Showing 3001 words to 6000 words out of 21093 words

Chapter 2 - TA DABAN BOOK COMPLETE By AMMEY LAYLERH.pdf

25 Apr 2025

1805

da tun ɗazun yake tsaye a bayansa
ne yay gyaran murya domin lura da yay kamar juraij ɗin ma be san da tsaiwarsa wurin ba. Wata
coffee cough ya janyo ya ajiye seti da inda Juraij ɗin ke tsaye yana ɗora ƙafansa kan ɗaya
yana tallafar kuncinsa da left hand nashi. A hankali cikin tsanani na nisan kiwon dayay a
duniyar tunani ya buɗe fararen idanuwansa da haskensu ya ɗan ragu na ɓacin ran daya ɗan
wanzu ya sauƙe akan Mohan ɗin wanda babu kamannin kowa akan fuskansa kai tsaye sena
Diamond Meesherh Sameer Jadeens. "Yaayaa sheikh beci ace har zuwan yanzun kana barin
damuwowi irin haka suna brain out naka har haka ba" Mohan Sameer Jedaans ya furta yana jin
shima ƙunci da damuwar gakan na sake mamaye zuciyarsa.
Bayansa ya juya may don a yanzun baison yin magana da kowa hakan da yay ne ya sanya
Mohan fahimtar mi hakan yake nufi. Wani abu me raɗaɗi Mohan ɗin ya haɗiye kafin ya buɗe
bakinsa ya furta. "Idan Yaayaa Sheikh ya dawo daidai ko zuwa safiya ne inason magana da
shine kai tsaye. Hannunsa yaɗan wara may alamun yaje yana jin sadda Mohan ɗin yay may
nisa da barin balcony ɗin ya buɗe fararen idanuwan san yana me bin bayansa da kallo.

*Meesherh*
Bayan bajewan kowa a dining room ɗin ne suka tattauna irin maganganunsu da ya shafi iyaka
su tsakaninta da tsohon daga haka tamay sallama tana wucewanta zuwa nasu ainihin Passes
ɗin.
Tana dap da shiga Annie kuma na kawo kai zata fito daga sassan da tayi niyar janye wa
amma da taga matar ne se kawai ta sa kai tana tafiyar ta. Daga inda yake tsayen yake kallar
komai hakan yasa shi ɗauke idonsa akansu yana jin wani abu me kama da gazawa ko kasawa
na son wanzuwa a ransa. Ganin yana wa'azi domin al'umma dama duniya su zauna ƙalau da
juna se gashi a familynsa sam hakan yana ƙoƙarin ruguzuwa. Zuciyarsa yaji tana sake
cunkushewa da wasu tarin abubuwa maban banta. Wasu shuɗaɗɗun al'amurra da suka jima da
shuɗewa na ƙoƙarin zeroying mind nashi.
Zaune takai gefen bed nata tana duba tarin reports na acct histories na duka companies nata
tana ganin yanda komai ke sake haɓaka kansa, Wasu rubutu masu ɗan tsayi tay kafin ta miƙe
akan laptop ɗin tana faɗawa toilet. Da alwula ta fito duk da kasancewar tasan ba sallah zatay ba
amma kuma hakan ya riga ya gama zama ɗabi'anta tun tana ƙanƙanuwanta, tun tana ƴar
renonsa shi da kansa ya ɗora ta akan duka tsarikansa. Kafin wani rubutaccen Al'amari me
kama da walƙiya yazo ya gitta wannan shaƙuwar. Ko bayan faruwan komai taso ta yafitar duka
al'adunsa sedai wasu kammm samm basu yakitun ba.
Saurin kawar da wancan tunanin tay tana tofe ko ina nata da addaan bacci.
A hankali Moh Ameern ya rufe ƙofar ya mayar sam babu ƙarar takun sa ko kaɗan akan floor ɗin,
shi yasa kuma bata lura ya ƙaraso har gaban gadon ba kasancewar ta riga da ta kashe bals,
bata rufe bedroom nata sauda dama amma kuma saran shigo mata room Kai tsaye da Moh
Ameern ɗin ya kowa ne ya tilasta fara rufe room nata. Ko a yau ɗin ba mantawa tay bata rufen
ba bayan fitar wata mets data biyota da cup me ɗauke da tea party bata na al'ada wanda shi
kansa hakan taso yakitarwa sedai shima hakan yaƙi yakituwan. Zamansa ya bakin bed ɗin

harma yana ƙoƙarin yaya blanket data rufa dashi shine ya farkar da ita daga gajeren bacci daya
soma ɗaukanta kasancewanta mutum bame wuyar bacci ba haka kuma bame wuyar tashi ba.
Zaune tay saurin tashi tana kunna bedside lam ɗin dake gefen gadonta. Ta cikin ɗan hasken
daya haska room ɗin ba da yawa ba ta nuna may hanyar fita a room ɗin tana me furta "Out
Moh!!!" Cikin mugun ɓacin rai. Hannunta yake ƙoƙarin ganin ya lalabo "kinga rilax beb wani
aikine yanzu aka turomin ta email address shine nake son nuna miki ba komi ba!" Ya furta yana sake matsota, "Amma get out nace ma ko?, Ko WhatsApp ba amfaninsa hakan
ba da seka ratso har room nawa? Kodan kawai kaga ina baka fuska shine a kullum kake sake
bayyanar min da munanan halayenka na ɓoye?"
Ta furta da ƙarajin da badan ace ƙofa ce mara fidda sauri da kuwa tsaff kowa da kowa dake a
side ɗin na iya jiwota. A sanyaye ya miƙe yana kama hanyar barin ɗakin. Ak'adansa ne kullum
se yayi zagaye don tabbatar da komi na dede ko wanne matashi kuma na a makwancinsa. Yazo
seti da window'n room nata yaji kamar ihun faɗarta, Hakan ya sanya shi zagayowa domin ganin
komi ke faruwa duk kuwa da yadda zuciyansa ke gargaɗansa akan aikata hakan. Gilmawar
inuwar kawai ya gani amma kasancewar mutum mai kaifin brain da kuma karantar halayyar ɗan
adam kai tsaye ya gane ko wanne ya gilma ɗin.
Dummmm haka yaji kansa ya bada sautin yanajin zuciyan sa kamar ana sauƙeta a ƙasa,
sassan jikin sa kuma tamkar ana kwara musu ruwan suna suna tashi a aikinsu. Da ba ya baya
ya shiga komawa cikin kamalallar takunsa har dogon wandon farar shaddar jikinsa na neman
shatalarsa. Da bibbiyu bibbiyu idonsa suke gani haka harya kaishi ga dangana da sashinsa,
jagwab ya kai zaune amma kuma cikin nutsuwansa da kuma cikakkar kamalarsa yay hakan.
"Kamar Yadda Allah yake juya dare zuwa Rana. Ya Ubangiji na roƙe ka ka juyar da
damuwarmu zuwa farin Cikinmu domin na san cewa ƙaddarorin yanzu ne suka fara! Yanzu
ne LABARINMU zai soma......"


*By Ammeylaylerh*

08104493215

_Tofa Fan's shi kuma wannan nashi salon kenan, da wannan muka fara_

_Jedaans Mention yau kuma ta kansu Labarin ze soma_

_to my fam nawa idan kunason ayi tafiyan daku seku biyo NI AMMEY LAYLERH domin jin
yadda wannan zazzafar tafiyar zata kaya_

_Karfa ku manta sunan wannan littafin TA DABAN, to wai ma wace ta daban ɗin kowa dai a
karan kansa yasan cewar ai shi na daban ne, to kuma ga wata AMMEY'NKU LAYLERH tace
wai ita ɗin SPECIAL ce ta daban...._

_to ya kuke kallon wasan ze kaya? Ya kuma kukaji salon rubutun wannan karon? _

_Ni ban ze ce ma kowa komi ba kawai dai nasan zance mu haɗu a kashi na gaba domin jin
yadda zata kaya_






https://chat.whatsapp.com/DGIo9iiSjlgJPPqFHNtddH

༺༻
*♡ ��☆*
༺༻
_ҽcⅈɑʟ_

ِ
مْسِب_* ِ
هَّللا ِنٰ
َمْحَّرلا *_ميِحَّرلا
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

�� ����� ᴺᵃˢᵉᵉʳ ɱⅈɑһ

_AMMEY LAYLERH_

BOOK ONE………… ✍
Page 3&4

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

_015/01/2025_

Paid Book

*Maman Ihsan tawa duka wannan page ɗin na sadaukar miki dashi kiyi yadda kike so dashi
idan ma kinso ki hana kowa ciki kuwa har dani AMMEY LAYLERH*

*MIKIYA*
*KAREN BANA*
*JALAAL AREEF*
*ƘAUNA BIYU*
*SANYI YA HAIFA WUTA*

✯ *~ JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... �~*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa

su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

# Ⲛᕪᐜ Ⲩᕪᵃʳ'ˢ
# ᑋᕪ ᵗᕪᐢˢᑊᐤᐢ ꕯᐢ ᑋᑊˢ Sᑦᕪᐢᕪ
# SoulmateVibes
# DeeplyInLove
# TogetherForever
# UnbreakableBond
# Endless Love
# SilentLoveAffair
# HiddenHeart
# ForeverAndAlways
# Ɩ૦ Ʀ૦Ꮇᑕ Ⲩ
# ɑ..ɑ ɱɱҽ ʟɑʟҽһ

https://t.me/+ISpf1lql0GwyNmJk

Duk me neman AMMEYLAYLERH ganan link nawa na Telegram Wanda kai tsaye idan kabi link
ɗin ze dinga kaika ga post namu kai tsaye.
https://www.facebook.com/share/1A1gMDViUG/

Sannan kuma ganan na facebook don samun post nawa kai tsaye shima.

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
.... Tun da ta mai da doorhandle ɗin ta koma ta jingina da jikin ƙofan abubuwa da yawo na son
dawo mata. tun da ga loƙacin da tafiyar su tasha banban da juna wacce wata shuɗaɗɗiyar
Ƙaddara tazo ta ratsa tsakani. Haka kuma idan taso wannan ita dai ƙaddarar itane zata zo ta
sake haɗe giɓin data riga da raba shekaru da ɗan dama.A zahirance duk inda Kalmar
KADDARA take to kuwa kowa yasan kalma ce dake motsa zuciyar ko wanne bawa domin kuwa
tabbas wannan kalmar ta KADDARA kalmace me girma da faɗi wacce ta ƙunshi abubuwa masu
yawan gaske. domin kuwa Rayuwa da ƙaddara a tare suke tafiya tamkar ƴan uwa juna.haka
kuma kowacce rayuwa tafe take da nata salon ƙaddarar.
Idan har bawa zeyi haƙuri wajen jure wannan tarin ƙaddarorin da suke jerin gwano a cikin
kowanne rai mai numfashi game da duk abinda ALLAH ya riga da ya ƙaddara a cikin
rayuwarshi,To kuwa duk ALLAH Ya zaɓa maka shi ne mafi alkhayri agareka.
♡ Wani kalan Runtse rinannun idonta tayi sakamon kanta da taji ya wani kalan mugun sara
mata da tsanin ciwo. Zaune takai bakin bed haryanzun hannuwanta riƙe da saman kanta dake
jujjaya mata. Alamun zurfi datai a tunani nason haifar mata da wani damuwan. Wani kalan
zazzafan numfashi ta fesar tana hana kanta bama damar tunanin. Domin kuwa ita ɗin mutumce
me tsananin taurin kai da kuma ƙarfin zuciya. Ba kowanne abu take bama yay crossed mind
nata ba, Wanda kai tsaye duk ta koya hakan ne daga garesa kasancewarta renonshi ce ita ɗin.
Ƙin bama ko wacce ƙofa dama tayi na zurfi a tunanin dake son bijiro mata. Knocking
doorhandle ɗin da akai ne ya katse mata tunani, zuwa loƙacin jikinta har rawa yake a mugun

wahalce ta nufi doorhandle ɗin tana buɗe. Mah ce Mah ɗin ta ce dama ta sani tasan itace don
kuwa bata iya kwanciya duk daren duniya se tazo taga Meesherh ɗin. Saurin rungumata Mah
ɗin tay "Subhanallahi Meeshel ɗin Papiey'nta What wrong? Me ke damun ki?" Duk kuma seta bi
ta ruɗe kasancewanta auta kuma ƴa mafi soyuwa a zukatan iyayen nata. Ganin duk yacce Mah
ɗin tabi ta ruɗe ne ya sanya Meesherh ɗan janye jikinta ana Mah ɗin tare da ƙaƙaro murmushin
dole tana furta.
"Headache ne kawai fa Maayh, Don't worry karki woni damu" ta furta wai duk a sonta na
kwantarma Mah ɗin nata hankali. "A ahhh ban Isa ba wllh Meesherh dole ko dactor Asia tazo ta
duba min ke" tay maganan ne kuma tana laluben number na dact ɗin, Maganan second sukai ta
datse ƙiran. Kai tsaye kuma ta maida akalan ƙiran kan Billionaire Sameer Jadeens. Se dai jin
ring na woyar dap da ƙofarn shigowane ya sanyata katse ƙiran, Cikin yanayi na nutsuwa da
hutu da wayewa suka gama ratsawa ya sanyo kansa bedroom ɗin.
Yana sanye cikin kamilallar shiga ta blue in jallabiya ta maza se hular nan irin ta kafiye nacin
nan. Zama yay a gefe da daman Meesherh ɗin suka sanyata a tsaƙiyansu. "Ꮇҽҽ ᙏααɳα
ђқ?" Kai tsaye prof ���� Jedaans ya tambayi Meesherh daidai yana kai hannunsa saman
goshinta. Maganan dayay shirin yine ya tsaya may a maƙoshinsa sakamakon knocking door ɗin
da akai. Umarnin shigowa kai tsaye suka bada don sun san Dr Asia jamaal ce ta ƙara so. A
natsenta ta shigo har cikin bedroom ɗin, gaidasu tay cike da mutumci da girmamawa take
kuma ta shiga duddubata Injection ta mata tare da ajje mata magunguna ganin ba normal
damuwa bane ya sanya Dr ɗin duban su Mah tare da furta. "Don't think about it totally don't
worry, the only stress paining her Ina ganin da zarar ta ɗan sama natsuwa shikenan zata
warware Insha Allahu" daga haka Dr ɗin ta musu sallama ta tafi bayan sun mata godiya.Ring
ɗin da woyarta a ɗauka ne ya sanya ta duba me ƙiran. Yayartace Ummetah mebin Mohan
Sameer Jedaans se ita kuma data kasance autarsu, "Meesherh kince zaki ƙirani baki ƙirani ba
tun ɗazun right?" Cikin muryan da yay low Sosai ta furta. "I'm sick fa Aunt"
"Subhanallahi Meeshel baki da lafiya amma baki sanar min ba?"
"No karki woni damu headache ne kawai da wata ƴar damuwa ya haifar min hakan" daga ta
can ɓangaren Aunty'n nata ta furta. "Bara na barki kiyi bacci se zuwa tomorrow morning Insha
Allah" daga haka suka yanke woyan tana me sake komawa jikin Mah ta kwanta abinta.Duka da
kallo suke binta a loƙacin da suka gama tabbatar ma cewan tayi baccin. "Allah ya inganta min
rayuwar ki Meeshel!, Allah ya dafa muku gaba ɗaya daga ke har ƴan uwanki ya kuma raba min
ku daga sharrin masharranta cikin gida dana woje" tayi maganar tare da jaho hannun Meeshel
ɗin ta haɗe da ƙirjinta ta rungume,prof kuwa sai wani kalan murmushi kawai yake saki. Shima
jikin Mah ɗin yaɗan motsa kaɗan yana kwantar da kansa setin shoulder nata. Yana rungumeta
Ya jima sosai rungume da Mah ɗin,Nan ya shiga musu addu'a shima Mah ɗin na amsawa da
ameen.
Seda suka gama tabbatar ma da kansu cewan baccin yay mata nisa sosai kana suka ja mata
duvet suna rufeta kana suka fita bayan Prof Sameer ya sake mata adda'an bacci.

The great Billionaire juraij Jedaans ne zaune kan wata ƙerarriyar cough yana snye ne cikin
wata rantsatstsiyar lallausan farin yadi wanda yake lafe a farar shiny skin nashi wanda kai tsaye
ke bayyanar da asalin hutu da luxurious life ɗin dayake cikinsa. Fuskansa sakaye cikin wani
yankakken farin gilashi, System ce a gabansa ya zuba mata fararen idanuwansa wanda a

zahirin gaskiya bawai kallon nata yake ba ya tafi ne duniya irin ta tunani.
Wani zazzafan numfashi mara sauti ya fesar jin yanda zuciyarsa ta sake karta masa a karo na
ba adadi.Yasan kaff duniya haka kuma kaff rayuwar Sheikh juraij Jedaans babu abinda yake
haɗawa da bautama ubangijinsa haka kuma shi kaɗai ne abinda keda tsananin mahimmanci
da girgiza dakkakiyar zuciyarsa. Me bi ma hakan baya kuma ita ce Zuciyarsa! Bugun numfashin
sa *MEESHERH SAMEER JEDAANS* domin ita ɗin ta kasance tamkar renonsa ce. Duk da
cewar Ƙaddara ta riga da ta buɗe tafin hannun kowannensu ta masa zanen rubutacciyar
ƙaddararsa, wanda har hakan kai tsaye yay sanadiyar ban bancin ra'ayin su koma yace
rabuwar su. Hakan ba shike nuna cewar ze barta har abada ba, kana hakan ba shike bayyana
cewar ze barta taci gaba dayin duk kalan abinda taga dama, sosai yaji ransa ya sosu da ganin
fitar Moh Saif Ameen a ɗakin nata wanda Allah ne kaɗai yasan yadda ya kwana da wani kalan
masifan ɓacin ran hakan a daren jiya. Wani gauron numfashi ya kawo yana sake zubama laptop
nashi farare ƙal ɗin idanuwansa.
Pisc na Meesherh yake kalla a cikin laptop ɗin idanuwansa har kalan bala'i bala'in yaji suke mai
na ɓacin ran ganinta cikin wasu shegun riga da wando outpit. Wanda kai tsaye yake tabbatar da
cewan a shooting film ne tayi koda ma a cikin Film ɗin ko waƙa. Ya rasa me Meesherh take
nema a duniyar ta rasa dahar ta jefa kanta cikin shirin fina finan Hausa. Idan suna take da
buƙatar yi ya tabbata Kaff Duniya babu inda sunan *JEDAANS POWER MENTION � PEACE
and RESPECT* be gama zagaya da kareɗe wa ba a duniya. Haka kuma Idan kuɗi take da
buƙatar ya tabbata ita kanta tana da dukiyar da bata san iyakarta. To amma me take da buƙata
a wasan Hausa?
A har kullum kwanan duniyar shine tambayar daya rasa amarya har zuwa yanzun kuwa da
yake a zaune gaban System nashi. Idan kuma yay duba da yadda Ubangiji yake juya
lamuransa daga kyawawa zuwa munana se ya sake jinjina lamarin ubangijin da babu kamarsa
a duniya dan kuwa shine kaɗai wanda ya isa yayi abinda babu wanda ya isa juya hakan. dan
yana da tabbacin idan wani na juya ƙaddarar wani da tuni ya jima da juya ƙaddarar Meesherh,
A kaf cikin duniyar nan ya tabbata babu abinda ya rasa a rayuwa hakama babu abinda bazai iya
zubar wa domin ganin ya dawo da Meesherh kan hanya se dai wannan maganar ta *TUN RAN
GINI* da tsarin ƙaddararta ya daɗe da rubuta komai da ze wakana da rayuwar ko wanne bawa
nashi. Amma duk da haka bazai gajiya ba wajen kaima Allah kukansa kan ya dawo mai da
Meeshel ɗin sa hanyar daidai.
Janye fararen idanuwansa da sukai ja yayi a kan laptop ɗin a sanyaye kuma ya maida ya rufe
yana sauƙe numfashi me zafin gaske. Knocking ɗin da aka danna ne ya sanya shi dawowa
duka cikakken tunaninsa. "Yes Come In" cikin wannan kamilallar muryan ya bada izinin
shigowa. Mohan Sameer Jedaans ne ya shigo hannunsa riƙe da wani kyakkyawan farin yaro
mai tsananin kamanni da ubansa,shi kuma uban me irin kamanni ɗaya Meesherh Sameer
Jadeens. A natse ya iso har inda yake Sheikh ɗin yake zaune,zama yay natse domin badan ban
bancin kamanni ba da babu abinda zai hana ace uwa ɗaya uba ɗaya ne suka haife su ba.
Yanayin sanyinsu iri ɗaya da yanayin shiru shiru ɗin su da kamala, wannan kamannin banbanci
shi ne kaɗai ze nuna maka cewan ba uwa ɗayan ce ta haifesu ba, sedai duk da haka suna
fisgen kamanni na alaƙar jini me ƙarfin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login