Showing 1 words to 3000 words out of 3370 words
Chapter 1 - LINZAMI DA WUTA Book Free Writing By Gidan Iko.pdf
*_LINZAMI DA WUTA_*
Pages
1️⃣5️⃣/1️⃣6️⃣
NA
GIDAN IKO
_Kirkirarren labari ne da Bai shafi Rayuwar kowa ba kuskure ne babba danganta kai ko wani
dashi babu mafi cancantar suyi suka akan labarin irin taurarun cikin labarin Wanda kuka San
Babu su a zahiri to kar wanda ba cikin jaruman labarin Yake ba yace don shi ko don wani akayi
Hakan jaruman cikin labarin ne kadai suke da damar sukar marubuci akan don me zai
fallasaww duniya sirrin su_
_Fatan alheri ne ga dukkan ma Aura ta sabon aure dama tsofaffin auren Allah ta ala ya kawar
da fitina da gidajen auren musulmi da auren su . Amare da angwaye Kuma fatan Aminci a cikin
auren ku har muddun Rayuwa_
_Da Sunan Allah Mai Rahama Mai jinkai salati da Aminci mara yankewa zuwa ga shugaban mu
fiyayyen halitta ANNABI MUHD sallalahu alaihi wassalam da ahalin gidan sa madaukaka da
masu bin su da kyautatawa har izuwa Ranar Alkiyama_
_MUGUN KULLI_
...............Rana ta kwalle tarwai har hannnun agogo na Shirin nuna Sha biyu da Rabi na Rana
Amma Dr Anam Yana kwance Yana bacci sakamakon wani nannauyan bacci da ya dauke shi
Mai kama da na ya Kora kayan karawa sama hazo....
Yayi juyi Akan faffadan gadon irin na hotel Wanda ya Ni imtu da Sanyin AC da Kuma lafiyayyan
gado da shimfida irin ta more kudin ka...
Ya Kuma juyawa da cike da wani irin Dadi da Nishadi musamman Akan mafarkin da Yake yi da
kyakkyawar yarinyar da tayi nasarar shiga zuciyar sa ta farat Daya wato heeling gabros...
Ya bude idon shi da kyar saboda har yanzu baccin Bai sake shi ba Don ji yake tamkar an watsa
mishi k'asa a cikin idon....
Yayi Mika tare da yaye blanket din da Yake jikin shi Yana wara idanu da son ya hango Heeling
agefen shi Amma sai ya ga wayam
Ya mike Zaune yana Kara caje dakin da idanu da son ya hango Heeling Amma Babu ko
burbushin sawayen ta...
Tunanin sa ya bashi ko tana toilet ne Amma da ya Dubi agogon dakin wacce take nuna mishi
lokaci ya Kuma hango Ranar da ta kwalle sai ya soma tunanin Heeling Bata cikin dakin Amma
duk da Haka Bai yankw tsammanin Tana toilet ba...
Ya mike daga Kan gadon ya sauko Yana tunanin baccin da yayi Mai nauyi Haka yayin da jikin
shi kuma Yake Jin shi ba daidai ba abinda ya kasa gasgatawa duk da zuciyar sa na Ray's mishi
akwai dalilin baccin shi.....
Layin wayar shi na network din glo da idon shi ya hango mishi a saman center table yashe shi
ya haska mishi cewa Heeling Tana da manufa tunda shi ya San layin Nashi a cikin waya Yake...
Sai ya soma waige waige da son ya lalubo wayar shi Amma waya tayi batan dabo....
Ya tura kofar toilet din Yana wara idanu Amma Babu kowa bare Heeling da yake zaton tana
ciki...
Ya dawo baya Yana nufar inda ya ajiye key din motar sa da kudaden sa dake cikin brife case
Nan ma ya Tara's da Jakar kudin tayi batan dabo...
Bai ja da nisa ba ya Gane Heeling tayi mishi Halin Yan bariki.
Ya Shiga wanka a gaggauce ya fito duk har yanzu baccin Bai sake shi ba Amma Bai koma ba
sai ya sauya Kaya Yana mamakin yarinyar. Baiji haushin satar da tayi mishi ba irin yadda ta
gujewa ganin shi da inda zai iya Samun ta don hakikatan baiji zai iya hakura da ita ba don Bata
shiga zuciyar sa don ta fita ba ko kusa Bai ji zafin abinda ta dauka ba irin yadda tagujewa
haduwarsu da Rashin sanin inda zai Sami ganin ta.
Ya dauko laying glo din sa da Mamakin yadda ta aje mishi layin ta kuma tafi da wayar da Kuma
dayan laying na MTN...
Ya sauko reception Yana bada key din dakin Yana tambayar bakuwar da yazo da ita wacce
suka sanarwa Basu ga fitar ta ba
Ya wuce ya siyi karamar waya kafin ya nufi asibiti duk da Yana cike da son Sanin meye hikimar
Heeling da daykar kudin sa da Kuma daukar wayar sa wacce ya San har da tsadar ta yasa ta
dauke ta don wayar Bata Jima da shigowa ba Kuma daga shi sai Hakim ke da ita Daddyn su ne
ya Aiko musu da ita daga London
Ya soma Aikin da ya kawo shi cikin nasara Don Ranar ma mutum uku yayiwa teather kuma cikin
nasara aka soma ganin haske kafin karfe hudu ya baro asibitin. Ya dawo hotel din da y Kama
yayi Oder abinci Yana cike da begen Heeling wacce zuciya ta kakabawa so da kauna bare
Kuma da ya Rungume ta fatar jikin su ta hadu sai Al amarin ya Zama tamkar fami ne a wani
dadadden ciwo...
Ya Gama cin abincin yayi wanka zuciyar sa na fada Mishi ya koma Park din da yaga Heeling ya
Kuma duba ko zaiyi nasarar ganin ta....
Ya wuce a cikin motar sa zuwa agege New sight inda ya Tara's da Yan Good Evening din
kasancewar tun biyar na yamma zaka samu Mata sunci Uban ado na neman fitina da son a
samu Wanda zai Taya a tsadance a buga a kwashe....
Yana isowa Park din ya Rage gudun motar shi Yana duban matan da suke wurin a tsaye Daya
Bayan daya da fatan yayi Ido hudu da ita ba don ya karbi abinda ta daukar mishi ba sai don
gangar jiki da ta azabtu da kaunar ta da son kasancewa tare da ita....
A can Bayan matan da suke tsaye ya hango ta Zaune ba kamar yadda matan suke dakon jiran
Mai tayawa ba. Ita Kam ba ma a layin take ba tana corner kanta Yana Kan wayar hannun ta
tana latsawa ga Alama chat take ....
Da sauri ya sauka daga hanya da son ya tsallako ya iske ta don har wata ajiyar zuciya ya sauke
saboda jin Dadi ...
Ya kulle motar ya nufi inda ya hango ta Amma sai me? Wayam Babu ita Babu dalilin ta abinda
ya bashi mamaki matuka Gaya ya juyo zuwa inda matan suke Yana fatan ganin ta a Nan din
amma Nan ma Babu ita Babu dalilin ta....
Mamaki ya ishe shi yayin da matan wurin suka soma rausaya suna nuna mishi abunda Bai gani
ba da son ya Taya....
Hikimar tambayar matan tazo mishi wata Kil su San ta...
Ya dubi wata da take mishi sigina da idanu da son ya matso...
"Hey beb...
"Hey my Guy ya kake?
Yayi murmushi Jin da hausa tayi mishi magana...
"Don Allah tambayar ki zanyi Babu damuwa?
Ya tambaye ta ta Amsa da go ahead...
"Jiya Naga wata yarinya a Nan na dauke ta shine na zo neman ta ....
"Kaga malam ban San ta ba in ba haja ta kazo siye ba don Allah Kara birnin gaba in kuma na yi
maka mu tsadance kawai....
"Bakiyi min ba ita nake so na Kuma gode...
Wata ta kusa da ita ta amshe da Fadin
"Ke kuwa Keena ai matambayi baya Bata in kin Sani ki fada mishi in kuma Baki Sani ba sai
kice mishi Baki Sani ba my guy me kake magana ne?
Ya matsa Yana Fadin
"Wata yarinya na dauka jiya shine yanzu ma da Nazo neman ta a can fa na hange ta Amma
Wai kafin Nazo Babu ita....
Tayi saurin waigawa ta dawo da kallon ta gare shi tana Fadin
"To my Guy mufa neman kudi muka fito in zaka biya income wata Kil na iya Amsa maka har na
Samu lokacin yi maka Bayani...
Dr Anam Bai tsaya wata wata ba ya zato kudi daga aljihun wandon sa FARAREN bugun Abuja
ya Mika Mata ta Karbe da sauri tana Fadin
"Shiyasa Mai garaje Yake wuce arzikin sa .
Ta fada tana danna kudin a Jakar ta tana Fadin
"Yaya kamannin ta suke?
Ya soma fasal Mata kamannin Heeling har da sarkar cross din da take wuyan ta....
"Queen ce Babu ko shakka a jiya ka dauke ta a Nan misalin bakwai na dare ko?...
"Ba Queen sunan ta ba Heeling ne sunan ta Kuma tabbas a wannan lokacin na dauke ta.....
"Queen ce malam Kar ka min gardama ba Mai sanye da Riga fich color da dogon wando Tite
skin da kitson kalaba ba?..
Da sauri ya kada kanshi Yana Fadin
"Kwarai kuwa itace ....
"Nayi mamaki ma da ka Fadi sunan nata don ba kowa ya San cikakken sunan ta ba gaskiya
Queen shi aka fi sanin ta shima ba kowa ya San ta ba don bakuwa ce ba Yar garin Nan bace
Yar kamaru ce gabros ne yazo da ita Kuma a jiyan suka koma kamaru don gabros din ya jima
Yana jiran dawowar ta ....
"Yanzu fa na ganta a corner can....
"Ba ita bace my Guy kaga wacce ka gani can ..
Tayi mishi nuni da yarinyar da take Zaune tana danna wayar...
Ya kalle ta da kyau ya Kuma tabbatar da gizo da son ya ganta ne ya sa yaga kamar itace....
"Yanzu Ina kike ganin Zan iya Samun ta?...
"Eh to in kana son ganin ta can kamarun zaka je Ina ganin zaka iya Samun ta.....
"Don Allah ki taimaka min da address din inda Zan same ta a kamaru ....
"Bani da shi .
Ta bashi amsa a shake ga Alama ta soma kosawa da tambayoyin Nashi...
Ya Kara damko Yan Dubu dubun ya Miko Mata ta Karbe tana Fadin
"Lallai garin Nan naku ne halan bakatsune ne Kai da baka Jin wuyar kyauta?...
Ya kada Mata Kai
"Zan iya siye lokacin ki gaba Daya in dai Zaki bani cikakken Bayani akan Heeling.....
"Iyakar abinda na Sani kenan Akan ta alaji na Ina ganin in har kwanan jiya ta ruda ka ne ka
gigice to Ina da abunda yafi nata Ina ganin kazo kawai na nuna maka Ni nafi Heeling komai
Wanda Zan firgita ka . Dube Ni da kyau ..
Ta soma juyawa tana karkada jiki...
Yayi murmushi Yana Fadin
"Kiyi hakuri ita kadai nake so maganar kin fi ta kuma wannan ne ban yarda ba Nagode da
amsar ki Nagode sai anjima...
Ya juya da sauri ya bar wurin.
Yana Zaune a Dakin hotel Yana ta faman tunani yayin da zuciyar sa take saka mishi ya Kira
lambar layin shi na MTN yaji idan zai Shiga..
Ya soma saka lambar ya Kuma kira ga Mamakin shi yaji wayar ta dauki tsuwwa Amma har ta
katse ba a dauka ba ya sake Kira shima ba a dauka ba . Sai da ya jera miss call biyar ba a
dauka ba Dole ya kyale ba don ya hakura ba sai zuwa lokaci na Gaba...
Babu abinda yake son sani sai in da zai Sami cikakken address din ta. Waye gabros a wurin ta?
Tace mishi sunan ta Heeling gabros Kuma ance tare da gabros tazo shin gabros Uban ta ne?
Kuma tare da shi take zuwa bariki? Abun fa da kulle Kai da mamaki Amma Kuma in akayi duba
da bariki Babu gaskiya to akwai lauje cikin nadi. Amma Kuma shi Yana da tabbaccin Babu karya
a cikin abinda ta sanar dashi don ta sanar da shi Sunan ta gaskiya Heeling Kuma ya yarda da
ita akan hakan . Amma Uban ta ne gabros? Me Kuma suka zo yi a garin Lagos?
Ya jima cikin shiru kafin ya mike ya daura alwala ya Tayar da sallah.
Duk yadda yake cike da kewa da bege baiji wata mace tana burge shi ba. Kai hatta da Nimra
da take matar shi dama hada su akayi ba shi yace Yana son ta ba shiyasa kawai ya Karbe ta
matar Hadi ne Amma ba Wai don ta mallaki abinda Yake so ba. Sai dai shigowar shi garin
Lagos yayi tuntube da yarinyar da ba ma musulma ba ahalul kitabi kuma yaji ya gani ...
Tunda ya Kira wayar Nan Yake ta faman jaraba Kiran Amma sai ya samu laying ma a kashe
Kuma har yau din da Yake da sati uku a garin Lagos Bai Kuma Samun laying ba
Bai taba sanin cewa ba da Wasa son Heeling ya kama shi ba sai da ya baro garin Lagos. Garin
da ya Samo tarin alheri Mai yawa na ban mamaki kasancewar shi kwararre Akan Aikin shi. Ba
don asibitin ta so tafiyar sa ba sai don Yana son Samun nutsuwa.
A Ranar da zai baro garin Lagos ma sai da ya koma Park din Nan da fatan ya gamu da Heeling
Amma Babu ko Mai Kama da ita. Dole ya sallama ya dawo katsina cike da wani irin Sanyi da
jimami
Nimra Kam ba wata matar aure ce cikakkiya ba don duk tsayin makonni da Dr Anam yayi a
Lagos Bata tab'a neman shi taji Yaya yake ba bare Yan kunji kunji irin na miji da Mata sai fa in
shine ya Kira . Kuma ko ya Kira din tamkar Yana Mata Dole take amsa wayar sa.
Sai Kuma yazo yayi Rashin contact Banda ma Yana da layin glo Wanda da shine Yake karbar
alert Kuma Yana da email komai NASA Yana ciki don Haka ya copo contact din sa zuwa layin
glo din don bai ma fara tunanin yin welcome back ba don Gaba Daya tunanin sa Yana ga
Heeling ba Kan daukar wayar sa da kudaden sa ba. A a sai don son ta da ya Hana shi sukuni...
A Daren da ya dawo Bai samu wata tarba daga Nimra ba hasali ma ita bata iya wannan Abu ba
Wai tarbar miji da nuna mishi shi din wani Abu ne
Tana zaune a falo sanye da Rigar Mai sulbi tamkar night gwon Mai siririn hannu wacce ta fito
Mata da Surar ta sai Kuma dogon wandon Rigar gashin ta yasha gyara sai sheki Yake Yana
walwali fuskar ta dauke da make up irin na Mata masu aji tayi kyau matuka Gaya ko da yake ko
dama can Nimra Mai kyau ce kyau kuma na MAMAKI...
Tana Rike da waya tana kishingide a kujera tree seater yayin da tv take ta Aiki Amma ba kallon
take ba face wani Abu da ya dauki hankalin ta a wayar ...
Ya shigo da sabuwar brif case din da ya sake siye Yana sallama
Nimra ta dago tana kallon shi ta Amsa sallamar kamar Mai ciwon hakori ta mayar da kanta ga
wayar ta..
Ya Zauna Yana murmushi Yana Fadin
"Madam ya na same ki? Kuma Babu ko neman ba Asin jimawa ta uhum?
Ta dago tana Fadin
"Wallahi da baka Nan na sarara Anam Amma yanzu da ka dawo yanzu ne kaina zai soma
ciwo...
Ya Rungumo ta Yana shafa dogon wuyan ta da son ya sumbaci bakin ta Amma ta soma kicin
kicin tana neman kwacewa abinda ka hada su Kenan har ya nuna Mata karfi idan ya Gane zata
tauye mishi hakki kamar yadda ta Saba..
Ta kwace da kyar Bayan ya samu abunda Yake so wato kissing din nata
Ta motse fuska tamkar zata saka kuka don ba karamin bakin cikin hakan tayi ba.
Yana mamakin yarinyar har wani lokacin Yana Mata uzurin wata Kil irin matan Nan ne Wanda
Basa son maza na kusantar su don shi dai Bai tab'a ganin nimra ta ziyarci dakin shi ba bare
kwanan turaka yakawo ta sai fa in shine ya Kai kanshi kuma ba za a kwashe kalau ba duk ranar
da ya nemi hakkin sa sai sai tayi kamar ta kashe shi don haka in dai ta yardar ta zaibi to ba zai
taba samun kanta ba sai fa in karfi ya gwada mata ...
"Wai kina tsoron Allah kuwa Nimra....
"Kai nake tsoro ai.
Ta mayar da bak'a...
"Wai Baki San mala iku suna tsinewa mace Mai bijirewa miji ba?...
"Sai dai suyi ta tsine min tunda na Gane maza Baku da burin da ya wuce ku kashe mata komai
sai kun nuna iko da gadara ...
Ya mike Yana Fadin
"Allah ya shirye ki tun Baki mutu kin afka Johanna ma ba a shirya min abunci Ina tare da
yunwa...
"Ka saka Mai Aiki ta shirya maka in ba neman magana ba ai Ni banzo wannan Aikin ba kafi
kowa Sanin Haka..
Ya wuce Yana hada Ruwan wanka yayi kafin ya fito ya Shiga kitchen din ba don ya so ba sai
don Babu yadda zaiyi cin abincin Mai Aiki
Ya shiryo abincin yazo ya Zauna Yana ci Yana saita tashar MBC action .
Tana ta dannar wayar ta kafin ta mike ta wuce Daki yabi ta da kallo zuciya na Raya mishi son
wani Abu wurin Nimra duk da ya San ba zasu kwashe kalau ba
Ya jima Yana kallon kafin ya kashe komai ya Rufe kofofin ya wuce yana yin brush ya fesa turare
ya tunkari dakin nata
Tana kwance Akan gadon bacci ya soma daukar ta taga shigowar shi
Da sauri ta mike Zaune tana Fadin
"Don Allah