Showing 1 words to 2950 words out of 2950 words

Chapter 1 - LABARIN KOSAU DAN SARKIN NOMA NA FARI by Alhaj Abubakar Imam .pdf

LABARIN KOSAU DAN SARKIN NOMA NA FARI.
Cigaban Labarin Sarkin Noma da 'ya'yansa II

Littafi: Magana Jarice
Mawallafi: Maegayi Alhaji Abubakar Imam
arewanovels.com.ng

Kosau kuwa da ya bi gabas, yana cikin tafiya, a kwana a tashi, ya kai wannan gari ya wuce, ya
kai wannan gari ya wuce, har Allah ya kai shi Sabon Birni. Da isarsa garin, da zai tambayi gidan
wani mai harka ya je ya yi barantaka, sai wata zuciya ta ce masa, “Kai Kosau, gadon gida alala
ga raggo, kowa ya bar gida gida ya bar shi.” Saboda haka ya tambayi gidan Sarkin Noma, aka
kai shi, ya sallama ya shiga.

Da suka gama gaisuwa da Sarkin Noma, ya kwashe abin da ya rabo shi da gida duk ya fadi. Da
Sarkin Noma ya ji haka sai ya ce, “To, in abin da ka fadi hakanan ne, zama da ni ba zai yi maka
wani alfanu ba, don ni ma manomi ne, ka ko san ribar noma sai mai hakuri. Kuma ma da
ubanka na son ka ka yi noma, ai da ya bar ka wurinsa. Abin da ya fi kyau sai ka sake wata
sana’a, don in ka zauna wajena an yi ba a yi ba ke nan, juyin gatar fara.”

Kosau ya ce, “Ni dai gare ka zan zauna, arziki duk ga Allah yake.”

Sarkin noma ya ce, “Hakanan ne.” Suka zauna nan da Kosau, ya bauta masa iyakar zarafi. Da
suka sami kamar wata tara, Sarkin noma bai ga Kosau ya yi masa wani abin Allah wadai ba, ko
da rana daya, sai ran nan ya kira shi, ya ce, “Ai ko lokacin komawarka gida ya kusa ko?”

Kosau ya ce, “I, zuwa saba’a wa ashirin ga watan nan na ke son na yi harama.”

Da lokacin ya yi Sarkin Noma ya ce "Yau wata tara kenan kana bauta mini. Rana daya kuwa
ba ka yi mini wani abin tashin hankali ba, tun ran da ka fara yi mini aikinka na ko wace rana.
Yau abin da na gani gare ka fam takwas da sule goma. Yanzu ka zabi daya, ina da wani
dan’uwa mai ba fatake sa’a in za su Gwanja, in kana son in kai ka ya ba ka sa'a , sai ka kai
masa fam takwas din nan da sule goma. In kuwa ka fi son kudinka, ga su, Allah ya gama
fuskokimmu da alheri.”

Kesau ya ce, “Tun da ya ke haka ne, baba, na fi son a ba ni sa’a. Ai malamai sun ce sa’a ta fi
manyan kaya.”

Sarkin Noma ya ce, “Ka fi son sa’a?”

Kosau ya ce, “I.”

Sarkin Noma ya tasa shi gaba, ya kai wajen kanen nan nasa wanda a ke kira, Malam Lamiri, ya
gaya masa duk abin da suka yi da Kosau.

Da Malam Lamiri ya ji haka sai ya dubi Kosau, ya ce, “Ai ko ka yi kasada, samari. Karbi
kudinka ‘ka tafi, kwai abaka yâ fi kaza a akurki.”

Kosau ya ce, “Ni dai a raina na fi son sa’a, sai dai na fawwala maka, abin da ka ga ya fi, shi
zam bi.”

Malam Lamiri ya ce, “A gaishe ka samari! Sai ka tashi gobe saba’a wa ashirin, in rana ta yiwo
guda za ta fito, tun ba ta baje ba. Allah ya taimake ka. Amma ka kula da abubuwan nan uku
da zan gaya maka. Na fari ko wane gari za ka shiga ka shige shi ta kofar yamma, in za ka fita
daga gare shi ka fita ta kofar gabas. Na biyu, kada ka kwana wurin da ruwa ke wuya. Na
uku, ka lura kuma kome tsoron da ka ke ji kada ka kuskura ka shiga gari da magariba. Shi ke
nan, ga sule uku ka yi guzuri. Allah ya taimake mu.” Kosau da Sarkin Noma suka fita.

Gari na wayewa, ko da rana ta yiwo guda, kosau ya shirya, ya sallami Sarkin Noma, ya sami
wadansu fatake ya shira cikinsu. Suna cikin tafiya, ran nan sai suka kai wani gari goshin
faduwar rana. Da har Kosau zai shiga, sai ya tuna da kofar da za su shiga ta arewa ce, shi ko
an ce masa kullum ya shiga ta kofar yamma. Saboda haka ya rabu da sauran abokan tafiyarsa,
shi ko ya kewaya ya tasar wa kofar yamma. Amma da ya ke garin na da yawa, kafin ya kai rana
ta fadi. Sai ya sami wuri nan bayan gari ya zauna har gari ya waye ya shiga, don Malam Lamiri
da ya bashi sa’a ya gaya masa kada ya shiga gari da magariba.

Yana nan zaune kofar gari, sai kuma ya tuna a ransa Malam Lamiri ya ce masa kwa ya yarda
ya kwana inda ba ruwa. Saboda haka ya ga ashe bai ga ta gindin zama ba tukun, sai ya
tashi ya yi ta yawo a bayan gari yana neman wata 'yar rijiya, ko wani dan rafi, ya kwanta
kusa da shi, har ya kai hurumin mutanen garin. Ya shiga yana ta kewayawa, yana famar
neman wajen ruwa, har Allah ya sa ya yi kici6is da wani tabki cikin hurumin nan ya je bakinsa
ya ajiye ’yan kayansa, ya kwanta. Can sai ya ce a ransa, “Da in kwana nan daji, ba
gwamma in tashi in rika yi wa Musulmin da aka binne wurin nan addu’a ba?” sai ya tashi
ya yi ta binsu yana yi musu addu’a.

Yana nan, zuwa talatainin dare ya ga hadarin ruwa ya taso, aka ko tsinke da ruwa kamar da
kwarya. kosau ya rasa inda zai sa kansa ya fake. Ya yi shawara ya shiga wani kogon
kuka da ke nan kusa, ya ga ba ya da girman da zai hoye shi. Saboda haka ya ba mutuwa kai,
ya fito waje ya tsuguna yana zargin kansa da wautar da ta sa ya ki karbar sulensa dari da
saba’in, ya huta da azaba.

Yana nan tsugunne yana makyarkyata, bayan an dauke ruwa sai ya ga wadansu mutane biyu
sun sako wani akwati-akwati daga bisa garun birni. Da ya fado kasa su kuma suka biyo ta
magangari suka fito. Suka dauki akwatinsu suka kai shi kogon kukar da Kosau ke shawara da
ya shiga, suka jefa. Suka koma gari, guda kamar zai taka kafar Kosau, don ana duhu
ba su gan shi ba.

Da suka wuce Kosau na tsammani 6arayi ne suka sato wadansu kudi suka boye nan. Saboda
haka ya tashi da murna, yana cewa a ransa, “Sa'a ta ci!” Yaje ya leqa cikin kogon, ya zaro

akwatin, sai ya ji shi jin-jin: Allah ya sa ba a kulle da kwado ba. Ko da ya ajiye kasa, yana dokin
zai buda ya kwashe abin da ke ciki, sai ya ga akwatin na motsi. Ganin haka fa ya ba shi
tsoro, har ya ja da baya zai ruga. Sai ya tuna Allah daya ne, ya dawo. Budawar da zai yi
haka, sai ya ga wani mutum a kwance ciki, sai numfashi ya ke yi dai dai. Kosau ya dube shi,
ya ce, “Kai taliki, mutum ko aljan?”

Mutumin nan ya ce, “Mene ne kuma na tambaya? Ku dai ku ida nufinku ku huta, amma ku
rubuta takarda ku yar, don in ’yan’uwana sun gani hankalinsu ya kwanta su dangana.”

Kosau ya dube shi hawaye na zuba, duk akwati ya cika da jini, sai ya ce, “Nan yanzu a hurumi
na ke, wadansu mutane suka zo da kai, ni ba ruwana. Ina nan labe na ga sun jefa ka cikin
kogon nan. Na yi tsammani barayi ne ke boyon kudi, shi ya sa na zaro ka. Gaya mini
labarinka in ji ko na iya taimakonka.”
Mutumin nan ya ce, “Ni yanzu kusa na ke ga mutuwa, ba na iya ba ka wani labari. Kai dai in
kana iyawa, taimakan ni daga baya in ina da sauran kwana gaba ka ji, in ko ba ka iya
taimakon , don Allah dauki wani dutse ka fasa kaina, in iyad da mutuwa in huta.”

Tausayi ya kara kama Kosau, ya dauki tsumman rawaninsa ya daure wani sara da ke zubar jini
a cinyar mutumin nan. Da gari ya kusa wayewa sai ya lallaba shi ya tafi da shi wani dan kauye
nan yammacin gari, ya ce dan uwansa ne, barayi suka tsare su. Aka ba su daki. Kosau ya yi ta
jiyyar mutumin nan, har Allah ya sa ya warke sarai. Da ya ga ya warke sa’an nan ya tambaye
shi sunansa, da sana’arsa, da kuma abin da ya sa wannan abu ya faru.

Mutumin nan ya ce, “Sunana dai Maikoma, sana’ata ko suu. Wata rana wani dan tsoho gajere
fari, mai ido guda, ya zo ya ce in ba shi sadaka don Allah. Na ji tausayinsa, na kawo sule, da
wata tsummar riga tawa, da wando, da hula, da rawani, na ba shi, ya yi godiya kwarai ya tafi.

“Dare na yi sai ya komo gidana, ya ce ni kuma me na ke so ya yi mini. Ka san kowa ba abin
da ya ke so ransa illa a san shi bisa kan sana’arsa. Saboda haka na ce ni ba ni da wani buri sai
daya, kome ya shiga cikin komata sa’ad da na ke su ya zama kifi, ko da ganye ne, ballantana
su kwadi masu rai. Sai tsohon nan ya yi murmushi, ya ce mini da tsakad dare wata aljana za ta
zo wajena, kada in ji tsoro in tambaye ta abin nan da na ce ina so. Ya gaya. mini wani ganye
kuma, ya ce duk sa’ad da na so ganinta in turara shi a dakina, ta zo nan da nan.

“Da dare ya yi tsaka kuwa ta zo, na tambaye ta, ta ba ni wannan iko. Da sauran ’yan uwa
suka ga na fi su suu, duk garin ba a maganar kowa sai ni, sai suka tasam mini har suka yi
dabarar da suka rabo ni da garimmu watan jiya, don su zo da ni nan garin su kashe ni. To, su
ne ka ga sun miqo ni ta kan ganuwa. Tsammani su ke sun kashe ni, ba su san ina da sauran
kwana gaba ba. Yanzu gobe daren Lahadi zan yi maka alheri guda, ni kuma. In aljanan nan ta
zo wajena zan gaya mata duk wannan abin da ya faru, in ce ta taimake ka in da dama.”

Kosau ya yi godiya, sa’an nan ya ce, “Ka ga tsohon nan da ka ke labari, lalle shi ne ni kuma ya
ba ni sa’a, sunansa Malam Lamiri. Ko bai gaya maka ba?”

Maikoma ya ce, “Lamiri kuwa.”

Kosau ya ce, “Lalle ya san haka zai faru ne, shi ya sa ya ce mini in zo don in taimake ka.” Ya
kwashe labarin da ya gudana game da shi da Lamiri duk ya fada wa Maikoma, suka yi ta
tu’ajjabi.

Kafin rana ta fadi Maikoma ya nemo ganyayen nan na turare ya ajiye. Sai da ya bari ba
sauran mai motsi, sa’an nan ya tashi ya dauki ganyen nan ya turara. Turarawarsa ke da wuya
sai aljanan nan ta fito. Ya kwashe duk abin da ya gudana gare shi ya gaya mata. Da ta ji sai ta
ce, “Ayya! Haba, gaskiya na ga ka rabu da kirana. Ina yaron da ya taimake ka? Shi ne nan
ke barci? To, tashe shi, mu kuma mu saka masa, ai tun kamar wata guda ke nan Malam Lamiri
ya ba ni labarinsa.” Aka ta da Kosau, suka gaisa da aljana. Da suka gama gaisuwa ta tambaye
shi abin da yake so.

Ya ce shi ba ya son kome sai in ya koma gida ya zama duk abin da 'yan’uwansa suka samo
nasa ya shafe nasu.

Aljana ta dauki wani zoben gorar ruwa daga hannunta, ta ce masa, “Karbi, ga sakayyar
aikinka nan.”

Kosau ya karba ya sa a hannu bai san amfanin zoben nan ba, aljana ta bace. Ya dubi zobe, ya
ce wa Maikoma, “Ko kai ka san amfanin wannan zobe? Ko na sayad da shi dai ba ya yin ahu.”
- Maikoma ya ce, “Wallahi ko ni ban san amfaninsa ba. Tsammani na ke da ko kudi za ta ba ka.
Abin da ya fi da wannan shiriritar, gobe sai ka bi ni garimmu in taimake ka da guzuri, kada
’yan'uwanka su yi maka dariya.”

Kosau ya ce, “Ai ba dama in koma baya, yanzu saura kwana uku ke nan mu gamu a inda
muka yi alkawari. In ma ba zango na ci ba sai na saba. Yanzu dai tun da ka warke sai mu yi
sallama, da asuba ni kuwa in rarrafa ko na rage hanya.” Suka yi sallama har da koke-koke don
sabo.
Asuba na yi Kosau ya tashi ya kama hanya, yana ta qutawa. Am ba shi sa’a, bai ga sa’ar ba.
Ya yi kamar ya yad da dan zoben nan don haushi, ya ga in ya yad da shi ba abin da zai nuna
wa ’yan’uwansa da ubansa, sai ya bari. Yana cikin tafiya, can ya kai qungurmin daji sai gari
ya waye. Ya nemi ruwa kasa da bisa ya yi alwala, ya rasa, sai ya tsuguna ya bugi kasa ya yi
taimama, ya ba da farali. Abin ka da wanda ba malami ba, bai san cire zobe ake ba in za a yi
taimama, shi sai ya buga kasa da shi sau biyu yana kakka6ewa, sa’an nan ya shafa a fuska,
ya shafo zira'ar hannunsa na dama ya tsettsefe yatsunsa, ya kuma shafo zira’ar hannunsa na
hagu. Ko da ya fara tsettsefe yatsunsa, ya kawo ga yatsan da zoben nan ya ke ya goge shi, sai
kawai kamar daga sama ya ga wani gwabjejen qato ya tsaya gabansa, ya ce, “Ga ni, fadi abin
da ka ke so yanzu in yi maka!”

Kosau bai san sa’ad da ya katse taimamarsa ba, yana tsammani dam fashi ne, ya ce, “Wayyo!
Wallahi ba ni da ko anini. Ga kayana kuma, buda ka gani.”

Mutumin nan ya ce masa, “Allah ya ba ka nasara, kada ka ji tsorona, ni ba dan fashi ba ne,
aljani ne. Ni ne bawan zoben nan da ke hannunka, duk wanda ke mulkinsa shi zan wa bauta.
Na ji ka murza shi, shi ya sa na fito. Umurtan ni, ka ga aiki da cikawa!”

Kosau na kaduwa, ya ce masa, “To, kawo mini ruwa in wanke ido.” Rufa bakinsa ke da wuya sai
ya ga aljani ya bace. Jim kadan sai ga shi da tulun ruwa. Kosau ya wanke ido, ya yi alwala,
ya yi salla, ya tashi ya ci gaba yana cewa, “A’a! Aljanin nan wasa ya ke mini, ko kuwa da gaske
ne? Bari mu gani.” Sai ya sake murza zobe.
Sai aljani ya fito, ya ce, “Ga ni, umurtan ni!”

Kosau ya ce, “In gaskiya ce ka ke fadi ba wasa ba, samo mini abinci.” Aljani ya bace. Can ya
dawo da kayan abinci iri iri, ya kawo wa Kosau. Kosau ya zauna ya nada, sai da ya kai masa6ar
gatari. Wadansu ma bai san ko mene ne ba, shi dai ya ci. To, da ma ya taba jin labarin irin
wadannan cikin Dare Dubu da Daya, saboda haka tsoron aljanin nan ya rabu da shi. Ya kama
hanyarsa ya nufi gida, yana ta amfani da aljanin nan sa’ad da bukatar wani abu ta same shi. Da
ya gaji da tafiya kasa ya sa aljanin ya kawo masa doki taka hau, ya dare ya yi ta tahowa
bisansa.

Mutane suka dauka gaba daya, “Wannan duk ya fi su sa’a.”

1

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login