Showing 12001 words to 15000 words out of 34797 words

Chapter 5 - ZUCIYA DA KWANJI BOOK 2 Writing by MAIMUNA IDRIS SANI BELI.pdf

wanda

zata iya kiransa fin karfin Abdullahi kawai da
iya
kirkinsa. ************ **********
*********** Tun
daga wannan ranar bakin fatima ya mutu, ta
daina kirkirar laifi domin ta bakanta masa. Ta
daina ja yana ja bare su yi tanki tanka, sai dai
ta
dauke masa walwalarta,ta rage kazarniya kamar
da,sai ya yi kwana biyu bai ji muryarta ba,
iyakaci ya yi kidansa ya yi rawarsa sai ta ga
dama ta kada masa kai, ko ta girgiza. Shi da
kansa ya dinga yabon da dan ta kan kula shi ko
da fada ne su yi, ya sami damar shigar da
kansa
da fada ne su yi, ya sami damar shigar da
kansa
da fada mata abin da ke cikin zuciyarsa,ko da
gwasalewa ne ta yi. Bayan wannan ta kara sakar
masa dawainiyar gida,ya yi hidimar waje,ya yi
ta
cikin gidanta,dauki ajiye ba zata yi ba, kai
wanke
wanken kansa sai ta daina sai ya ga haza ya
wanke, girki ma idan ba ta so ba sai ya yi abincin

ta nuna bai mata ba,dole ya canja mata wani.
Ga
kuma su sadiya da tasu matsin lambar ta tutiyar
shigarsa wajen fatima ranar girkinsu da
dawainiyar da yake mata ta jiki da aljihu,duk
da
su kansu albarkacin kaza kadangare na samun
damar shan ruwan kasko,amma da yake ba haka
aka so ba, wai kanin miji ya fi miji kyau,sai
hidimarsa ba ta burge su komai ma ya yi sai a
gwasale,ban da kanana maganganu suka dinga
yi
masa yajin tsakar gida da na daki, ke nan duk
inda ya dafa babu dadi. Amma da yake
soyayyarsa na kan sharafinta take tare da
fatima
sai ya zabi soyayarta da kyautata mata kawai ko
da ba zata mayar masa raddi ba, shi babban
tashin hankalinsa ma bai fice na lafiyar da ta yi
mata karanci ba tsawon watan ni biyu ke nan,
yau zazzabi,gobe ciwon kai,jibi na ciki, kullum
matsaloli sababbi. Ya yi kuma juyin duniya ya
kai
ta asibiti ta nuna masa ta yanke gita har ranar
mutuwarta. Ya san duk cikin muntukus din da

ta
ke masa ne wato ta kashe kanta ta bar masa
duniyar. Ko yanzu zai iya dorar da auren
kyakkyawar mace da dawainiyarta wadda ta
bambanta da sauran mata,sai dai bai debe
kauna
ba. Yana saka ran akwai nasara da zai girbi ribar
abin da ya shuka. Wata rana ya tashi da
zazzabi,hindatu na ta fama da dawainiyarsa
kasancewar a dakinta yake, amma shi
hankalinsa
na kan mai ciyar masa da fatima da yi mata
sauran hidimominta. Bayan ya karya da kyar ya
sha magani ya dan kwanta yana cike da fatan
idan ya farka ya dan ji ya ware ya je ya yi
hidimar fatima,amma fatansa bai ci ba sai ma
abin da ya karu. Cikin wannan magagin ya samo
shawara inda ya umarci hindatu kira masa
malam a wayarsa. Wayar na shiga ta mika masa,
bayan sun gaisa malam ya yi masa jaje saboda
ya ji canji a muryarsa,Abdullahi ya ce. "Malam
don Allah ka taimaka min ka ba mu aron
maryam
ta karasa mana hutun a nan, dan ta dinga
taimakon fatima da 'yan ayyukan gida saboda

ita
ma ba ta da lafiya,yanzu ma muka dawo asibiti
gaba daya. Malam ya ce da shi. "Assha! Me ya
same ta ita kuma?" Sai da abdullahi ya ja
fasali
sannan ya shara karya. "Faduwa ta yi a
abndaki
ta buge kafada". Malam ya jajanta sannan ya
ce". "Babu komai,ka yiwa maryam din waya ka
ce
ta taho in ji ni, dan ba na gida a halin
yanzu,kuma sai dare zan koma". Abdullahi ya
yi
godiya,suka yi sallama ya yi fuska ya kira
maryam ya ce mata. "Kin ga maryan kome kike
yanzu ki ajiye ki hado kayanki ki taho nan, na
tambaye malam ya ce na sanar miki,ki zo yanzu
don Allah akwai wata kafa da nake so ki toshe
min" Bai jira cewarta ba ya kashe wayar yana
jan
bargo dan ba ya son irin kallon da hindatu ke
masa. Ta gaji da kallonsa dole ta soke kishi da
bacin rai ta basar,ko awa daya maryam ba ta
hada ba ta karaso,yana jiyo sallamarta da
surutanta da su ya tashi zaune yana Allah Allah

ta shigo dan karya fita ya cika azarbabi. Can ya
ji shigowarta falonsa tare da su hindatu,ya
lallaba
ya fito falon,ya yi fuska ya zauna dan yasan
tsegumi da neman rigima ya kawo su sadiya,a
dai sami abin da za a yi masa korafi. Maryam na
gaishe shi tare da yi masa sannu, shi kuma
idonsa akan jakarta da ta janyo,ya ce. "Ki
sauka
wajen fatima,ba ta cika jin dadi ba ne. Ga shi
nima haka sai ki dinga taimakonta da wasu
abubuwan,ina tsammamnin yau ko karyawa ba
ta
yi ba. Tashi ki je". Da kuzarinta ta mike tana
bayyana jimami. "Allah ya sauwake,bari na
karasa". Ya koma ya kishingida yana fadin.
1 · Like · React · Report · May 16, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
.19) "Na gode maryam". Ya yi
murmushi,maryam na fita sadiya ta hau rafta
salati da innalillahi,ya yi kamar bai san tana yi
ba. Hindatu ta muskuta ta ce. "To wai me ya
hana ba ka zube mata barori ba?" Ya yi shiru
kamar ba zai tanka ba, sai kuma ya tanka din.

"Saboda ba bakuwar mallakar barorin ba ce, zai
fi
armashi idan ni na zama baranta". Sadiya zata
yi
magana Hindatu ta yi saurin tare ta dan san
zata
hargitsa musu gayyar,ta ce. "Kuma kamar babu
riba". Ya amsa ba tare da nuna damuwa ba. "Ke
ce kike ganin haka,tunda ba ke ya shafa ba.
Amma dai kin san idan babu kwadayi babu
dalilin
da zai sa a lashi wuta? To ki ji a ranki kokari ke
bude kofar da ke kulle". Kufulalliya sadiya ta
kasa
hadiyewa. "Babu wata riba wallahi, ita ta zo
bauta amma ita ake bautawa,to wai ita ta biya
sadakin ne ko kai?" Ita ma tana rufe baki ya
amsa mata. "Akwai riba mana tunda ba dan ta
yi
wahalhulun gida na aure ta ba. Abin da na
aureta
dominsa na samu, don haka babu ruwana da
biyan sadakinta. Bautar da nake mata idan
akwai
lada Allah ya ba ni....." "Idan kuma babu fa?"

Inji
Hindatu tana kallonsa,ya ce. "Allah ya sa ya
zama kaffara". Sadiya ta kara kufula, ta gyara
zama ta ce "Abu Turab kana zunguro
maganganu
fa. Dazu haka ka ce wai ita bakuwar barori ba
ce,to mu ne bakin barorin ke nan? Ko ba tasan
kai talaka ba ne ta aure ka? Ta sani akwai
dawainiya a gidan talaka,kuma tunda ba ita
kadai
ba ce a cikinsa ta sani tsab dole ta zage damtse
ta yi abin da sauran 'ya'yan talakawa suke yi.
Kai ma kuma tilas ka dai daita mu tunda
alfaharin mace shi ne gidan mijinta ba na
iyayenta ba". Ya kara yin fuska. "Idan ta san
ni
talaka ne ta aura,ina tsammanin na fi ta sanin
ba
ni da wadatar da zan samar mata jin dadin da
ta
saba da shi. Idan kuwa babu maganar shiga
hakki,na gamsar da kaina hikimata ta zabar
bauta mata da karfi KWANJI dan samar da
zaman
lafiya a tsakaninmu,kuma kar ta tsane ni

saboda
neman ta rasa,sai dai kawai idan akwai wadda
ta
haife ni a cikinku,sai kawai ta ladabtar da ni".
Sadiya ta mike saboda kai wa bango tana cewa.
"Kan na ka kawai ka gamsar,ita dai ihu bayan
hari kake a wajenta. Ga shi nan tana son kai ka
kabari da bakin ciki,dan ma ba ka da da balle
jika,bare ta mayar da shi maraya karfi da yaji.
Tana hanyar ficewa yana ba ta raddi. "Da bakin
ciki na ajali ai da fatima ba ta tarar da ragowar
ruhina ba,naki da tuni ya mayar da ni gawa".
Babu yadda ta iya dole ta fice din, sai Hindatu
ta
bari da 'yan kame kame. "Allah Abu Turab ka
mayar da hankalinka. Ba a taka ruwa a daki
ruwa. Matsayin sadiya da fatima daya a
wajenka,bai kamata ka dinga daga hakarkari a
kanta haka ba.... Ga shi kana ta faman
numfashi". Ya saki dogon tsaki, ya ce. "Kun
damu da lalurar tawa ne hindatu? Hassadarku
ta
fi ni kima a idonku,saboda haka duk wadda ta
ce
kulle zan ce cas! In yaso daga yanzu ta yanke

ciyar da ni tunda ita ta auro ni,ke kun fara
fitina
ta wallahi,kullum magana daya ake yi ta
yagwangwanata,kun hana kanku sukuni kun
hana
ni.... Kun koya min masifa,kun koya mata......
Ita
ma Hindatu da ta ga abin ba sauki,sai kawai ta
bar masa dakin. ****** ****** ******
******** Duk
da a bakin maryam fatima ta ji labarin
zazzabin
Abdullahi ta yi dabarar hadiye rashin
saninta,sai
dai dauko mata maryam din da ya yi, ya yi wani
tasiri a zuciyarta, har ta ji wani dan sanyi.
Zuwan
maryam din ya yi mata dadi,dan tana da tarin
bukata kamar na dauke kewa,da wata hidima
tata
ta musamman da ta shafi sirri. Dan haka ta
karbi
maryam hannu biyu fiye da zaton
mutum,maryam
kuma ta canji Abdullahi inda ta dinga yi mata

hidima kan jiki kan karfi kusan fiye ma da
Abdullahi tun da ita mace ce. Kwanaki ukun da
abdullahi ya yi yana jinya,kwana daya a dakin
Hindatu,biyu a girkin fatima sai suka zame
masa
wasu kamar na sallah,ya sami hutu kuma ya
sami kusanci da hira tsakaninsa da
fatima,domin
da ta karbi girki sai ya kwashi jinyar tasa ya
tare
a can dakinta,babu halin ta daure masa
fuska,kuma dole ta dinga yi masa sannu tana
nuna masa kulawa saboda idon maryam da ke
tare da su. Da dare ma dole suka kwana daki
duk
da ta takura kanta ne akan sofa. Kwanan
sadiya
daya da karbar girki ya dawo gida da yammaci
ya
ci karo da maryam zata shiga gida,sai ya ji babu
dadi a ransa,dan malam ba ya son fitar su
maryam kamar matan aure yake kullensu,to ina
ta je? Tana yi masa sannu da zuwa yana bata
fuska da tambayarta. "Ina kika je?" Ta daga
masa ledar da ke hannunta mai dauke da

tambarin wani pharmacy,ta ce. "Anty fatima ce
ta
aike ni". Ya bi. Leadar da kallo cikin rashin
fahimta,ya ce. "Kika siyo mata me?" Sai ta yi
dariya kawai tana cewa. "Oho! Rubuta min ta yi
na zaci ma magani ne". Da sauri ya mika hannu
ya karbi ledar ya zazzago abin ciki,sai
numfashinsa ya nemi daukewa,ya zare ido yana
kallon maryam,ya ce. "Me zata yi da pt-strip?"
Fuskar maryama ta bayyana tsoro saboda rikitar
da ta ganshi a ciki. Ta debo in ina tana cewa.
"Ni
.... Ni wallahi ... Ban sa.... Sani ba...... Ban ma
san na me ye ba". Zuciyarsa ta kara saurin
bugu,numfashinsa na son shakewa.da kyar ya
dake ya mika mata tare da murmushin karfin
hali,ya ce. "Ungo! Kai mata". Maryam ta wuce
sukuku shi kuma sai shiga gidan ma ya gagare
shi gaba daya,saboda fargabar yadda zai je wa
sadiya a rikice, kila wannan ya janyo su tashi
dan
karamin yaki saboda rudanin da zuciyarsa ke
ciki.
Fata! Fargaba! Sun hade masa waje daya kawai
sai ya shige cikin motarsa ya dinga fama da

rigimarsu. Sallar magriba ta tashe shi ya wuce
masallaci amsa kiran mahalicci tare da dokin kai
wancan fatan nasa gare shi. Sai karfe tara ya
nemi gida bayan ya sallaci sallar isha,dadewarsa
a wajen bai hana shi shiga gidan a birkice ba,
saboda tsannain kaunar hada ido da fatima da
ya
mamaye ransa,ba kuma hada idon kawai ba har
da kaunar sauke mata tambaya daya kacal
wadda a ma'auni ta fi dutse dala nauyi. "A
kawo
maka abinci?" Da tambayar da sadiya ta kori
shirun da ke tsakaninsu ke nan, bayan ta gama
cikarta da batsewa,shi kuma ya nuna halin
ko'inkula.to a nan ma sai aka kuma
kwatawa,domin girgiza mata kai ya yi alamar
kar
ta kawo,tunda bai ga amfanin tambayar ba.
Sadiya fa ta zo wuta iyaka! Ta hadiye wani
katon
kullin bakin ciki,ta ce. "To wai me yasa ba zaka
sallama ni gaba daya ba? Ka hada mata kawai
da
kwanakin nawa,sai ka bar ni gadin dakinka
kawai,tunda ba zan ce ka barni zaman 'ya'ya

ba". Ya share ta,fuskarsa a hade ya dauki
remote
ya latso tashar kallon kwallo,sannan ya ajiye
remote ya wuce fridge ya dauko fura ya
markada
abarsa cikin matsakaicin jug ya hado da kofi ya
dawo ya zauna ya fara sha hankali kwance
abinsa. Da ta kalle shi sai ranta ya kara mungun
baci,kamar ta mike ta rufe shi da duka,sai ta
zabga wani katon tsaki,ta ce. "Me ye amfanin
zama da makiyi don Allah? Na rantse maka
yadda kake jin ka tsane ni haka nake jin
tsanarka
dan dai kawai ba zan iya sakin kaina ba ne".
Nan
ma ya shanye ya ki tanka mata abin da dama
ya
dinga gudu ke nan,ga shi kuma bai tsira ba, ya
kasa gane wannan bala'in na sadiya wadda ke
neman so da masifa. Har ta karaci maganganun
cin fuskarta bai tanka mata ba, ta fice daga
falon
cikin fushi,shi kuma ta ba shi damar fita ya
tunkari dakin fatima da nufin yi mata
bankwana.ita ma da nata cin kashin ya yi

kwankwasawar duniya ta share shi, dan maryam
ta yi bacci, dole ya kwashi sassanyar gwiwa ya
doshi dakin Hindatu domin yi mata tata asubar
ta
garin. A ranar bai yi bacci kirki ba saboda tsabar
fata da fargaba.ya rasa inda zai aza tunaninsa
akan farin cikin cikin fatima ko kuma a farin
cikin
yadda cikin zai iya matsanta mata zama da shi,
ko kuma idan labarin bai kasance haka ba akan
bakin cikin yadda zata iya masa wasarere da
cikin?
2 · Like · React · Report · May 16, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 2
.20) Da ya rasa mafita sai ya zabi ta tashi kai
wa ubangiji kokensa na godiya tare da neman
dauki. $ da safe ma bai sami ganinta ba, ya
sami
shiga falon saboda maryam ta tashi har ta fara
hidimominta amma dakin uwar dakin a kulle.
Sai
ya share ya fice kawai dan ya lura da take
takenta idan ya matsa sai ta tsinka shi wajen
maryam. ******************************

******
************************************
'Innalillahi
wa inna ilaihi raji'un! Kawai fatima ke fada
tana
maimaitawa tana ja da baya da jikin jikin din
bayan ta yar da tsinken gwajin da sauri. Tana
bin
kayan gwajin da kallo tare da shafa cikinta
lokacin da ta ke ja da baya kamar su be cikin ta
ke son gudar musu ba wanda ke jikinta ba. Ta
runtse ido ta girgiza kai da karfi tana dokin
abin
da ya faru ya zama mafarki,amma hakan ba ta
samu ba sai cikin nata ne ya yi mata inkiya da
wani karamin motsi da bayar da shaida. Ta
sulale
cikin jiri zuwa kan mat shower ta zauna cikin
kuka da girgiza kai tana hadawa da
ambaton,"A'a,a'a insha'Allahu ba zai kasance
ba!" Fiye da rabin awa tana fama da kuka da
wannan sambatun,can ta mike da wani karfin
hali
kamar na dan daudun da ya kama kadangare
ta

kuma farke wata takardar ta canja tasa ta sake
wani gwajin.tana tsaye a kansa ba ta ko kifta
ido
har lokacin ya cika ta zare tsinken shi ma ta
shiga gadinsa fiye da mintuna biyar sannan ta
daga shi cikin bugun zuciya. Har yau ba ta canja
zani ba,yanzu ya fi dazu fitowa rangadadau ma
kamar ya san shakka ta ke, kawai sai ta kece da
kuka!..21)
Tun kafin biyar ta cika Abdullahi ya dawo gida a
hikimarsa ta neman dalilin da zai sami ganin
fatima,su kebe idan ma da hali ya tambaye ta
sakamakon da gwajin ya bayar. Har biyar da
Rabi
yana zaune a dakinsa sadiya ba ta leko shi ba
bare ya hutar da tata zuciyar har ya sami
damar
tafiya ganin fatima,ga shi kuma yana kyashin
binta ya rarrashe ta tunda bai ga laifin da ya yi
mata ba. A karshe kawai sai ya fada wanka ya
shirya ya zari mukullin mota ya nufi dakin
fatima.ya same ta da maryam suna cin tuwon
shinkafa miyar danyar kubewa kwano daya.
Suna
gaisawa shi kuma yana duban agogo,sannan ya

sauke ganinsa akan fatima wadda kallo daya ya
yi mata ya karanto damuwa a kwayar idonta,ya
ce. "Abincin dare kuke ci ko na rana?" Ta yi
murmushi yake ta kawar da kai,da haka kuma
ta
bar tambayar tasa ta bi ruwa, saboda
makoshinta
ya toshe da haushinsa ba ta ko kaunar bude ido
ta ganshi,sai maryam ce da ta ke zaton jikin da
fatima ke ji ne ya hana mata magana,ita ta
amsa
masa. "Na rana ne, Anti ta kasa cin komai sai
tuwo". Shi ma ya gyara zama a gabansu ya
watsa hannu a kwanon yana cewa. "To Anti
sannu,dama yanzu shigowa nayi mu je asibiti.
Daga nan sai mu mayar da maryam gida tunda
ni
na sami sauki". Sai da ta ji fasali, sannan ta
amsa. "Rashin son cin wani abinci sai wani, ai
ina tsammanin ba cuta ba ce,ra'ayi ne kawai
saboda haka ni ba zani wani asibiti na, maryam
kuma ban shirya ta tafi yau ba". "Ya kai lomar
tuwo uku kafin ya amsa mata ba tare da ya
dube
ta ba. "Na sani,ni 'yar burum burum ce ba na

so.... Sannan malam ba ya son su maryam su yi
nisa da gida, idan muna son gaba a bamu ita ai
dole mu mayar da ita akan kari,amma dai in
ranki
bai so hakan ba ki yi hakuri. Ya kare maganarsa
da tausasa murya dan son ya ragewa zuciyarta
dacin da ta ke ji. Suka yi tsit har suka gama cin
abincin maryam ta nemi wanda zai kara
Abdullahi
ya amsa zai kara,har fatima ta yi musu
shiru,sai
da maryam na dab da shiga kicin ta dan daga
murya. "Shi ma ya koshi dan kadan zaki. Zubo
masa. Sannan ta bishi da harara tana cewa.
"Ban
ga fa dalilin da zaka zo ka cinye min abinci ba,
alhalin ga naka can". Ya kura mata ido tare da
wayon kallon cikinta,dan haka ya kasa damuwa
da ma'anar kyarar da ta ke masa har ta fara
tsarguwa da salon kallon nasa,sai da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login