Showing 9001 words to 12000 words out of 59226 words
Chapter 4 - MAZAN JIYA Littafi 2 Na Abdulaziz Sani Madaki.txt
duk sa'adda ya waigo yayi arba da dabbobin sai yaji zuciyarsa ta karaya domin ya san cewa akwai iyakar lokacin da zai iye jure wannan gudu, don haka idan ya gaji dabbobin za su bankeshi sai abin da hali ya yi.
Komai jarumtakar mutum da juriyarsa idan ya ga yadda wadannan dabbobi suka tuso Hantaru a gaba dole ne zuciyarsa ta karaya domin ya san cewa idan ma zai tsaya ya ci gaba da yakarsu ba zai iya karar da su ba a cikin kwana bakwai saboda yawansu. Sai da Hantaru ya shafe sa'a bakwai yana gudu a cikin daji, wadannan mugayen dabbobin na biye da shi babu daga kafa.
Sa'a bakwai na cika ne suka iso cikin wani irin daji mai yawan surkukiya da duhuwoyi gami da kayoyi masu tsini. Bisa mamaki sai Hantaru yaji kayoyin na huda jikinsa har jini na tsartuwa. Alamarin da ya janyo ya fara layi da tangadi ke nan. Amma saboda naci da juriya bai fasa gudun ba su kuwa dabbobin da?a matsawa suke ta cikin kayoyin tamkar suna hawa kan kalmami jikinsu ko kwarzAnewa baya yi.
Sannu a hankali Hantaru ya fara gani dishi- dishi sakamakon jinin da ke zuba a jikinsa mai yawa ya zamana cewa yana gudu ne kawai amma baya ganin abin da ke gabansa. Kwatsam! Sai yai karo da ka da wata katuwar bishiya tamkar fyadashi aka yi a jikinta. Nan take jini yai fitar burgu daga cikin bakinsa de hancinsa ya fado da baya a sume ya baje a kas. Takobin Saiful Lujara ta subuce daga hannunsa ta fadi gefe daya.
A dai-dai wannan lokaci ne wadannan miyagun dabbobin suka iso kansa suka yi masa kawanya suna shirin yuyyagashi. Daya daga cikin dabbobin wani murgujejen tsohon Zaki sai ya yi girgiza ya rikide ya zama wani tsohon aljani wanda shekarunsa sun haura dubu ashirin. Kawai sai ya nufi inda takobin Saiful Lujara take da nufin ya dauka. Kwatsam! Ba zato ba tsammani, sai ga wata irin guguwa mai karfin tsiya ta baiyana ta tarwatsa gaba dayan wadannan dabbobi tayi jifa da su can nesa har shi kansa wannan tsohon aljani mai shirin ?aukar takobin Saiful Lujara.
Kafin dabbobin sU Sake rugowa da gudu inda Hantaru yake kwan ce a sume, tuni guguwar ta ?auke Hantaru da takobin Saiful Lujara tayi sama da su ta luluka a cikin gajimare ta 6ace bat tamkar basu taba wanzuwa ba a saman. Kawai sai wanann aljani da dabbobin suka tsaitsaya cak suka daga kawunansu sama suna kallon dai-dai wajen da guguwar ya kule da Hantaru. Daga can kuma sai suma suka 6ace 6at.
Lokacin da Hantaru ya farfado daga dogon suman da ya yi, sai ya tsinci kansa a cikin wani kasaitaccen ?aki kwance akan wani luntsumemen gado mai taushin gaake.
Komai na cikin dakin an yi shi ne da zinare, don haka gaba dayan dakin sheki da walwali yake.
Abu na farko da Hantaru ya fara arba da shi shi ne, takobin Saiful Lajara jingine a jilkin bango bisa wani ma'ajiyi. Koda ganin takobin sai Hantaru ya saki murmushin murna ya mike zaune sanann ya zuro kafafunsa kasa daga kan gadon ya nufi inda take yana tafiya da kyar a lokacin da yaji gaba dayan jikinsa ya yi tsami.
Saura kiris! Hannnunsa ya kai kan takobin sai ya dubi wani madubi da ke kusa da takobin. Nan take ya ga ashe gaba dayan fuskarsa a kumbure take ba kyan gani, kuma tayi kaca-kaca da rauni sakamakon muguwar buguwar da ya yi da bishiya, musamman idanunsa sun yi luhu-huhu da kyarma yake iya budesu. Koda Hantaru ya ga yadda fuskarsa ta baci, sai takaici ya kamashi, amma da ya tuno gimbiya Larziya sai farin ciki ya cika zuciyarsa bisa ganin cewa ya sami nasarar dauko takobin Saiful Lujars, da zarar ya koma birnin Darul Habur sai dai a...
Koda Hantaru ya ga yadda fuskarsa ta baci, sai takaici ya kamashi, amma da ya tuno gimbiya Larziya sai farin ciki ya cika zuciyarsa bisa ganin cewa ya sami nasarar dauko takobin Saiful Lujars, da zarar ya koma birnin Darul Habur sai dai a daura aurensa da gimbiya Larziya.
Cikin hanzari Hantaru ya dauki takobin Saiful Lujara ya nufi kofar fita daga dakin, kawai Sai ya ga wata tsaleleliyar budurwa ta baiyana a gabansa fuskarta cike da murmushi.
Cikin tsananin mamaki da firgici Hantaru yaja da baya yana kallonta ya ce, "Mutum ko aljan?".
Ba komai ne yasa Hantaru ya yi ma ta WannAn tambaya ba face ganin tsananin kyawunta wanda ya ninka na gimbiya Lariya sau uku.
Budurwar tayi murmushi wanda ya kara baiyana kyawunta karara har Hantaru ya kara dimancewa sannan kuma sai ta murtuke fuska ta dubeshi ta ce,
"Haba gwarzon shekara wane irin sauri kake yi haka? Shin baka ga yadda fuskarka take bane har kake tunanin komawa birnin Darul Habur cikin wannan sifa? Yaya masoyiyarka gimbiya Larziya za ta kasance idan ta ganka a cikin wannan siffa? Bai zamo dole ba ma ta shaidaka ba, kamanninka gaba daya sun sauya. Ka sani cewa jikinka a cike yake da raunika da kuma taruwar jini, idan ka ce za ka cigaba da tafiya a haka wa?annan mugayen dabbobin na kogon da takobin Saifal Lujara take za su sake binka su rabaka da takobin, kuma su hallaka ka, kaga kenan kayi biyu babu, babu ranka, kuma babu takobin, duk wahalar da ka sha a baya ta zama ta banza.' Burin dangin mahaifiyarka na cin gasa bai cika ba, kaima burinka na auren gimbiya Larziya ya rushe, bare kuma har ka koma birnin Kisra ka sadu da mahaifnka sarki Kusaidu wanda kullum dare da rana a cikin begenka yake."
Sa'adda kyakkyawar budurwar tazo dai-dai nan a jawabinta sai Hantaru ya cika da tsananin mamaki ya kura mata idanu kawai yana mai kara kankame takobin Saiful Lujara a kirjinsa. Sannan ya ce,ya ce, *Ya ke wannan kyakkyawa, wace ce ke, kuma me yasa
kika ceto rayuwata daga hannun wadannan dabbobi na kogon
da wannan takobi take ciki kika kawoni nan?".
Koda jin wadannan tambayoyi sai buduwar tayi ajiyar zuciya
sannan ta ce, "A gaskiya ba zan iya gaya maka amsar
wadannan tambayoyi ba a yanzu, sai bayan ka sami lafiyar
jikinka gaba daya, wato ranar da zamu yi bankwana ka tafi
izuwa birmin Darul Mahabul.
Wata kila daga Wannan rana ba zamu sake saduwa ba, wata
kila kuma daga wannan rana ba zamu sake rabuwa ba".
Hantaru yai shiru a karo na biyu yana nazarin abin da ta fadi.
Amma bai fahimci komai ba, kawai sai ya dago kansa ya sake
dubanta ya ce, "Tsawon kwana nawa ne zan yi na gamna jinyar
jikin nawa na tafi?",
Budurwar ta ce, "A kalla kwana goma sha hudu. A sannan ne
fuskarka za ta yi fes ka koma ga masoyiyarka cikin kyakkyawar
siffa, Koda jin haka sai Hantaru ya yi murmushi. Amma da ya
dubi budurwar sai ya ce a ransa. "Ina ma ace gimbiyu Larziya ce
da kyau irin na Wannan budurwa, da na gama morewa a duniya,
domin na tabbatar da cewa a duniya kaf ba za a sami kamarta
ba. Ashe har akwai wadda tafi Larziya kyau a cikin wannan
duniya?".
Hantaru ya tambayi kar sa a cikin zuciyarsa. Kamar budurwa ta
��San irin Zancen Zucin da yake yi sai ya ga tayi masa murmushi
sannan ta tako kafafunta a hankali cikin tafiyar kasaita tamkar
dawisu tazo daf da shi ta kamna hannayensa ta jashi izuwa kan
gadonta ta zaunar da shi ta ce,
"Ya kamata yanzu ka ci kasha sannan ka sha magani ka kwanta
ka huta".
Kafin Hantaru ya ce wani abu sai ya ga wadansu kyawawan
kuyangi guda biyu Sun baiyana tsulum a gabansa. Daya na
dauke da katon faranti cike da abinci iri-iri dayar kuwa kayan
shaye-shaye ne kala-kala har da na magani. Har a Wannan
lokaci budurwar na rike da hannayen Hantaru, wani irin laushi
da yaji a hannayenta ne yaji ko kadan baya son ta saki
hannayensa, domin bai san sa'adda ma ya fara lumshe idanu ba
amma da zarar ya dubi fuskarta sai ya ga tana rikida tana zama
gimbiya Larziya.
Kaico! Hakika soyayya dafice wadda idan ta ratsa sassan jikin
mutum, fitarta sai yaki. Duk tsananin kyawu irin na wannan
budurwa wanda ya ninka na gimbiya Larziya sau uku bai sa
Hantaru ya fi sonta ba akan Larziya saboda tuni zuciyarsa ta
gama cika da begen Larziya babu sauran gurbi wanda wata za
ta samu! Ba tare da bata wani lokaci ba kuyangin suka ajiye
farantan biyu bisa kan wani tebur da ke gabansu Hantaru
sannan suka bace 6at!
Bacewarsu ke da wuya sai budurwar ta fara ciyar da Hantaru da
hannunta kuma tana ciyar da kanta. A haka sai da suka koshi
sannan ta baiwa Hantaru ruwan magani kala shida ya sha. Yana
gama shan maganin sai ya dubeta ya budi baki domin ya
tambayeta sunanta amma sai yaji bakin nasa ya yi masa nauyi
ya kasa magana, idanunsa kuwa sai suka kama lumshewa
kawai sai ya tuntsure akan gadon ya kama barci. Koda ganin
haka sai budurwar ta kura masa idanu tana murmushi, daga
Can kuna sai idanunta suka ciko da kwalla ta fara zubar a
hawaye.
Jim kadan kuma sai ta fashe da matsanaicin kuka sai da ta
shafe sa'a guda tana ta kukan tamkar wacce ta rasa ivayenta a
lokaci guda sannan ta mike tsaye ta fice daga cikin dakin tana
waigen Hantaru kamar har abada ba Za ta sake ganinsa ba.
Daga Wannan rana kullum Wannan kyakkyawar budurwa na
tare da Hantaru dare da rana tana jinyarsa kuma tare suke cin
abinci safya, rana da dare, sannan su yi ta hira basa rabuwa
face ta ga Hantaru ya soma jin barci sannan tayi masa sallama
ya tafi turakarta.
Tsawon kwanaki goma sha hudu, Hantaru bai taba fita ba daga
cikin dakin da ake jinyarsa face ya shiga Wani kewaye idan
bukata ta kamashi. Hatta wanka Hantaru ba ya yi da kansa budurwar ce take yi masa don haka
ne suka shaku ainun suka saba da juna amma babu wani abu
da ya taba shiga tsakaninsa.
Wani abin mamaki shi ne a tsawon kwanaki goma sha hudu
basu taba yin hirar soyayya ba kuma Hantaru bai taba jin sunan
budurwar ba a duk sa'adda yaso ya tambayeta sunanta sai ta
bagarar da zancen ta sauya hirar da suke.
A iya rayuwar Hantaru in ka ?auke Salimat wadda ta raineshi a
matsayin mahaifiyarsa bai taba samun kusanci ga ya mace ba
gami da sabo face wannan budurwa. A ranar da kwanaki goma
sha hudu suka cikane, Hantaru ya tashi da sassafe daga barci
koda ya - dubi kansa a cikin madubi sai ya ga fuskarsa da
jikinsa sun yi kyau matuka kuma sannan ya yi haske da kiba har
wani irin sheki fatar jikinsa ke yi. Nan take yaji wani irin farin ciki
ya baibayeshi musamman da ya tuna cewa yau ne zai bar
Wannan gida domin ya tafi izuwa birnin Darul Mahsbul.
Hantaru na tsaye a gaban madubi yana kallon kansa sai kawai
ya ga wannan budurwa tsulum a gabansa, idanunta sun kada
sun yi jawur kai da gani ka san cewa ta dade tana kuka,
Al'amarin da ya matukar ?ugunzuma hankalin Hantaru ke nan
yaji kamar ya fasa tariya a yau, kawai sai ya budi baki da nufin
ya tambayeta dalilin da ya sa ya ga idanunta sun yi jawur, kawai
sai budurwar ta juya masa baya ta dauko takobin Saifal Lujara
ta mika masa ya karba sannan ta kama hannunsa ta jashi suka
fita daga cikin dakin.
Nan fa suka kama yawo a cikin harabar gidan, su shiga nan su
fita can. Nan fa Hantaru ya cika da matukar al'ajabi ya zama
cikakken dan kauye, saboda ganin irin daular da aka shirya
gidan ko a tarihi bai taba jin labarin gidan sarautar da ya kawatu
ba kamar wannan. Duk wani abu na jin dadin duniya an
tanadeshi a cikin gidan har da ma wanda ido bai ta6a hasashen
gabaninsa ba.
Sai da guka shafe sa'a ukU suna shiga sako sako, lungu-lungu
na gidan amma Hantaru bai ga alamar Sun kusan kure gidan
ba.
A?amarin da ysa yaji ya kagu ke nan, domin hankalinsa na kan
tafiya birnin Darul Habul. Koda budurwar ta fahimci halin da
Hantaru ke ciki sai ta ruko hannunsa suka tsaya cak kuma suka
fuskanci juna, kawai sai ya ga hawaye ya zabo daga cikin
idanunta.
Alamarin da ya matukar baahi mamaki ke nan ya dubeta cikin
kaduwa ya ce, "Ya ke Wannan ma'abociyar karamci da kyawu
ina dalilin zubar wannan hawaye nak?i?"
Koda jin wannan tambaya sai ta yi murmushi mai taushi a
gareshi ta ce, "Ya kai jarumin jarUmai, gwarzon zamani, kuma
traron wannan shekara, kayi sani cewa sunana Hayatul Lumhas.
Na kasance 'ya guda daya jal ga sarki Thibur na birnin Hindu.
A halin yanzu masAna bincike sun tabbatar da cewa duk duniya
babu wata mace mai kyau kamata, amma tun ina jaririya
mahaifina ya boyeni a cikin dakin tsafinsa ban taba fita ko Ina
ba har na girma na cika shekara goma sha takwas, shi yasa a
duniya ba a sanni ba.
Kaine Damijin fark? da na taba gani a rayuwata ban da
mahaifina, hatta mahaifiyata ban taba ganinta ba, ban San ta ba
umn ban sha nononta ba har aka kawoni wannan gida kimanin
shekaru hudu da suka gabata sa'adda nake da shekaru goma
sha hudua duniya.
Lokacin da mahaifina ya kawoni wannan gida ya ajiye ni a
sannan ne na ga ya dubeni ya fashe da kuka. Al'amarin da ya
dugunzuma hankalina kenan na ruke kafadarsa cikin matukar
damuwa na ce, "Ya kai Abbana ina dalilin kukanka, kuma me
yasa ka kawoni cikin wannan gida wanda ke tsal
kiyar dokar daji?.
Sa'adda mahaifina yaji wannan tambaya sai ya share
hawayensa sannan ya ce, "Ya ke yata ki yi sani cewa ba komai
ne ya sani wannan kuka ba face sanin cewa yau ne ranar da zan
rabu da ke rabuwa ta har abada, domin yau saura kwana bakwai
kacal na bar duniya. Abin da ya sa na kawoki nan na ajiyeki
kuwa shi ne, anan ne kadai ZA ki iya zama lafiya har izuwa
karshen rayuwari, idan na barki a can kasarmu kika gaji
karagata ta mulki duniya ba za ta zauna lafiya ba domin gaba
dayan sarakunan duniya za su tayar da hankalinsu a kan sai sun
mallakeki saboda tsananin kyawunki, al'amarin da zai janyo
yakin duniya ke nan ayi asarar rayuka da dukiya wacce bata da
adadi.
Bisa wannan daili ne yasa na rabaki da mahaifiyarki tun daga
ranar da aka haifeki kuma na Boyeki da karfin sihiri yadda babu
wani mahaluki walau mutum ko aljan da zai iya ganinki bare bar
ya kai labarinki wani wajen.
Baki san kowa ba, kuma ba ki shaku da kowa ba face ni, yau
gashi lokacin rabuwarmu ya yi, don me ba zan zubar da hawaye
ba? Na yi bincike a cikin taskar tsafii na gAno Cewa nan da
shekaru hudu za'a sami wani gawurtaccen jarumi wanda zi
shiga kogan mazzabatal Dulshul wanda ya gagareni shiga ya
dauko wata takobi da ake kira Saiful Lajara WaR'nnan jarumi zai
sha bakar wahala a cikin kogon tamkar zai rasa rayuwarsa da
kyar zai iya guduwa daga cikin kogon.
Aljanun da ke gadin takobin Saifal Lujara za su biyoshi domin
su halaka shi, a sannan ne nake son ki je ki ceci rayuwarsa ki
kawoshi nan gidan tare da takobinsa ta Saiful Lajara. Na sani
cewa wannan jarumi idan ya ganki dole ne yaji yana sonki,
fatana shi ne ki zamo abokiyar rayuwarsa domin shi kadai ne
zai iya aurenki ya iya zama da ke lafiya". (Sai kuma ni mai typing
Shuraih 99%)?
Sa'adda mahaifina yazo nan a zancensa sai na dubeshi cikin
mamaki na ce, "Haba Abbana ta ya ya zan iya zuwa na ceto
rayuwar wanan jarumin alhalin ban kasance jaruma ba kuma
bani da wani sihirin tsafi?". Koda jin haka sai mahaifina ya yi
ajiyar zuciya ya ce,
"Ya ke 'yata kiyi sani cewa yanzu tate zan baki dukkan sihirin
tsafina sannan mu yi bankwana na koma kasata na jira
mutuwata".
Koda naji haka sai na fashe da kuka na rungume mahaifina
sannan na ce, "Ya kai Abbana me yasa baka nuna mini
mahaifiyata ba koda sau daya ne mun ga juna kafin ka kawoni
nan tunda gashi yanzu kaima za ka rabu da ni rabuwar da ba
zamu sake saduwa ba".
Koda jin wannan tambaya sai mahaifina ya kamu da tsananin
tausayina har ya kasa cewa komai ya fashe da matsanaicin
kuka har izuwa lokaci mai dan tsawo. Daga can sai ya janye
jikinsa daga cikin nawa muka fuskanci juna ya ce,
"Ya ke yata kiyi sani cewa ka'idar sihirin tsafina ce ta hanani na
hadaki da mahaifiyarki idan kuwa na karya wannan kaida
shikenan sihirin tsafina Zai rushe, duk dukiyar da na mallaka za
ta salwanta. Da wannan furuci nake yi miki sallamar karshe."
Koda gama fadin haka sai mahaifina ya dada kankameni a
kirjinsa ya sake fashewa da matsanaicin kuka. Al'amarin da ya
karya zuciyata ke nan nima na kama kuka, Ina cikin wannan hal?
ne naji wani irin gagarumin karfi yana shiga jikina. Kafin na
gama shiga sai mahafina ya bace 6atl Na nemashi sama da
kasa na rasa.
Nan fa na rushe da kuma na kama guje-guje da iface- iface a
cikin Wnnan gida. Kawai sai Da...
MAZAN JIYA
Littafi na biyu 2
Part E
Na Abdulaziz Sani m gini
Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey
Nan fa na rushe da kuka na kama guje-guje da iface- iface a
cikin wannan gida.
Kawai sai naga kuyangin gidan sun baiyana a gabana sun
kewayeni suna rarrashina, sannan suka yi sujjada a gareni suna
cewa, "Ya shugabarmu ki ?auki hakuri da kaddara, ki sani cewa
mu masu debe miki kewane da biyan duk bukatunki daga nan
har izuwa karshen rayuwarki".
Koda naji haka sai na dubesu cikin mamaki na ce, "ldan kuma
mutuwa ta daukeki waye zai ci gaba da kula da ni?". Cikn hadin
baki suka ce "Ai mu ba mutane bane kamar ke, mun kasance
aljanu, muna dadewa a duniya fiye da ku bil'adama.
Daga Wannan rana ne na shiga sabuwar rayuwa a cikin wannan
gida kuma ya zamana cewa ina yin abubuwan al'ajabi cikin
karfin sihirin tsafi wadanda ni kaina nake mamaki. Haka na ci
gaba da rayuwa cikin, koshin lafiya da kwanciyar hankali amma
duk sa'adda na tuna da mahaifina sai na fashe da kuka, haka
kuma idan na tuna cewa ban taba ganin mahaifiyata ba sai naji
wani irin bakin ciki yai katutu a cikin zuciyata.
Haka dai na kasance a cikin wannan matsayi har tsawon
shekara hudu. A ranar da na ga hoton duk abubuwan da suka
faru gareka a cikin kogon Mazubatul Dulshal ne naji na kamu da
tsananin kaunarka don haka sa'adda wadannan aljanu suka
biyoka za su hallaka ka sai na bi umarnin mahaifina na zamo
guguwa naje na daukeka kafin su illataka na kawoka nan, nayi
jinyarka kawo izuwa yanzu tsawon kwana goma sha hudu har
ka sami lafiya.
Wannan shi ne takaitaccen tarihin rayuwata ya kai jarumin
jarumai, kayi sani cewa na gani a cikin bincikena na tsafi cewar
idan har ka koma wajen gimbiya Larziya za ta umarceka da ka
aikata wani mummunan aiki wanda zai zamo sanadiyyar
batawarka da Salimat matar da ta rene ka har ka girma a
matsayin danta na cikinta