Showing 1 words to 2640 words out of 2640 words
Chapter 1 - KUNDIN TSATSUBA Book 5 By Abdulaziz Sani Madakin Gini .docx
KUNDIN TSATSUBA
BOOK 5 COMPLETE
Writing by
Abdul'aziz Sani Madakin Gini
07032707179
hatsabibi na hatsabibiya, hannu biyu maganin kazamar miya.
Ko da Yelisa ta zo nan a wannan kirari, sai dadi va kama Jafar, va dakatar da ita ya ce "Dakata kawata, bari zuga ni haka ka da kaina va fashe Tunda ai an ce yaba kvaata tukuici, ni ma ya kamata na da wasaki. Gaishe ki karama mai babban aiki. Ke ce tsafi, kuma kin sha tsafia nono. Kyalkyali ki ke mai dadin kallo daga nesa, da zarar kin matso kusa sai ki zama wuta mai kuna. Gaba kadan za k zama tauraruwa mai haske duniya. Sannu da fama yar matsafa."
Sa'adda Yelisa ta ji wannan kirari da Jafar yayi mata, sai ta bushe da dariya ta ce "Lallai na yarda ka gaji hikima, sai dai ka sa ni a duhu, me kake nufi da ni ce tauraruwar da zan haskaka duniya nan gaba?"
Yayin da Jafar ya ji wannan tambaya, sai yai ajiyar zuciya ya ce "Ya ke kawata, hakika kin yi mini tambayar da ba zan iya ba ki amsarta ba a yanzu, ki yi hakuri lokaci yayi halinsa za ki ga amsar da idanunki."
"Shi kenan zan jira izuwa lokacin. Yanzu me muk yanke shawara dangane da batun wannan tafiya ta mu?"
Jafar yayi murmushi ya ce "Ai mun gama Magana kawai gobe za mu konta ga mahaifinki mu sanar da shi cew mun amince ya hada mu da bawansa Nargaz mu tafi izuw jejin Kalkim. Sauran al'amari ki bar komai gare ni, tabbe zan kubutar da mu daga dukkan wani tarko da makirci."
"Na san zaka iya abokina." Yelisa ta fadi sa'adda tada hannayenta biyu, sai ga abinci da ruwan sha ya bayyan bisa kan wata shimfida da ke gabansu.
ko." Yelisa ta dubi Jafar ta ce "Ai sai ka zo mu ci abinci
Ba tare da bata lokaci ba suka zauna tare suka wanke hannayensu da ruwa, sannan suka hau abincin da ci. Suna cikin haka ne, idanun Yelisa suka ciko da kwalla ta fara zubar da hawaye, al'amarin da yayi matukar tayar da hankalin Jafar, ya dube ta cikin alamun tausayi ya ce "Ya ke kawata, ina dalilin wannan kuka naki?"
Yelisa tasa hannu ta share hawayenta, sannan tace "Ba wani abu ba ne ya sani kuka face tunowa da mahaifiyata, wadda ta rasu tun ban fi shekara shida ba a duniya a Kokarinta na hada wani tsafi mai hadari. Ya kai abokina, ka sani cewa har yau ina iya tunowa da lokutan da nake zama tare da ita muna cin abinci. Hakika ta nuna mini matukar soyayaya, kai duk sihirin tsafin da na samu ma daga gareta ne, ban taba samun sihiri guda ba daga wajen mahaifina. Duk sa adda na zauna zan ci abinci, sai na tuno da ita, wannan dalili ne ya sa ka ga ina kuka."
Sa'adda Yelisa ta zo nan a zancenta, sai ta dago kai ta dubi Jafar, bisa mamaki sai ta ga shi ma yana zubar da hawaye. "Abokina, mene ne dalilin naka kukan?"
Jafar yai ajiyar zuciya, sannan ya ce "Wani abu ne ya ba ni mamaki. Kusan komai na rayuwarki irin nawa ne. Ki sani cewa sunan mahaifiyata Zuhura, kuma yau shekara guda kenan da rasuwarta. Lokacin da mahaifiyata ke raye babu irin gatan da bata nuna mini ba, saboda tsananin son da take mini ya sa take ziyartar bokaye don su bincika mata irin rayuwar da zan kasance a ciki. Duk wajen bokan da muka je sai ya ce da ita 'Danki zai shahara a duniya, kuma zai karói
wani bakon addini wanda zai kawar da dukkanin sauran addinai a doron kasa. Amma ki sani cewa ba za ki kai wannan lokaci ba, domin ajalinki na nan kusa."
Sai da mu ka je wajen bokaye arba in suna fadin haka, bayanin dayansu bai saba da na sauran ba. Tun daga wannan rana hankalin mahaifiyata ya dugunzuma, ta shiga bincike don ta gano irin addinin da aka ce zan karba, har ajalinta ya zo ba ta gano addinin ba. Ni ma yanzun da nake miki maganar bangano ba. Lallai zan ci gaba da bincike da kuma tambaya har sai na gano wannan addini. Tabbas na san ina da babban aiki a gabana, amma sai bayan mun sami nasarar bude Kundin Tsatsuba sannan zan mai da hankalina kansa."
Haka dai Jafar da Yelisa suka ci gaba da hira, har dare ya raba sosai, barci ya sace su.
BABI NA BIYU
Da ranar taliya jejin Kalkim ta zo, Boka Jinshan ya sa Jafar da Yelisa a gaba yana karanto musu dokokin da za su kiyaye don samun nasarar dauko takobin Sarjis, inda ya fara da cewa "Ina so ku nutsu ku saurare ni da kyau, domin idan kuka mance abu guda daya daga cikin abubuwan da zan lissafa muku, tamkar kun hallaka ne. Kafin na sanar da ku dokoki bakwai na shiga jejin Kalkim, zan fara yi muku bayani akan jejin Kalkim da kuma maridi Magulus, halayyarsa da ta iyalansa.
"Shi dai jejin Kalkim ya kasance mai tsananin girma, tsayi da fadi, domin daga farkonsa zuwa karshensa tafiya ce ta kwana arba in bisa aljani Nargaz. A duk shekara maridi Magulus na haihuwar 'ya'ya dubu uku, saboda wannan dalili ne jejin ya cika ya batse da 'ya'yansa, ko ina ka duba su ne babu masakar tsinke. Tarihi ya nuna cewa fiye da shekaru dubu baya babu wani mahaluki da ya isa ya keta ta cikin wannan jeji, walau ta sama ko ta kasa ba tare da ya zama abincin Magulus da iyalansa ba. Kai sai da ta kai ta kawo cewa, Magulus da iyalansa su cinye gaba daya dabbobin da cikin dukkanin dazuzzukan da ke kewayensu, hatta kananan tsuntsaye ba su bari ba. Yayin da suka ga babu sauran namun daji, sai suka hau bishiyoyi da ci har suka karar da su. A halin yanzu ta kai cewa ba su da abinci face duwatsu da turbaya, don kada yunwa ta kashe su. Wani babban abin mamaki shi ne, ba su da ikon barin kewayen da suke, domin da zarar sun dara muhallin nasu, sai iskar wajen ta zame musu guba, duk wanda ya sheke ta, sai ka ga jikinsa na tsattsagewa yana rushewa tamkar mutum mutumin da a ka gina da yunbu. Ku yi sani cewa tsafi ko karfi baya tasiri akan wadannan maridai. Babu yadda za a yi ku shiga jejin Kalkim ba-ku fada hannunsu ba, amma ku sani cewa ba za su cinye ku ba farat daya. A duk inda suka kama ku, sai sun tafi da ku izuwa ga mahaifinsu Magulus. Da zarar sun kai ku, za a sanya ku cikin wani kejin ice mai tananin kwari da karfi a kulle. Za ku zauna a cikin kejin tsawon kwana uku, ba don komai za a ajiye ku na tsawon wannan lokaci ba, sai don jiran yajin da matar Mugulus za ta daka, wanda da shi ne Magulus zai yi amfani wajen cinye ku
Idian har ku na so ku kubuta daga haka, san k kayaye dokoki bakwai. Doka ta farko ita ce, kadia kan korsikra ku ce za ku yaki wadiannan maridkai. Doka ta buyu yangia da kou ka fada bammumsan koa da dayamku ya sake yum magama da Hanawansa. Haka kuma bawon kwama ukum dia za kau yi a cikin kejun ice, kar ka ci ko ku sha chuk abăm của sanka Barco maku, ko da kuwa kuma jim kamar yumwa dia Kirshirwa za sa kashe kan. Doka ta handin sta ce kadin ku jarraben alkoi dia tusalu Absa za biyar, duk sa adta misaridkam stalkka zo suma kallonka ku sunkui da kai kas kar ku dunga hadia idhamu dia sua. Album shoda shi nc, akwai wata bishiyar zimare agiye a kolfar god Magules, daf da india kejën da za a sa ku yake. Kullamad safe ku yi sajjada ga wannan bishaya tsacom Bamnuk Abu na karshe shi ne, ranar da za a fito da ku daga cik kejên nan don a cinye ku, kada ku yi gardamar fita. Da zama an zo giftawa da ku ta gaban bishiyar nan ta zinare, sai k daga kai sama ku dubi ganyayyakinta, ku na yum haka ganyayen za sa zuzzubo kasa ba adladi iyakar gaman m Da faruwar hakan, gaba dayan maridan man za stu kamme s zama gumaka, har uam masan Magalus da matarsa. To sannan ne za ku sammu damar shunga cikim gidam ma Magulus, don ku dauko takobin Sarjas. Kun shiga izumwa cik gidam kai tsaye ba dis jüm tsorom komai ba. Za ku iske faku dari uku a ciki wannam na bin wannan. Ku ratsa ta cikim
bar ka isa
daki ma karshe. A cikin wannam daki me za kua taran Kokumam kavunan bil adama birjak ba adadi. Wadfanma Kokuman kan me ma iyakar bill adaman da maridi Magulus ci a duniya. A jakin bangom gabas na dakin daga sama za
ga takobin Sarjis sakale a jikin wata kusa. Wannan takobi an yi ta ne da sassan kashin bil adama, tsawonta hai wuce katnu biyu ba, amma tana da matukar nauyi, imda za a tara motum dari sadaukai majiya karfi ba za su iya daukarta ba. Anuna idan kuka dauki kokon kai guda daga cikin kokunann kawunan bil adaman da ke dakin, kuka jefi takobi da shi, shike nan kun karya alkadarin nauyinta, kowa daga cikinku zai iya daukarta. Kuna daukar takobin sai ku hanzarta fita Jaga cikim gidan, ku yi ta tafiya da kafalunku ba tare da kun bugi gunki guda ba daga cikin gunkunan maridan har tyawon sa'a guda, sannan ku haye bisa kan aljani Nargaz ya tashi da ku sama, ku bar wannan jejin na Kalkim. Ku sani cewa idan ku ka yi kuskure kaka bugi gunki guda na maridan har ya fadi kasa, take za su tashi gaba daya su kama ku su dasa muku wawa, wapi ma ko figon jinin ba zai samu ba."
wind Sa'adda Boka Jinshan ya zo nan a zancensa, sai hankalin Yelisa ya tashi, ta dubi Jafar ta ce "Abokina, ka ji sofa irin hadarin da ke cikin jejin Kalkim, yaya zaka iya zuwa? B
Jafar yayi murmushi ya ce "Ai ko da hadarin ya linka haka sau goma ba zan sauva ra'ayina ba. Ya kai wannan boka ka sani cewa, na fito da shirina ba gudu ba ja da baya, kai na ke jira kawai. Ke kuma kawata, idan kin karaya da wannan tafiya, ki yi zamanki na hutassheki, amma mai miki alkawarin laltai zan dawo gare ki bayan na sami masarar fauko kubar Muftahul Zarbil."
Da jin wannan batu, sai Yelisa ta ji kamar an cire mata dukkanin tsoron wani abu da ke doron kasa, kawai sai
ta ce "Lallai maganganunka sun karamin kwarin guiwa. Babu makawa da ni za a vi wannan tafiya."
Tana gama fadın hakan ta juya ta dubi mahaifinta ta ce "Ya kai abbana, ga mu gareka sallame mu mu kama gabanmu.
Boka Jinshan ya bushe da dariya ya ce "Haka na ke so na ga yara da dakakkiyar zuciya irin ta manya, domin nan gaba ku zama ababan tsoro.
Nan take Jinshan ya kallawa aljani Nargaz kira sau uku, ya kuwa bayyana gabeninsu, ya risina cikin girmamawa ya kwashi gaisuwa.
Boka Jinshan ya dube shi ya ce "Yau ne ranar tafiyarku izuwa jejin Kalkim, ina so ka yiwa su Yelisa rakiya, duk sa'adda ka ga aljani Gulzum ya gaji sai ka dauko su gaba daya har shi ku ci gaba da tafiya. Ka sani cewa daga nan zawa jejin Kalkim tafi ce ta kwana goma sha bakwai amma idan kuka yi hanzari za ku iya isa cikin kwana tara Kamar yadda ka san dodokin shiga jejin Kalkim, su ma sun sani, don na sanar da su, haka kuma ina tunatar da ka umarnin nan da na ba ka lallai kar ka manta da shi."
Ko da jin wannan lafazi, sai Yelisa ta dubi mahaifinta cikin alamun rashin yarda ta ce "Ya abbana, wan umarni ne kuma ka baiwa Nargaz wanda mu ba mư sani ba?
Jinshan yayi murmushi ya ce "Wannan kuma wan abti ne wanda bai shafe ku ba. Ya ke 'yata don me za damu? Kin sani cewa har abada ba zan cutar da ku ba."
Yelisa ta gyada kai ba ta cewa komai ba. Nan tak Boka Jinshan yaiwa aljanun biyu izinin tashi. Cikin hanza Yelisa da Jafar suka dane bayan Gulzum, Kundin tsatsuba
makale a hammatar Jafar. Gulzum ya bude fukafukansa yai sama, Nargaz ya bi bayansa, suka ratsa ta cikin saman ginin fadar kamar yadda haske ke gauraye wuri, suka m
Bayan sun sami kamar rabin sa a suna tafiya a cikin gajimare, sai aljani Nargaz ya matsa kusa da aljani Gulzum wanda ka fauke da Jafar da Yelisa, ya dube shi ya ce "Kai Gulzum, ka san wani abu kuwa?utub
Gulzum ya ce "Ina fa? Sai ka fadi
"Tun sa'adda muka fara tafiyan nan nake jin kanshin dan uwanmu aljani a bayanmu, amma na waiga iya waige ban ga komai ba."
Gulzum ya ceAshe ba ni kadai ne na ji ba, kawai dai ka riga ni fadi ne. Lallai ina zargin cewa wani na biye da mu, yanzu mene ne abin yiwend
Caraf Jafar ya tari numfashinsu ya ce "To mene ne abin damuwa, don wani na biye da mu? Ko ma waye ai bai cika jarumi ba tunda har ya ji tsero ya boyo kansa, in ya isa ya fito fili mana. Kun ga ku kwantar da hankalinku, ko ma wane ne ya cĩ gaba da bin mu din, abin da na sani shi ne babu wanda ya isa ya raba mu da Kundin Tsatsuba ko kuma kubar Muftahul Zarbil idan har mun sami nasarar dauko ta."
Ba wani ba ne boyayyen aljanin da ke biye da su Jafar ba, face aljani Durfas wanda ke dauke da Gimbiya Sima tare da guntun wazirinta Kuddaru. Duk hirar da ke wakana tsakanin Jafar da abokan tafiyarsa, suna ji har ma al'amarin ya baiwa Gimbiya Sima dariya ta dubi Kuddaru ta ce "Ka ji kuri irin na yaron nan, wai har cewa yake ba a isa a raba shi da Kundin Tsatsuba ba. In ba don muna kan
umarnin Boka Sulbaini ba, ai da mun ganar da shi kuskurensa.
Kuddaru yayi murmushi ya ce "Ke dai rabu da shi, idan kare na yawo, zomo na yawo, wata ran za a hafu."
Duk da cewa su Kuddaru na daf da su Jafar, amma ba su ji wannan hirar ta su ba, saboda karfin sihirinsu. Lallaj tsafi kogi ne, idan mutum ya shige shi sai dai ya debo iya rabonsa ya bar saura. Haka dai tafiya ta ci gaba da wakana har tsawon kwana uku. A rana ta ukun ne da la'asar, Jafar ya dubi Yelisa ya ce "Ke kwawata, a gaskiya na gaji sosai ina da bukatar hutu."
Ko da jin haka sai Yelisa ta yiwa Gulzum umarnin sauka kasa. Nan take ya bi umarni, shi ma Nargaz ya bi shi a baya suka yi kasa. Al'amarin su Gimbiya Sima kuwa, ashe ita ma ta gama gajiya tilis. Ko da ta jin an ce a sauko kasa a huta, sai murna ta kama ta. Ba tare da bata lokaci ba shi ma aljani Durfas ya sauko kasa, ya dira bisa turba baya kadan da inda su Jafar suke.
Gimbiya Sima da Kuddaru suka sauka daga kan Durfas sannan ta dube shi ta ce "Za mu dan taka sawayenm don mu ji dadın jikinmu, lallai ka tsaya nan ka na lura da su Jafar, kada su shammace mu su tafi ba mu sani ba."
Durfasu ya ce "An gama ranki ya dade, amma fa ku kula da kanku sosai, don babu mamaki a samu mugayo aljanu ko dodanni a wannan jejin."
Sima tayi murmushi ta ce "Kar ka da mu zan iy kare mu daga sharrinsu."