Showing 1 words to 3000 words out of 4479 words
Chapter 1 - Labarin KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHARUZZAMAN by Abubakar Imam .pdf
Labarin KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHARUZZAMAN
Littafi- Magana Jarice 2
Mawallafi- Margayi Alhaji Abubakar Imam
A cikin zamanin da an yi wani Sarki a nan gabas wai shi Shahruzzaman. Ga shi da arziki, abin
har ba a magana. Cikin zamaninsa an hakikance ba a taba samun mai arziki irinsa ba. Abin zai
ba ka tausayi in ka ji duk abin nan da Sarkin nan ya tara ba shi da mai gadonsa, sai fa ’yan’uba.
Abin ya bakanta masa ciki, kullum in ya yi zaune ba ya kome sai zulumi. Yana nan ran ran sai
wani tsoho ya zo gunsa, ya ce, “Abin da na ga ya fi a cikin wannan al’amari sai ka sa a tara
shaihunan malaman kasan nan duka a rokam maka Maiduka.”
Sarki ya ce, “Gaskiyarka, malam. Ya ko ce roqan ni in amsa maka.” Sai ya aika kasashensa
daka, aka tattaro masa manyan malaman da ke can, suka taru. Sarki ya gaya musu bukatarsa.
Ko wannensu ya duka ba barci har kwana arba’in.
Allah maji qan bawa, kwanakin nan arba’in ba su cika ba sai da wata daga cikin matansa ta
dauki ciki. Bayan kamar wata uku ciki ya bayyana, duk gari aka yi ta murna a kan wannan.
Da ciki ya yi wata tara, matan nan ta haifi da namiji wanda sa’ad da aka haife shi don tsananin
kyawunsa mutane na tsegumin ko ba mutum ba ne, aljani ne. Da ya cika kwana bakwai aka sa
masa suna kamaruzzaman. Ba mai iya bayyana farin cikin Sarki bisa ga wannan.
Yaro yana nan yana ta girma, har ya sami kamar Shekara goma sha biyu. Da ubansa ya ga ya
yi girma haka ya ce zai yi masa aure, shi ko ya yi murabus, ya nada dan tun yana da rai.
Kamaruzzaman ya ce, “Sarauta dai ya nyi, amma aure har abada.” Uban ya yi biris da
maganan nan, sai da aka yi kamar shekara guda kuma ya tabi dan da maganar aure. Yaro
ya ce, “Allah ya ba ka nasara, ai na gaya maka ni da aure faufau.”
Da Sarki ya ga abin da gaske ne yaron ya ke yi, sai ya kira Wazirinsa ya gaya masa abin da ya
ke ciki da yaro. Ya shawarce shi dabarar da za su yi su ciwo kansa.
Waziri ya ce, “Ba yadda za a yi sai in Hakimai da Sarakuna da Alkalan kasan nan duka sun
taru da Salla, a kira shi cikin taro a tambaye shi. Na san cikin wadannan ba ya musaya mana
ba.“ Sarki ya ce, “To, shi ke nan, sai mun gani.” Da aka taru da Salla, Sarakunansa suka
taru suka tafi gaida Sarki, sai Sarki ya kira Kamaruzzaman ya tayar masa da wannan
magana.
Kamaruzzaman ya duqad da kai, ya ce, “Allah ya ba ka nasara, tun bara waccan ka ke
tambayata, na ce maka ba na yin aure har im mutu.”
Sarki ya husata, don yaro ya ba shi kunya cikin taro. Sai ya sa dogarawa suka kama shi, aka
kai shi wani tsohon gida can kusa da wani rafi, aka tsare. Da mutane suka tashi, Sarki ya dubi
Waziri, ya ce, “Tsohon banza! Ka ba ni 6atattar shawara, ka sa dana ya ba ni kunya a cikin
taro. To, sai ka fadi abin da kuma ka ga ya fi a yi masa, mu ji.”
Waziri ya ce, “Allah ya huci zuciyarka, sai a bar shi can bakin kogin nan mu gani, ko ya ji tsoro
ya amsa shawararmu.”
Sarki ya ce, “To.” Aka bar yaro can tsare kwana da kwanaki, ba mai zuwa wajensa, shi ba a
barinsa ya zo wurin wani. Sai bayan kwana bakwai Sarki kanzo da shi da Wazıri su tambaye
shi ya yarda a yi masa aure? In ya ce har abada ba ya aure, sai su fuce. Ka ji labarin
Kamaruzzaman.
To, ashe kuma a can qasar Sin akwai wata yarinya ’yar wani babban Sarki na Gayur, an yi an yi
ita kuma ta yi aure, ta ce ba ta yi. Sunan wannan ’yar Sarkin Badura. A wajen Birnin Sin kuwa,
tun da a ke ganin kyakkyawa ba a ta6a ganin kamar Badura ba.
Abin da ya sa ko ita ta qi aure, tana da dan dalilinta. Wata rana ne dai tana shan iska, sai ta iske
tarko ya kama wani namijin gwara, ta ga matar ta duka tana tsuntsunke tarkon da bakinta
mijin ya fita. Badura ta tsaya tana kallonta, tausayi ya kama ta, ta sa aka kwance gwaran aka
sake shi.
Ran nan kuma abin kamar na kaddara, ta sake fita yawo sai ta tarad da wani tarko kuma ya
kama wata macen gwara, amma mijin ko da ganin ta fara fakafaka sai ya gudu, bai tsaya ya
taimake ta ba. Da Badura fa ta ga wannan abu, sai ta sa aka saki matar gwara, ta ce, “To, ashe
haka halin maza ya ke? Har abada ko ba na yin aure.” Ka ji nata dalili.
Da ubanta Sarkin Gayur ya ji haka, ya yi ta rarrashin yarinya, ta ki aure. Sai ya sa aka kai ta
wani gida can bayan gari, aka tsare, wai ko ta ji tsoro ita kuma ta yarda. Tsakanin garin Sarki
Shahuruzzaman da garin Sarkin Gayur tafiyar wata duniya ce mai nisa, ba wanda ya san
abin da a ke yi a qasar wani. Ka ji labarin Badura.
To, wata rana da dare Kamaruzzaman na barci, sai wata ’yar Sarkin aljani da a ke kira
Maimunatu tana tashi, ta shaki kanshin jibda na fita daga cikin gidan da Kamaruzzaman ke
tsare. Da ta san gidan nan ba kowa ciki, sai ta sauka, ta nufi dakin da Kamaruzzaman ke barci.
Ta dube shi, ta yi salati ta ce. Kai! Tsarki ya tabbata ga Mai aikatawar abin da ya so. Ashe
har cikin mutane, ana haihuwar aljani? Kai, wannan bari ta cikin mutane, ko cikin aljannu
samun kyakkyawa kamarsa babu.” Sai ta tashi ta nufi yawo.
Tana cikin yawo sai ta gamu da wani aljani bawan ubanta wai shi Danhash. Ashe shi kuma
wajen yawensa ya ga Badura a Birnin Sin tana barci. Ya yi al’ajibin kyaunta. Saboda haka ko
da ya gamu da Maimuna ya gaishe ta, sai ya ce, “Allah ya ba ki nasara, ba ki tambaye ni
labarin kome ba. Ni ko ga ni da shi yana cina.”
Maimuna ta ce, “Yadda labari ke cinka, haka ni ma ya ke cina. Neman wanda zan gaya wa na
ke yi na rasa, sai fa kai yanzu da Allah ya koro mini. Amma fada mini naka mu ji.”
Danhash ya ce, “Allah ya daukake ki, yau na ga wata ’yar Sarki na barci. Nan duniya duk,
na rantse har da girmanki, in kin debe kamar ke, tsakanin mutane da aljannu duk babu irinta
don tsananin kyau.”
Maimuna ta dube shi, ta yi tsaki, ta ce, “Sakarai, maqaryaci! Kuna cika baki ba ku san inda
ajiyar Allah ta ke ba. Dan Sarkin da na gani yau, tun da Allah ya yi ka ma, ka ta6a jin mai
kyaunsa ko cikin aljannu? Ni ma da labarinsa zan gaya maka.”
Sai gardama ta kaure, kowa na tsammani nasa ne yafi kyau. Sai suka tashi gaba daya suka
tafi qasar da Kamaruzzaman ya ke, suka dube shi da kyau yana barci. Danhash ya ce, “I, lalle
wannan ba shi da laifi, amma wadda na gani ta shafe shi fat.”
Maimuna ta fusata, ta daka masa tsawa, ta ce su tafi Birnin Sin su ga tasa. Nan da nan abin
aljannu, suka isa. Maimuna ta dubi Badura, ta ce, “I, kana da ’yar gaskiya, amma in ana
maganar yaron can, sai a yi shiru. In dai ka debe shi, nan duniya ba kamar wannan.”
Danhash ya ce, “Allah ya daukake ki, ko kuwa kina nufin in dai ka debe wannan, nan duniya ba
kamar wancan?”
Sai Maimuna ta harzuka, ta buga kasa da Gafarta, sai ga wani aljani wai shi Kashkash ya tsago
kasa ya fito, ya fadi gabanta ya yi gaisuwa. Ta sa shi da Dahash su dauko Badura su kawo
ta qasar Shaharuzzaman, a gwada a ga wanda ya fi kyau.
Aljannun suka yi yadda Maimuna ta ce, suka dauko ta suka ajiye gado daya, duk suna barci.
Maimuna ta dubi Kashkash, ta ce, “Kai, wa ka ga ya fi kyau? Duba fa da kyau ka gani.”
Kashkash ya ce, “Ai ba wanda ya fi wani kyau.”
Maimuna ta ce, “Mutumin banza, wanda bai san kyau ba! A ta da su dai dai, a ga wanda ya fi
begen dan’uwa, to, shi aka fi kyau.”
Suka ta da Kamaruzzaman. Da ya farka ya ji mutum bayansa, ya duba sai ya ga yarinya
wadda ba irinta nan duniya, ya ce a ransa, “Da wannan za a aura mini da na yarda.” Ya yi
kamar ya ta da ita, ya ji tsoron ko an kawo ta ne don ta dauke hankalinsa. Saboda haka ya
kanne, ya hade begensa. Aljannu suka sa ya yi barci. Ka san fa ko da ya ke suna kallonsa, shi
ba shi da ikon ganinsu.
Da ya yi barci, suka ta da Badura su ga abin da ita kuma za ta yi. Da farkawarta ta ga
Kamaruzzaman, sai ta ce, “A a a a! In dai wannan baba ya ke so ya aurad da ni ga shi, na
yarda.” Ta fa kafa masa ido ba ta ko kiftawa, sai ta zare zoben hannunta ta sa masa, ta zare
nasa ta sa hannunta. Sai aljannun suka sa ta yi barci. Suka dauke ta, suka mayar da ita Birnin
Sin. Sauran aljannun nan suka ce wa Maimuna Kamaruzzaman ya fi kyau, don suna tsoron
kada ta yi fushi da su. Ka ji inda wannan ta kwashe.
To, da gari ya waye sai Kamaruzzaman ya ce wa bawan da ke tsaronsa, “Shin yarinyar da Sarki
ya sa ta zo nan wurina jiya da dare ’yar wane Sarki ce? In dai ita ce da ma a ke so in aura, to,
ka gaya masa na yarda na yi aure.”
Bawa ya ce, “Allah ya ba ka nasara, ai ba a kawo wata nan ba jiya da dare.-”
Kamaruzzaman ya ce, “Kar ka yi zancen banza. lna wasa da kai ne? Ka tafi ka ce wa Sarki
ina sonta.”
Bawa ya tsaya cif shi bai ga yarinya ba. Da Kamaruzzaman ya yi fushi sai ya kama gemun
bawan nan, ya yi ta dukansa, wai sai ya gaya masa gaskiya. Bawa da ya ji za a halaka shi sai
ya ce', “Na san maganar, da ma an kawo ta a gani ne ko ka ce kana so."
Kamaruzzaman ya ce, “Waddare gulya'e! Da da girma da arziki an ce ka fadi, ka tsaya yi mini
wadansu Qusurwoyi.” Ko da bawan ya samu ya kubuta, da ya garzaya bai zame ba sai gaban
Sarki, ya kwashe labarin dansa duk ya fada masa.
Da Sarki ya ji haka sai ya bushe da dariya, yana tsammani ya kusa biyuwa ne. Ya aike Waziri
ya je ya jiwo. Da Waziri ya isa sai Kamaruzzaman ya ce masa, “Yarinyar da kuka kawo mini jiya
in ita za a nemam mini, to, na yi aure, amma im ba ita ba ce, ba na yi.”
Ka san wannan al’amarin ba wanda ya san an yi shi, daga yaran nan biyu sai fa aljannin nan.
Saboda haka Waziri ya ce ba su san wannan magana ba. Kamaruzzaman ya rarrashe shi,
Waziri ya yi ta rantse-rantse ba a kawo wata yarinya ba. Sai Kamaruzzaman ya hau masa da
duka. Waziri ya kwace da kyar, ya ruga buza- buza har wajen Sarki, ya kwashe abin da ya
auku duka ya faddi, ya ce, “Lalle dai aljannu suka ta6a shi jiya.”
Sarki ya dubi shi, ya ce, “Kai, tsohon banza! Kai ka sa na daure shi can, to, ka tabbata in wani
abu ya same shi ka kuka da kanka.” Ya tashi ya nufi gidan da kansa, Waziri na biye. Da
isarsu yaro ya tashi ya gai da uban da harshe mai dadi. Sarki ya amsa, sa’an nan ya dube shi,
ya ce, “Wace yarinya ka gani ne na ke jin wai ka ce kana sonta?”
Kamaruzzaman ya duqad da kai don kunya, ya ce, “Wadda kuka kawo mini jiya, har kuka sa ta
sauya zobenta da nawa, ga shi. Ba na son wata magana a neman mini ita, na aura.”
Sarki ya ce, “Wallahi mu ba mu kawo maka wata ba. Ko kuwa aljannu ke son taba ka ne? Bari
mu gani. Yau wace rana ce?”
Kamaruzzaman ya ce, “Lahadi, gobe Litinin, sai Talata, Laraba, Alhamis. Aljumma’a,
Asabar, ko ba su ba ne?”
Uban ya ce, “Hakanan ne fa, ashe kana da sauran hankali, amma ba mu kawo kowa nan ba."
Kamaruzzaman ya ce, “Na ce naa aure ta, to, mene ne kuma na qin amsa mini? Yaya za ku ce
ba ku kawo kowa ba? Ga ko zobe, kowa ya san ba nawa ba ne. An ta6a ganin inda mutum ya yi
mafarki yana yaqi, ya tashi ya gan shi da takobi a hannu?”
Hankalin Sarki fa duk ya dugunzuma da ya ga yaro ya rude. Aka sa malamai da bokaye su yi ta
kawo masa maganin aljannu. Duk a banza. Kullum Sarki sai laifin Waziri ya ke gani, ya ce wai
shi ya ba da dabarar, Kamaruzzaman wasa-wasa abu ya koma ka mar ciwo, ba ya ci ba ya sha
kwana da kwanaki, sai da kyar a dura masa kunu. Ka san soyayya babbar abu ce. Ka ji abin
da ya faru ga Kamaruzzaman.
Amma abin da ya faru ga Badura ya ba Yu mamaki in kun ji, duk daya ne da abin da ya faru
ga yaron nan , Ita kuma ta kwanta ba ci ba sha, ana nemo malamai da bokaye suna ba ta
maganin aljannu.
Na gaya maka inda aka tsare Kamaruzzamaiı da ma kusa da kogi ne. To, tun da yaron nari
ya rude haka zaman fadanci ya koma a zauren gidan. Ran nan ana zaune sai aka hango wani
mutum kogin nan ya ciwo shi. Aka tashi aka fada aka dauko shi, aka matsa cikin, ruwa ya yi ta
fita. Aka jiyyace shi, bayan kamar kwana uku ya warke.
To, ashe shi falke ne, ba inda ba ya bugawa, har Birnin Sin ya tafi. Yanzu ma daga wajajen can
ya fito. Ya ko baro Badura ’yar Sarkin Sin tana ciwon wani yaron da ta gani da dare, har ta
musaya zobe da nasa. to da kuma ya zo nan ya ji abin da Kamaruzzaman ke ciki, ya ji kuma
labarin abin da ya auku gare shi kamar na Badura ne, sai ya ce a ransa, “Watakila yaran nan
aljannu suka gama su. Watakila wannan shi ne wanda Badura ke so. Amma bari in gani. ln na
ga kyaunsa ya dace da Badura ta yi begensa haka, na yi sa’ar fatauci.” Aka kai shi ga
Kamaruzzaman. Ko da ya gan shi sai ya ce, “Ba shakka wannan shi ne.” Ya dubi Sarki, ya ce
yana da magani, amma sai a watse a ba su wuri su biyu.
Sarki ya ce, “ln ko ka warkad da shi, zan yi maka kyauta wadda za ta ishe ka zaman
duniya har ’ya’yanka.”
Falke ya ce, “To, madalla.” Ya shiga daki ya tarad da Kamaruzzaman, ya ce, “Albishirinka.”
Kamaruzzaman ya ce, “Goro.”
Falke ya ce, “Bukatarka ta biya.” Ya kwashe labarin Badura duk har da siffarta ya gaya wa
Kamaruzzaman. Koda Kamaruzzaman ya ji ya ba da siffarta daidai da yadda ya ganta da dare,
sai ya yi wuf ya tashi, ya rungume falke yana cewa. “To, yaya za mu yi mu sadu da Birnin Sin
gobe?
Falke ya ce, “Allah ya ba ka nasara, ai daga nan zuwa Birnin Sin tafiyar wata duniya ce. Abin da
dai ya fi yanzu sai ka ce ka warke. Amma kada ka gaya wa kowa abin da mu ke ciki. Im mun yi
kamar wata guda sai ka ce mu je kilisa. Ka sami jaka ko biyar ka kai mana wani wuri ka 6oye
don guzuri. Daga wajen shan iska sai mu wuce. Ka san im ba haka ba Sarki ba zai bari ku rabu