Showing 1 words to 3000 words out of 4434 words
Chapter 1 - Labarin AMJADU DA ASADU Littafin Magana Jari Ce By Abubakar Imam .pdf
 Labarin AMJADU DA ASADU 
Cigaban Kamaruzzaman dan sarki Shahruzzaman. 
 
Littafi: Magana Jarice 2 
Mawallafi: Margayi Alhaji Abubakar Imam 
 
Kamaruzzaman na nan Ebone suna  cin duniyarsu  da  matansa, sai Allah ya ba Badura ciki ta 
haifi da, aka sa masa suna Amjadu. Badura ba ta yi wata guda ba da  haihuwa  sai  
Hayatunnufusi  ta haifi da namiji, aka sa masa suna Asadu. Suka tashi gaba daya kamar ’yan 
tagwaye. Da ka gan su ka ga uban, in kun tuna yadda aka bayyana muku kyawun ubansu dazu,  
ba lalle  ba ne sa’an nan im bayyana muku siffar ’ya’yan  nan. 
 
Da yaran suka yi shekara goma sha biyu, sai Kamaruzzaman ya fara koya musu sha'anin mulki. 
In zai kewaya kasa sai ya bar su gida su yi sarauta. Aka ce su riqa rabawa, in wannan ya hau 
gado yau, gobe ya sauka gudan ya hau. Kome suka aikata  kuwa  ya zartu. 
 
Ran nan Amjadu na bisa gado, sai wata makira daga cikin sadakun uban ta rubuto masa 
takarda. Ta ce ya kamata ya tashi tsaye, Hayatunnufusi na nan na neman magani za ta  sa a  
kashe shi, a kashe Badura, don danta ya yi  sarauta.  Ta  ce,  “Saboda haka ya kamata mu 
kuma mu tashi tsaye, mu riga su. Ni zan nemi guba im ba ka, mu sa cikin abincin Asadu da shi 
da uwarsa, in sun ci duk su mace mu huta. Kai kuwa in ka yi sarauta ka sa ni babbar 
jakadiyarka. Ka san fa an ce kashe macucinka  kafin  ya cuce ka.  In kai ba ka iyawa, ka ba ni 
izni ni na yi kome.” 
 
Da yaron nan ya karanta wannan takarda sai ya yi ta kuka, ya sa aka kashe tsohuwar da ta 
kawo ta, aka nemi dalili aka rasa, ko uwarsa bai gaya mata ba. Ya dauki takardar ya sa a aljihu. 
Gari na wayewa kuma Asadu ya hau gado, shi kuma sai ga takarda daga wata makulliya ta aiko 
wa Asadu, ya bude ya karanta sai ya tarar da daidai abin da waccan makulliya ta aiko wa 
Amjadu. Wai shi kuma Asadu ya yi hankali da Amjadu, suna nan suna qullawa da uwarsa za su 
kashe shi da Hayatunnufusi. 
 
Shi kuma da ya karanta ya aikata yadda wansa Amjadu ya yi duka, ko junansu ba su gaya wa 
abin da ya faru ba, balle wani. Ashe abin da ya sa makullan nan wannan makirci hassada ce 
don sun  ga su  ba su da ’ya’ya, kuma Sarki  bai  kula da su  ba kamar yadda ya kula da Badura 
da Hayatunnufusi. Su ba bayi ba, amma am mai da su kamar bayi, don ba mai fadi a ji gidan, 
daga Badura sai Hayatunnufusi. Suka gama kai suka aiko da takardun nan haka, wai da su 
niyyarsu ko wanne ya tasam ma dan’uwa. Su kuma su yi ta kara iza su, iyayen mata ba su sani 
ba, har su sa su  yi mutuwar kasko, fada ta zama tasu. 
 
Da suka ga abin da yaran nan suka aikata, suka yi tsammani in Kamaruzzaman ya dawo za su 
nuna masa takardun nan ne, suka ga kuwa lalle in Sarki ya ga takardun nan, ba abin da zai 
hana su kwana lahira ran nan. Saboda haka suka taru su biyu, suna shawarar abin da za su 
fadi in Sarki ya dawo, don su riga yaran nan, ko Allah ya ba su sa’a su ku6uta. Suna shawara 
kullum har suka sami dabara.
Ana nan Sarki ya dawo, da saukarsa ba su bari ya ko fito waje ba sai suka iske shi, suka ce 
suna da magana. Ya qaurace, suka tsuguna suka yi ta kulla qarairayi. Suka kwashe abubuwan 
nan da suka rubuta, suka ce yaran ne suka aiko musu  su  taimake  su. Suka ce ko wanne bai 
san dan’uwansa ya aiko ba. Suka ce wai bayin nan da ya ji an kashe su ne suka aiko, wai don 
kada su karar shi ya sa suka kashe su. Kai, makirci dai duk wanda ka sani, har wanda ba ya 
faduwa, matan nan suka ce duk yaran nan sun yi shi, da Sarki ba ya nan. Suka ce sun gaya  
masa  ne,  don  kada  abu  ya rude nan gaba, a rasa abin da ya sa shi. “In kuma kana tsammani 
karya mu ke yi, ka kira su dai dai ka tambaye su, ko sa iya gaya maka kowa abin da ya sa 
dan’uwansa ya kashe baiwa guda. Ka san in da suna zaman lafiya, lalle kome guda ya aikata 
gudan ya sani. Ka ji kowa ya ce bai sani ba, dan’uwan  bai gaya masa  ba.” 
 
Da Sarki ya ji haka ya kira yara ya tambaye su dai dai, suka kasa fadin wani abu, don ba su 
gaya wa juna ba. Ya tambaye su kuma dai dai abin da ya sa suka kashe bayinsa, aka rasa 
maganar kamawa, don ko wannensu  na jin  tausayin  ya  bayyana  asirin sosai, kada Sarki ya 
sa a kashe matan nan. Suna ganin in sun yi haka sai a ce don ba iyayensu ba ne.  
Da Sarki yaga ba su fada masa wani abin kirki ba, sai ya harzuqa, idandunan nan suka jujuye, 
ya tashi ba ya ko gani ya sa aka kira tsohon nan, uban Hayatunnufsi,  ya  kwashe  al’amarin 
nan duk ya gaya masa. Tsohon Sarki ya harzuka, shi  kuma  ya ce, “Tun muna da rai ke nan, 
ina ga im muka mutu?” Sarki Kamaruzzaman bai tsaya neman shawara ba, sai ya kira hauni da 
dare, ya ce ya tafi da ’ya’yan nan nasa daji, ya sassare su  duka. 
 
Hauni da ya tsaya wani ’yan noqe-noqe, Sarki ya buga masa tsawa ya ce, “Don me na ajiye ka, 
ba sai da ka dauki alkawari ba  ka sa6a mini ba na nada ka. Kome sonsu da ka ke yi, ka san na 
fi ka. Tun da ka ji ko na ce a kashe su, ka san kada a tona. Abin da ka ga ya koro 6era har ya 
sa ya fada wuta, to, ka tabbata hakikan ya  fi wutar zafi.”  
Hauni ya dauki gayawa-jini-na wuce ya rataya, ya tasa yara gaba da tsakad dare, ba wanda ya 
san abin da a ke ciki, daga shi hauni sai fa Sarki, ya fita, suka shiga daji,  suka  yi  ta tafiya  har 
gari ya waye da zuwa hauni ya ce musu “Kamaruzzaman ya ce in zo in kashe ku. Amma ni ban 
san dalili ba. Ni ko lalle na yi alkawari ba na wuce umarnin Sarkin. Duniyan nan duk, ko 
Shahruzzaman ubansa ya ce in sare ina sare shi.” 
 
Yara suka ce, “Allah  ya dade da ran baba,  in ka qi cika  aikinsa, ina amfanin ajiye ka ke nan?” 
 
Ko wanensu ya gane laifinsa wajen kashe baiwan nan ne da kwarkwaran uban ta aiko. Amma 
har yanzu ba wanda ya fadawa dan’uwa abin da ya sa ya kashe baiwa guda ran da ya hau 
gado. Hauni ya ce, “To, ku raba, wa zam fara kansa?” 
 
Amjadu ya ce, “Sai ka fara kaina, ba ni ne babba ba?” 
 
Asadu ya ce, “A’a, in am fara kanka watakila na ji tsoro in motsa, in ta kawo kaina. A dai fara 
kaina, don kada in yi fargaba.”
Amjadu ya ce, “Ba na iya ganin an sare ka, tun kafin a zo gareni ma bakin ciki ya kashe ni.” 
 
Suka yi ta gardama, kowa na cewa a fara kansa. Hauni yace, “ln kunqi gaya mini wanda zam  
fara sarewa,  sai  ku tsaya  ku gama bayanku kuna tsaye, ni ko in daure ku da igiya gaba daya, 
tun daga hannuwanku har ya zuwa kafadu don kada wani ya goce, ku sa ni in sara sau biyu. Na 
ko yi alkwari da Sarki ran da na sari kato, ban dauke kansa ba a fid da  ni.”  
Yara suka ce, “I, haka ko ya kamata a yi.” Hauni ya sa  asalwayi ya daure su tamau. 
 
Amjadu ya ce, “Sai ka komo ta gabana ka  fara  sarawa,  don kada Asadu ya ga sa’ad da za ka 
sara hankalinsa  ya tâshi.” 
 
Hauni ya juyo gabansa zai sara sai dokinsa ya fırgita, ko me ya gani ya barzama dawa da gudu, 
Allah kadai ya sani. Hauni ya yar da takobi, ya bi doki kada ya bace. Ya bar yara nan  tsaye,  
tun  safe har rana ta yl zafi ba su motsa ba. 
 
Da suka ga bai dawo ba, suka ce, “Ya kamata mu kwance kawunammu in muna iyawa, mu 
dauki takobin mu bi shi  ya  kashe mu mu huta. Ga yunwa da qishirwa na cimmu a banza.” 
Suka yi ta kici-kici har suka kwance kawunansu, suka tafi kowa na gayawa dan’uwansu dalilin 
da ya sa ya kashe baiwa. Suka ga ashe duk al’amarin daya ne, kowa ya fidda takardar da 
kwarkwarar  Sarki  to aiko masa,  suka  karanta,  sai suka  gane makirci ne dai matan nan suka 
qulla musu game da Sarki. Suka kyale, ba su ce kome ba, har suka kai ga inda ya ke. 
 
Da suka iske shi, ashe dawan da wata zakanya mai ’ya’ya, doki ya sa huni ya haye mata ba 
sanannen ciki. Zakanya ta durmushe  shi za ta kashe, sai ga yaran nan. Amjadu ya sa 
gaya-wa-jini-na- wuce, ya sare zakanyar Hauni ya ku6uta yana kaduwa. 
 
Asadu ya ce wa Amjadu, “Ba shi takobin maza ya kashe mu, mu kuma mu huta, ni yunwa na ke 
ji.” 
 
Hauni ya dube su jiki na rawa, ga zakanya tim kwance, jini ko ina face-face, ya ce, “Kai, ku rufa 
mini asiri, imbi ta ina in kashe ku? Ba don ku ba, ni da ko labarina a ji? ku dai ku san inda kuka 
nufa. Ni ko na tafi ga Sarki in ce na kashe ku.” 
 
Amjadu ya ce, “A’a, ni sai ka kashe mu mu huta, to, ina za mu? Don me Sarki ya ajiye ka?” 
 
Hauni ya ce, “Bari ta ku ma, daga wannan na tuba da sare mutane. Ku kyale ni, ni na san abin 
da na gani. Ku dai ku tafi, in kuna da sauran shan ruwa, to, in ko ba ku da shi, kuma wannan ba 
da jinina ba.” 
 
Da yara suka yi suka yi, ya ki kashe su, sai suka fid da takardun matan nan suka ba shi, suka 
ce, “In ka je ka ba baba wadannan takardu, ka ce kuma da za ka kashe mu mun ce a gaya
masa wanda ya ce zai riqa kama maganar mata da gaskiya ya ko yi da na sani. Amma mun ce 
ya yi mana gafara.” 
 
Hauni ya kar6i rigunansu ya tsoma cikin jinin zakanya, ya kamo dokinsa ya hau, ya tafi gari da 
riguna jina-jina, watau shaidar ya cika aikin Sarki. 
 
Da Sarki ya ga haka ya yi murna, amma da hauni    ya ba shi takardu ya karanta su dai dai, ya 
kuma gaya masa saqon da suka yiwo, sai Sarki Kamaruzzaman ya fado daga bisa kujera ya 
some. Aka watsa masa ruwa ya farfade. 
 
Ya dauki takardun nan ya kai wa surukinsa, shi kuma ya karanta. Aka ba iyayen yara su kuma 
suka gani. Aka jawo matan nan aka sa musu kiri a wuya, aka kewaya da su gari kowa ya tsine 
musu. Sarki ya sa aka tsire su, aka barsu nan suna haure-haure, suna bude baki har suka 
mace. Hauni dai bai ce ya saki yaran ba, balle a bi. Amma batun bakin cikin Sarki 
Kamaruzzaman da surukinsa da iyayen yaran nan, in an ce za a tona, kai kanka ba ka jin dadin 
labarin ba, domin bakin ciki. Abin da yafi dai sai mu rufa Ka ji labarin Kamaruzzaman da 
’ya’yansa. 
 
Amma su yaran nan da suka ga hauni ya tafi, sai su kuma suka miqa cikin daji ba su san inda 
za su ba. Ba su da abinci sai ’ya’yan itatuwa. ln dare ya yi su sami ice su haye su kwana bisa, 
da safe su tashi su mika. Suka yi ta yin haka har kwana goma sha biyar, ba su kai ga gari ba. 
 
Ran nan suna cikin tafiya sai suka tarad da wata barewa matacciya, ba su san abin da ya kashe 
ta ba. Suka yi murna, suka  dauka, suka sami kartajiya suka yanyanka barewan nan kamar 
kilishi suka shanya. Da ya bushe suka dauka suka riqa ci sannu sannu, suna gamawa da 
’ya’yan itace. Suka yi ta tafiya kwanaki, sa’an nan suka isa wani gari kato. Amjadu ya ce wa 
Asadu,  “Sai  ka tsaya nan, ni in shiga in yiwo mana bara,  in  na ga mutanen garin na kirki ne in 
zo in kira ka, mu shiga mu nemi wani gida mu yi  barantaka. 
 
Asadu ya ce, “A’a, sai dai ni in tafi, ba na iya zama nan daji ni kadai.” Amjadu ya bar shi ya tafi, 
ya shiga  gari. 
 
Yana shiga sai ya fara isa gidan wani mutum, ya tsaya qotar gidan yana cewa, “Masu gida, ku 
taimake ni da sadaka, domin kaunarku da Shugaban talikai. Masu gida, ku ji  qaina,  yadda 
Allah ya ji kanku.” 
 
Yana cikin bara sai wani tsoho ya fito, ya ce masa, “Samari, halama  kai bako ne nan ko?” 
 
Asadu ya ce, “I, yanzu na shigo, dan’uwana na nan bayan gari, na zo in samar mana abinci ne.” 
 
Tsoho ya nuna alamar yana jin tausayinsa, ya kama hannunsa  ya ce, “Shigo ciki in sama maka 
abin da za ku ci, ka ji?”
Asadu ya ce, “To.” Ya bi shi yana cewa, “Allah ya  karba, Annabi ya gode, Allah ya sa muna 
cikin cetonsa.” 
 
Ya saurara bai ji tsohon ya ce amin ba, sai dai shiga su ke, suka wuce can quryar gida, sai ya 
kai shi wani daki ya kulle ya sa wata ’yarsa ta riqa kiwonsa kamar yadda a ke turke rago. Ya ce 
kullum ta ba shi abinci sau biyu, da safe da dare, ruwa kuma sau biyu ko wace rana. 
 
Ashe mutumin nan wani majusi ne, har Sarkin magiro ma a ke kiransa,  watau Sarkin Tsafi. Ko 
wace shekara ashe abin da ya ke  yi ke nan, sai ya kama Musulmi in watan zuwa tsauninsu na 
tsafi ya tsaya. To, Musulmin nan shi ya ke yankawa ya ba gunkinsa jinin. Sauran Arna masu  
yanka  raguna  na  yi,  masu  shanu  na  yi, har da masu kaji. Amma shi Sarkin tsafin sai mutum 
ya  kan  ba gunkin ko wace shekara. To, yanzu watan zuwa bautar gunkin ya kusa, shi ya sa ya 
sami Asadu ya ajiye don wannan bukata. Ka ji labarin  Asadu. 
 
Amma  Amjadu  da  yayi jira  har  kusan  rana  faduwa  bai ga dan’uwansa ya dawo ba, sai shi 
kuma ya biyo ya duba shi. Yana shigowa sai ya gamu da wani Musulmi,  ya tambaye shi ko ya   
ga danuwansa mai kama kaza a nan inda ya fito,  Mutumin ya ce a’a, bai gan shi ba. Ya ce, 
“Hala ku baki ne.!  
Amjadu ya ce, “I.” 
 
Mutumin nan ya ce, “O, ai ba ku san cikin garin ba, akwai wadansu Majusawa  masu bautawa 
wuta da gumaka, in ya  fada hannun daya daga cikinsu, kai da ganinsa sai wani ikon Allah. Abin 
da ya fi, kai ma kanka tun da ya ke magariba ta kusa, sai ka biyo ni mu je gidana ka zauna nan, 
kullum ka riqa shiga gari neman dan’uwanka, in Allah ya sa kuna da rabon ganawa ku gana.”  
Amjadu ya ce, “To,” Ya bi shi, suka tafi gidansa. Ashe mutumin baduku ne, Amjadu ya zauna 
nan yana koyon dukanci. Da rana kuma ya shiga gari neman Asadu, kullum sai  kuka.  Asadu 
shi kuma can kulle kullum hakanan. Ba wanda ya san  inda dan’uwansa  ya ke. 
 
Ana nan wata rana Amjadu yana yawo sai ya gamu da wata karuwa. Da ta gan shi sai ta ce ya 
aure ta. Shi  ko ya ce a’a,  shi yaro ne, ina shi ina auren karuwa? Ga shi ko na fari ma bai yi ba 
tukun. Karuwa ta bi shi, ta ce ita ko ina ya shiga sai ta ga gidansu. Ba ta ko son kowa sai shi, 
lalle kuwa ya aure ta. Amjadu ya rasa yadda zai yi da karuwan nan, ko ina ya sa kafa sai ta mai 
da tata nan, shi ba dama ya kai ta gidansu yana jin kunya.  Saboda haka ya kwashe ta suka yi 
ta yawo cikin gari, su bi wannan rariya su bulla wannan. Da ma shi dabarasa, in ta gaji da 
ragaita ta kama gabanta ta rabu da shi, ya je gida. in ta tambaye shi ina gida,  sai  ya ce, “Mun 
kusa dai”  Ka san abu  ga  bako,  yana cikin  tafiya sai ya bi wata ’yar hanya ashe ba ta bullewa, 
iyakarta  kofar  wani gida. Suka tarar gidan kulle. 
 
Karuwar ta ce, “Gidan ke nan? Ai ko mai kyau ne, yaran naka duk sun tafi yawo ne? Na  ga 
gida kulle.”
Amjadu ya rasa abin da zai ce, shi ba damar ya ce ba gidansa ba ne, tun da hanya ta kawo su, 
mutum ya taba mance hanyar gidansu? Shi ko ba ya son ya ce shi bako ne don bai san hannun 
wanda zai fada ba. Saboda haka









