Showing 3001 words to 4434 words out of 4434 words
Chapter 2 - Labarin AMJADU DA ASADU Littafin Magana Jari Ce By Abubakar Imam .pdf
ya ce, “I’ ni na aike su.”
Karuwar ta ce, “im ba su dawo ba sai mu balle marufin kofar in ga gidanka, don wata rana
in dawo, ni dai im ba kai na aura ba, hankalina ba ya kwantawa.”
Amjadu ya ce, “To, mu dakata dai su taho.”
Karuwa ta tsaya jim, ba wanda ya zo, sai ta dauki dutse ta balle kyauren, ta ce, “Ni ba zama na
zo ba, daga dai in ga gidanka kawai don gaba.” Sai ta kutsa kai ciki. Amjadu ya yi kamar ya
ruga, ya dai kanne, ya yi kasada ya shiga, ko da ya ke bai san mai gidan ba.
Suna shiga sai suka tarar ga shimfidu nan anyi, ga abinci iri iri an sa bisa wani tebur, ga
kujeru biyu an ajiye. Sai karuwar ta haye guda, ta bude kwanon abinci ta fara ci, tana cewa,
“Ashe yaran naka aiki suka sha. Su suka dafa?”
Amjadu ya ce, “I” Ta sa ya zauna shima ya fara ci, duk gabansa na dar dar, bai san ko gidan
wane ne ba ya fada. Da karuwar ta gan shi sukuku, sai ta yi masa magana, ta tambaye shi
lafiya?
Ya ce, “Lafiya lau, wadansu kudi ne nawa yara suka zubar.” Suna nan sai suka ji wani tafe,
Amjadu ya tashi ya tarye shi. Ashe Sarkin Fadan garin ne, wannan gidansa ne ya sa aka gina
nan don shan iska. Abincin da na ce maka Amjadu sun tarar shi ya aiko da shi daga babban
gidansa don yau zai zo nan shan iska.
Ko da Amjadu ya gan shi sai ya kwashe labarin karuwar duk ya gaya masa, ya ce in zai kashe
shi ya kashe shi, da ma shi tun da ba ya tare da Asadu, bai kula ba ko ya mutu.
Sarkin Fada ya ce, “Ba na kashe ka. Yadda ka ce gidanka ne in na shiga ka dauke ni kamar
baranka, ka yi mi ni fadan abin da ya sa na fita, ka yi ta sa ni ’yan aike-aike.”
Amjadu ya ce, “To.”
Ko da ya koma Sarkin Fada ya bi, sai ya fara masa da fada, wai don me ya tafi yawo, an ce ya
share gida ya tsaya ya fita.
Sarkin Fada ya durkusa, yana ta tuba. Karuwar ta ce, “Ya fi kyau a ba shi kashi.”
Amjadu ya ce, “Gaskiyar ki, amma sai ya kara.” Suka ci gaba da cin abinci. Sarkin Fada ya
debo masu ruwan wanke hannu, ya koma gefe guda, sai barci ya kwashe shi.
Ko da ganin ya yi barci sai karuwan nan ta ce sai Amjadu ya kashe shi, ita dai ta tsane shi,
muddin kuwa yana nan gidan ba ta aurensa. Ta ce wai ya faye muni, kamar Amjadu kuwa ko
yaron gidansa bai kamata a tarad da mummuna ba.
Amjadu ya ce shi ba ya kashe shi. Karuwa ta ce im bai kashe shi ba ita ta kashe shi. Ta tashi ta
dauki takobi za ta sare shi, sai Amjadu ya kar6e takobin, ya ce ta bari, ya sare shi da kansa. Ta
miqa masa, sai ya dauke kanta. Ya ta da Sarkin Fada ya gaya masa abin da ya faru duka.
Sarkin Fada ya yi mamaki, ya ce sai su nade ta cikin tabarma, shi da ya ke mutumin gari ya
dauka cikin daren nan, ya kai ta cikin teku ya jefa. Amjadu ya ce, “To.” Ya tashi ya taimake shi,
suka nade karuwa cikin tabarma, sa’an han ya sallami Sarkin Fada, shi ko ya koma gidan da ya
sauka na baduku.
Da dare ya yi Sarkin Fada ya dauki karuwa ya nufi teku. Ashe Alqalin garin na can, ya je shan
iska da dare. Ko da ya ga Sarkin Fada sai ya ce, “A’a, Sarkin Fada! Ina zaka da wannan kaya
cikin dare?”
Sarkin Fada ya rasa abin da zai ce. Alkali ya matsa kusa, ya ce sai ya ga abin de ya dauko. Da
ya ga mace ce matacciya sai ya ce, “A a a a, Sarkin Fada! Ashe har ka fara kashe mutane
haka kana kwace dukiyarsu? Da ma na san arzikin nan naka ba banza ba.” Da ya tashi bai
zame ba sai gidan Sarki, duk ya kwashe labarin Sarkin Fada ya gaya masa. Ko da Sarki ya ji
sai ya aika aka kira Sarkin Fada, ya tambaye shi, bai yi ko musun qarya ba, don ba dama.
Da gari ya waye sai Sarki ya sa Dogarai suka bankare Sarkin Fada, aka tafi da shi kasuwa za
a sare kansa. Mai yekuwa kuma ya shiga gari titi titi, yana fada wa mutane abin da Sarkin
Fada ke aikatawa, da kuma yadda aka same shi, da hukuncin da Sarki ya ce a yi masa. Yana
cewa ba a dauke wa kowa ba ya fito kasuwa ya gan shi don ya zama gargadi ga na baya.
Amjadu na gida yana dinkin takalmi, ya ji shela, sai ya san abin da ya faru. Ya watsad da
kayan dinkin, ya rugo kasuwa, ya tarar har Sarki ya fito, an kewaye za a sare Sarkin Fada. Sai
Amjadu ya kutsa ya tarad da Sarki ya fadi ya ce, “Sarkin Fada ba shi da laifi, don ba shi ya
kashe ta ba, ni ke da laifi, ni za a kashe!”
Sarki ya tambaye shi labarinsa, ya kwashe duka ya fadi, har ya kawo inda ya gamu da matan
nan, da yadda ya kashe ta. Da Sarki ya ji haka sai ya sa aka saki Sarkin Fada. Ya sa
mutane suka watse, ya yi ta mamakin Amjadu, da kuma wannan alkawari da ya cika. Ya ce
masa yana jin labarin Sarki Kamaruzzaman tuni, daga nan garin tafiyar wata biyu ne cur zuwa
can, ba mugama ba cin zango. Sabo da jaruntakan nan da ya yi, da kuma labarinsu da ya ba
shi tausayi, ga shi kuma dan Sarki, sai ya yi masa Wazircin garin. Dama dame ya fashe kan
kaba, na da ya mutu. Sarkin Fada kuwa aka qara masa girma, don ’yancin da ya yi. Suka zauna
nan da shi da Sarki da Waziri.
Sarki ya sa mutane kullum suna ta bin gari ko sa ga Asadu, ba su gan shi ba, don yana can
kulle Muryar gidan Sarkin tsafi dakin awaki, ba mai zuwa wurin sai fa shi da ’yar, mai gadin
yaron. Ka ji labarin Amjadu.
Amma Asadu kullum im Majusin nan ya kewayo sai ya yi masa bulala hamsin. Suna nan haka
har wata uku, sa’an nan lokacin tafiya wajen tsafi ya yi, ya sa Asadu cikin akwati ya kulle, ya
dauke shi ya kai bakin teku, ya sa cikin jirgi, suna shiri za su tashi sai ga manzannin Waziri,
watau Amjadu, sun zo dubawa ko sa ga Asadu, don ko da ya ke shi hankalinsa kwance ne, duk
da haka kullum ba ya rabuwa da kuka da aikawa ko ina ko a ga dan’uwansa. Aka duba mutane
kaf, ba Asadu, suka dawo, jirgi ya miqa. Yana tafiya cikin teku, sun yi kwana uku sai iska ta
tashi, igiyoyin teku suka murda, sai aka kwashe jirgi aka tafi da shi can wani babban tsibiri inda
ba hanyarsa ba suka tarar wata Sarauniya ce Musulma wai ita Magiyanatu ke mulkin tsibirin.
Arnan nan sun san Sarauniyan nan Musulma ce, sabo da haka da ta tambaye su inda za su sai
suka ce su masu sayad da bayi ne, sun sayad da wadanda suka kawo duka, sai guda daya.
Suka fid da Asadu suka nuna, suka ce, “Amma wannan ba mu sayad da shi.”
Sarauniya ta dubi Asadu, ta ga hasken musulunci a goshinsa, ta ga kuma lalle ba dam banza
ba ne. Sabo da haka ta yi ta yi su sayar mata da shi, suka ki. Sai ta dubi Asadu, ta ce, “Ka
iya rubutu?”
Asadu