Showing 1 words to 2897 words out of 2897 words

Chapter 1 - SHAGALA! FREE BOOK NA MUJAHEEDAH MATAR MALAM AMMYN KHAUSAR.pdf

24 Jul 2025

662

*SHAGALA!!! _ FREE BOOK*

_RUBUTA ✍️ LABARI DA TSARAWA
MUJAHEEDAH MATAR MALAM AMMYN KHAUSAR



*GAJEREN LABARI MAIƊAUKE DA DARUSAN RAYUWA,. IDAN KINGA LITTAFIN YAZO
DAIDAI RAYUWARKA RAYUWARKI PLZZZ AGAFARCE NI BADAN KE NAYI BA SAIDAI INA
FATAN ZAIZAMA SILAR CANZAWARKI KO CANZAWARKA... ALLAH MUDACE*

*(8/11/2022 TUESDAY NOV.....)*

_Ada nace nadaina harkar rubutu gaba ɗaya amma Abokan Arziki kuma ƴan'uwana marubuta
suntaka rawar gani dan ganin naci gaba dayi.. saidai haryanzu banace nadawo dika ba amma
zanriƙa ƙoƙartawa dai naɗanyi...... Mmn Amatullah zuwa Mmn Nusaiba butulci bazaisa nakasa
faɗar Alkairanku gareni ba, Ƙwarin gwaiwarku yasa nadawo kan typing, Mmn Amatullah kinjima
kina taka rawar gani gareni kan rubutuna ina gdy sosai Allah bar Ran SOOO INAYINKU
DUKA Kuma inayin Ƙungiyarku JARUMAI_……………………

*Godiya ga Allah maɗaukakin sarki daya sake bani ikon Kawo muku sabon littafin nan nawa
maitaken SHAGALA!!! Ina roƙon Allah daya bani ladan Ayukan Alkairi dake ciki saɓanin
hakan kuma Allah yamun Afuwa*

_Ina daɗa godiya gareku masoyana Inasonku nima harko yaushe_



_Dasunan Allah mai rahama maijin ƙai…………… BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM._

️1&5

GOVERMANT HOUSE.... Haka nagani ruce da manyan baƙaƙen Haruffa,.

Ciki nasamu nashige babban Holl na nufa inda nakejin Alamar magana Ƙasa ƙasa tana
tashi ba tinanin komai nasamu nashige ciki,

Mutane 10 Rak nagani zaune suna meeting,

"Kota halin ƙaƙa dole ni Alhaji Bashir sale nazama Shugaban ƙasa ko Anaso ko ba'aso"


Da mamaki ɗayan ya ɗago wanda naƙare masa kallo nagano ba musulmi ba ne, Yace

"Amma taya kake wannan tinanin excellancy bayan ga Abunda muka musu sanda muke
Governors ma Ai bazasu sake bamu damar hawa kan mulki ba tinda ko yanzu bamu tsinana
musu komai ba," Yaƙarasa maganar cikin gurɓatarciyar hausarsa.

Hahhhhh "Haryanzu baka san meye siyasa ba Samual Ai su talakawa kamar dabbobi su
basuda kaifin tunani sudai kabasu ƙuɗi kawai, Inada goyon bayan manyan ƙasa tare dani
kagako mulki bazai ban wahala bayan inada Sarakuna manyan ƙasa malamai Attajirai suma fa
dika Ƙuɗi na siyensu, kai duniyar nan ba Abinda ƙuɗi basayi kaidai inzaka jajirce to zaka zama
deeputy presdent kawai,"

Hahhhhhh
Fashewa dika sauran mutane sukayi da dariya harda shewa,

Ɗayan yace "Ai Excellancy ƙuɗi shegune wllh Akan ƙuɗi ba Abunda mutum bazai iyayiba, To
amma Akwai wani hanzari ba gudu ba, Kasanfa wancan shegen nason mana fintin kau kaga
yawan jama'ar da yatara lokacin da yayi Campain ɗinsa kuwa? idan natina jikina yakanyi sanyi
fa kasanfa shi Akwai gaskiya," Cewar Sulaiman sani Charman paty
Mtssss "gaskiyar sa tabanza Aka gayama yanzu gaskiya na tasiri ne? Abu ɗaya kasake ƙuɗi
shikenan kuma inadasu ga goyon bayan manyan ƙasa danake dasu ga bokayen mu kai wllh
kota wacce hanya ma ni Alhaji bashir sale sainayi shugabancin ƙasa, dacan Aka gayama su
Ƴan siyasa zama suke Abanza basa shige shigen bokaye? kudai kucigaba da ƙoƙarin fidda
ƙuɗi kuna siye jama'a sauran kubarmu kwasha mamaki,'"

(OHO SHIFA TALAKA ANRAINASHI WLLH, KODA YAKE MUNE MUKA RAINA KANMU
DAMUKE SON ƘUƊI SAMA DA ƳANCINMU, WLLH MUGYARA KO MAGA DAIDAI WANNAN
SHAWARAR AMMYN KHAUSAR CE KAWAI..)

Ahaka dai sukayi ta tattaunawarsu harsuka kagama .....………………

NIMADAI ANAN ZAN GAMA AMMAFA WANNAN PAGE ƊIN ZANCIGABA NEXT COMMENTS
AND SHARING PLZZZ.......

WhatsApp Number 07064904617 OR Call 07031012948

_BASEERATA ITACE ARZIKINA_
*SHAGALA!!! _ FREE BOOK*

_RUBUTA ✍️ LABARI DA TSARAWA
MUJAHEEDAH MATAR MALAM AMMYN KHAUSAR

*GAJEREN LABARI MAIƊAUKE DA DARUSAN RAYUWA,. IDAN KINGA LITTAFIN YAZO
DAIDAI RAYUWARKA RAYUWARKI PLZZZ AGAFARCE NI BADAN KE NAYI BA SAIDAI INA
FATAN ZAIZAMA SILAR CANZAWARKI KO CANZAWARKA... ALLAH MUDACE*

_Ada nace nadaina harkar rubutu gaba ɗaya amma Abokan Arziki kuma ƴan'uwana marubuta
suntaka rawar gani dan ganin naci gaba dayi.. saidai haryanzu banace nadawo dika ba amma
zanriƙa ƙoƙartawa dai naɗanyi...... Mmn Amatullah zuwa Mmn Nusaiba butulci bazaisa nakasa
faɗar Alkairanku gareni ba, Ƙwarin gwaiwarku yasa nadawo kan typing, Mmn Amatullah kinjima
kina taka rawar gani gareni kan rubutuna ina gdy sosai Allah bar Ran SOOO INAYINKU
DUKA Kuma inayin Ƙungiyarku JARUMAI_……………………


️10&20

_________Waye Alhaji bashir sale?

Cikakken ɗansiya maitarin dukiya yana da mata 2 Hajara da lami, tafiyarsa da lami tazo
ɗaya domin itama *TASHAGALA!!!* Da duniya tamanta Ana mutuwa sam burinsu kawai duniya.
Ƴaƴansu 4 inda hajara keda 3 Haisam Hisan Ishan, lami keda ɗaya Namir.

Zaune yake gaban bokansa ya sanda kai ƙasa yana kora masa bayani Akan wannan
takarar ta shugaban ƙasa da yake nema,

"Tinda kazo wurinmu magana taƙare dama tinda kasanmu karabu da matsala, Yanzu
munason ka kawo idon jarairai sabuwar haihuwa na yara 8 da gashin gawar namiji wanda
yashekara 10 da mutuwa, zakayi wanka da jinin mutum wanda zai Aikama ka yau da dare A
banɗakinka zaka daina sala natsawon kwana 40,"...
"……Amma boka wannan aikin yamun tsauri nadaina sallah fa, bayan na kashe mutane kuma
saina daina sallah haba boka kasauya wani Abin dai,"

"Kaiiiih Bashir damu zakayi gardama? kasan kanason yin sallah kazo nan? tokaje can kanemi
buƙatar ka nafasa baka taimakon, ni zaka kawowa shashanci?,"

"A'a yi haƙuri boka zanyi wllh zandaina indai Zansami biyan buƙatata to badamuwa zanyi,
gawannnan"

Maƙudan ƙuɗi ya zube sannan yawuce.

Yana fita ya kira ɗaya daga cikin yaransa Manta sabo, ya zayyane masa Akan yaje ɗebo
gashin gawar dama idan jarirai.

Kamar yadda boka yace haka Alhaji yadaina sallah kuma yayi wanka da jinin mutum,

Loƙacin zaɓe nadaɗa matsowa inda Alhaji bashir da manyan ƙasar suka kwashe ƴaƴansu
zuwa ƙasar waje suka maida namu ƴan ƴan natalakawa nasu suna ta tabbaka ta'asa na faɗace
faɗace da kashe kashe da ƙone ƙone da raunata junansu,

Agan idanuwansu sukan nuna sune nasu bayansu kuwa sune Abun zagi,


Alhaji bashir yayi Amfani da ƙarfin mulki na samun ɗaurin gindin manyan sarakuna bokaye
malamai da siye ƴancin talakawa dasuke Akan ɗan ƙannanen Abu yazama shugaban gasa...



Sam Haisam bayajin daɗin ta'addancin ubansa dayake Amma bayar da zaiyi tinda ubansa ne
sai haƙuri kawai amma yana masa fatan shiriya,.

Namir kam kasuwa ta buɗe inda dik wani gidan rawa dana giya ansan dashi gashegen bin
mata,.

*******************

Aina kiji tsoron Allah kidaina *SHAGALA!* Haka kadafa kimanta ke marainiya ce, bakida Uwan
wllh kidaina biyewa samarin nan dik badan Allah suke tare dake ba dama ƙawayen banzan nan
dik kiwatsar dasu kidawo hanyar gaskiya kidaina *SHAGALA!*" Cewar Ashna ƙawar Aina tinta
yarinta
"Naji nagode Allah bada lada," cewar Aina tana wani tauna chinwingom haɗida latsar wayar ta

"Aina kisaurare ni gaskiya nake faɗa miki A matsayina na ƙawarki dik waɗanda kike tare
dasu wllh ba masoyanki bane tinda bazasu iya faɗa miki gaskiya ba, kum wllh dik mazan nan
dakike gani dasun gama ɓata rayuwarki wllh Zasu gujeki hakama ƙawayen nan Inaƙara faɗa
miki kidaina *SHAGALA* Kiji tsoron Allah"
"Sai mun sake haɗuwa ni nazantafi baby na ya kirani, so kike nazauna na lalace narasa ƙuɗin
kashi dana fantamawa bayan ga matsin rayuwa wllh to badani ba kinga tafiya ta inzaki hau
hanya kema zaki iya inko kikace A'a saiki zauna kiyita ƙaurin talauci kuma kinaganin baƙinciki ni
dai bazan iyaba Uban kowama zai iya *SHAGALA* Ai"
Tafiyar ta tayi tabar Ashna tana girgiza kai haɗida mata fatan shiriya..

*****

"Abokina wai haka zamu zauna talauci ya kashe mu baya ga hanyar samun maƙudan
ƙuɗaɗe?"
Cewar Ayuba

.

"To ni Ayuba wacce sana'a zamuyi bayan kiwon shanu damuka gada kuma ko masu ilimi
gasunan suna wahala ba aiki balantana mu ƴan ƙauye kuma fullani,"



Mtswwwww "kaifa wawa ne tukur ga sana'ar kidnapping kwashe muta ne,"

"kidnapping kuma Ayuba............

COMEN AND SHARING PLZZZZ

WhatsApp number 07064904617 or Call 07031012948



_BASEERATA ITACE ARZIKINA_


Page 30&40

"Eh kidnapping fa nace yadda kunnuwan ka suka jimaka haka nafada, kai inbanda sakarci irin
naka wacce sana'ace zamuyi tabada k'ud'i sama da wannan"?


"Amma Ayuba kasan tanada hatsari kuma ba kyau,"


"kai dalla can yo mutum nawa keyin Abunda baida kyau Aka gayama su manyan namu sunayin
Abu maikyau ne? nagama magana inzaka kashirya gobe zamu fita birni fara aiki,"



"to kayan Aikin fa? irin su bindigogi da sauransu"?

"kada kadamu da wannan kaidai muhade bayan gari Agobe kawai".

Hakance takasance samun makamai baibasu wahala ba karon farko suka kwashe mutum 3
basu badasu ba saida Aka biya millan 2..



***********


"Daddy Amatsayina na d'a nake gayama gaskiya wllh Abunda kake *SHAGALA* ne kamanta
lahira ka sai neman duniya kake wai duka saboda mulki abunda zaka bari nan duniya, bakomai
cikin mulki face wahalhalu da za'a bud'e lahira ka hango Hukuncin masu mulki koda masu
Adalci ne wllh da Daddy shugabanci kona gidan kane wllh daka barshi bakomai face masifa,
daddy kafarka kadaina *SHAGALA* Haka,"


"Naji Allah gafarta malam kuma nagode zaka iya tafiya inka gama, yo ma inbanda rashin
kunya dame Ake cidakai? dame kake fita k'asashen duniya? saboda me Ake girmamaka? badik
saboda mulkin ubanka bane amma kazo kamun rashin kunya wllh kafita idona inko bahaka ba
zanyi maganinka mara mutunci kawai,"

barin gun haisam yayi cike da haushin halin ubansa amma yana masa fatan shiriya..


(((NI KO NACCE WADDA YAYI NISA AI SAM BAYAJIN KIRA))

_BASEERATA ITACE ARZIKINA_




Page 50&60



............Aina kuwa tawanke dayawa yau bata gun wancan gobe bata gun wancan samari nata
rusa mata rayuwa da dad'ad'an mayaudaran kalaman nasu, Ashna tayi fad'a harta gaji tazuba
mata ido dan talura tagama *SHAGALA* baki d'aya,



Ahaka har Ashna tayi auren ta amma banda Aina...

Rayuwa tayi zafi Abubuwa suntsananta ga talakawa ba mafita, tsadar rayuwa ta Addabe kowa
inda maza masu k'arancin tauhidi suka fad'a harkar kisa da sace sace mata kuwa karuwanci ba
inda zakaje kasami sauk'i manyan k'asa sunyi shuru Anata aikata b'arna dukansu sun
*SHAGALA*


>>>>>>>>>>>


BANYI LITTAFINA DAN FADA'A DA GWAMNATI KO CIN ZARAFIN WANI BA A'A NAYI DAN
MUFALKA MUDAINA SHAGALA DOMIN MUTUWA NATAFE....




Dik Abunda muke kawai Allah yana Aramana ranane Akwai ranar k'arb'ar saka mako, Allah
kabamu ikon Aikata Alkairi Allah kashiryar damu baki d'aya.



page 70&80


Wannan buk d'in bana iya nishad'i kawai bane nasan zaibaki haushi amma idan zaki kallesa da
idan basira to zaki fahimta.....




lamura sunfara kwab'ewa Alhaji bashir inda wannan karon kujerarsa kemasa barazanar
rasata, d'ayan b'angaren kuma bokansa yayi mutuwar walak'anci.


kamar yadda yasa ba yana zaune yana tsibbace tsibbacensa, kawai saiya fara tari garin
shure shuren nasa yabuge kaskon wutar da kegabansa aiko take gun yakama yanaji yana gani
harya cinye cikin wutar ihu kam Mutan garin sunshashi.

Mutuwar tagirgiza ilahirin mabiyansa musamman su Alhaji bashir,



Mutane sunduk'ufa gun neman sauk'i da rahamar Allah...




b'angaren Ashna kuwa lafiya k'alau take zaune da mijinta da samun Albarkar
rayuwa...................




Page 90&100


final final page insha Allah



......Ciwo maitsanani ya kama Aina inda tinkan taje Asibiti k'awayenta dama samarinta duk
suka fara ja baya da ita, bayan taje Asibiti gwajin farko ya nuna tad'auke da H.I.V tincikin
Asibitin take rusa kuka hartaje gidan d'aya daga samarin Bata, Amma yamata korar kare
hakama k'awayenta dake k'ara d'aura ta kan hanyar banza suna *SHAGALA* r da ita duk suka
barta Ciwo yaci k'arfinta ba k'ud'in magani ba mai kula da ita hakan yazama silar mutuwarta
Atake...



Ashna taci kuka sosai bayan samun labarin amma tana mata Addu'ar samun haramar Allah..



Alhaji Bashir kuwa ba'a mutu ba Amma ga matanbaya domin dik yazare ga rashin lafiya ga
hauka ga talauci dika y'ay'an nasa dayake sangartawa sungujeshi hakama Abokansa saboda
Ayanzu ba mulki ba dukiya, mama dasu haisam be kawai kewahala dashi garin haukar tasa
yafice batare da sunsani ba k'atuwar tirela tabi takansa, Nan take ya mutu.....

Tab'angaren su Ayuba da mugu kuwa garin sace sacen su da cutarda Al'umma Allah yak'arb'e
rok'on bayinsa dan kuwa hargitsi yataso tsakaninsu bawanda zaice ga sila saikawai suka hau

kashin junansu, harsuka k'are Akayi ragas.....



Alhmdllh Anan nakawo k'arshen wannan d'an guntun gajeren labarin nawa maitaken
*SHAGALA* Inafatan zaku amfana da hasken da keciki, ba tawan labarin ne ma'anarsa ba
samun Abunda zaisa ka k'aru harkayi takatsantsan shine burgewa...




((Zama Ayi labari maicike da batsa wannan kuskure ne domun kuwa Akwai randa Allah
zaitanbayeku Akan Wannan littafin dakika cika da batsa., Kuma makaranta Allah zaitanbayeku
Akan Wannan littafin dakuka zauna kuka karanta maicike da batsa, so mukula mukuma maida
hankali mugyara kabarukanmu tinkan mushigesu wannan shawara ce kawai Daga Mujaheedah
Matar mlm AMMYN KHAUSAR inbata muku dad'i ba to kumun Afuwa Dan Allah.....))




{{{{{{IDAN ZAKU FAHIMCE WANNAN LITTAFIN NAWA MAITAKEN SHAGALA ZAKU
FAHIMCE YANA MAGANA AKAN ZALUNCI DA SHAGALA BASA D'AUREWA KAWAI NAD'AN
LOKACI NE, DIK HALINNAN DAMUKE CIKI NARAYUWA ALLAH YANA SANE DAMU KUMA
SUMA MASU ZALUNCIN ALLAH YANA SANE DASU, KADA MUD'AUKA SUNFI K'ARFIN
UBANGIJI A'A RANACE ALLAH YA ARAMUSU IDAN YATASHI KAMASU TO ZAIKA KAMASU
AKAN DIKA LAIFUKANDA SUKA AIKATA.. TO KAWAI MUCIGABA DA ADDU'A DIK TSANANI
WALLAHI YANA TARE DA SAUK'I, ADDU'A BATA FAD'UWA K'ASA BANZA KODA BA'A
ZALUNCEKA BA BALANTANA ANMAKA TOMUCIGA SAUK'I NAZUWA INSHA
ALLAH........ALLAH KAKAWOMUNA K'ARSHEN WAD'ANNAN FITINTINUNNAN AMEEN...}}}}}}






====GAREKI MAIBIYEWA MIYAGUN ABOKAI........GAREKA MAIB'ATA RAYUWAR Y'AR
MUTANE....
Kasani dik tsiyar da kashuka wllh saika girba, ka lalata Matar wani to kajira randa wani zai lalata
Matar ka! Ka lalata uwar wani to kajira randa wani zai lalata uwar ka! Ka lalata y'ar wani to kajira
randa wani zai lalata y'ar ka, domun baka Isa kaci banza ba wllh ita zina bashice dik Wanda
yaci saiya biya wllh.......... Kinzama shasha hartana iya baki shawarar banza ki d'auka idan
taje jeki shiga wuta Bata miki komai ai, shin zakishiga?? A'a Amma saboda rashin ganewa tace
kibi maza dadik wasu Ayukan b'arna dazasu saka ki SHAGALA Harkishiga wuta Amma kiyi..

Muji tsoron Allah mudube k'awayenmu idan basu dace da rayukanmu ba murabu dasu kawai
tinkan su halakamu. Allah yakaremu da kariyarsa Allah kasa mudace Mufalka mudaina
SHAGALA Ameen)))..




(((FARIN CIKI FARIN CIKI☺️☺️☺️ YAU Y'ATA KHAUSAR TACIKA SHEKARA 1+ ADUNIYA,
INA ROK'ON ALLAH DAYA K'ARA MATA WASU SHEKARUN MASU ALBARKA, ALLAH
YAK'ARA MATA LAFIYA, ILIMI HAK'URI BASIRA BAIWA D'AUKAKA TAUSAYI TA WAKKALI
K'AUNAR IYAYENTA DA DIK MAISONTA AMEEN.. HAPPY BIRTHDAY TO YOU MY
DOUGHTER KHAUSAR ONCE AGAIN ❤️..... TUESDAY 15/11/2022
NOVEMBER..))))




SAIMUN HAD'E A NEXT BUK D'INA





WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948



_BASEERATA ITACE ARZIKINA _

1

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login