Showing 1 words to 3000 words out of 15337 words
Chapter 1 - UWANI YAR KASHIN GWIWA Book Complete by Ameera Adam.txt
 *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA*
            ©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.
  
  SHAFI NA ƊAYA
   Cikin karayar zuciya da ɗacin rai wasu tagwayen hawaye  suka fara 'yar tsere a saman dakalin fuskar Baba Isuhu, ya kai kallonsa wurin mai sunan malam da ke wutsul-wutsul a hannun Lami ya ce. "Mai sunan malam ba zan iya rabuwa da kai ba, don Allah Lami kada ki azabtar da ruhina da rashinku." Kuka ya sake ƙwace wa baba Isuhu da ya sauke idanunsa a kan ƙullin kayan Lami da ke ɗaure a ɗankwali.
  Sai da ya sharce majina da gefen rigarsa sannan ya sake kwantar da murya yana faɗin.
"Lami kin san irin so da ƙaunar da nake yi miki? Ko so kike ki mayar da ni marayan ƙarfi da yaji? Matuƙar za ki tafi gidanku sai dai ki tafi da ni Lami, domin ni na fi maye maita indai a kanki ne." Baba Isuhu ya janyo hannun Lami ya haɗa da na mai sunan malam ya rungume a ƙirji sai ya sake ɓarkewa da kuka. 
"Don Allah ki haƙura da yajin nan da za ki yi Lami. Matuƙar naman ƙauri ne zai datse igiyoyin so da ƙaunar da ke tsakaninmu ko sayar da kaina zan yi, amma na yi miki alƙawari duk inda zan shiga zan yi koma me ye na nemo miki abin ƙaurin nan Lami."
Lami ta taɓe ba ki sannan ta ce.
 "Wallahi Isuhu ba abin da zai hana ni tafiya a daren nan, don in gaya maka na ce wa Goggo Sala ko awa guda ba za mu ƙara a gidan nan ba. Saboda Allah kamar a kaina tsiya ta ƙare, haihuwar fari a ce yau kwana biyu cir babu kajin ƙauri ballantana na saka rai da ɗan akuya ko tinkiya. Kai tir da halinka Isuhu, wallahi da Isa mai tsire na aure na san nama har sai na ci na ture..." Cikin sauri Baba Isuhu ya katse ta.
 "Me aka yi aka yi Isa ne Lami? Wai ko kin manta Isuhun Lamisuwa mai hadarin naira?" Lami ta sake taɓe baki ta furta. "Ai a banza man kare, tun da a haihuwar ɗanka na fari guda a ce abin ƙauri ya gagara, kenan haka zan zauna har hakikar sunan ita ma ta gagare ni. Wallahi ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa."
  Jin haka ya sake tsuma Baba Isuhu ya zabure haɗe da ɗaga hannu sama ya ce. "Sai ni isuhullen Lamisuwa mai hadarin nairori, sai ni Isuhun da ya sha gaban zaratan mazaje ya samu Lamisuwa." Lami ta ɗan saki murmushi sannan ya kalle ta ya ce. 
"Wai ina Lami take?" Da sauri Lami ta amsa. "Ga ni mana."
  "A yau ba sai gobe ba zan kayar miki da tinkiya." Sai da ya kalli hagu da dama ya yi ƙasa da murya sannan ya matsa saitin kunnenta ya ce. "Kin san Allah yau uwar garke zan girke miki." Da sauri Lami ta washe baki cikin zumuɗi ta furta. "Uwar garke fa..."
 "Ki yi ƙasa da murya mana haba Lami, ko so kike asirina ya tonu?" Baba Isuhu ya katse ta da sauri.
 "Ɗan Isuhullena ai sai yanzu na fahimce ka, Allah Ya ba ka sa'a kada hatsabibiyar yarinyar nan ta ganka lokacin da za ka ɗauke mata uwar garken nan." Lami ta yi maganar murya can ƙasa zuciyarta fes.
 "Ai maso abin ka ya fi ka dabara Lamisuwata, dare zan bi na san yadda zan yi da ita. Ke dai kawai ki zuba wannan ki sha kallo." Baba Isuhu da Lami suka kwashe da dariya.
 
 "Lami! Ke Lami ki fito mu wuce kin shanya ni ke 'yar daɗi miji, kin san dai idan ana jego ko kyakkyawan zama a wurin miji ba a yi ballantama wannan mijin na ki..." Lami ta yi saurin katse Goggo Sala, "Goggo zo mu je ciki ai tuni mun riga da mun gyaro ta ni da shi." Baki sake Goggo Sala ta bi ta da kallo sannan ta ce. "Hmmm namiji kenan! Ke yanzu daɗin bakin namiji har zai sa ki zauna..." Lami ta yi saurin yi wa Goggo Sala raɗa a kunne, da sauri Goggo Sala ta washe ba ki ta furta.
 "Ke 'yar nan da gaske?" Lami ta gyaɗa kai tana murmushe.
  "Haba ko da na ji wannan ita ce harkar arziƙi, ko ni ƙanwar uwarki ai na samu na lasa wa a bakin salati. Ni fa kin san ni dama na fi kwarkwasa kwaɗayi, duk wurin da ake samun mai maiƙo-maiƙo a nan na fi ƙarfi." Lami ta yi gaba tana tafiya cikin ƙwambo tana jin ita ma ta isa, kuma ta tabbata matuƙar aka wayi gari da an yi mata ƙauri da tinkiya ta san daraja da ƙimarta ta ƙaru a idanun facalolinta.
 CIKIN DARE
  A hankali Uwani ta buɗe idonta sakamakon jin fitsarin da ya zame mata kamar farilla cikin talatainin dare, sai da ta gama murtsike idanu sannan ta fara tashin Dada.
 "Dada! Dada don Allah ki tashi ki raka ni fitsari nake ji." Dada cikin takaici ta saki dogon salati sannan ta ce. "Ni kam wallahi Dijen Iro ta cuce ni da ba ta gashe miki mara tun kina zanin goyo ba, wallahi Uwani ki kiyayi haƙƙin tashina tsakiyar dare da kike yi..." 
 "Dada kamar kukan uwar garke nake ji." Uwani ta katse Dada cikin sauri tana sake kasa kunne, don sama-sama take jin kamar kukan dabbobinta kasancewar suna da ɗan nisa da sashen Dada. Dada ta yi mata shiru saboda takaici. "Dada don Allah ta shi mu je ko wani abu ne yake damun su..."
 "Ai wallahi ko Umaru ne ya dawo daga Lahira bai isa ya fid da ni waje ba, tun wuri ki kama 'yan matan ƙafafuwanki ki yi gaba." Jin takaicin abin da Dada ta faɗa ya sa Uwani tashi fuuu ta suri buta ta yi waje.
 Tamkar sabon munafiki haka Baba Isuhu yake tafe cikin sanɗa yana waige har ya ƙarasa sashen da awakin Uwani suke, sai da ya karkace maƙogaro ya maƙe murya kamar yadda Uwani ke yin magana sannan ya ce. "Uwar garkeruruna tayya maza mu je ki ci dusa." Shiru ya ga uwar garke ta yi babu alamin za ta motsa, ganin za ta ɓata masa lokaci ya sa ya ɗago ta ya fara ja a hankali. Sai da ya ƙarasa bakin katanga sannan ya taka turmin da ke jingin, sama-sama ya ɗan fara jiyo motsi don haka ya yi kasake. A ɓangare ɗaya ƙirjinsa na bugawa don kada uwar garke ta yi kuka asirinsa ya tonu. Yana raɓe a gefen katanga ya ga Uwani ta wuce da buta a hannu sannan ya sauke gwauruwar ajiyar zuciya, tirmi ya taka a hankali ya leƙa ya hango Mai gari da ke tsaye yana jiransa.
  "Haba Isuhu tun ɗazu ɗauko tinkiya ya gagare ka, ko so kake asirinmu ya tonu mutumcina ya bi rariya ya tsiyaye tas a garin nan ina matsayin mai garin garin nan." Baba Isuhu ya yi ƙasa da murya ya ce. "Kai Talle ka san dai fita da uwar garke ta ƙofa ba zai yuwu ba saboda tsaro, yanzu ga ta ka matso zan cicciɓo maka ita." Da sauri Mai gari Talle ya matsa jikin katangar. Baba Isuhu ya koma wurin Uwar garke da ke cin dusa, ya tattaro iya ƙarfinsa ya ɗago ta sai ji kake ɓaaaarrrrrrr wata uwar tusa ta ƙwace masa. Uwani da kawo kanta kenan ta saki murmushi ta ce.
"Kai da jin wannan tusar ka san su uwar garke bacci ya yi daɗi." Har za ta gota sai ta leƙa garkensu, sai dai haskarwar da ta yi babu uwar garke babu alamunta. Da sauri ta juyo tana shirin fasa ihu ta hango Baba Isuhu rungume da uwar garke, ita kuma uwar garke jin matsar da Baba Isuhu ya yi mata ya sa ta ware baki ta ce.
 "Meeeeeeeeehhh." 
Cikin sauri Baba Isuhu ya miƙa wa Mai gari Talle, Mai gari na karɓa ya fara kici-kicin hawa mashin. Uwani na ganin Baba Isuhu ya miƙa uwar garke ta yi caraf ta kama katanga, sai dai tana gani Mai gari shi da wani da ba ta gane fuskarsa ba suka haye mashin suka fita da gudun gaske.
  A haukace Uwani ta diro daga kan katangar ta ɗora hannu a kanta cikin tashin hankali ta ce, "Wayyo Allah uwar garkena." Sai kuma ta yi sashen Dada a guje. Ganin haka ya sa Baba Isuhu da sauri ya nufi sashensa. 
  A tsakar ɗaki ya sami Lami don haka tana ganinsa ta ce, "Ya dai Isuhullena an dace kuwa?" Baba Isuhu da ke faman haki ya ce, "Maza ki tafi ɗaki ki kwanta, ni ma lamfo zan yi shegiyar yarinyar nan ta kama mu ni da Talle."
 
 Zaro ido waje Lami ta yi ta ce, "Mun shige su Isuhuna ya za ka yi?" 
"Babu lokaci Lami ke dai ki je ki yi yadda na ce miki." Lami ta yi saurin ficewa shi kuma Baba Isuhu ya faɗa uwar ɗaki ya haye gado sannan ya fara sauke numfashi kamar wanda ya jima yana bacci.
  "Wayyo uwar garke." Uwani ta furta haɗe da ɓarkewa da matsanancin kuka. Ganin Dada na sakin bacci har da minshari ya sa Uwani ta buga tsalle haɗe da faɗin. "Wayyooo uwar garkena!" Sai a lokacin Dada ta ji ihun Uwani.
  "Kai ni kam Mamman ya cuce ni da ya haɗa Uwani da kiwo tun tana ƙanƙanuwarta. Yanzu ban da masifa a ce yarinya har cikin bacci tana ambatar tinkiya, wannan bala'in da me ya yi kama..." Dada ba ta ƙarasa magana ba ta ji Uwani ta faɗi a gefen ƙafarta tim! Ta fashe da wani irin matsanancin kuka. A razane ta tashi zaune sannan ta kai hannu ta kunna fitilar ɗakin, hannuwa biyu ta sa ta dafe ƙirji a firgice Dada ta furta.
 "Uwani ke ce nake gani a gabana ko buɗe mini ido aka yi?" Uwani ta ji tamkar Dada ta watsa mata ruwan zafi, don haka ta fyace majina da gefen zaninta cikin ihu ta ce.
 "Uwar garkeeeeeena! Baba Isuhu ne uwar garkenaaaa." Dada ta zaro ido waje. "Ke Uwani ko dai gamo kika yi ne? Shi Isuhun ne ya zama uwar garke? An ya lamarinki Uwani babu jifa a ciki?" Dada na gama magana ba ta ji daga bakin Uwani ba ta fashe da kuka tana faɗin.
  "A'ubikalimatillahi tamma min sharrin ma kalaƙa. Aniya bi aniya wallahi aniyar kowa ta bi shi, Allah Ya kai mu wayewar gari wallahi sai na je gidan Sarkin aska na karɓo miki ƙaiƙayi, ni za a kashe da ƙullutun baƙinciki..." Uwani ta katse Dada daga dogon jawabin da take yi.
  "Dada wallahi ganin idona Baba Isuhu ya ɗauke mini uwar garke ya miƙa wa Mai gari ta katanga." 
"Ke yarinyar nan ki ji tsoron Allah, shi Isuhun nawa ne kike jifa da sata? Isuhun da ko yatsa ba za a saka masa a baka ya tauna ba?" Ganin haka ya sa Uwani ta fice daga ɗakin tana faɗin, "Wallahi ko sama da ƙasa za ta haɗe sai ka dawo mini da uwar garkena. Wayyo Allah garkeruruna!" Jikin Dada nan take ya ɗauki karkarwa don haka ta miƙe cikin sauri ta bi bayan Uwani. 
  Kafin wani lokaci wasu daga cikin mutanen gidan suka fara fitowa, kowa ya tambayi Uwani amsa ɗaya take bayarwa 'Uwar garke, Baba Isuhu ya miƙa wa mai gari ta katanga.' Carko-carko suka yi domin ga dukkan alamu sun fara aminta da kalaman Uwani, sakamakon sun duba garken awakinta sun ga babu uwar garke.
 "Ina shi Isuhun ne?" Baba Idris ya tambaya. Kallon juna suka shiga yi don haka ya bayar da umarnin a je sashen shi a kira shi. 
Sahabi da Tasi'u ne suka nufi sashen Baba Isuhu, sun jima suna buguwa sannan ya buɗe ƙofa, yamutsa fuska ya hau yi tamkar wanda aka tasa yana bacci ya ce. "Kai waye a tsohon daren nan yake mana bugu haka?" 
"Baba Isuhu dama Baba ne ya ce a taso ko?" Suka amsa masa. 
"Ni kuma? A tsohon daren nan? Ko ciwon Yaya ne ya tashi?" Baba Isuhu ya jefa musu tambayoyi kamar bai san abin da yake faruwa ba. Girgiza masa kai suka yi, suka wuce gaba yana biye da su a baya. Yana zuwa ya samu mutane a tsaye carko-carko, tun daga nesa gabansa ke dukan uku-uku amma gudun tonuwar asirinsa sai ya yi hanzarin aro mayafin jarumta ya lulluɓa wa jikinsa. Ya sake aro fuskar mamaki ya ɗora a saman tashi, cikin mamaki ya furta.
  "Yaya lafiya na ganku haka a tsohon daren nan?" 
 "Uwani ce ta zo mana da wata magana..." Duk abin da ya faru Baba Idris sai da ya zayyane masa sannan ya ɗora da cewar, "Ina Uwar garke take?" Duk da ƙirjinsa bugawa yake amma bai hana shi fututtukewa ba ya ce. "Haba Yaya yanzu duk faɗin gidan nan a rasa wanda za a laƙa wa sata sai ni? Me zan yi da wata uwar garke? Shekarar uwar garke nawa a gidan nan? Amma kawai don yarinyar nan ta shirya ƙaryarta sai a hau kai a zauna, shi kenan tun da ni ne ɓarawon da kuke zargi a faɗa mini nawa ne kuɗinta zan biya." 
Ganin yadda ran Baba Isuhu ya ɓaci ne ya sanyaya jikin ilahirin mutanen da ke wurin, Dada ta zauna daɓar haɗe da rushewa da matsanancin kuka.
 "Tsakanina da wannan ɓarawon ni kam sai na kai kukana gaban Ubangiji, ina zaman zamana zai haɗa mini husuma a cikin zuri'ata." Baba Mustafa ya ɗago Dada sannan ya ce, "Yanzu dai duka mu bar maganar nan ni nan zan sayo miki wata ƙatuwar tinkiyar da ta fi uwar garke girma kin ji Uwani." Jin haka ya sa Uwani ta rushe da kuka.
 "Wallahi ni uwar garke nake so, kuma ko kur'ani aka ba ni zan dafa ganin idona na ga Baba Isuhu da uwar garkena..." Baba Mustafa ya yi saurin katse ta don haka kawai ya ji ya yi na'am da kalaman Uwani, don haka ma ya ce. "To shi kenan ba tinkiya kaɗai zan saya miki ba, kina son ɗan maraƙin sa ko?" Ba don Uwani ta daina jin zafin rashin uwar garke ba ta amsa, sai don son da take wa ɗan maraƙin sa. Saboda haka ta gyaɗa masa kai tana goge hawaye, a gefe ɗaya tana  kuma ƙudurtar irin fansar da za ta ɗauka a kan Baba Isuhu don ta yi rantsuwa da Allah jinin Uwar garke ba zai tafi a banza ba. Daga haka gabaɗaya kowa ya watse, Uwani da Dada suka yi sashensu sai dai buta ta sake ɗauka ta fito kamar za ta banɗaki kai tsaye ta wuce sashen Baba Isuhu cikin sanɗa, ta ci sa a bai rufe ƙofa ba don haka tana laɓe daga bakin ƙofar ɗakinsa ta ji Lami na faɗin.
 "Isuhullena ai ka birge ni da ka ƙaryata shegiya, haka kawai da tuni da tozarta ka a gaban mutane." Baba Isuhu ya saki dariya ya ce. "Ke zan cen da nake miki gobe warhaka mun riga da mun gama ɓarje dabgen kan uwar garke." A gefe ɗaya ta ji muryar Goggo Sala na cewa. "Yanzu dai tun da aikin gama ya gama ai sai ku ja baki ku yi shiru, amma dai Isuhu dole ka badda kama idan za ka shigo da uwar garke don ka san dole a saka maka idanu." Baba Isuhu ya fashe da dariya yana shirin yin magana daga can bayan ƙofa suka ji muryar uwar garke ta ce. "Meeeeeeeeh." A zabure suka kalli juna cikin tashin hankali. 
"Kukan uwar garke nake ji a tsakar gida Isuhu leƙa ka gani..." Lami ta faɗa da sauri.
"Ba ki da hankali Lami, ya za a yi ganin idona Talle ya tafi da uwar garke kuma na ji muryarta ke ki leƙa mana..." Kalaman bakinsa suka katse sakamakon sake jin kukan Uwar garke ta ce, "Meeeeesuhuuuu." 
Wani abu ne ya tsargawa Baba Isuhu tun daga tafin ƙafarsa har tsakiyar kansa.
 
"Isuhu kamar sunanka na ji a cikin kukan uwar garke." Lami ta faɗa a tsorace.
"Meeeeeesuuuhuuuu." Uwani da ke laɓe ta sake maƙale murya ta faɗa da yanayin kukan uwar garke, tana gama faɗa ta dokon ƙauren ɗakin da suke ciki. A zabure Lami, Isuhu da Goggo Sala suka faɗa uwar ɗaki, Goggo Sala da ke ɗaure da ɗaurin ƙirji tun a falo zanin jikinta ya faɗi ba tare da ta sani ba. Goggo Sala da baba Isuhu suka shige bayan ƙofar uwar ɗaki ita kuma Lami ta maƙale a gefen gado, shirun da suka ji ba a ƙara kukan tinkiyar ba ne ya sa suka fara dawowa hayyacinsu. Goggo Sala ta kai idonta jikinta sai a lokacin ta yi ido biyu da tsurar ɗan fatarin (Under wear) da ke ƙugunta, ga ƙirjinta zube a saman kan Baba Isuhu da ke tsugunne a ƙasa. Sai a lokacin ta lura da hannuwan baba Isuhu da ke riƙe da ɗan fatarinta. Cikin matsananciyar kunya ta ce.
 "Kai Isuhu wanne irin iskanci ne haka saboda Allah za ka nemi shigewa cikin fatarina, ni fa ƙanwar mahaifiyar matarka ce ." Cikin rashin sani Baba Isuhu ya miƙe tsaye sai jin ƙirjin Goggo Sala ya yi a saman fuskarsa, yana ɗagowa suka haɗa ido da ita. Ganin abin kunyar da aka tafka cike da borin kunya ta ce, "Amma dai Isuhu yadda ka kwaso mini ƙirji ina a matsayin sirikarka Allah Ya kwashe maka albarka."
07062062624
#Ummou Aslam Bint Adam🌚
*UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA*
            ©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.
  
  SHAFI NA ƊAYA
   Cikin karayar zuciya da ɗacin rai wasu









