Showing 168001 words to 171000 words out of 180493 words

Chapter 57 - Noorul Huda Complete Book Written by 0mmer Farouk.txt

ita bata ki kar in sake ma ko wace mace magana ba in dawo muyi ta xama bana xuwa ko ina" dariya Hajiya Mariya tayi tace "How will dat be possible kuma" Sau biyu Mami na xuwa gidan da su ilham ganin Arshaq da Ashraf, ana gobe Noor xa su yi arba'in Abuturrab na gidan tun yamma har bayan isha sbda ruwan da ake, Hajiya Mariya tace "You spend the nyt here sbda ruwa Aliyu" yace "Yea am thinking of that" Noor na daki kwance wajen karfe goma da rabi, har tayi shirin bacci Hajiya Mariya ta shigo mata da yara ta kwantar kusa da ita tace "Baxa ki sha furan ba kuma Samha" tace "Na koshi Mum" Hajiya Mariya tace "Toh shknn sai da safe" daga haka ta fita, Noor ta d'an yi mamaki don in har mai gidanta bai gidan ta kan kwana da su, Hauwa kuma ta wuce gida, ranan da yake nn kuma Hauwa ce ke tsayawa ta kwana da su, bude kofar dakin aka yi ta dago kai, tayi mamakin ganinsa don bata san yana nn ba har lkcn, ya rufe kofar ya karaso cikin dakin har xai kunna Ac ya tuna da yaran dake kwance ya rage kayan jikinsa kawai ya kashe wutan dakin ya nufi kan gadon ya kwanta, turo baki tayi ta mike xaune ta dau Arshaq ta sa shi a tsakiyarsu, ta dauko Ashraf shima ta ajiyesa duk yana kallonta ta koma can karshen gado ta juya masu baya, daukan yaran yyi gaba daya ya ajiye su can gefensa ya dawo kusa da ita, ta mike xaune tana kallonsa, tashi xaune yyi shi ma xata sauka kan gadon ya fixgota, fadawa jikinsa tayi ta fashe da kuka yace "Na rashin gaskiya koh?" A hankali take kukan bata ce komai ba, can yaji a hankali tace "Am sorry...." ya dago kanta yace "For?" Kin cewa komai tayi ta mayar da kanta kirjinsa, ya lumshe ido yana murmushi yace "Sorry for ur new habit baby, in dai kika kashe ni shknn sai kiyi ta rainan yaran ki ke kadai" kuka ta fara yi sosai, ya kai bakinsa kunnenta yace "Alryt baxan mutu ba sai kin haifa min yara shidda koh?" Abbansa ne ya fado masa ya lumshe ido, ita kam gyada masa kai tayi yace "Alryt, tel me u love me" murya can kasa tace "It's nt worth sayin....." bata rufe baki ba ya fara kissing din ta, Nan ita ma ta nuna masa tayi kewarsa fiye da yanda yyi, washegari da sassafe Abuturrab ya bar gidan tun kan Small mum dinsa ta fito, ita kanta Noor bata san ya wuce ba don tunda tayi sllh ta koma bacci, karfe sha daya Hajiya Mariya ta kirasa da yake ranan lahadi ce sai ga shi ya taho, a daki ya sameta bayan sun gaisa tace "Kaga yau suka yi 40 days son, ya kamata ku koma can gidan tare, before then kuma lefen da baka yi mata ba sai kayi xa su koma" dariya yyi yace "Kai mum" tace "Yes in raka ka kasuwan, kuma miye na wucewa da asuba" ya d'an shafa kai yace "Ba komai mum" mikewa tayi tace "Toh ni dai bari in shirya mu je kasuwan ynxu" fita yyi ya shiga dakin da Noor take ya sameta xaune tana ta wasa da yaranta, xaunawa yyi kusa da ita yace "Tom kin gama da su, it's now my time" hararansa tayi tace "Ni bn gama da su ba" rungumota yyi yace "Ashe kema kin yi missing dina baby?" Ta rufe ido bata ce komai ba tana murmushi tana shakan kamshinsa me ddi, murya can kasa yace "yesterday was great...." Bude kofar dakin Hajiya Mariya tayi, Noor ta janye jikinta da sauri, yi tayi kmr bata gansu ba tace "Ina jiranka ne Aliyu" ya mike da sauri yace "Okay mum" tana fita yayi kissing dinta a lips yace "Sai mun dawo baby" bin sa tayi da ido don ba karamin kyau kananun kayan jikinsa suka yi masa ba, yana fita Hauwa ta shigo dakin. Abuturrab ya langwabar da kansa bayan sun isa Atm yace "Mum kudin account dina is nt up to 500k fa, kuma...." Tace "Baka da damuwa sai in ranta maka idan ka samu ka mayar min da kayana" dariya yyi yace "Kai mum" tace "Ehh, xan dai bada tawa gudunmawar kayan jewelries" yace "Toh nagode mum" dubu dari biyu da hamsin kawai ya ciro a account dinsa, ita ma ta cire kudi me yawa bata dai gaya masa ko nawa bne suka shiga kasuwa, akwatuna masu kyau na xamani ta fara sa suka siya set guda, daga nn kuma suka shiga shagunan atamfofi ta siya manyan atamfa guda sha biyar snn ta siya masu d'an saukin kudi guda goma, ta siya lace masu tsada biyar, sai materials da abaya kala kala, mayafai, hijab, jakunkuna, takalma, kayan shafe shafe, turare, sabulai, kai duk abinda tasan ana xubawa a lefe har da su pray mat, alqur'an da carbi, sae jewelries da ta bata lkci wajen xabansu, Abuturrab dake xaune sai kallon ikon Allah yake yace "Mum kashe ni kike son yi kawai" kallonsa tayi tace "Wato ga yarinya ka samu a bnxa koh" dariya yyi yace "Wayyo mum a dai tausaya min, ni fa ne naki" tace "A'a mamar ka na can inda ka baro ta, wnn ce tawa a ynxu" ba su suka bar kasuwan ba sai kusan la'asar, sae da ta tabbatar bbu abinda ya rage bata siya ma Noor ba uwa ynxu xa ayi auren, sai da suka isa gida ta juya tana kallonsa tace "Kudin da xaka ban nayi lissafi 450k bnda kudin jewelries" xaro ido yyi yana kallonta, bata kuma kallon inda yake ba ta fita motar, ta kira mai gadi ya taimaka mata shiga da kaya ciki, Abuturrab ya fito motar yana murmushi a xuciyarsa yace "Lallai mum" Noor bata iya tace ma Hajiya Mariya dake ta nuna mata kayan tana jera su a akwati komai ba, duk jikinta yyi sanyi wanda hakan yasa bata san lkcn da hawaye ya shiga sakko mata ba, jin shirunta yyi yawa Hajiya Mariya ta dago tana kallonta, ganin kuka take tace "Ikon Allah, kuka kuma Samha" dawowa tayi kusa da ita tace "Kukan me kike daughter" rungumeta Noor tayi cikin muryar kuka tace "I love you mum, nagode Allah kara maki tsawon kwana" Hajiya Mariya tayi murmushi tace "Toh Amin my daughter, you take me as ur mother kin ji" karfe biyar da wani abu Hajiya Mariya tayi mata duk abinda tasan ya dace dai na gyaran jiki, ta kira mijinta ta rokesa alfarmar siya masu foodstuffs, ba a dau lkci ba driver ya shigo da buhun shinkafa biyu, carton din taliya uku, jarkan man gyada da manja manya, maggi, gishiri har da kwalayen indomie biyu, Abuturrab na shigowa tace "Toh ga gara nn Alhaji yyi mata nasan har ku bar duniya baxa ka mata gorin hakan ba wataran tunda ku din ba tabbas ne da ku ba, kayan daki kuma in shaa Allah idan kudi ya shigo min xan siya mata nata" dariya yyi sosai yace "Mum you are making me feel ashame, haba my mum" bata sauraresa ba ta kara gaba abunta, bayan magrib Hajiya Mariya ta rakasu can gidan nasu da aka yi furnishing tuni, duplex ne mai kyau da parlor sama da kasa sai dakuna huda ko wanne da bathroom, sannan babban kitchen, xa a iya cewa col ne ya gina masa gidan don kudinsa ba mai yawa bane a ginin gidan, Da yake abban nasa yasan halinsa shi yasa bai yrda ya tare gidan ba da dadewa sai masu gadi har uku dake rayuwa cikin gidan, Kuka Noor ta dinga yi da Hajiya Mariya xata wuce, Hajiya Mariya dake dariya tace "Ae sai yaran ki su maki dariya Samha, kar ki damu ko xuwa jibi Hauwa xata dawo ta dinga xama da ku sai in nemi wata mai aikin" tun barin Hajiya Mariya gidan Noor taki daina kukan da take, ita har xuciyarta take son matar, duk iya rarrashin da Abuturrab yyi mata kin saurarensa tayi, ya kyaleta ya maida hankalinsa kan boys dinsa dake kwance kan gado, ana kiran isha ya tafi masallaci da xai dawo ya dawo masu da take away da fresh milk, shi kadai ya ci don ko kallon abincin ita bata yi, yyi wankansa ya sauya xuwa pyjamas ya kashe wutan daki yyi kwanciyarsa kusa da yaran dake bacci, ta gaji don kanta bayan kusan awa daya ta mike ta shiga bathroom ta dauro alwala ta fito tayi sllh, tana idarwa ta canxa kayan jikinta xuwa rigar bacci don tayi wanka a can gidan, ta je can karshen gado tayi kwanciyarta ta juya masu baya, dawowa yyi kusa da ita ya jawo ta jikinsa murya can kasa yace "Oya ci gaba da kukan" turo baki tayi xata kwace kanta yace "Baki isa ba, ci gaba ina son rarrashin ki yanda ya kamata ne" cikin muryar shagwaba tace "Ni ka bar ni, bana soo..." Tsit tayi ta lumshe ido don bbu bata lkci ya fara rarrashin nata yanda ya kamata kuwa.

*Haske writers asso*

tnx for d prayers everyone.
💫 *Noorul Huda*💫

By khaleesat Haiydar📚✍🏻

101.....

Zama irin ta masoya Abuturrab da Noor suka shiga yi, bai taba tunanin Noor xata ajiye komai ta fito masa da tsantsan so ba, ko kadan bata son bacin ransa kamar yanda shi ma bai son nata, bbu abinda ya sa ta kara samun kwanciyar hankali irin yanda Abbanta kan xo gidan nasu duk end of month ganin Arshaq da Ashraf da yanxu ke dosan shekara daya, yaran maa sha Allah bbu abinda suka mance na babansu, ga su da farin jini duk inda xa su sai an tanka su, ba don Hauwa dake gidan ba da ba xata iya rainon nasu ita kadai ba don matsalarsu na rigima yyi yawa, Mami kan xo lkci lkci ita ma ganin jikokin nata, wani lkcn kannin Abuturrab kan biyo ta har su kwana gidan amma fa sai ran da Col bai gari, Hajiya Mariya kam dama yaran har sun saba da ita ba a daukan lkci bata je gidan ba, su ma duk sati biyu ko uku su kan je su wuni a gidanta ran lahadi, duk ran Friday Abuturrab kan tura ma Mahaifinsa text din gaisuwa da barka da juma'ah bai taba fashin yin hakan ba, duk da shi ma bai taba masa reply ba, Anty Maryam ma taje gidan nasu sau daya amma bata kwana ba ta wuce, Abuturrab kan je gombe once in a while don gaida Ummi, Noor dai bata taba binsa ba sai dai su gaisa ta waya, Xumunci sosai suke yi da Umma don so tari ta kan je gaida su ta yini da su Arshaq, idan ma suka dade basu je ba, Ahmad kan je ganin takwararsa da matarsa Maryam dake kara koya ma Noor xamantakewar aure, har lkcn idan Noor ta tuna mahaifiyarta fushi take da ita hakan na hana mata walwala kusan kullum kuma sai tayi tunaninta, duk tsawon lkcn nn bata xauna haka ba sau daya Abuturrab yyi mata maganan islamiyya washegari kuma tasa ya kai ta, duk karfe goma take tafiya ta dawo karfe biyu, ita kuma Hauwa tayi rainon yara, ana haka har yaran suka cika shekara daya da watanni biyar nn kuma Hajiya Mariya ta xo ta daukesu tare da Hauwa don ita xata yaye su, duk sai Noor taji ba ddi, wanda hakan sai da ya sa mata xaxxabi, ganin ta ki dawowa normal har bayan sati biyu har abinci ma ta fara ignoring Abuturrab ya sa ta gaba don jin ko an taba ce mata xa a rabata da yaran ne, kasa ce mata komai yyi yana kallon kwayar idonta, lkci daya maganan Abbansa ya fado masa wanda hakan sai da yasa gabansa ya fadi, d'an murmushi ya kirkira yace "Ae shknn sai in je in samu mum in ce mata kince a karbo maki yaran ki" xaro ido tayi tace "Ni ai bn ce maka haka ba" yace "Toh me ke damun ki?" Ta bude masa hannu alamar bata sani ba, hancinta ya ja yace "Fadi gaskiya boys din ki kike tunani" bata ce masa komai ba ta koma tayi kwanciyarta, ya mike yace "On Saturday xa ta kawo su ae wife, ita ma xata je Malaysia ne" fita yyi dakin ya koma parlor ya xauna yyi shiru, can ya mike ya dau makullin mota ya koma dakinta yace mata yana xuwa snn ya fita, pharmacy ya nufa direct, ya siya injections da xai siya da drugs ya dawo gida, bacci ya sameta tana yi, ya kalli agogo ya xauna kusa da ita ya shiga tashinta, a hankali ta bude ido yace "Baki ci abinci ba har ynxu baby" ta girgixa kai tace "Am nt hungry" yace "No u re, tun safe tea kawai kika sha dear, gaya min me kike son ci?" Ta d'an yi shiru sai kuma tace "Tuwo xan ci" yace "Toh bari in siyo maki a eatry" daga haka ya mike ya fita, tuwo da miyar vegetable ya siyo mata yana xuba mata a plate ta sakko kasa, a hankali ta kauda kai, yace "What?" Da kyar tace "I think i want to throw up, ka rufe abincin, it's..." Rufe fuskar tayi gaba daya, ba musu ya dauke abincin ya rufe ya ajiye gefe yace "Toh me xa ki ci" ta mike xata koma kan gado tace "I told you am nt hungry" yace "Noo kin ga akwai xaxxabi jikin ki ki ci ko kadan ne sai in baki magani" tace "Baxan iya ci ba" yace "In kawo maki shayi?" Gyada masa kai tayi ya fita ya hado mata shayin, kadan ya lallabata ta sha snn ya dauko maganin da har ya ballar mata da cup din ruwa ya mika mata ta amsa ta sha, yace "Saura allura" da sauri tace "Bana so" yace "Guda daya fa dear" da kyar ta amince yyi mata alluran snn ta kwanta ya kwashi take away din tuwo da cups ya fita xuwa kitchen, yana fita bacci ya dauketa, a gida yyi la'asar don bai son barin ta ita kadai, karfe biyar saura ya rufe laptop din gabansa ya mike ya wuce dakinta, ganin bai ganta kwance ba ya kalli kofar bathroom dake a bude, ya karasa ciki da sauri, durkushe ya ganta a bathroom din cikin jini, ya dagota yace "Subhanallah what happened, me ya faru, kin ji ciwo ne" a rude yake tambayar ganin kallon da take masa sai da ya sha jinin jikinsa ya kasa cewa komai kuma, a hankali ta mike tsaye ta cire kayan jikinta, Yana tsaye ya kasa cewa komai har ta gama kintsa kanta ta fice bayin, sai a snn ya juya shima ya fita kwance ya ganta kan gado ya karasa a hankali yace "Sannu wife, u were bleeding....." Lumshe ido tayi bata ce komai, pain reliever ya dauko mata yace "Tashi ki karbi magani ki sha pls" bude ido tayi ya duka kusa da ita yace "Pls wife" mikewa xaune tayi ta karbi maganin ta sha, yace "Ina ke maki ciwo" kasan cikinta ta nuna masa yace "Allah xai sauwake kin ji" komawa tayi ta kwanta ya mike ya fita, duk jikinsa yyi sanyi, but he have no other alternative. Kafin kwana biyu Noor ta warware kamar ba ita ba, a ranan Asabar Hajiya Mariya ta dawo mata da boys dinta, har ranta tayi murnan ganinsu amma bata nuna ba, Sai da Hajiya Mariya xata tafi ta tambayeta Anty Hawwa fa, Hajiya Mariya tace "Taje garin su amma sati biyu xata yi ta dawo" Noor tace "Allah ya dawo da ita lafiya" Abuturrab ne ya maida small mum din tasa gida. Haka nn rayuwarsu ya ci gaba da kasancewa gwanin sha'awa, he was very careful kar Noor ta kara conceiving, Har Ashraf da Arshaq suka cika shekara biyu da rabi, a nan ya sa su a islamic schl mai hade da boko, sai a snn Noor tasan ashe Abuturrab ba baya ba a fannin addini kawai ya fi fito da boko fili ne, during weekend gaba daya lkcnsa na gun yaransa yana coaching din su don bai son su yi lacking komai na bangaren addini ynda baxai ji fargaban duk inda xa su shiga ba ko ba ynxu ba, don yasan baxai taba rabasu da dangin mahaifiyarsu ba, mugun tsoronsa yaran suke sbda strictness dinsa ita kuma a lkcn tana shirin fara Diploma a fannin Islamic studies, idan Noor na rera maka karatun qur'an ko tana karanto ma litattafen addini baka taba cewa she was once a Christian, hakan yasa Abuturrab ke alfahari da ita, a cikin kankanin lkci Arshaq da Ashraf suka fara larabci a shekararsu ta biyu a makarantar ga hadda dake kansu, Abbansu ya daina masu Hausa gaba daya sai dai Noor, in dai xai yi communicate da su sai dai Larabci ko Turanci, Mahaifin Noor ya maida gidansu wajen frequent xuwansa sbda jikokin nasa dake mugun sonsa shi ma kuma yake ji da su, ba don kowa yake xuwa gidan ba sai don su, yau ma kamar ko wace Friday Mr David ya xo gidan da yamma rike da chocolates dinsu, yan biyun na xaune gun da Abbansu ya tanadar masu don studies ko wannensu da qur'an a hannu, Noor kuma na kitchen tana girki, duk suka taso gaida kakan nasu, ya zauna kujera yana kallonsu ganin mood dinsu yace "What happen to my boys" Ashraf dai yyi shiru, Arshaq da har idonsa ya kawo ruwa yace "Abbu promise to cane us today" Noor ta fito kitchen ta gaida Abban nata tana murmushi, ya amsa ya maida hankalinsa kan yaran yace "Wht have you 2 done wrong" Ashraf ya juya yana kallon Ummun sa, Mr David ya kalleta yace "Me suka yi" yar dariya tayi tace "Abba k'arin hadda yyi masu tun jiya dan yana nyt duty sai suka ki yi, to yace idan ya dawo daga masallaci xasu bada haddan shine fa ka gansu haka" yace "Toh ke me yasa baxa ki masu ba" tace "Abba basa ji, kallonsu ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login