Showing 3001 words to 6000 words out of 59226 words
Chapter 2 - MAZAN JIYA Littafi 2 Na Abdulaziz Sani Madaki.txt
sai ya rike takobin da hannayensa biyu yana reto a sama kuma ya cigaba da kokarin zare takobin amma sai ya kasa.
A duk sa'adda ya girgiza takobin sai halittar ta kara kwarara ihu ta kawo masa cafka da mangari amma sai ya wurkila kafafunsa ya goce.
Shi kansa Dujalu ya yi mamakin yadda ya kasa zare takobin duk da cewa gaba dayan nauyinsa a kanta yake.
Daga can sai Dujalu ya yi amfani da dukkan karfinsa ya finciko takobin ya zarota daga cikin hancin halittar. Takobin na zarewa sai ga jini na shatata tamkar teku ta balle.
Dujalu ya rikito izuwa kasa, itama halittar sai ta taho kasa a sandare. Dujalu da halittar suka taba turba a lokaci guda. Kafin Dujalu ya goce wuyan halittar ya fadi a tsakiyar cikinsa, amma sai ya yi gwafa bai taba jikinsa ba, amma ya rufeshi yadda ba zai iya fitar da kansa ba.
Halittar dai ko motsi bata sake yi ba, domin
ta zama gawa. Har a sannan kuma jini na malala
daga cikinta yana kwarara a dajin, tamkar ruwan
samansa ake yi. Dujalu dai bai san sa'adda ya
bushe da dariyar farin ciki ba, bisa ganin wannan
gagarumar nasara da ya samu ta hallaka halittar,
amma da ya dago kai ya dubi wuyan halittar
wanda yai gwafa a kansa ya tokareshi sai
hankalinsa ya yi mummunan tashi domin bai san
yadda zai iya ture gawar haittar ba ya fito, saboda
jikin halittar ba zai saruba da takobi bare ya
sareshi.
Dujalu na cikin wannan tunani ne ya hango
yar uwarsa Hursiya ta rugo gareshi da gudu ita kadai tana murmushin farin ciki. A sannan ne
kuma aljani Rauzuf ya farka daga dogon suman da
ya yi, ba zato kuma sai ga sauran dakaru suna
fitowa da dai-dai daga wuraren da suka buya sunaa
rugowa wajen Dujalu suna ihu bayan hari.
Duk wanda yazo ya ga wannan katuwar
halitta kwance a kas a mace sai ya cika da
tsananin mamaki. Nan fa dakaru suka kama fashewa
da murna suna yiwa Dujalu jinjina. Duk wannan
abu da ke faruwa zuciyar Dujalu tafarfasa take
kamar za ta fone saboda tashin hankalin da yake
ciki na ganin kansa a karkashin gawar halittar bisa
sanin cewa ba zai iya fitowa ba. Daga can sai
Hursiya ta lura da fuskar Dujahu ta fahimci cewa
lallai a cikin tsananin damuwa yake. Cikin firgici
Hursiya ta dubeshi ta ce, "Ya kai dan uwana ina
dalilin wannan matsanaiciyar damuwa a gareka?".
Koda jin wannan tambaya sai sarki Dujalu
yai ajiyar zuciya cikin karaya ya ce, "Ya ke 'yar
uwata kiyi sani cewa wannan murna da kuke yi
bisa samun nasarata dai-dai take da farin ciki da
zuwan mutuwata. Ki dubi yadda na kasance a
karkashin gawar wannan halitta, yenzu ta ya ya za
ku iya zaroni daga karkashinta, shin a cikinku
Wane ya yi tunanin wannan hali da na ke ciki?"
Sa'adda Hursiya taji wannan tambaya sai ta
dubi gawar halittar da kyau ta ga yadda ta rufe Dujalu ruf babu wata karamar kofa da za a iya
zareshi. Nan take hankalinta ya dugunzuma ainun
ta rasa abin da ke ma ta dadi a duniya, don haka
sai ta mike tsaye ta dubi gaba dayan dakarun da ke
wajen mutane da aljanu ta daka musu tsawa. Gaba
dayan dajin yai tsit! Kowa ya zuba ma ta idanu. A
sannan ne hawaye ya zubo daga idanun Hursiya ta
budi baki ta ce, "Ashe gaba dayanku nan taron
banza ne taron wofi? Ku dubi halin da sarkinku ke
ciki, ashe dayanku ba zai yi tunanin hanyar da za a
bi a zaroshi ba daga karkashin gawar wannan
halitta ba?".
Koda jin wannan batu sai kowa yai tsuru-
tsuru ya shiga taitayinsa aka marmatso ana nazarin
yadda za a yi a janye gawar katuwar halittar daga
kan sarki Dujalu. Nan fa aka shiga yin
shawarwari. Wasu zaratan jaruman yaki guda uku,
wadanda babu kamarsu a cikin dakarun suka ware
gefe.
Zan ci gaba.
MAZAN JIYA
Littafi na biyu 2
Part B
Na Abdulaziz Sani m gini
Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey
Daya daga cikin wadannan zaratan jarumai aljani
sunansa Karbazu, a gaba dayan dakarun
aljanun da ke wajen babu sadauki kamarsa, kuma
ma'abocin hikima ne da sanin dabarun yaki
daya
kuwa mutum ne,
sunansa Barsuma. Barsuma shi ne sarkin yakin birnin
Hawaru din. Shima ya kasance gagarumin
sadauki kuma gwarzon mayaki a cikin jinsin
bil'adama wadanda babu kamarsu a gaba dayan
nahiyar. Shima ya kware matuka a sanin makama
da dabarun samun nasara a yaki.
Mutum na uku wani tsohon sadauki ne
wanda shekarunsa sun haura casa'in amma har
gobe yana dakawa matasa gumba a hannu wanda
ake kira da suna Shurkaib bin Dallas.
Lokacin da Kurbazu, Barsuma da Shukaib
suka ware gefe daya domin su yi shawara bisa
dabarar daza a yi a sami nasarar zaro sarki Dujalu
daga karkashin gawar halittar sai Karbuza ya dubi
Barsuma da Shurkaib ya ce,"Yanzu ku mene ne
shawararku, ta ya ya kuke ganin za mu iya zaro
sarki ba tare da lafiyarsa ta tabu ba?
Abu na farko dai, janye gawar wannan halitta
daga kansa ba karamin aiki bane, saboda girmanta
da nauyinta. Idan gaba dayanmu zamu taru ba
zamu iya ture ta ba da karfin tsiya. Idan muka ce
zamu zauna anan muna kula da sarki har izuwa
lokacin da halittar za ta rube mu sassareta to
tabbas warinta ma zai iya zama ajalinmu gaba
daya. Yanzu sai ku fadi shawarwarinku kafin na
fadi tawa ku ji mu zabi wadda za ta fi inganci"
Koda jin wannan batu sai tsoho Shurkaib ya
yi murmushi ya ce, "Ni ba zan fadi tawa dabarar
ba sai naji taku, kuma zan fadi tawa dabarar ne bayan an jarraba taku ba a sami nasara ba, kuma
bisa sharadi guda".
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama
Karzuba da Barsuma. Barsuma ya ce, "Ya kai
Shurkaib ka shiga taitayinka fa ka san abin da
kake fadi. Yanzu har ka isa ka sanya wani sharadi
don ceton rayuwar sarki? Baka tsoron cewa idan
dabararmu ta yi nasara sarki ya kubuta fishinsa zai
iya tabbata akanka?".
Koda jin wannan batu sai Shurkaib ya bushe
da dariya, sannan ya ce, "Ku a tunaninku ni ina
tsoron mutuwa ne? Ku tuna cewa shekaruna sun
haura casa'in a duniya, na haifi ya'ya, ya'yanma
sun haihu, nayi yake-yake da dama ba adadi.
Babu irin masifar da ban gani ba a duniya, kuma
babu wani buri da ban cika ba face guda daya,
kuma yanzu ne na samu damar da zan cika wannan
buri nawa bisa wannan uzuri da ke gabanmu. Inaa
tabbatar muku da cewa duk dabarar da za ku kawo
domin a kubutar da rayuwar sarki ba za a yi nasara
ba. Tawa dabarar ce kadai za a bi a samu nasara.
Yanzu na baku dama ku fara gabatar da taku
dabarar idan ba a dace ba sai na fadi tawa, idan
har sarki ya amince da sharadina".
Sa'adda Karbuza da Barsuma suka ji wannan batu,
sai suka fara cika da mamakin Shurkaib suka
tabbatar da cewa da gaske yake.
Karbuza ya ce, "Shi ke nan ai yanzu sai ka zo
mu je wajen sarki domin mu gaggauta yin abin da
ya kamata mu yi domin bata lokacinmuu cikin
wannan daji tamkar baiwa abokan gaba dama ne
su rigamu zuwa inda takobin Saiful Lujara take."
Koda jin haka sai Basuma da Shurkaib suka
ce a cikin hadin baki, "Zancenka dutse ne".
Nan take su ukun suka dawo inda sarki
Dujalu ke kwance a karkashin gawar wannan
halitta. Duk su ukun suka durkusa a gabansa.
A wannan lokaci Hursiya ta tallafo kan sarki
Dujalu ta dura masa ruwa a baki. ya sha. Gama
shan ruwan nasa ke da wuya ya yi arba da su
Karbuza tsugunne a gabansa sai ya
fusata ya ce, "Me kuke jirane har yanzu baku yi
tunanin dabarar da za ku yi ba ta ceto rayuwata?"
Kurbazu ya numfasa ya ce, "Ya shugabana ai
abin da muka je muka tattauna ke nan, kuma
kowannenmu yana da tasa dabarar dabam. Zamu
fara jarraba tawa dabarar, in yaso a jarraba ta
Barmusa, idan tawa ba tai nasara ba, idan shima
tasa bata yi ba sai a jarraba dabarar Shurkaib."
Sarki Dujalu ya ce, "Na umarceku da ku
aikata hakan cikin gaggawa domin idan muka kara
kwana hudu anan cikin wannan daji rundunar Su
sarki
Maharaz za ta zo ta riskemu. Ni kuwa a
shirina shi ne mu rigasu zuwa tekun bahar Sufiya ya zamana cewa kafin su isa tuni mun danko
takobin Saiful Lujara."
Karbuza ya dubi dukkanin dakarun aljanun
da ke wajen ya ce, "Na umarceku da ku ruga
izuwa cikin wannan daji ku tsunko murtuka
murtukan jijiyoyin bishiyoyi dogaye ku zo da su
yanzu.
Kafin Karbuza ya gama rufe bakinsa tuni
gabe dayan dakarun aljanun sun bace bat! Kafin
cikar dakika sittin sai gasu sun dawo dauke da
dogayen jijiyoyin murtuka-murtukan bishiyoyi
masu yawan gaske tamkar za su yiwa dajin gaba
daya rufi da su. Ba tare da bata lokaci ba Karbuza
ya umarcesu da su kukkulla jijiyoyin wasu jikin wasu. Nan da nan aka samar da dogayen igiyoyi
na jjiya barkatai. Karbuza ya saké bada umarnin a
daura jijiyoyin a jikin gawar katuwar halittar.
Kowacce doguwar jijiya daya aka sa kartin aljanu
majiya karfi guda dubu suka riketa. A kalla an
sami sama da aljanu miliyan daya. nan take aka
basu umarni da su ja igiyar sama a lokaci guda,
domin su daga gawar sama daga kan sarki Dujalu
domin sami damar zareshi. Aljanun gaba
dayansu suka tattaro karfin daratsensu suna jan
jijiyoyin a lokaci guda.
Maimakon gawar halittar ta rabu da kasa, sai
gaba dayan jijiyoyinPartFaka daura a jikinta suka tsittsinke, aljanun suka fado kasa gaba dayansu
Al'amarin da ya baiwa kowa mamaki ke nan a
wajen, kuma hankalisu ya dugunzuma.
Sarki Dujalu ya juyo da wuyansa da kyar ya
dubi Barsuma cikin alamun karayar zuciya ya ce,
"Ya kai Barsuma babban gwarzo, NAMIJIN
DUNIYA, mai dakawa maza gumba a hannu, ka
ga yadda dabarar Karbuza ta kare, kai kuma wacce
dabara ke gareka?"
Barsuma yai gyaran murya sannan ya ce,
Ina son aje a nemo mini giwaye adadin ninkin
wannan aljanu sau dari. Ma'ana kowanne aljani
guda giwa dari ce za ta wakilceshi, sanann a nemo
mini dogayen sarkoki murtuka-murtuka na karfe a
daura a jikin gawar wannan halitta sannan a daura
a jikin giwayen domin su ja sarkar su janye
gawar".
Koda jin hake sai dakarun miliyan dubu daga
cikin aljanun sulka 6ace bat a lokaci guda. Kafin
kiftawar ido sai gasu sun dawo tare da wadannan
giwaye da sarkokin karfe. Kamar yadda Barmusa
ya bada umarni haka aka yi, amma koda giwayen
suka yunkura suka ja sarkokin karfen, sai
sarkokin suka tsittsinike saboda tsananin nauyin
katuwar halittar sai gani aka y giwayen na
faduwa wasu na danne wasu.
Nan fa hankali ya kara dugunzuma fiye da ko
a yaushe, zuciyar sarki Dujalu ta kara karaya ya
fitar da rai ga cikar burin rayuwarsa ya fara tunanin
cewa tabbas ajalinsa ya gabato.
Duk da sanin hakan sai ya yi ta maza ya dubi
Shurkaib ya ce, "Ya kai tsoho mai dabara, ya kai
tudu mai nisan da yaro ba zai hango ba. Ya kai
masanin jiya, kuma masanin gobe, ka ga yadda
dabarun yan uwanka suka kasan ce. Ka sani cewa
karfin tsafina da karfin damtsena ba za su ceceni
ba daga cikin wannan hali da na shiga ba, wacce
dabara ce da kai wadda in dai aka yi ta zan tsira da
rayuwata? Na yi maka alkawari idan har ka ceci
rayuwata duk abin da kake bukata zan baka shi in
dai akwai shi anan duniya domin rayuwata ta fishi
daraja a idanuna".
Sa'adda tsoho Shurkaib yaji wannan batu na
sarki Dujalu sai ya cika da tsananin farin ciki bai
san sa'adda ya saki murmushi ba sannan ya dubi
Dujalu cikin nutsuwa ya ce, "Ya shugabana idan
na fadi dabarata ba a cimma nasara ba na yarda
kasa a kasheni a take a wannan wuri. To amma ka
sani cewa ba zan fadi dabarata ba face ka dada
jaddada alkawarin da ka furta yanzu kuma ka
rubutashi a rubuce tare da sa a buga hatiminka".
Koda jin haka sai sarki Dujalu ya girgiza kai
yana mai nuna alamar cewa ya aminta da hakan.
Nan take ya sa aka kawo masa tauwada da
alkalami gami da fatan rubutu. Har ya dangwalo
tawada zai yi rubutun bisa fatar sai Hursiya ta yi
sauri ta rike hannunsa a lokacin da hawaye ke
zuba daga idanunta ta ce, "Haba ya dan uwana ina
amfanin rayuwa idan buri bai cika ba? Yanzu idan
Shurkaib ya ce abin da muka fito nema ya ke so fa".
Koda jin haka sai kowa da ke wajen yai
tsuru-tsuru har shi kansa sariki Dujalu kuwa. Shi
kuwa tsoho Shurkaib sai ya yi murmushi ya ce
"Ko kadan bani da muradin kayan yakin MAZAN JIYA"
Da jin hake sai sarki Dujalu yai mumushi,
nan take ya yi rubutun yarjejeniya cewa ya amince
duk abin da Shurkaib ya furta yana so zi bashi
bayan dabararsa ta cimma ga ci.
Bayan ya gama rabutawar ne aka kawo
hatimi ya buga, kuma ya mikawa Shurkaib bada
shakkar komaiba. Shurkaib ya karbi fatar
yarjejeniyar ya sanyata cikin aljihunsa sannan ya
dubi gaba dayan aljanun da ke wajen ya ce,"A
cikinku wane ne mafi sanin sirrin hakan kasa?",
Koda jin haka sai wani tsamurmurin aljani ya
daga hannu ya ce, "Yau shekarata dubu saba'in ina sh
akin hakan kabari a garinmu" Shurkaib ya dubeshi yai murmushi ya ce,
"Matso nan kusa da inda sarki yake. Ina son ka
haka rami karami dai-dai fadin gangar jikin sarki
a farkashinsa yadda zai fada cikin ramin ba tare
da kasa ta zabtare ba gawar wannan katuwar
halitta ta sake danne shi ba".
Nan take kuwa wannan aljani ya bi wannan
umarni ya kama aikinsa. Ko sa'a daya bata cika ba
sai ya kammala aka ga sarki ya fado cikin ramin
daga karkashin katuwar gawar halittar. Cikin
matukar zafin nama akayi sauri ake zare sarki
Dujalu daga cikin ramin. Ai kuwa ana gama
zareshi ke nan sai kasar wajen ta rusa saboda
nauyin gawar halittar, gawar ta lume a cikin
ramin, dajin gaba daya ya kama girgiza saboda
gawar halittar, ta ci gaba da nutsewa izuwa cikin
karkashin kasa. Ba shiri kowa da kowa ya kama
gudu. Sai da aka yi gudu na sa'a shida sannan aka
isa inda kasa bata girgiza sannan aka tsaya ana
haki.
Daga inda aka tsaitsaya ana iya hango yadda
komai na wancana dajin ya nutse izawa cikin
farkashin asa ya zamans cewa ba sauran
bishiyoyi da duwatsu wadanda ake iya hangowa.
A wannan lokaci ne kowa hankalinsa ya
dawo jikinsa. Bayan an nutsu sai sarki Dujalu ya
tako da kafafunsa yazo gaban Shurkaib ya tsaya
daf da shi yadda har suna iya jin numfashin
junansu. Sarki Dujalu ya dubeshi cikin murmushi
ya ce, "Yanzu sai ka fadi muradinka naji domin na
cika alkawarina".
Koda jin haka sai kowa ya yi tsit! Dajin gaba
daya yai shiru tamkar mutuwa ta gifta, kamar
suma sauran halittun da ke dajin sun yi shiru suna
sauraron munafunci.
Tsoho Shurkaib yai gyaran murya ya ce, "Ba
wani abu nake so ka bani ba face auren yar
uwarka gimbiya Hursiya, kuma ba nine mijinta ba,
dana za ka aurawa".
Koda sarki Dujalu yaji wamnan batu sai gaba
dayan jiikinsa ya kama karikarwa saboda tsananin
bakin ciki, zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar za ta
kone. Nan nan Dujalu yaji nadama tazo masa bisa
alkawarin da ya dauka, saboda wasu babban siri
da ya 6oye a cikin zuciyarsa wanda duk duniya
babu wanda ya sanshi face shi kadai. Inda sarki
Dujalu ya san cewa abinda Shurkaib zai bukata ke
nan da ya zabi a barshi a cikin halin da yake ciki
ya rasa rayuwarsa, burinsa ya rushe in yaso
gimbiya Hursiya ta koma gida ta ci gaba da
sarauta.
Kawai sai aka ga idanun sarki Dujalu sun
kada sun yi jawur tamkar an gasa danbuda a wuta.
Cikin sanyin jiki ya sunkui da kansa kas ya ce,Lallai zan zamo mai cika alkawari a gareka bayan mun samo abin da muka fito nema"
Koda gama fadin haka sai sarki Dujalu ya
tafi izuwa gaban wata korama ya zauna ya kurawa
ruwan koramar idanu yana zubda hawaye.
Ya yin da Hursiya ta ga hakan sai itama ta
nufi inda yake. Koda sarki Dujalu ya waigo ya ga
ita ce ke tahowa gareshi sai yai sauri ya goge
hawayensa.
Hursiya tazo ta zauna daf da shi sannan ta
dubeshi cikin murmushi ta ce, ya kai dan uwana
ina dalilin da yasa na ka ga shiga cikin halin
damuwa bisa jin bukatar tsoho Shurkaib? Shin
baka son na auri dansa ne saboda bai kasance
jininmu ba?".
Lokacin da sarki Dujalu yaji wannan
tambaya sai ya dubeta ya maida mata da martanin
murmushin cikin yake sanann ya ce, Ya ke 'yar
uwata kiyi sani cewa bukatar Shurkaib tazo mini
da shammace, ban taba tsammanin cewa kece
muradinsa ba ga dansa. Ki tuna cewa a tarihin
zuri'armu babu wani jininmu da ya taba auren
bare, yanzu gashi Shurkaib zai karya mana
wannan tarihi. Bugu da Kari, ina bakin ciki ace
ranar da babu ni, mulkinmu da dukiyarmu da duk
wannan daukaka da nake nema mana a yanzu Za ta
koma wajen zuri'ar tsoho Shurkaib, domin idan
kika auri dansa tamkar hakan ta tabbatu ne."
Lokacin da Dujalu yazo nan a zancensa sai tausayinsa ya kama
Hursiya ta rungumeshi ta fashe da kuka. Shi kuwa sai ya cika
da tsananin farin ciki a cikin zuciyarsa. Hakika rashin sani yagi
dare duhu. Inda Hursiyya ta san sirrin da sarki Dujalu ya boye
ma ta da taji ta tsaneshi fiye da yadda ta tsani mutuwarta Haka
dai Hursiya da sarki Dujalu suka ci gaba da hira a nan bakin
koramar har izuwa lokaci mai dan tsawo.
Da fatan an tashi lafiya, sannan duk wanda yake son complete zai iya tuntubata ta wannan number 08138873799 kira ko whatsapp.
MAZAN JIYA
Littafi na biyu 2
Part C
Na Abdulaziz Sani m gini
Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey
Daga can sai Hursiya ta dago kai ta dubeshi ta ce, "Ya ki ?an
uwana kayi sani cewa zuciyata ta kasa samun sukuni saboda
rashin jin ci gaban labarin sadauki Hantaru. Lallai ina son naji
yadda karshen rayuwarsa ta kasance". Sa'adda sarki Dujalu yaji
wannan batu sai ya yi mrumushi sannan ya ce, "Ya ke yar uwata
dama na san cewa kina cikin kaguwa bisa son jin ci gaban
wannan labari, saboda haka Zan yi iyakar kofarina na kammala
miki wannan labari kafin wayewar gari, domin so nake gobe da
sassafe mu ci gaba da tafiya domin mu isa tekun bahar Sufiya
akan lokaci, kafn su sarki Maharaz su zo su riskemu".
Ya yin da Hursiya tajii wannan batu, sai ta cika da farin ciki ta
nutsu tana mai kurawa sarki Dujalu idanu, shi kuwa sai ya yi
gyarsn murya ya cigaba da ba ta labari kamar haka.
Lokacin da hantaru ya zama katon dutse wannan jibgegegiyar
Micijiyar ta hadiyesthi, sai macijiyar ta shiga cikin wani irin
mugun hali domin dutsen ya zame ma ta masifa a cikin cikinta,
yai ma ta nauyi, ya ZAmana cewa da kyar ta ke iya motsawa.
Koda taji dutsen na damunta sai ta fara kokarin ta sake yin
amansa waje da karfin taiya. Idan ta turo dutsen izuwa
makogwaronta sai dutsen ya koma da baya, wato ya ki yarda ya
ito. Nan fa Macijiyar ta kama tumuwa da kasa, tana dukan
kowacce kusurwa ta kogon da kawunanta, al'amarin da ya sa
gaba dayan kogon ya ragurguje ke nan ya kama girgiza. A duk
sa'adda micijiyar ta tumu da kasa sai dutsen cikin cikin nata yaji
kamar zai tarwatse don haka bisa dole dutsen ya taho da kansa
izuwa makogwaronta.
Koda jin hakan sai Macijiyar ta wangame bakinta wanda dutsen
ke ciki, sannan ta sake wangame wani bakin dabam ta sokashi
a cikin wancan domin ta zaro dutsen. Koda dutsen ya ga haka
sai ya rikide ya zama wuta. Ai kuwa Macijiyar na hadiye dutsen
wutar sai tayi bindiga ta tarwatse, sassan jiikinta ya yi flla-flla a
kasa tamkar an yankashi gutsun- gutsun, sai ga dutsen wutar
ya gangara Can gefe daya.
Nan take dutsen ya rikida ya zama sadauki Hantaru