Showing 1 words to 1591 words out of 1591 words
Chapter 1 - LABARIN KALALA DA KALALATU, Magana Gari ce .pdf
 LABARIN KALALA DA KALALATU 
 
Littafi: Magana Jarice 2 
Mawallafi: Margayi Alhaji Abubakar Imam 
Inda za ku samu : arewanovels.com.ng 
 
Akwai wani mutum wai shi Kalala, yana da matarsa wadda a ke kira Kalalatu. Kalala Allah ya yi 
shi wani irin mutumin da ne, ba abin da ya fi da qi illa a yi masa abinci ya ci shi kadai. Da suna 
ci tare da wani makwabcinsa, sai makwabcin ya zama wani iri ne mai mita. Ya kan rika cewa 
Kalalatu ba ta iya miya ba, wai kullum miyarta daga ta cika gishiri sai ta cika ruwa.  
Da Kalala ya ga tsegumin yafa yi yawa sai ya bar kai abincinsa wurin mabwabcin. Ya riqa fita 
karauka yana nemo baki, yana kawowa  gidansa  suna ci tare. 
 
To, Kalalatu ba ta kaunar wannan  dabi’a  ta  mijinta,  domin bisa ga misali, ran da Kalala ya 
yanka kaji biyu, iyaka Kalalatu ta sami cinya, domin duk Kalala zai kai wurin  bakin da ya jawo 
ne  su cinye. Ta yi, ta yi ta hana shi wannan dabi’a, ya ki hanuwa. Saboda haka sau da yawa in 
ya ba ta dahuwa sai ta tsame rabi ta cinye, in Kalala ya yi magana ta ce ya kone ne, ko kuwa ta 
ce ta sauke ta shiga daki dauko kwano, kafin ta fito ta tarar kyanwa ta cinya rabi. Dalilai dai irin 
wadannan marasa kan gado ga su nan kullum Kalala na ta sha, amma saboda hakurin da Allah 
ya zuba masa ba ya cewa kome. 
 
Ran nan, ko ina Kalala ya sami kudi sai ya tafi kasuwa ya nemo dakwalen kaji guda  biyu  ya 
sayo.  Ya  yiwo cefane  ya  kawo gida, ya ce wa Kalalatu ta soye kajin nan gaba daya. Ta tashi, 
bayan ya  fige ya gyara mata, ta sa tukunya ta shiga suya. Abu  ga dakwalen kaji, duk kitse yâ 
cika tukunya, sai wani abu su ke coi, coi, coi, in tana juya su. Duk kuwa kwadayi ya kama ta, da 
ma ga ta idonta idon nama sai ka ce kura sai yawu ke zuba dalala. Ta sa dan yatsa ta dandana 
ta ji ko gishiri ya yi daidai, sai ta ji abin dadi ya kamo ta har ga keya, ta ce, “Kai, wadannan kaji 
yau suna shirin ganin wata irin gajerar suya. Amma  dubi  duk  yawan  kajin  nan,  rabona bai fi 
cinya ba daga cikinsu. Ka san dai halin mai gidan  nan  ya miskile ni.” 
 
Ta ci gaba da suya qanshi na jifarta, ta yi kamar ta jure ta  kasa, sai  ta fara  tsame tana ci,  wai 
ta  kau da  mugun  yawu.  Kafin  su soyu ta kusa cinye rabin kaza. Da ta sauke  sai  ta  je  ta  
gaya  wa mijin  sun soyu. 
 
Kalala ya ce, “To, sai ki cire cinya guda, taki ke nan.  Saura kuwa a ajiye, har in je in samo 
abokan ci.” 
 
Kalalatu ta ce, “To.” Ta tafi ta  cinye  ’yar  cinyar  da  aka ce ita ce tata, ta tsuguna tana kallon 
saura, sai mai ke zuba nash, nash. Ta ruga wajen kofar zaure ta leka ko ta hango mijin  tafe  da  
bakin, ba ta ga kowa ba,  ta  komo  wajen  kaji  ta tura musu  ido. Sai ta ce, “Af, ashe ma 
fikafikai guda biyu  sun  kone  tun dazun, bari in cinye na dayar kuma don su zo daidai, kada 
mai gida ya gane.” Sai ta kama fikafikai ta fiffizge ta  lakwame. Ta sake rugawa bakin zaure ta 
gani ko mijin na tafe, ba ta ga kowa ba. Ta dawo, ta tsaya bisa kwanon da kaji su ke, ta ce,
“Shin mai gidan nan zai zo dai? Ga kaji har sun fara yin  sanyi.  To, ni Kalalatu, yanzu in ya zo 
ya tarar wannan kazar duk na fiffige  ta, ya  tambaye ni, in ce me? Ba abin da yafi sai in cinye ta 
gaba daya, in ya zo in ce kyanwar gidan nan ta sace ta.” Sai ta tsuguna ta cinye ta sarai, ta 
kwashi kasussuwa ta kai masai ta zuba.  
Ta koma kofar zaure ta hanga, ba ta ga mai gida ba. Da ta ga haka sai ta dawo, ta ce, “A bari ya 
huce shi ya kawo rabon wani. Bari in karkare cinya guda, kowa ya huta, in ya so in  ya dawo 
kome ta  tafasa ta  kone.” Sai   ta   kama   kazar  guda   kuma   ta lakwume. Ta nufi randa ta 
debi ruwa ta kora, ta yi gyatsa, ta ce, “Madalla,  kome ta  ke zama  ta zama.”  
Ta zauna ke nan, sai ga mai  gida  ya  shigo.  Ya  ce  wa  Kalalatu, “Yi maza ki nika yaji ki 
barbada musu, kin san yanzu lokacin sanyi  ne, ba abin da ya fi yaji amfani.  Na  manta  ne in 
gaya miki   ki nika yaji dazun. Yi hakuri, yau dai kin sha aiki.” 
 
Kalalatu ta ce, “Ai ba kome, ku dakata mini dai kadan.’ Ta shiga daki tana ta shawarwarin abin 
da za ta ce wa mijin ya faru  ga kaji. Tana can cikin daki, sai Kalala ya dauki wuka ya nufi 
manika yana wasawa kararas, kararas, wai don ta yi kaifi ya sami ta yanka kaji kanana kanana, 
in an  kawo.  
Kalala na can na ta fama da washin wuya, sai Kalalatu ta ji ana sallama. Ta yi farat ta fita bakin 
zaüre wajen mai sallama, ta dube shi ta rike baki, ta ce, “Kai bako, kai ne mai gidan nan ya 
kirawo, wai ku zo kucï abincï?”• 
 
Bako yace, “I, Allah ya saka  muku dâ alheri.” 
 
Kalalatu ta ce, “Kai, tafi can, sakarai' ba  ka san abin da a  ke ciki ba. Kana tsammani mutum 
mai hankall ya sa a yi masa abinci ya fita karauka neman abokin ci? In kana kama gabanka ka 
ruga, tun da wuri ka ruga. Ka ji shi can yana washin wuka, kunnenka guda  zai yanke.  Kullum  
haka  ya  ke yi, motsattse ne.”  
Bakon nan, ko da ya saurara ya ji Kalala na washin wuka sai ya dafe qeya ya zura a guje. 
Kalalatu kuma ta ruga wajen Kalala, ta ce, “Ga irin jaye-jayen naka nân, ba ka san irin mutanen 
da ka ke jawowa gida ba.” 
 
Kalala ya ce, “E?  Mahaukaci ne?” 
 
Kalalatu ta ce, “Mahaukaci mana, ko ba mahaukaci ba ne ai barawo ne, da barawo ko da 
mahaukaci ai duk tafiyarsu ke nân. Kajin da na barkadawa yaji, ko da ya gan su sai naga ya yi 
wuf ya fizge, ya shafa a guje da su. Ga shi can ya mika, ya tasarwa kasuwa.” 
 
Kalala ya fusata, ya ce, “Allah wadan dan banza! Mutanen duniya ba wanda ke iya musu. Da 
ma ya bar mini ko da guda daya, ai da na sami ta kalaci. Dakwalen kajin nan duk ya cinye shi 
kadai? Bari in leka ko na hango shi, mu raba.” Sai ya ruga wajen zaure ya hanga, sai ga bakon 
nan can ya tattake da gudu kaca kaca kaca yana korar iska. Kalala ya ce, “Kai abokina! Kai
tsaya, don Allah ko guda daya ka ba ni! Wallahi su ke nan, mai dakina ko lasawa ba ta yi ba, ka 
dauke.” Bako ya yi kamar bai ji ba. 
 
Kalalatu ta ce wa mijin, “Bi shi mana, a guje dai na san ba ya tsere maka. Duk wahalan nan da 
na sha ta zama a banza,  ko lasawa ban yi ba, ai ka san ka dauki alhakina.” 
 
Sai dalala ya runtuma a guje da wukarsa a hannu, ya bi bako yana  kira,  “Tsaya don  Allah,  
daya  kadai na  ke so, na  bar maka daya!” 
 
Bako tsammani ya ke Kalala na nufin kunnensa daya kadai ya ke so ya yanka. Ya waiwaya sai 
ya  ga  ya  taso  masa  da  wuka  tsirara  a hannu. Saboda  haka ya kara mai,  ya dai  yi wa 
Kalala fintinkau  yana ji yana gani. 
 
Da Kalala ya ga abin ba girma, sai ya juyo ya nufo gida da wukarsa a hannu, yana kutawa, 
yana Allah  ya isa.  Da  matar  ta ganshi ya dawo yana zage-zage sai ta tarye shi, ta ce, “Ya ba 
ka? Ka ga irin abin da na  ke gaya maka nan  tuni.” 
 
Kalala ya ce, “Ko tarad da shi na yi? Wannan akwai dan banza da gudu! Ga shi kamar tsoho, 
amma da ya zura sai ganinsa a ke kamar ba ya taka qasa. Bar shi ya je ya ci, ban dai yarda 
masa ba duniya da lahira. Allah ya isa. Daga yau ko sai yau,  ba  na  sake kiran dan kowa yaci 
abincina, tunda duniya ta sake. Mts, Allah wa- dai! Talaka dai ba aboki ne ba, ko ka so shi . ran 
biki kwa bata.” 
 
Mutane da suka ji wannan labari suka fashe da dariya. Da suka yi shiru Waziri ya soma:









