Showing 3001 words to 6000 words out of 61349 words

Chapter 2 - Halysaah Book Complete By Khaleesat Haydar -1.pdf

dinta suke shi ma taga kayan
abinci ya siyo, Safiyyah ta rike haɓa tace "Duk a kudin scholarship din yake facakan nan? Ko
dai bashi da hankali ne bai san bin komai ake a sannu a kasar nan ba" Khaleesat dai ta dau
Noodles dinta ta bar wajen tana kallon Safiyyah tace "Ga Indomie ki dafa mana, ina son inyi
magana da Ummanmu kafin Aunty Sha'awa ta fita kasuwa" Safiyyah tace "Ohk to" Khaleesat ta
bar kitchen din ta dau jakarta ta wuce dakinta, WhatsApp dinta ta bude ta shiga contact din
makociyarsu Sha'awa tayi mata voice note kamar yanda ta saba a duk sanda take son magana
da Ummanta. Sai kusan karfe hudu na yamma Khaleesat ta raka Safiyyah zuwa gun Lyft din da
tayi ordering don tun daxu Cousin brother dinta ke kiranta ganin bata dawo gida ba, Safiyyah ta
shige motar ta kulle tana daga ma Khaleesat hannu, sai da Lyft din ya bar wajen sannan
Khaleesat ta juya tana tafiya a hankali ta nufi apartment dinta, dai dai apartment din taga mota
yayi parking a space din da aka tanadar don parking for that apartment, bata karasa ba ta
jingina jikin fence din dake inda take tsaye tana kallon motar ta little space din dake between the
wooden fence din, taga ya fito daga motar ta bi sa da ido har ya shiga apartment din yana
danna wayarsa, ta fi minti biyar tsaye a inda take, daga karshe tana tafiya a hankali ta karasa
apartment din ta murda kofar parlon taji ya kulle, hade rai tayi tana kallon kofar, daga karshe da
ta gaji da tsayuwa kawai tayi knocking, sau uku tana knocking sannan ya bude kofar, yana
ganinta yace "Hi" ita dai ko kallonsa bata yi ba fuskarta babu yabo babu fallasa ta bi gefensa ta
shiga parlon, direct gun wayarta dake kan kujera ta nufa ta dauka tare da reading materials
dinta dake saman kujeran, har zata dakinta sai kuma ta dawo ta tafi kitchen ta dau goran ruwa
daya sannan ta nufi dakin, sai da ta bude kofar tayi masa kallon gefen ido taga he is just busy

sorting out some textbooks that were inside a carton he came with, har ta shiga dakin nata bai
juya ba balle ya kalli direction dinta....


07087865788✍
[20/05, 11:37 pm] +234 813 644 0264: https://chat.whatsapp.com/KVY8hjs3iNq5ntSN4Z5g6V



✨✨ HALYSAAH ✨✨



By _Khaleesat Haiydar_✍




2.....

Washegari har karfe sha daya Khaleesat na dakinta bata fito ba duk da yunwan da take ji, tayi
tagumi don gaba daya ta ma rasa what is her problem particularly, ta dau wayarta jin shigowar
WhatsApp message, tun daxu suke chatting ta VN da Ummanta ta wayar makociyarsu
Sha'awa, da taji shiru ta ma zata an maida ma Aunty Sha'awa wayar nata ne, ta bude VN din
tana sauraren voice din mahaifiyarta, Addu'a Ummanta ke mata tana mata fatan nasara a
karatun ta, sannan kamar ko da yaushe ta sake jaddada mata ta kula da mutuncinta ta kula da
kanta, daga karshe ta ƙare da cewa za a kai ma sha'awa wayarta don zata fita kasuwa,
Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya ta ajiye wayar a hankali sannan ta mike ta dau hijab din
sallanta ta saka ta nufi kofa ta bude a hankali ta fita daga dakin don ta gaji da horan kanta da
yunwa ita da ke breakfast da wuri, kitchen ta tafi almost bumping into her new House mate shi
kuma yana kokarin fitowa daga cikin kitchen din, komawa baya yayi at the same time yace
"Good morning" Bata yarda su hada ido ba ta matsa gefe allowing him to pass, ya fito daga
kitchen din yayi wucewarsa without looking at her, sai a sannan ta shiga ciki, tsaye tayi tana
kallon littered cups da plates din da yayi amfani da su ya bari a sink din wanke wanke without
washing them, ga bowl din fruit salad da shi ma ya ajiye bai sha ba, bin kofar kitchen din tayi da
kallon mamaki, to wa ya bari yayi masa wanke wanke? Ta fi minti daya tsaye a inda take da
tunani iri iri a ranta, wata zuciyar ta ce mata kawai tayi abinda ya kawota ta fita daga kitchen din
ta bar unclean utensils din a yanda ya bar su, amma dai kawai ta jawo liquid wash da sponge
fuskarta a daure ta fara wanke kayan wanke wanken kawai, bayan ta gama ta goggoge kitchen
din ta hada shayi ta debi cookies a plate sannan ta fita daga kitchen din ta wuce dakinta. Wajen
karfe uku Khaleesat ta fito daga dakinta, tun da ta gama breakfast take karatu sai sallah kawai
ta tashi tayi da azahar, jin ko ina shiru and to be sure baya gidan ta nufi kofar parlon zata bude
taji an kulle da makulli, dakinta ta koma ta dauko makullinta ta bude kofar tana duba garage

taga babu motarsa a ciki, komawa cikin gidan tayi ta kulle kofar sannan ta tafi kitchen, tun
shekaranjiya take son cin shinkafa da miya amma kasancewar she is not comfortable tun da ya
dawo gidan yasa ta hakura da girkawa, yanzu da taga baya nan kawai tayi deciding tayi
shinkafa da miyar, bayan ta daura shinkafar, ta fara hada miyar dama tana da sauran chicken
thighs a fridge, fitowa parlor tayi da sweeper zata yi shara, ta ajiye sweeper din hannunta to tidy
the couch first, dukawa tayi tana kallon takardun Housemate din nata da ta gani, sai kuma ta
kyabe baki ta bar su nan yanda ya bari a kan kujeran, share rug din parlon ta fara yi bayan ta
dauke makullin da ta gani a kasa, ta dinga juya makullin ganin kamar na Bedroom ne, kafin
minti arba'in ta gama girkin da take ta tsaftace ko ina na gidan, ta debi abincinta ta tafi daki da
shi, sai da ta fara yin sallahn Asr sannan ta dau wayarta tana dubawa, sosai gabanta ya fadi
ganin miss call din Abdul, nan da nan taji abincin ya fita ranta gaba daya, ta zauna gefen gado a
hankali tana kallon wayar, ta fi minti goma zaune a haka, she was soo worried, to yanzu me
zata ce masa ma in ta kirasa, daga karshe ta daure tayi dialing number nasa, har ya katse bai
daga ba, ta sake kira nan ma bai daga ba, duk da yunwan da take ji haka nan taji abincin ya fita
ranta, ta tsani duk wani abu da zai sa Abdul ya daga mata hankali, haka tayi forcing din kanta ta
ci abincin sannan ta kwanta side din gado, bata san sanda bacci ya dauketa ba a haka....
knocking kofar dakinta da ake yi ne ya farkar da ita daga baccin da take, ta mike zaune da kyar
tana murza idonta tana kallon kofar at the same time tana mamakin me zai sa ya dinga
bubbuga mata kofa haka, to ko dai bashi da kai ne?? ta jawo wayarta tana duba agogo taga
karfe shidda da mintuna, bata yi tunanin ta dade tana bacci haka ba, sake knocking da aka yi
yasa ta mike tsaye ta saka hijab fuska daure tace "What is that??" Ta ji yace "Ohk i think i
misplaced my keys, just want to know if you saw it while tidying up the parlor?" Sai a sannan ta
tuna makullin da ta gani a parlor daxu da take shara, tana tafiya a hankali ta karasa kofar
dakinta ta murda key din jiki sannan ta bude door din, tuni har ya bar corridor din ya koma parlor
ya tsaya yana jiranta, da alama dawowarsa gidan kenan a lkcn, ta karaso cikin parlon ba tare
da ta kallesa ba, shi dai duba message din da ya shigo wayarsa yake with all his attention, ta
tafi inda ta ajiye makullin sannan ta dawo ta ajiye masa kan takardunsa dake kan kujera tace
"Here" Yace "Ohk" dakinta ta koma ta shiga tana mamakin wai Ohk, ba ma thank you ba kamar
irin ya ajiyeta din nan, kwafa tayi ta saka ma kofarta key, bayan Khaleesat ta idar da isha ta
sake kiran Abdul bai daga ba, sau hudu kenan tana kiransa tun karfe bakwai bai yi responding
ba, yanzu dai tafi tunanin yana bacci don dare ne sosai a can kasar, even at that tasan she is in
soup, mikewa tayi ta dau plate din da ta ci abinci daxu ta nufi kofa ta fita daga dakin, a parlor ta
ga sabon Housemate dinta yana tattara takardunsa at the same time yana answering phone call
taji yana cewa "I am on my way now" Daga haka ya katse wayar ya mayar aljihunsa ya dau
takardunsa da makullin mota ya mike tsaye, ido hudu suka yi for the first time tunda ya dawo
gidan, ita dai ta dauke kai kamar bata ma gansa ba ta karaso cikin parlon zata tafi kitchen taji
yace "I ate a little out of the food you cook, and...." Yayi pointing takeaway din da ke kan kujera
yace "I am taking some to my frnd too" duk wannan abun bai kalli inda take tsaye ba yake
magana, sai ita ce ma da ta dinga kallonsa da mamaki babu ko kiftawa, ya dau takeaway din ya
nufi kofa cikin hanzari, yace "Good night" Ta bi sa da kallo har ya fita ya kulle gidan da makulli ta
waje, mamaki yasa ta kasa karasawa kitchen din, after some seconds ta tafi kitchen din, da
plate din da ya ci abincin, da cup din da ya sha coffee, da bowl din da ya sha fruits salad duk
suna ajiye a sink babu wanki, ta jingina da kofar kitchen din ta rungume hannu tana kallon sink

din kamar zata fashe don bakin ciki, can ta karasa ciki tana duba shinkafar da ya bar mata, taga
da kyar in zai yi spoon uku, gashi duk yayi littering din wajen da shinkafar wajen diba kuma ya
bar shi haka, haka nan ta juye er shinkafar da ya rage a karamin bowl, ta wanke duk utensils
din, ta gyara ko ina ta goge sannan ta hada shayi ta koma daki da bowl din sauran abincin,
zaunawa tayi gefen gado ta dau wayarta tayi dialing number Safiyyah, sai da ya kusa katsewa
Safiyyah tayi picking daga daya bangaren tace "Allah da gaske baki da kirki Khaleesah, to ko
baki kira ba dai na isa Virginia cikin koshin lafiya" Khaleesat ta ɗan yi murmushi tace "Dama
nasan kin isa lafiya ai, hope you are doing good?" Safiyyah ta tabe baki tace "Oho dai, wannan
ba matsalar ki bane" Khaleesat tace "Amma don Allah ina kika ce ma Ya Musty za ki?" Safiyyah
tace "Ahaf tsaya wasa, sai kace baki san ni ba, munafukar matarsa da yake ba son zamana a
gidan take ba ita ce ma ta kara convincing dinsa, duk zatonsu ina gidanki muna group reading
with some of our Coursemate" Khaleesat tayi murmushi tace "To ai shikenan, yanxu yaushe
zaki dawo?" Safiyyah tace "Gobe ne birthday din ai, in sha Allah i will be back on Monday"
Khaleesat tace "Toh Allah ya kai mu, kinsan mene?" Safiyyah tace "Aa" Khaleesat ta sauke
ajiyar zuciya tace "Wallahi in gaya maki Abdallah ne ya kirani nayi missing call dinsa as i am
speaking to you now tun daxu nake kiransa yaki picking, nasan fushi yayi sosai, ni kuma...."
Safiyyah ta dakatar da ita tace "Ke kuma me? Shikenan rayuwa babu uxuri dama?" Khaleesat
tayi kasa da murya tace "He warned me times without number kar in sake missing call dinsa
Safiyyah, kuma wallahi ina kitchen sanda ya kira wayar kuma na daki ba da gangan nayi
missing kiransa ba" Sounding so pissed off Safiyyah tace "Wai don Allah me yasa kika dauki
tsoron duniya kika dora ma mutumin nan ne Khaleesat? For how long will things continue this
way? Yaushe za ki fara nuna masa ke fa mace ce? yanzu haka za ku yi auren ya maida ki slave
a gidansa tunda kin nuna masa kina mugun tsoronsa tun a waje? wannan wani irin gantalallen
relationship ne? Gaskiya ina jinjina maki Khaleesat, don wallahi in nice bazan iya ba Allah ma
ya gani sai dai duk abinda zai faru ya faru" Cikin sanyin murya Khaleesat tace "I have no choice
nor option Safiyyah...." Tana fadin haka hawaye ya fara gangarowa idonta, a ɗan fusace
Safiyyah tace "To wai ke kadai ce mace a gidanku ne da ya gani? Naga ga Labibah da
Lamisah, ina ce sati biyu kika ba Labibah a shekaru, ita kuma Lamisah wata daya, ga kuma
yayyinki Samira da salamatu, to wai halan su ba mata bane sai ke??" Khaleesat dai bata ce
komai ba tana goge hawayen dake zuba idonta, Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "Ai
shikenan, but u really need to speak up for ur self Khaleesat, ni dai nasan their worst mistake is
sending you to school abroad, aje dai zuwa, ke kuma in har baki waye kin kwatar ma kanki
'yanci daga karshe ba to sorry to say this, wallahi u will live a miserable life in the nearest future
Khaleesat, this is just the fact i am saying, na gaji da lamarin so called Abdul din ki" Cike da
karfin hali Khaleesat tace "Ki daina cewa haka pls Safiyyah, ke me tayani addu'a ce kan Allah
ya kawo min komai da sauki amma ba ki dinga fadin wa ennan maganganun ba...." Safiyyah ta
taɓe baki bata dai ce komai ba, a hankali Khaleesat tace "Pls ko zuwa gobe da safe ki masa
magana ta Whatsapp ki tayani basa hakuri cause nasan bazai daga kirana ba no matter what..."
Safiyyah tace "To naji, Allah ya kai mu goben" Khaleesat tace "Ameen" Sallama suka yi,
Khaleesat ta ajiye wayarta. Karfe goma saura na safe Khaleesat ta fito daga dakinta rike da
wayarta don kar ma Abdul ya kira by mistake tayi missing call dinsa, tun jiya take makale da
wayar duk don kar ya kira bata sani ba, kuma sau uku tana kiransa bayan da tayi sallan asuba
bai daga ba still, yanzun ma da ta tashi sae da ta kirasa sau daya nan ma no answer, zaune

taga new Housemate dinta a ɗan reading nook da aka tanadar a living Room din studying with a
huge textbook dake gabansa, she had no idea ma ya shigo gidan, don bayan da tayi sallan
asuba ta fito ta hada shayi ta sha da cookies a nan parlon sannan tayi karatu har zuwa bakwai
na safe, daga nan ta shiga daki ta kwanta sai kuma yanzu da ta tashi feeling hungry, sau daya
ya kalleta yana ci gaba da duba Textbook din gabansa yace "Good morning" Ta karaso cikin
living room din a takaice tace "Ok" Ajiye wayarta tayi kan 1 sitter ta nufi kitchen, Ya daga kai
yana kallon direction din da ta bi da harshen turanci yace "In baki yi breakfast ba, ga wani nan ki
dauka....." Tsayawa tayi sai kuma ta juya ta kalli Centre table da yake nuna mata, ledan abinci
ne kan table din duk da bata san wani kalan abinci bane a ledan, ta kallesa taga ya ci gaba da
karatun da yake, girgiza kai tayi with no interest tace "No, tnx" Daga haka tayi wucewarta
kitchen, ta fi minti uku tsaye kitchen din tana tunanin me zata yi, seeing her House mate sitted
in the living room yasa ta zama uncomfortable to cook anything, hakan yasa kawai ta dauko
kwalin cereals da bowl zata hada cornflakes, wayarta ta ji yana ring a parlor don tun jiya ta cire
wayar a silent, bata san sanda ta saki both d bowl and the Cereal din hannunta ba ta fito daga
kitchen din within few seconds, House mate dinta ya bi ta da kallo har ta nufi gun wayarta ta
dauka da sauri, sai da gabanta ya fadi ganin Abdul ne ke kiranta, babu bata lokaci ta daga call
din, zuciyarta na bugawa tayi masa sallama, jin shiru tace "Hello" kallon wayar tayi ta sake
maidawa a kunnenta har sannan bata daina cewa Hello ba, House mate dinta dai ya ajiye
Textbook dinsa gefe ganin yanda ta rude ya maida duk concentration dinsa akan ta, Khaleesat
ta sake kallon Screen din wayar jin shiru Abdul ya ki ce mata komai kuma tana jin maganar
mutane a background, marairaicewa tayi ta duka nan kasan living room din ta saka wayar a
handsfree tace "I know u can hear me pls, don Allah kayi hakuri, i am making u this promise
hakan bazai sake faruwa ba wallahi, don girman Allah kayi hakuri" Sai a sannan yayi magana
da husky voice yace "Hold on to ur promise malama, sau biyar kenan kina missing call dina
within a short period, are you out of ur senses or is anything wrong with ur brain?" Da sauri ta
girgiza kai kamar zata yi kuka tace "Wallahi ina kitchen ina girki san da ka kira jiya, kuma...."
Cutting dinta yayi yace "ke, bana bukatar jin komai daga gare ki, none of ur lies and excuses will
convince me, naga kamar u are beginning to take me for granted this days.... Kinsan Allah kika
sake missing call dina zaki sha mamakina wallahi cause it will take me nothing to be in
America...." Hawaye ya cika idonta cikin sanyin murya tace "Amma me yasa baka min uxuri?"
Yace "Baza ayi uxurin ba, ni za ki gaya ma uxuri? A kanki aka fara karatu?" Shiru tayi bata ce
komai ba, yace "Wato ke kin fi karfin ki bude baki ki bada hakuri ko" Kasa cewa komai
Khaleesat tayi don tun da ta daga kiransa ta fara basa hakuri bata kuma san wani hakurin yake
nufi ba, A takaice yace "Anyway, i called to warn you to stop disturbing me with unnecessary
calls, na biyu kuma ki ja ma kawarki kunne she should never come into my DM and tell me
nonsense again don zan dau mummunan mataki a kanta, ke kuma duk sanda yayi suiting

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login