakkyawan murmushi tan nan me kyau. Nan aka soma
gudanar da duk abinda ya tara sun bayan ta nemi afwan su akan cewa wani uzirine me girma
ya ɗan riƙe ta. Seda ta ɗan rumtse idanunta sakamakon tunowa da musabbabin hanata fitan
kai tsaye. Bayan masu camera's sun gama haskata kana suka buƙaci data ɗan gudanar musu
da show haka koda ba me yawa bane. Cike da wannan fara'an da son farantama masoyanta
Kamar yadda suma suke faranta nata ranta ta soma gudanar musu da wani zazzafan show ɗin
daya sake haukata ƙaton hall ɗin. tana tsaka da gudanar da show ɗin ne kuma Moh Saif Ameen
turaki ya bayyana shima cikin hall ɗin nan sukaci gaba da gudanar da show ɗin a tare. Sosae
yanayin ya musu daɗi Kamar yadda suma fam nasu suke jin daɗin show ɗin na yau, dan burin
ransu ne ya cika A yau gasu ga manyan masoyansu,Suna gudanar musu da show a tare wato
*DIAMOND MEESHERH SAMEER JEDAANS* da kuma *MOH SAIF AMEERN JEDAANS* Cike
da jin daɗi da kuma farin cikin kasancewar su a tare Masoya suka shiga ihun murna. Tsitttt
kuma hall ɗin yay sakamon tsaya wa da sukay suna kallon masoyan nasu.
Ihun murna masoyansu sukaci gaba dayi haka har taron ya tashi, Moh Saif ne ya zagayo ta
inda Diamond Meesherh ke tsaye bayanta zagaye da security. Hannunta ya kama bayan
mutane sun gama murnar yin pisc dasu kai tsaye har inda tay parking car nata ya kaita seda ya
tabbatar da shiganta kana shima ya koma yana jan tashi motar ya rufa mata baya. Sun zo
daidai shan kwanar
Mobil filling station na round about wani shegen goslow yay blocking na hanyan.
Ɗan tsuki kaɗan tayi tana jin gundura da zaman motarn baki ɗaya hakan ne kuma ya sanya
Meesherh Jedaans fita don ganin ko me yay blocking hanyan har haka. Duk da kasancewar
face nata rufe yake cikin mask amma hakan be hana wasu ƴan mata biyu da suke cikin napep
kasa gane taba. Wacce face nata ke waje tana leƙen woje ta window'n napep ɗin ta furta
"Laaa A'isha kalla can ki ga kamar Diamond Meesherh Fa?” ta faɗi cike da ɗaukin ganin
babbar jaruma kuma sananniya a duniya. Da sauri wacce aka ƙira da A'ishan itama ta dawo da
kanta setin inda ake nuna matan, "Wllh kuwa Rumaisa itane da da gaske!" Ta faɗi tana ɗan
zaro idonta woje alamun mamaki.
Cike da zumuɗi wacce aka ƙira da Rumaisa ta sake furta.
"Kinga tashi don Allah muje muy photo"
Ɗan numfasawa A'ishah tayi tana sauƙe numfashi tare da duban Rumaisa tana me furta.
"Ki na ganin zata yarda kuwa Rumaisa? Karfa ki manta cewa Diamond Meesherh ⭐ Cikakken
sunanta *Meesherh Sameer Jadeens* wannan shine full name nata bayan haka kuma role
models da duniya jeji da ita gaba da baya. A yanzu haka ita kanta Meesherh Jadeens na ɗaya
daga cikin world billionaires da duniya ke ji dasu ta gama zama cikakkiyarn attajira a loƙacin
data mallaki manyan company's dake tashe a ƙasashe daban daban. Bare azo ga ahalinta kai
tsaye kuma. Kana ƴa ce ga Sameer Jedaans Kuma sanin kankine kamar cewar Meesherh
Sameer itace zuciyar duka alhalin Jedaans baki ɗaya! taya kike tunanin ma zata tankamu bare
ma harta kula mu?.Sannan kuma kin manta cewan duka wasu campanies da zaki kalla na
*MEESHERH LUXURY PRODUCT* Ina nufin M.L.P fa nata ne ko kin manta kamfanine da suka
lashe maƙudan dukiya wajen ƙirƙiran campanies ɗin kawai.
Wanda bako wanne kamfani yasamu irin wannan shaharar ba bayan latex cars da campanies
nata suke ƙera ma duniya. Kana tana da hannun jari da wannan shegen campanies ɗin nan da
ake sarrafa laptops, iPhones da suke ƙerama duniya da duk wasu nau'o'in na'urori kolo daban
daban. Wato babban Ɗa ga JEDAANS kuma me Jedaans ɗin baki ɗaya wato *SHEIKH JURAIJ
THABIT JADEENS*"
A'isha ta ƙarishe maganan tana fesar da numfashi me ɗan zafi daga bakinta.
"Wllh naji mutane kam na yabonta sosae A'isha wllh kamar ba ruwanta"
Sake fuskantar Rumaisa A'ishah tayi kafin ta furta."To shikenan mu gwada sa'ar mu! Allah
yasa mu dace" ta furta suna ɗaukan eskis wa me napep ɗin. Tana dab da shiga motan nata da
ɗaya daga cikin securities ya buɗe mata Cike da ɗoki da zumuɗi Rumaisa ta isa gareta.tana me
furta "Amm.... Am don Allah Sis kozan.... Securities ɗin da suka dakatar da itane suka sanya
Jikin Rumaisa yin sanyi sosae tana jin tamkar ta muzanta kanta, kana tayi kutse wa matsayin
da tasan ita bata isa takai koda kwatar wurin bane. "Ku..ku yi haƙuri amma dama photo ne
kawai zamu ɗauka dama" Ɗaya daga cikin securities ne ya sake doka musu tsawa cikin
buɗaɗɗiyar muryarsa yana furta.
"ku ɓace min a wurin nan, ko kunga Hajiya tayi kolo da ƴaƴan talak....
Shiru yay sakamon tsawar da shima Meesherh Jedaans ta kotsa masa.
A tare securities ɗin duka suka juya suna kallonta. Mask da kuma Baƙin shade ɗin idonta ta
zare tana watsawama securities ɗin kallon me yasa kunnenku har abada baya ji?.
Kana ta juyo da dubanta zuwa ga ƴan matan biyu fuskanta ɗauke da wannan murmushin nata
wanda yake ƙaramar fuskanta kyau. Ta sakar musu tana amsan woyan dake riƙe a hannun
A'isha ƙurar OPPO tana furta. "Ayya I'm a so sorry sister's Password fa?" Ta faɗi cikin muryanta
me shegen daɗi. Jikinsu har rawa yake suka bata password na woyar ta buɗe tana nemo
camera na woyar. kana ta matso tana shiga tsaƙiyansu ta dafa duka shoulder's na ƴan matan
tana ɗaukan su photo. Kuma duk ta ɗauka ne suna kallonta irin na mamakin nan lol.
Wayar ta sauƙe bayan ta gama musu pisc ɗin kana ta koma motarta bayan ta mayda mask
ɗinta fuska, Har driver na shirin tada car ɗin tayi saurin dakatar dashi magana tasa ya mata da
ƴan matan ID card nata me ɗauke da phone nata da kuma full address ta basu kana ta amshi
phone na ɗaya daga cikinsu tana faɗin idan ta sama free time haka zata neme su. Mamaki, Al'ajabi sune suka bi suka sake daskarar dasu Rumaisa a wurin, wuri kuwa tuni ya
cika sedai ita kamm har tayi saurin ba driver umarnin suje kawai don hayaniyan mutanen
harsun fara hawan mata ka.
Kai tsaye katafaren dogon ginin da kai tsaye zamu iya ƙura da da aljannar duniya suka nufa,
Mention ne babba domin kuwa *_Respect and peace_*
Gidane babba wanda a yanzu haka yana daga cikin best and top mansions dasuke most
expensive and attractive a cikin faɗin Nagerian kai harma da duniyan baki ɗaya.Faɗin irin
tsarinsa da haduwarsa ma ɓata time ne abinda kawai zance na sani shine cewan gidane
haɗaɗɗe tsararre kuma ƙerarren dayake gari guda a girma.
Sam bata leƙa ko inda Mah take ba kasancewar a gajiye ta dawo, kai tsaye samanta ta wuce
kasancewan dama bata tarar da kowa ba a parlour'n. Bata fito Sai bayan anyi sallar Isha'i kana
ta saƙko daga saman stairs nata.A loƙacin dakkanin jama'ar gidan suna kammale ne a babban
parlour'n gidan domin yin dinner. Kai tsaye inda Abbie'nta ke zaune ta nufa fuskanta a ɗaure
taki sakinta don ma gudun kada wani daga cikin mutanen parlour'n ya kawo mata wargi.B Tana
sanye ne wannan karon cikin wani Turkey gown Wacce ta fidda shape ɗinta kai tsaye sosai,
inda ta yi rolling gyalen a kanta.Ba laifi kuma tayi kyau sosai cikin shigar illa kawai shape ɗin ta
daya fita sosai ne kawai matsalan shigan nata.
Iyaka iyayensu mata ne a wurin kai tsaye jikin Mah ta faɗa tana maƙaleta "Mah yau duk a
gajiye na dawo amma ko nemana bakiy ba" ta faɗi tana tura bakinta gaba. Bakin data tura
matan Mah ta ɗan mirza ba da yawaba "Ni kuma duk yau na wuni aikine gyaran room na babyn
daddy" Sautin tsuƙin da aka jane ya sanya su su duka kalla duk da kuwa sun riga da sun san ko
wace ɗin tay kai tsaye. Basu wani tanka ba haka har metres ɗin dake aikin ta na saving kowa
dinner tazo ta jerema kowa abinda yake so.
pancake breakfast ɗin da ta fi so with honey aka jere a gabanta, kasancewar harta da
metres na gidan sun san Diamond Meesherh bata cika son abu me nauyi ba. Ta gefen idon
taga sadda ya shigo parlour'n,Nan parlour'n ya sake ɗaukan shiru kowa na rige rigen gaida
babban yayan nasu wato *SHEIKH JURAIJ THABIT TURAKI* Kanta ta ɗauke ko kaɗan bata
nuna wata alamar ta kula da shi ba har kuwa loƙacin daya kai zaune daidai kujerarn dake
pacing nata. Cikin sauri Annie ta miƙe fuskanta babu alamun Rahman ko kaɗan. "JURAIJ tashi
dawo nan!"
Wani irin Shiru daƙin ya ɗauka na wani ɗan loƙaci kafin ka fara jin sauƙe numfashin wasu
mara sauti sosai Domin kuwa kowa ya riga da yasan halin Annie akan rashin son zamar
lafiyanta, da kuma kalan tsanan da tama Meesherh ɗin.
Me ran ƙarfe Jedaans Turaki na shanu dake dap da shigowa parlour'n ne ya ƙarasa shigowa
cikin ɗan hanzarin Sameer Jadeens ya ja may Sofa yana kaiwa zaune. Wani ɓoyayyen
numfashi Sheikh juraij ɗin ya sauƙe mara sauti numfashin sa na cunkushewa da bugun
zuciyarsa, ba tare da yace komi ba ya miƙe da niyar komawa inda mahaifiyarsan ta bashi
umarni Jedaans Turaki na shanu ya ɗauke fuskansa daga kallon bugun zuciyar nashi Sheikh.
"Koma zaune a idda kake"
Haka kowa yaji sauƙan muryan tsohon, Mah ce ta miƙe da niyar barin wurin domin ita
zuciyanta bame iya jure ana wulaƙanta nata bane ta ƙyale. Shirun kuma da tay tsumawa kawai
namomin jikinta keyi ta kuma yunƙuro ne da niyar medama Annie da zazzafan martanin da ke
kusan halaƙa nata zuciyan Muryan tsoho Jedaans ya katse mata tunani. "Kin yi lonch da zaki
tashi ne Zulfa'u?" Haka ta sake tsinkayar Muryan tsohon a karo na biyu. Chakkk ta tsaya ba tare
data juyo ba ta furta. "Ina da buƙatar na kaɗaice kainane kawai Baaba!"
"Da akay mike mene?"
Kai tsaye ya wulla mata tambayrn shima. Shiru tay taƙi bashi amsa zuciyanta na sake turara
da wutar tsanar duk wani JINI daya danganci Annie. wata kyakkyawar ijiyar zuciya me nauyi
tsohon ya kawo yana jin abu ɗaya shine zeyi maganin duk wannan matsalan {*AURE*}
zuciyarsa ya furta mashi idan yace zuciyarsa seda yau tsalle to kuwa tabbas beyi ƙarya ba.
Wani bahagon murmushi kuma ya saki daidai da Shigowan zaratan magidan tan gidan guda
biyar. THABIT JADEENS, AMEERN JEDAANS,SAMEER JEDAANS,JAMAAL
JEDAANS,EL-MUAZ JEDAANS. A natse suka ƙara shugowan kowa na nemar inda ya dace ya
zauna, Baaba suka fara gaidawa kafin daga baya nan ɗaya bayan ɗayan yaran gidan suka fara
gaida iyayen nasu cike da girma mawa. Wancan maganar tuni ya fice suna me fuskantan yin
dinner nasu kawai. Sedai a wasu zukatan lamarin kuwa be shuɗe ba yana nan daram
matankwacin yadda ake ɗora kwarya a gurbinta.
Sheikh juraij Jedaans da yafisu ƙarfin halin danne abu a zuciyarsa ne ya fara miƙewa zuwa
balcony na side ɗinsa.
Idonsa toshe da bakin gilashi ajiyan zuciya ya saki abinda ya danne ƙirjinsa da daɗewa yaji ya
yana ɗan lafa masa yana jin ɗan sassaucin ba kamar ɗazun ba. Shiru yay yana tsaye daga
jikin doguwar Sofa irinta hutawar nan, lumsassun fararen idanuwansa ya buɗe yana fesar da
wani abu me kama da ɓacin rai. Mohan Sameer Jedaans