Showing 9001 words to 10261 words out of 10261 words

Chapter 4 - BAGIDAJIYACE free pages by Hassenan Masoya .pdf

lankwashe murya tana bashi hakuri,adole antare mata
d'innan,tasamu fada.

Batai auneba saidai taji tayi kukan kura tayi caraf ta cafki nonuwarta.da duka hannayen ta biyu

lilo takeyi kamar tasama jaka,dama ga abu zudun zudun kamar jarka,

kururuwa iya tashiga yi ji take kamar za'a yage mata k'irjin .

Salati da sallallami su baba me gadi suka d'auka lantai maishara kam dariyarta takeyi son
ranta,don ita bata tab'a karo da irin salon fad'an indoba ,dama gashi sunada jik'ak'k'a da iya
ladi.

Anyi juyin duniya tasaketa tak'i saki ,saima k'ara damk'arsu datayi uwa tasamu igiya.sukuma
gasu maza ba abun su rababa,ita me rabawar kenan lantai ,tayi gefe abinta tana dariya.

Ganin ba sarki sai Allah, yasa farouk ya finciki indo tagaba,aliyu ya finciki iya tabaya

Nan iya tawatse yaraf a wajen kamar tsumma.
"Jama'a kukallanmun kirjina nonuwa na sunanan,ko sun fita?"

Indo nadak'wak'wo gula gulan idonta ta je gabanta ta tsaya tana numfarfashi,"don uwar mace
tasake yi mun magana...alkur'an sainacire ma mutum hanci ...kinyi sa'a ba wuk'a kusane...
Dakin sha yanka,nid'in nan dakike gani cikakkiyar 'Yar dabace,ina jiran yaran naki darabon
lakhira tayi bak'i"
"Lamarin ashe babbane,tabbas kwalwar yarinyar nan ba lafiya" cewar farouk kenan cikeda
al'ajabi

Ganin shikaran kansa ya jinjina ma al'amarin yasa ma'aikatan gidan dayazo kowa yafara ja
baya yina sulalewa,kar tama hango fuskar shi ,bugun jujunta,nagaba tayo kansa.











I needs more and more comments so,
Vote
Share
Comment
[8/19, 10:15 AM] Haisahhtttttt💅🏻: *👠👠💅🏻BAGIDAJIYACE👠👠💅🏻*

*©ï¸HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*(Home of peace ,joint entertainment to educate and enlighten our readers)*


Story and written by
Hassenart
☎ï¸090 -659 -902 -65



Happy marriage life💞
Nafeesah,Allah ubangiji yasanya albarka acikin auranku,yakauda duk wata fitina,yabada
dawwamamiyar zaman lafiya,da 'Karin k'aunar juna,yakawo zuri'ar da al'ummar annabi (s.a.w)
zasuyi alfahari dasu.
Congratulations dearí ¾í´í ¼í¿»



*Last free page*

*Daga wannan page d'in pajin kyauta ya k'are ,duk wacce takeso kibiya kudinki ,ki karanta #200
zaki biya na katin MTN zaki turama wannan number, 09065990265* *saiki screen shot as
evidence ki turama wannan number dai*
*Inkuma VIP kikeso #300 ne, shima wannan number dai nasama zaki tura mawa*


1ï¸âƒ£5ï¸âƒ£~1ï¸âƒ£6ï¸âƒ£

Indo kam tunda tashiga gidan zaman lafiya yayi masu k'aura,yau da wannan gobe da wancan
basu samu arzik'iba saida anty safiya takwasheta tamaidata garinsu saboda admission d'inta na
cigaban karatunta nagabada primary yafita

Iya ladi kam tanaji tana gani haka tunda suka sami wannan matsalar da indon,dole tahak'ura
tabar aikinta.
Don tace watarana indo zata iya d'aukan ranta.kowa yayi jimamin rashin ta don dai ba laifi suna
jin dad'in girkinta,amma daga baya suka share aka sama wata da zata maye gurbin na ta.
************************
*WANENE UMAR FAROUQ*

Umar mak'ota suke dasu haidar anan GRA dukda dai dama tun su haidar na hanwa kafin su
dawo nan d'in,Abokai suke ajinsu d'aya a makarantansu tundaga Js 1 suke tare har ss3
So,lokacin da suka dawo GRA sai sukazamo makota nan shak'uwarsu takuma k'arfi har

yazama komai tare sukeyi cin abinci ,kaya iri d'aya komai don hatta bacci baya rabasu,don idan
wannan yaje gidansu wannan ya kwana yau ,gobe wancan zai je gidansu d'ayan su
kwana,abotansu shi ya had'a kawancen iyayen su suma .
Farouk su biyu ne rak wajen iyayen su,shi da k'anwarsa maryam maryam sa'oine da en biyu.

Baban farouk major general ne a NDA don haka,koda suka gama secondary takardunsu kawai
yakarb'a yanemar masu NDA .
shi haidar da fari bayason soja amma farouk nason yagaji babansa,kuma baison su rabu,dole
yacanja ra'ayin abokin nasa ,haidar yabi bayan abokinsa aka Neman masu navy acan d'in
yanzu haka a wannan shekaran suka shiga .
Farouq jarababben yarone,ga miskilanci baison magana mai tsayi balle hayaniya

Tunda indo taje gidan ya janye jikinsa da gidan saidai haidar shi yaje.
Bai saki jikinsa da gidan ba saida yaji indon tatafi.
********************
Indo anshiga makaranta cikin nasara,anfara karatu cikin farinciki gunin ban arziki,kafin daga
baya komai ya kwab'e.
Tazamar masu bala'i a makarantan k'ungiyarsu akeb'e yake na zallah marasa ji maza uku sai ita
da aminiyarta rahane.
Basa shayin tab'a koma waye harta 'yan ajin gaba dasu in sukayi cacan baki to ranar hanyar
makarantan in an tashi zama yake kamar filin badar tsabagen rigima,tunda set d'in su indo suka
shigo makarantan seniority yawatse ,kowa yasamu liberty yayi duk abunda yaso.

Akwai gonakin mutane ata bayan makarantan suma kaf sun gallazesu da sata daidai da masara
saisun karye masu sun gasa inbeyiba su zubar.6arna yadda kasan 6eraye.
Ba laifi tana d'an k'ok'ari tunda daman bawai batada k'walwar bane rashin maida hankali ne.
Saidai kuma me,tunda tashiga makarantar ta bud'e sabon salon tsinin balaga ga rawa uwa
mazari duk kalar wak'ar dayafito ta iya rawarshi.
Tuni tashiga sahun 'yan gaba gaba a Hausa club na makarantan su,daita ake zuwa makarantu
fadan rawa don aciyo Kofi.
Kad'an kenan da aikin indo
*******************
*CIGABAN LABARI*
"Haidar bi iznillah yau a gida zan kwana...I missed ma mom"
"Kaima kafad'a haka bareni....ni danake so har zuntu inje a hutun nan...kawai ka shirya zuwa
anjima mubi motan dady"
Harhad'a komai nasu sukayi ,suka gyara ko'ina .very important abubuwan su suka d'auka a
jakan bayan su na sojoji,daganan Zaria tayi kira.basu shaida ma kowa ba saidai kawai gidan
sukayi masu tsinke .gidansu haidar suka soma sauka,nan gida yarikice da murna "gasu
yaya,gasu yaya" lokacin indo tanata baccinta batasan bidirin da akeyiba Suna sauka basu tsaya 6ata lokaci ba suka shige gidansu farouk ,basu kuma fitowa ba saida
sukayi wanka sukayi sallah don har abinci acan sukaci.sannan koda suka dawo farouk d'akin
haidar ya tafi,shi kuma haidar ya wuce sashen dadynshi ,dayake dawowarsa kenan.

Indo da farkawanta barci labarin dawowar haidar ya risketa
Ai da fyallelen zaninta tayi sashen shi dagudu.
Gab da zata shiga tafara slow tunawa da abokinshi datayi,"kardai suna tareda wannan mai k'irar
samudawan... Mutum kullum fuska gintse sai nace an aiko masa da sak'on mutuwar uwansa?...
To wannan karon da cikinka nazo kana mun kan kara zan idasa maka Dana gumagumai"

Sand'a tasoma yi,ta tura k'ofar a hankali,cikin d'akin ta kutsa kanta tsaye,me zata gani.....

Farouk tagani kwance shemesheme a katifa daga shi sai boxer da singlet,gefen sa laptop
d'insane yana kallo ,Sam hankalinsa yayi nesa a kallonsa baisan ma tashigo ba dayake yabama
'kofar baya

Wani irin gurnani ne ke fita tajikin laptop d'in.
Daddalo idanuwarta tayi waje ganin mace zir da namiji suna aikata masha'arsu ,suna wani irin
murning kamar kuraye.

K'ara ta k'walla mai aka tafita da gudu,hanyar bq tayi

Dafarko yaso share ta ,amma yana tuna surutunta ya zabura ,yayi cikin BQn da gudun gaske
shima don bai fatan ta tons masa asiri and she can do that....

Caraf ya damk'eta ,zare ido ya hauyi waiko y furgitata.

"Ke dan gidanku meye yasaki gudu har kike kwalla mun ihu aka?"

Ware duk idanuwarta tayi tana kantara masa rashin kunya

"Abubuwa marasu asanin kyan dubiya... Hmmm andai d'uma abun kunya...."

Borin kunya yahau k'okarin yi

"Ke lallai kinada aljanu,ko kuma kin fara kur6awa,inko ba hakaba,kije ki kuma nazari ....nida
kika shigo kika sama ina istigfar .....zaki sa mun magana?"

"Sankaci? Ashe haka kuke mazan bunni?...ina kallonma idona ace bahaka bane.....koda
yake ba laifina bane ba nakaba ....kasan inada laluran jinnu ,gasuda hegen tonon silili

2
3
4

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login