Showing 3001 words to 4479 words out of 4479 words
Chapter 2 - Labarin KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHARUZZAMAN by Abubakar Imam .pdf
ba.” Kamaruzzaman ya ce, “Hakanan ne.”
Falke ya kira Sarki, ya ce, “Kamaruzzaman ya warke, da ma aljannu ne suka ta6ashi, na
ko yi masa addu’a.”
Batun murna da aka yi a wannan rana sai ya yi qurum. Ta ishe ka ma har tambura aka buga,
hankalin kowa ya kwanta, tun ba Waziri da da za a daure ba. Alherin kuwa da wannan falke ya
samu, ka san wannan ba sai am fadi ba. Ana nan ana nan, bayan kamar wata guda sai
kamaruzzaman ya yi yadda falken nan ya shawarce shi, suka dunguma. Da suka shiga daji sai
suka sami awakin wadansu Filani suka saya, suka yanka, suka zubad da jinin ko ina.
Kamaruzzaman ya jefa rigarsa cikin jinin, farke kuma ya yi hakanan. Dabararsu don in an zo
nemansu aka ga wannan sai hankali ya kwanta, a dangana. Su kuwa suka hau dawaki, suka yi
ta yi. Falke shi ne aboki, shi ne bara. Ka ji abin da ya faru ga Kamaruzzaman.
Amma Shahruzzaman da la’asar ta yi ba a ga sun dawo ba sai aka hau dawaki aka bi. Aka yi
nema har dare ba a gan su ba, aka komo. Da safe kuma Sarki ya ce a koma, kada kowa kuwa
ya sake dawowa sai an ga inda Kamaruzzaman ya ke. In ko ba su gan shi ba. su yi ta bin
duniya har su mutu duka can garin nema.
Mutane suka bazu, ana ta nema. Can sai wadansu suka iske inda rigar Kamaruzzaman ta ke,
ga jini faca-faca ko ina. Suka rugo da kuka, suka gaya wa Sarki. Ya hawo ya zo ya gani da
idanunsa. Daga nan fa batun baqin ciki a garin nan da wajen Sharuzzaman, sai in kyale ka in
gani in kana da ikon ka riya iyakarsa ko da cikin ranka. Ka ji kuma inda wannan tasa ta kwashe.
Bari mu koma kan kamaruzzaman. Suna nan suna tafiya, a kwana a tashi suka isa Birnin Sin.
Kafin su kai garin suka sai da dawakinsu, suka isa a kasa. Da zuwansu suka tarar Sarkin Birnin
Sin ya gaji da mutane masu zuwa suna cewa suna da magani na qarya, har ya yi alkawari
wanda duk ya ga Badura ya ba ta magani ba ta warke ba zai kashe shi. Kadan ko ta warke zai
ba shi aurenta, ko tana so ko ba ta so. An kashe mutane da yawa da suka yi qoqari suka kasa.
Da isar Kamaruzzaman sai ya tafi fada, ya ce yana da magani. Sarki ya dube shi, ya ce, “Kai,
wannan yaro mutum ko aljan? Abin da ya fi da ma ka rufawa kanka asiri, ka dangana da
wannan baiwa da Allah ya yi maka.”
Kamaruzzaman ya ce, “Cewa ka yi duk wanda ya gan ta, bai warkad da ita ba, za ka kashe shi.
To, ni maganina ba na ko so in gan ta, a kai ni qofar dakin in tsaya daga weje in yi kokari, in na
kasa na san tun da dar ban gan ta ba ba a kashe ni sai dai in za a ba ni wani horo a ba ni.”
Sarki ya yi murmushi, ya sa aka kai shi kofar dakin. Ya ce a kawo masa alkalami da tawwada da
takarda, aka kawo masa. Ya rubuta mata takarda, ya bayyana mata siffarsa da yadda suka
gamu, ya dauki zoben nan nata da ta musaya da nasa, ya kunshe cikin takardar ya aika mata
da shi. Shi ko yana kofar daki. Koda ta karba ta bude ta ga zobenta, sai gabanta ya fadi.
Da karantawar takardar sai ta yiwo wuf ta bude qofa ta leqo. Ta ga Kamaruzzaman ta rungume
shi.
Nan da nan aka je aka gaya wa Sarki 'yarsa ta warke. Ya shigo da sauri ya gani. Ta dauki
zobenta na da, ta nuna wa uban. Sarki ya ce, “Haba, ko da ganinsa na san bai dace da kowa
ba nan duniya sai ke.” Aka tambayi Kamaruzzaman labarinsa duk ya fadi. Da aka lissafa
kwanakin, sai aka ga rana daya ce da safiyar da Badura ta tashi tana haukan sonsa. Aka yi ta
mamaki ana cewa aljannu suka gama su, don sun ga ba kamarsu kyau nan duniya.
Sarki ya ce, “Tun da Allah ya nufa haka, ai ba wani abu sai a yi aure. Ga shi kuma abu ya zo
daidai, kai dan Sarki ita ’yar Sarki.” Aka tara mutane aka gaya musu, aka yi ta murna, abin sai a
yi shiru.
Da aka yi kamar kwana goma sha biyar ana murna, sa’an nan aka shiga sha’anin bikl. Aka yi
biki irin wanda ba ka taba ko jin labarin kamarsa ba.
Ana nan suna cin duniyarsu a Birnin Sin da abokinsa falken nan, sai wata rana da dare
Kamaruzzaman ya yi mafarki da ubansa. Da gari ya waye ya je ya gaya wa Sarki yana so in
ya yarda ya tafi qasarsu ya ga ubansa, don hankalinsa ya kwanta ya san bai mutu ba.
Sarki ya ce, “Wannan shi ne hankali, sai Ka dauki matarka ku yi shiri ku tafi, amma kada ku
dade can, ku dawo da wuri.”
Kamaruzzaman ya yi shiri ya kwashi raquma, da kaya, da bayi, da kudi, abin ba a cewa kome,
ya sa matarsa Badura gaba, suka tasam ma kasar Shahruzzaman.
Suna nan suna tafiya ba dare ba rana, ran nan da maraice sai suka iske wajen ruwa.
Kamaruzzaman ya ce a sauka a ba raquma. Aka sauka aka ba su, aka bar su su huta su ta6a
kiwo kafin safe. Can da tsakad dare, kowa ya yi barci, sai Kamaruzzaman ya dauki buta
ya kaikaita wa hanya don ya kewaya, yana kai gindin wata tsamiya sai ya ji an ce, “Yi hankali
kada ka taka mini kore, na yi shanya.”
Kamaruzzaman ya duba, bai ga kowa ba, sai ya tsorata ya juyo da baya. Daga qafan nan da ya
ke yi sai ya ji an ce, “Ka ko taka, don tsaurin kai! Wai kai kyakkyawa ko? To, ka san taurin kai
na da amfani.” Sai ya ji kamar wani mutum ya yi sama da shi, aka yi ta tashi da shi, bai ga mai
tafiya da shi ba, har aka kai shi can wani lambu cikin wani tsibiri, aka ajiye. Ya rasa inda ya ke
a duniya.
Yana nan kwance har gari ya waye, ya tashi yana kewaya lambu sai ya tarad da wani tsoho,
ashe shi ne mai lambun. Kamaruzzanıan ya gaya wa tsohon yadda abin ya faru duka.
Tsoho ya ce, “Kayan aljannu ne ka taka, amma ba kome tun da dai ba su halaka ka ba. Akwai
jirage masu zuwa nan, amma daga shekara sai shekara. Ga shi kuma ka yi sa’a, yau saura
wata guda za su zo. Da sun zo sai in sa su dauke ka su mai da kai qasarku.” Kamaruzzaman ya
yi murna, ya zauna nan da mai lambu yana ta yi masa budi kullum in ya tashi ban ruwa. Ka ji
abin da ya auku ga Kamaruzzaman.
Badura kuwa, ko da ta tashi da asalatun fari ta nemi miji ba ta gani ba, sai al’amarin aljannu ya
fado mata a rai, don ta tuna abin da ya auku gare su da fari. Ta tashi tana kewaya wurin, sai
ta kai gindin tsamiyan nan ta ga buta a yashe, sai ta dawo ta hakikance aljannu suka dauke shi.
Ta rasa abin da za ta yi. Ita ba abin ta korna ba ta bar shi, ita ba abin ta ci gaba ba, to, ta ce
me? Sai ta koma ta sake dabara. Ka san da ma sun yi kama, sai ta yi shiri irin nasa, ta hau
raquminsa, ta yi wa wata baiwa shiri irin nata, ta sa ta yi lullu6i yadda ta kan yi, ta hau
raquminta. Suka yi ta tafiya, ban da su biyu ba wanda ya san abin da ya faru. To, dabarar
Badura su isa Birnin Ebone inda za ta sa a riqa duba Kamaruzzaman a boye har ta sami
labarinsa.
Da Badura ta sauka garin, sai ta tarar ashe Sarkin garin kuma na da wata ’yarsa wadda a ke
kira Hayatunnufusi, ba shi da wani da ba jika, sai wannan yarinyar ita kadai. Duk nan qasarsu
ita kuma ba a ta6a ganin wanda ya kai ta kyau ba.
Na gaya maka Ba’dura fa da shiri irin na maza ta k