Showing 6001 words to 9000 words out of 15337 words

Chapter 3 - UWANI YAR KASHIN GWIWA Book Complete by Ameera Adam.txt

11 Jun 2024

5655




"Allahu Akbar."


Da ya yi kabbara sai ya sauke wa Jafar wani dundu a baya. Uwani na ganin haka ta ɗebo ruwa a randa ta fara yayyafawa Dada, babu jimawa Dada ta fara sauke ajiyar zuciya sannan ta buɗe idonta.


Jafar tun yana ganin dukan da Na Madina yake yi masa wasa ne har ya ga ya cukwikwiye masa wuya, har wani zullo yake yana kabbara yana kai masa duka tamkar mai jifan shaiɗan. Jafar ya haɗa hannuwan dattijon wuri ɗaya ya murɗe su sannan ya ce.


"Wallahi Na Madina ko ka sauko daga kaina ko na bi yatsun hannunka ɗaya bayan ɗaya na tsike su kamar yadda ake tsinkar mangwaro." Jin matsar da Jafar ya yi masa da kuma furucinsa ya sa cikin Na Madina ya karta, yana shirin yin magana ya ji Dada na salati daga kwance.


Tamkar ɗan biri sai ga na madina ya yi tsalle ya faɗo ƙasa, Jafar ya gyara wuyar rigarsa ya fice daga ɗakin. Kai tsaye ya wuce ɗakinsa da Dada ta sa aka gyara masa. Malam na Madina ya tsugunna a daidai kan Dada ya ce.


"Sannu da farkowa Kulu." Dada ta dube shi luuuu da idanu a shanye sai kawai ta ɗaga ɗan yatsa ɗaya ta ce.


"Ashhadu anla'Ila'ha'illahu wa anna Muhammadur Rasulillah."


Malam na Madina ya sake cewa. "Mun auna arziƙi Dada wannan yaron ashe harbe ku ya so yi?" Dada ta sake yin luuuu da idanu fuskar na Madina na yi mata gizo ta ce.


"Ismi Hauwa kulu wa ana musulima." Jin haka ya sa Na madina ya fashe da kuka, kukan da Dada ta ji ne ya sa ta ɗan wartsake sai a lokacin komai ya fara dawo mata. Zumbur ta tashi zaune ta fara bin su Uwani da kallo.


"Uwani kina jin maganata ko kuma da gaske Jafaru ya harbe ni na mutu?" Uwani ta saki dariya ta ce.
"Ina jin ki mana Dada ga Na Madina ma a zaune." Dada ta kalli na Madina suna haɗa ido kamar haɗin baki suka fashe da kuka a tare.


"Uwani maza ɗauko mini wayata."Dada ta furta cikin kuka.


Da sauri Uwani ta ɗauko mata don ta san ba ya wuce ta ce a kira mata baba Mamman.


"Maza kira mini Mamman."


Uwani ta karɓi wayar ta gama dube-dubenta sannan ta ce, "Lambarsa ce mai hotan zuciya ko?" Da sauri Dada ta gyaɗa kai. Uwani ta kira tana jin an ɗauka ta miƙa wa Dada.

"Assalamu Alaikum. Hajiya Dadata yau ke ce da kira da kanki..."


"Dakata Mamman! Kiranka na yi ka gaya mini waye shugaban 'yan sanda na duk faɗin duniya?" Dada ta katse Baba Mamman a zafafe.


"Shugaban 'yan sanda na duniya? Dada me ya faru kuma?" Ya tambaya a sanyaye.


"Me ye ma bai faru ba Mamman? Ka gaya mini shugaban 'yan sanda na duniya da inda zan same shi, domin a yau ba sai gobe ba wallahi zan ce ya tube Jafaru daga wannan aikin kakin. Kai ni dai Sa'idu ya gama cutata, a ce 'ya'ya duka babu mai aiki ƙwaƙƙwara daga Soja, Rosafti sai Ɗan sabda. Wai kamar ni 'yar limamai jikar limamai ace duka 'ya'yana babu limami ko malamin makarantar allo." Sai da Dada ta fyace majina sannan ta cigaba.


"Mamman ko ka sa a tube Jafaru ko kuma wallahi sai dai ku nemi wata uwar ba ni ba..."


"Don Allah Dada me yake faruwa?" Baba Mamman ya katse ta hankali a tashe.


Nan take Dada ta zayyane masa duk abin da ya faru, ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba. Cikin kwantar da murya ya fara lallashinta har ya samu ta daina kukan sannan ta ce.


"To yanzu Mamman yadda aiki yake wahala, idan aka tube Jafaru daga aikin nan wacce sana'a zai fara? Tsorona Allah tsorona kada ya fara ɗauke-ɗauke, ni dai na san Jafaru da tsoron Allah ko mage ba zai iya kashewa ba, to ko dai a Lagas ɗin nan ya fara 'yan zuƙe-zuƙe ne da ya zo zai harbe mu?" Murmushi baba Mamman ya yi ya furta. "Dada da ya kashe mana ke ai gara a tube shin kawai, amma dai ba na jin Jafar yana shaye-shaye ki bar ni da shi zan kira shi yanzu a waya wallahi ransa sai ya ɓaci." Dada ta ɗan yi jim sannan ta ce.


"Ni fa Mamman ban ce ka kira shi ka yi masa tijara ba, ina zaman zamana Jafaru ya zo ya cika ni da nunkufurcin tsiya. Ni ban san ma lokacin da Saratu ta koya maka masifa ba, yara irinsu Jafaru sai addu'a da lallashi. Kai kanka Mamman ba don tsayuwar da na yi a Harami ba ai da ban san abin da za ka zama ba, Allah dai Ya shirya mana zuri'a." Baba Mamman ya yi murmushi ya amsa mata sannan suka yi sallama. Uwani sam ba haka ta so wayar ta kasance ba, don haka ta miƙe har za ta fita sai kuma ta wuce uwar ɗakin Dada tana sakin murmushi. A can ƙarƙashin gado ta ciro bankinta ta ƙwaƙulo kuɗaɗen da suke ciki, sai da ta ƙirga su kusan dubu ɗaya da ɗari biyar ne. Ta ɗaure su a ɗankwali haka kawai ta fara sakin murmushi, Dada ta bi ta da kallon mamaki baki a sake.


Baba Mamman na kashe waya ya kira Jafar ya yi masa faɗa sosai, tare da nuna masa illar tsoratar da Dada da ya yi musamman da shekarunta suka tura. Jafar ya fahimci mahaifinsu sai dai shi tsokanar Dada yake da ya ce harbe ta zai yi. Can ƙasan akwatinsa ya je ya tura bindigar ya ajiye sannan ya shiga banɗaki ya watsa ruwa ya wuce ɗakin Dada. A nan ya shiga tsokanarta suka fara hira har Malam na Madina kamar ba shi ne ya gama kabbara yana naushinsa ba.


Uwani na fita can kantin Ɗan bala ta wuce ta sayo alawa irin da raɗin suna leda biyu, sai ta ƙarasa wurin Ali mai dabino shi ma ta sayo gwangwani uku. Sai da ta tsaya a gefen hanya ta kunce kowacce leda ta zuba kofato biyu da ragowar jelar tumaki ɗai-ɗai sannan ta ɗaure. Tana tafe tana sakin murmushi har ta ƙarasa gida, kai tsaye sashen Baba Isuhu ta nufa za ta shiga kenan ta gan shi ya fito da alama masallaci za shi don an kira sallar Magriba.


"Sakaryar banza ke ba kya ganin mutane ne?" Baba Isuhu ya furta yana wurga wa Uwani harara.


"Ga shi wata mata ta ce na kawo maka." Uwani ta faɗa tana miƙa masa ledar hannunta. Da mamaki ya karɓa ya furta, "Wata mata kuma? Ba kuma Lami aka ce ki kai wa ba?" Uwani ta girgiza kai cikin alamun tsoro ta ce.


"Kai ta ce a kawowa kuma ni fa idanun matar ya ban tsoro wallahi, Baba Isuhu dama mutane suna da kofato ne ban taɓa sani ba sai yau?"
A firgice Baba Isuhu ya saki ledar alawar ya ce.


"Kofato fa? A ina kika ga kofaton?" Uwani na ganin yadda ya firgice sai ta basar ta ce, "Bari dai na wuce wurin Dada..."


"Don ubanki za ki tsaya ki mini bayani ko kuwa?" Baba Isuhu ya yi magana jiki na rawa, don bai jima da barin gidan Talle Mai gari ba, da yaje duba shi sakamakon yana kwance sharɓan. Kuma a dubiyar da ya je ne yake shaida masa abin da ya faru da shi a banɗaki da kuma ɗakinsa.

"Eh matar ce na ga ƙafarta da kofato, sai ta miƙo mini ledar nan ta ce na ba ka. Kuma ta ce na faɗa maka idan ka wurgar da saƙon nan a kan mai sunan malam za ta fanshe."Da sauri Baba Isuhu ya tsugunna ya fara tattaro dabino da alawar, a nan idanunsa suka ci karo da kofato, tuno abin da Uwani ta faɗa ya sa jikinsa na rawa ya haɗa ledar ya sa a aljihu ya dubi Uwani ya ce.
"Ina matar take yanzu." Uwani ta zuba hannu biyu ta yi tagumi ta ce. "Ni fa tana ba ni ledar nan da na waiga sai ban ganta ba, wallahi ina jin ɓacewa ta yi don kamar ƙiftawar ido haka na neme ta na rasa." Wani irin sanyi ƙafafun Baba Isuhu suka yi, Uwani ta yi kamar ba ta gane yanayin da yake ciki ba ta shige cikin gidansa.


Baba Isuhu yana nan tsaye har zai fita ko me ya tuna da sauri ya faɗa cikin gida, yana tafe hawaye na zuba don jikinsa ya gama ba shi ta shi ta zo ƙarshe. Uwani na daga ɗakin Lami ta hango shi nan da nan ta ƙunshe dariyarta, yana shiga ɗakin ita kuma Goggo Sala na sirka ruwan wanka don aiki ne ya hana ba ta yi wanka da wuri ba.


"Lami ni kam na shiga uku!" Da sauri Lami ta kalle shi, Uwani na jin haka ta muƙe ta fice. Da yake ta lura hankalinsu ba ya kanta kai tsaye ta bi hanyar banɗakin da Goggo Sala ta bi domin yin wanka.


Lokacin da Uwani ta je wurin banɗakin Goggo Sala ta riga da ta tuɓe har ta fara wanka, a hankali ta saɗaɗa ta janye kayan da ta cire. Sannan ta fara wani irin gurnani tana kukan tinkiya. Goggo sala ta riga da ta saɓa sabulu a fuska da sauri ta dakata, jin ta daina wankan ya sa Uwani ta yi wani gurnani mai ɗan tsoratarwa sannan ta maƙe murya ta ce.
"Gani gare ki Goggo Sala, ki nutsu ki saurari abin da zan faɗa miki domin zai yi miki amfani a matsayinki na jinsin bil'adam." Nan take jikin Goggo Sala ya ɗauki karkarwa kamar mazari, hannu biyu ta sa ta fara kiciniyar goge kumfan fuskarta amma yajin sabulu ya hanata buɗe ido.


"Nan wurin da kike wanka masarautarmu ce, kuma kina tsaye ne akan karagar shugabarmu ga hadimanta nan sai zagaye ki suke yi. Wani abin haushi kin saka su kallon tsiraici, don ma Allah Ya taimake ki aljani Manu ɗan kwarto ba ya kusa da tuni ya haike miki." Jin haka ya sa Goggo Sala ta fashe da kuka, Uwani ta gimtse dariyarta ta cigaba da cewa.


"Ni ce uwar garke wacce kika dafa namanta, to yanzu haka na dawo domin ni dama ba tinkiya ba ce. Kuma namana da kika dafa a tukunya na ɗauke shi na kai garkena, sannan zan kafa miki wani sharaɗi matuƙar kika saɓa masa zan ɗauke ki zuwa duniyarmu."


Goggo Sala baki na rawa ta ce. "To Babata uwar garke faɗi kowanna sharaɗi ne ni mai biyayya ce a gare ki." Uwani ta sa hannu ta toshe dariyarta ta ci gaba da cewa.


"Sharaɗin shi ne kullin za ki dinga goya Isuhu sau uku a rana, safe, rana da kuma dare. Idan kika zo goya shi ki dinga yi kina lasar baki, kuma idan kika kuskure koda na lokaci ɗaya ne ba ki yi ba take zan ɗauke ki ko kuma na tsotse romon kanki."


"Wallahi zan yi ba dai goyo ba, ko har da Lami aka ce zan haɗa na goya su." Goggo Sala ta faɗa cikin kuka.


"Kin taimaki kanki, yanzu kayan da kika cire zan kai shi garkena amma zan bar miki ɗankwali, kuma kada ki kuskura ki fito sai an kira sallar Isha'i domin anfara tattaunawar fadar aljanu da ke. Sannan ɗan autan shugabanmu ya ce da baya da baya za ki tafi ɗaki kina cewa nasara a kanku Isuhu da Lami." Goggo Sala ta amsa, a zuciyar tana da-na-sanin zuwanta zaman daɓaro gidan Lami.


Uwani na gama maganar cikin sanɗa ta koma har lokacin baba Isuhu yana ɗakin don ta hango shi ta cikin labule, ta raɓe a gefen ƙofar ɗakin ta karkace murya ta fara kukan tinkiya. Shiru ta ji sun yi sannan ta yi wani gurnani tana yi tana buga ƙafa irin tsalle-tsallen da awaki suke yi.


"Shi kenan Lami ta zo ina jin tafiya za ta yi da ni." Baba isuhu ya faɗa cikin kuka.


"Ba zan tafi da kai yanzu ba. Ni uwar garke ni ce na aiko maka da saƙo ɗazu. Ku buɗe kunnenku da kyau, uwar garke ba mutum ba ce. Na zo na kafa muku sharuɗɗana idan kuka bi su zan yafe muku zunubin da kuka aikata mini, idan ba haka ba kuma a gabanku zan yi farfesun mai sunan malam na saka ku cinye shi kuma ku shanye romonsa."


"Wallahi ko mene ne kika ce mu yi za mu yi miki biyayya." Lami ta faɗa a tsorace.


"Kai Isuhu da farko taimakonka za mu fara yi kafin ka ji sharaɗinmu. Ƙanwar mahifiyar matarka babbar matsafiya ce a ɓoye, kuma dama da biyu ta zo zaman daɓaro gidanka. Idan kuma ka yi yunƙurin korarta za ta halakaka da iyalinka gaba ɗaya. Daga gobe ne wa'adin aikin da take yi a kanka zai fara, don haka yanzu ma za ku ga ta fito tana tafiya da baya-baya tana ambatar sunanku don haka kada wanda ya tanka mata. Kuma gobe za ta zo da sassafe ta ce maka za ta goya ka. Duk rintsi kada ka bari ta taɓa maka jikinka."


A zabure Baba Isuhu ya ce. "Goyo fa? Ni Isuhu za a goya da giramana ban da iskanci?" Uwani ta katse shi.


"Idan muna magana ba a tankawa. Sannan Sharaɗin da za mu kafa maka ya zama wajibi ka ɗauki rigunan mama na Lami guda uku ka kai wa mahaifiyarka Dada ka ce ta saka su..."


"Dadar ce za ta saka bireziya..." Baba Isuhu ya furta cikin suɓutar baki. Uwani ta buga masa tsawa cikin gurnani ta ce.


"Idan ka saɓa mana wallahi sai mun hallaka ka da kisa mafi muni." Nan take Baba Isuhu ya ce. "Duk abin da kika ce na bi Inna uwar garke."


"Na dawo gare ki Lami. Ke kuma akwai dafin da Goggo Sala ta saka miki a ruwan wanka wanda wa'adinsa gobe zai cika, ko ba kya ganin irin maganin da take zuba miki a ruwan wanka kullin?" Da sauri Lami ta gyaɗa kai.


"Idan kika sake shayar da ai sunan Malam daga gobe ke da shi mutuwa za ku yi, domin dodonta zai zuƙe jininku tas." Da yake Lami ta san Goggo Sala da shegen bin malamai nan take ta aminta da kalaman Uwani.


"Sharaɗin da zan kafa miki ya zama dole daga gobe ki dinga ɗaukan mai suna Malam kina kai wa Jafar shi yana shayar da shi a sashen Dada." Cikin haɗin baki Lami da Baba Isuhu suka ce.
"Jafaru kuma? Shi zai shayar da mai sunan Malam?"


"To kada ku kai shi dama ɗan autan Goɗiya kwaɗayin romon jariri yake ji sai na dafe masa shi." Uwani ta faɗa cikin wata irin murya, don ita kanta dagewa take da tuni dariya ta kwace mata.


"Wallahi za mu kai shi, Allah Ya kai mu gobe." Gabaɗaya suka amsa.


"Kuma ya zama wajibi a gare ka, kai Isuhu ka saka ƙarfi ka danne Jafar domin a shayar da mai sunan malam idan ba haka ba komai zai iya biyo baya. Kuma sharaɗin da zan kafa muku na ƙarshe ko da wasa kuka faɗi abin da ya faru tsakanina da ku, sai na sa wuƙar aljanin mahauta ya yaɗe fatar jikinku sannan na ɗauke ku zuwa duniyarmu a azabtar da ku kamar yadda kuka azabtar da ni." Uwani na daga tsaye ta fara jiyo shasshekar kukan Baba Isuhu. Sai da ta lallaɓa ta ɗauke tukunyar naman da aka yi farfe su ta ajiye a soro sannan ta ce.
"Tukunyar namana da kuka dafa ku same ta a wurin garkena, kada wanda ya fito har sai an kira sallar isha'i domin tuni an zauna zaman fadar aljanu da ku. Kuma idan kuka bari namana da kuka dafa ya kwana a garkena cikin dare zan gayyato tawagar jinsinmu su ɗauke mini ku." Uwani na gama maganar ta fara kukan tumaki tana wani irin dire-dire sannan ta ɗauki tukuyar ta tafi a hankali, kai tsaye ta wuce garken awakinta.


Da yake duhu ya yi awakin Uwani duka sun kwanta, a hankali ta isa turken uwar garke ta ajiye tukunyar. Ta janyo igiyar uwar garke ta saƙale a jikin ƙafar tukunyar, zuciyarta fes ta wuce sashen Dada don ta yi sallar magriba tana tafe tana dariya kamar sabuwar kamu. Har alla-alla take gari ya waye ta ga irin diramar da za a tashi da ita.


A lokacin da ta shiga ɗakin Dada Jafar na zaune ta kofin shayi a gefensa , ga laptop a gabansa yana dannawa, dawowarsa daga masallaci kenan. Uwani na ƙare masa kallo ta tuntsire da wata mahaukaciyar dariya, domin yanayin zaman da ta ga ya yi ne har ta hango yadda Baba Isuhu zai danne shi a shayar da mai sunan malam.


Ɗagowa ya yi ya kalle ta sai kuma ya ci gaba da danna laptop ɗinsa, Uwani ta sake kallonsa ta ga yadda yake jin magani sai kawai ta tsugunna a wurin tana sheƙa uwar dariya.


"Uban me kike yi wa dariya?" Jafar ya furta a daƙile. Tamkar wacce ya sake ingizawa, sai Uwani ta sake fashewa da dariya har da hawaye da ta tuna duk irin haɗe fuskar da yake yi wai shi za a danne a shayar da mai sunan malam.


"Ba tambayarki nake yi ba?" Jafar ya buga mata tsawa.


"Dama wani wasa ne muka fara bugawa ni da ƙawata Lantana shi ne na shirya mata yadda zan cinye ta gobe." Uwani ta yi maganar tana ɗan murguɗa baki.
"Ba na son shashanci idan wannan iskanci za ki yi ki fice mini ba na son hayaniya." Uwani ba ta kula shi ba ta gimtse dariyarta ta shige uwar ɗakin Dada.




Ku kawo wa Jafar ɗauki zai shayar da mai sunan malam🤭🏃🏼‍♀️😂


07062062624
#Ummou Aslam Bint Adam🌚


*UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA*


©AMEERA ADAM


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*


Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login