Showing 24001 words to 27000 words out of 180493 words

Chapter 9 - Noorul Huda Complete Book Written by 0mmer Farouk.txt

ni fa na fi ka hauka bani da kyau, before the count of 5 get out from this premises, it's my husband's not ur father's" Abuturrab yace "Kiyi hakuri Mama ya ma ce min ba nan bane can gaba ne" daga haka ya kalli Samantha cikin ido snn ya juya ya bar wajen, ta bi sa da kallo uwar ta fixgo hannunta tana cewa "Mahaukaci kai"
Ilham ta warce hannunta daga rikon da Khaleesat tayi mata tace "Meye ne baxa ki iya gaya min parlor ba sai kin jawo ni nan" Khaleesat tace "It's about ya Abuu, and bana son Sis Ramla ta ji, I know she might tell Mami...." Ilham tace "What about him?" Khaleesat tace "That boys qtr he is staying is doing him more harm then good, kin san me na gani ranan?" Ilham tace "Meye kika ga" khaleesat ta bata fuska tace "I saw a lady in his bedroom...." Ilham tayi shiru sai kuma a hankali tace "I don't know what yaya Abu is turning to now" kamar xata yi kuka ta kare maganan, Khaleesat tace "Ke ma kin taba ganin ta koh?" Ilham ta gyada kai tace "Ehh, but warce kika gani ya take?" Khaleesat tace "Tall, fair, slim, sai kyan dan maciji" Ilham tace "Yess ita ce...." khaleesat ta dafe kanta tace "Toh ya xa muyi yanxu?" Ilham na gyada ksi tace "nasan maganin yar iskan, kuma fa arniya ce ba ma musulma ba" khaleesat ta xaro ido tace "What?" Kamar xata yi kuka tace "Me yasa ya Abu ke haka...." Kwafa ilham tayi tace "I know what to do" daga haka ta fita Khaleesat ta bi ta tana cewa "Toh me xa mu yi" washegari Saturday bayan azahar Abuturrab ya tafi gun aiki, su kuma su Ilham da khaleesat na ta kai komo part dinsa tun safe don ko islamiyya basu je ba duk suna jiran ganin xuwan Samantha amma har dare shiru, Ranan lahadi yana cikin bedroom su kuma suna xaune daga balcony dinsa, Khaleesat na neat din table cloth duk don kada ya xargi komai idan ya fito ya gansu, shi kam ko sanin suna gun bai yi ba, Ilham ce ta fara jin motsin gate ta mike da sauri haka ma khaleesat, a hankali ta turo gate din ta shigo sae dai bata bar kusa da gate din ba, suka labe jikin pillar suna kallonta, Abaya ce jikinta ta daura bakin dankwalin a kanta, hannunta rike da bible, jira suka dinga yi ta karaso amma bata karaso ba, sae jujjuya bible din hannunta take kamar Mara gaskiya tana kalle kalle, gani suka yi ta juya a hankali xata fita, ilham tace "Keeeee" cak ta tsaya sai kuma ta juyo da sauri tana kallonsu, duk suka fito suna mata wani matsiyacin kallo, ilham tace "In tambaye ki mana, nan kin ga yayi Kama da club?" Shiru Samantha tayi tana kallonta, khaleesat ta mata tsawa tace "Ke kurma ce xaki dinga kallonmu haka, idan baki fadi me ke kawo ki gidan nan ba sai mun yi maki shegen duka" Sauke idonta tayi bata ce masu komai ba, Ilham ta fincikota tace "Are you daft, ki fadi me ke kawo ki gidan nan kar mu maki shegen duka" hawaye ne ya cika idonta cikin rawar murya tace "Assignment yake taya ni....." Khaleesat kmr xata yi kuka ta dungureta tace "Assignment din uwarki, kina dai xuwa koya ma yayanmu iskanci koh? Ance maki prostitute ne shi kamar ki...." Xaro ido Samantha tayi tace "Ni ba prostitute bace...." Ilham tace "Karya kike, you are a prostitute...." Ta fashe da kuka tace "Am not a prostitute believe me...." Shakota khaleesat tayi a fusace tace "Wllh wllh daga yau kika sake xuwa kusa da gate din gidan nan sae mun cire maki hakora, kina xuwa kina lalata mana yaya, arniya kawai" sosai Samantha take kuka cikin raunin murya tace "Ni ba arniya bace, I have my religion, I am a Christian...." Ilham tace "Toh suwaye Christians din idan ba arnaye ba, ke katuwar arniya ce......" Bude kofa aka yi duk suka juya da sauri, kallon mamaki yake masu gaba daya, Khaleesat ta saketa da sauri, ya karaso a tsawace yace "Meye haka?" Khaleesat da ilham suka xumburo baki, ita kuwa Samantha banda kuka babu abinda take, duk ya rikice ya kuma yi masu wani mugun tsawa yace "Meye haka nace?" Ilham ta murguda baki tace "Warning muke yanka mata ta bar xuwa....." Hannu ya kai xai dalla mata mari ta bar gun a guje khaleesat ta bi bayanta, da sauri ya bi Samantha da har ta bude gate, ya rikota ta fashe da kuka tana son kwace kanta, ya ki saketa yace "No plss kiyi hakuri frnd, listen to me...." Cikin kuka tace "They called me a prostitute....." Lkci daya idonsa ya kada ya ma rasa abinda xae ce mata kawae ya jawota jikinsa yace "You are not dear....." Ganin yanda take kuka ya ja ta xuwa parlor, ya fi minti ashirin yana aikin lallashinta, ya lura tana da rauni sosai, ta maimaita an kirata prostitute ya fi sau biyar, da kyar ya samu tayi shiru yana rungume da ita, a hankali tace "And ni ba arniya bace, I have my religion, I am a Christian" shiru yayi bai ce komai ba, sun fi wani minti goma a haka snn ta xame jikinta a hankali ta mike ta kallesa tana goge fuskarta, mikewa yayi shi ma ya kamo hannunta yace "Plss am sorry on behalf of those stupid gals, I promise to teach dem a lesson" girgixa kai tayi tace "Ni basu min komai ba" daga haka tayi ficewarta a parlorn. Lumshe ido yayi ya bude shi ma ya fita, main house ya nufa fuskarsa daure, Ramlah kadai ce xaune parlor tana assignment fuskarsa daure yace "Ina su Rabi'ah?" Sama ta kalla tace "Suna sama" sama ya nufa ya bude dakinsu bbu su, ya bude na Mami ya gansu xaxxaune gefen ta.

By
_Khaleesat Haiydar_ hope this is enoughπŸ˜…
*Haske writers asso*πŸ“šβœπŸ»
πŸ’« *Noorul Huda*πŸ’«

12___13
Hade rai yayi ya xauna Mami dake kallonsa tace "Ya aka yi Aliyu?" Kin cewa komai yayi Ilham da khaleesat suka yi lamo jikinta, lkci daya duk ya jefa masu wani arnen kallo ya mike kamar wanda aka tsikara ya fice daga dakin kamar xae tashi sama, Mami ta kallesu tace "Kun nemi tsokanarsa koh?" Ilham ta turo baki tace "Ba abinda muka yi masa" har magrib su ilham basu yarda sun bar dakin Mami ba, nan ta tabbatar ba karamin laifi suka yi ma yayan nasu ba, bbu yanda bata yi da su ba su fadi me suka yi masa suka ki magana, har part dinsa Mami taje bayan Isha ta shiga har bedroom dinsa ganin baya parlor ta gansa xaune gefen gado hannunsa rike da waya, karasawa tayi tana kallon kofar bathroom jin k'aran washing machine, ya ajiye wayar hannunsa yace "Mamina...." Mami tace "dama akwai washing machine a nan?" Yace "Ehh akwai...." Tace "Wanki kake?" Yace "No, just singlets..." Xaunawa tayi tace "Laifin me su ilham suka maka ne wai?" Ya shafa kansa yace "Ya wuce Mami...." Mami ta tabe baki tace "Toh ku kuka sani, naga tun daxu baka shigo ba" yace "Ehh Mami dama yanxu xan shigo" tace "Ohk, toh xan samu a d'an siyo min fruit?" Ya kalleta yace "Toh Mami" mikewa tayi tace "kar ka siyo lemo just apples, grapes and watermelon" yace "Toh Mami, yaushe Abba xai dawo" tace "Baka da numbersa ne?" Murmushi yayi tace "Atoh" daga haka ta nufi kofa ta fita, mikewa yayi ya shiga bathroom ya kashe machine din ya fito da har xai dau makulin mota ya fasa don bbu wani nisa ya dau kudi kawai ya fita, kamar bai son tafiyar yake yi, duk bai da sukuni, yana isa bakin hanya dai dai gun masu saida fruits yayi xaman sa har sai da aka tambayesa mai xai siya, ya kalli mutumin ya gaya masa, wata mota ce tayi parking dai dai gun, ya dinga kallon motar har aka bude, gabansa ya fadi ganinta ta fito, bata ko lura da shi ba ta taho gun mai sayar da fruits din, mikewa yayi yana kallon cikin motar yana son sanin ita da waye, ido hudu yayi da Mum dinta da ta hakikince bayan mota, da ganinta kasan daga church suke, dauke kai yayi ya taka xuwa gun mai fruit din da har ya gama xuba masa nasa a leda yana xuba mata nata, kallonta kawae Abuturrab yake ganin mood dinta kamar mara lafiya yasan kuma tun abun da ya faru daxu ne, lkci daya kamar ance ta juyo ta juyo, kasa daina kallonsa tayi sae shi ne ya dauke ido sanin uwarta baxa ta rasa kallon su ba, ai ko kamar ya sani kallon nasu take kamar idanuwanta xa suyi magana, xagawa yayi ya dau ledan fruits dinsa ya sa hannu aljihu ya ciro kudi hade da wayarsa ya d'an saci kallon uwar ta yaga fa har lkcn kallon direction dinsu take, yi yayi kamar xai mika ma mai fruits kudi, ya tsaya daga bayanta cikin dubara ya kamo hannunta ya saka mata wayarsa a ciki, snn yayi saurin mika ma mai fruits kudinsa ya juya ya bar wajen, ita kanta jikinta ya bata mum dinta na kallon gun duk ta tsorata kada ace taga sanda ya bata waya, tana karban ledan fruits din tayi saurin jefa wayar a ciki ta basa kudinsa sannan ta juyo ta nufi gun mota, tana shiga motar mumy ta jefo mata tambayar da ya tsorata, "Samantha kin san wannan mutumin ne?" Cewar mumy kenan tana kallonta ido a zare, Samantha da Gabanta ya shiga faduwa tace "Wani mutum mumy?" Uwar tace "Wanda ya siya fruits yanxu" Samantha ta girgixa kai da sauri amma bata ce komai ba don bata iya karya ba, cike da masifa uwar tace "Karya kike, I saw the way he was looking at you, ina raba ki da non believers din nan baki ji ko, meye hadin ki da musulmi?" Hawaye cike idonta tace "Kiyi hakuri Mumy...." Wani tsawa tayi mata tace "Sorry for ur self, stupid girl kawai, ina cross din wuyar ki, Kin kara cirewa koh?" Hawaye cike idonta tace "Na mance shi gaban mirror" har suka isa gida masifa Mumy ke mata, Ta kankame ledan fruits din Don tasan kashinta ya bushe idan ta karbi ledan ta ga waya, a dinning ta ajiye ledan tayi saurin ciro wayar ta boye a rigarta ta wuce sama da sauri. Misalin sha daya tana durkushe gaban gadon ta hade hannayenta biyu idonta lumshe tana addu'a xata kwanta taji vibration din wayar a karkashin pillow da ta ajiye, mikewa tayi da sauri ta isa gun kofa ta sa key snn ta dawo ta dau wayar, number ne bbu suna, a hankali ya daga ta kai kunne, daga daya bangaren taji ance "Hellow frnd!" Murya can kasa tace "ina yini" yace "Lafiya lau, baki yi bacci ba?" Ta gyada kai kamar yana ganinta tace "xan yi yanxu" cikin sanyin murya yace "Ohk, am sorry dear for what happened in the afternoon, plss Kiyi hakuri...." Da sauri tace "Ae ya wuce" yace "No nasan it's still touching you, for my sake kiyi hakuri don Allah" hawaye ya cika idonta a hankali tace "I've already forgiven and forget.... My religion prohibit us from not forgiving, cause we are also being forgiven by the almighty God" ya lumshe ido yace "Ohk my dear, thanks much, ya daren?" Tace "It's nyc..." Yace "Good, gobe xa ki sch koh?" Tace "Ehh" yace "Toh sai da safe...." Da sauri tace "Toh ina xan baka phone dinka?" Yace "No, na baki so that xan dinga jin muryar ki" murmushi tayi tace "Muryata kuma?" Yace "Yeah dear, ur sweet voice..." Xaro ido tayi, tayi dariya tace "Ni ba ruwana, byee" murmushi yayi ya lumshe ido jin dariyarta, cikin sanyin murya yace "Ohk dear, sleep tighttt" a hankali tace "Thank you...." Daga haka ta katse wayar, kwanciya tayi tana kallon wayar kirar Infinix, ganin a bude yake ta shiga gallery, hotunan sisters dinsa ta fara cin karo da, gabanta ya fadi sosai tana kallonsu, A hankali ta dinga wuce su, yawanci duk hotunansu ne, sai na mami tana gani kuma ta gane mum dinsa ce sbda kamar da ta gani, wani hotonsa ta gani yana sanye da white Coat dinsu na likita, wuyarsa sakale da stethoscope fuskarsa dauke da murmushinsa mai kyau, sosai hoton yayi kyau, pink lips dinsa ta tsura ma ido, lkci daya incident din ranan ya fado mata gabanta ya fadi sosai, da sauri ta wuce hoton, haka tayi ta kallon hotuna har suka kare, ta lumshe ido daga haka bacci ya dauketa wayar na kwance kirjinta. Washegari da asuba vibration din wayar ne ya tada ta, mikewa xaune tayi da sauri, ta jawo wayar tana kallo taga number jiya ne, a hankali ta d'aga ta kai kunne, daga daya bangaren taji yace "still sleeping" murya can kasa tace "Na tashi" yace "Noo na tashe ki dai" murmushi tayi yace "Alryt, na dawo mosque shine nace bari in tashe ki duk da nasan bbu abinda xa ki yi....." Tace "Xan yi addu'a mana" yace "Wani addu'a?" Tace "Wanne kai kayi yanxu?" Yace "Sallah naje masallaci nayi mana" tace "Toh nima yanxu xan yi nawa addu'an" ya tabe baki yace "Toh ayi addu'a lfya" tace "Ohk thank you..." Katse wayar yayi ya ajiye yana girgixa kai. Mikewa tayi ta durkusa jikin gadonta ta hade hannayenta ta lumshe ido, ta kusa minti goma a haka kafin ta mike ta shiga bathroom ta wanke baki ta hada ruwan wanka tayi ta fito, bata 6ata lkci gun shiryawa cikin uniform dinta ba ta fito ta shiga dakin mumy ta ganta xaune kan study table dinta idonta sanye da glass bible a gabanta, karasawa tayi tace "Ina kwana Mumy" Mumy ta rufe Bible din tace "Lafiya lau, kin yi addu'a?" Ta gyada kai tace "Nayi" Mumy tace "Yaushe ne waec din naku?" Tace "Ba na gaya maki ba, it's on Monday" Mumy tace "Good, kina karatu dai koh" tace "Ina yi Mumy" daga haka ta fita, sai kusan takwas da rabi ta bar gida don revision kawai suke a sch, a motar gidansu xa a kai ta sch din, suna isa layin gidansu Abuturrab sai ga shi shi ma ya fito da mota, bai yi gigin hawa kan titi ba ya jira su fara wucewa, gaba daya ya tsura ido ya ga Inda xai ganta cikin motar, dama ita ma tun daga nisa ta hangosa, a hankali ta sauke glass har suka iso dai dai gate din, ta wara ido hade da d'aga masa hannu, kashe mata ido daya yyi, ta xaro ido hade da toshe baki kar tayi dariya, haka ya bi motar da kallo har suka wucesa, ya lumshe ido ya karasa motarsa ya shiga ya dau hanyar gun aiki,
Tun daga ranan basu sake haduwa ba, bai kuma damu ba don ko da yaushe cikin waya suke, ita kuwa kwata kwata ta daina bin hanyar gidansu don ma kada su hadu, ta gwammace taje ta xagaya duk da nisan tafiyar don ita tsoron sisters dinsa take, a haka har suka fara waec. Ta fito daga wanka knn bayan ta dawo daga 3rd paper dinta, tana tsaye gaban mirror tana goge dogon gashinta don karkashin shower tayi wankan kuma bata rufe gashin ba, vibration din waya taji ta koma gun gado ta dau wayar, d'agawa tayi ta kai kunne hade da langwabar da kai, daga daya bangaren yace "How was the paper?" tace "Uhm yayi sauki...." Yace "Upon the runs?" Wara ido tayi tace "No, ni ban Karba ba" yace "Alryt, me kike yi yanxu?" Tace "Wanka nayi...." Ya d'an yi shiru sannan yace "Ohk, kin ci abinci?" Ta girgixa kai tace "Nobody is at home, yanxu xan girka" yace "Me xa ki dafa?" Ta yi shiru kamar me naxari sannan tace "Kila in dafa indomie" yace "Uhm nima xan ci" ta xaro ido sai kuma tayi dariya tace "Indomie din?" Yace "Yeah, am very hungry, no body is at home here also" tace "Eyya, kuma baka iya girki ba koh?" Yace "Eh mana, but gashi xa ki yi mana ae" murmushi tayi tace "Da gaske zaka ci?" Yace "Ehh mana am jet serious..." Shiru ta d'an yi sai kuma tace "Ohk, toh wa xai karbar maka?" Yace "Oh baxa ki kawo min ba" shiru tayi sai kuma tace "A'a ka dai xo ka karba" yace "Toh shknn just leave it" tace "Ka fasa ci?" A takaice yace "Ehh" tace "Ohk toh" katse wayar yayi, tayi murmushi, ta karasa goge jikinta ta shafa lotion ta fito da abayar ta red and black ta sa, ta daure kanta da dankwali ta feshe turare ta fita, irish ta shiga ferewa cikin kankanin lkci ta gama ta soya, snn tayi sauce din hanta, tuni kamshi ya bade gidan ta xuba su a warmer ta tsaftace kitchen din ta fito, abincin ta dauka ta fita ta kulle gidan don tasan sae bayan isha mumy xata dawo daga service, tun fitowarta gate dinsu gabanta ke faduwa tunawa da su Ilham da tayi, amma cewa da yayi babu kowa gidan yasa hankalinta ya d'an kwanta, ba karamin karfin hali tayi na tura gate ba ta shiga bayan ta isa gidan, a hankali ta rufe gate din, ta nufi kofar parlor da sauri, ta murda kamar me tsoron handle din ta shiga snn ta rufe, kwance ta gansa kan doguwar kujera singlet da short nicker kadai ne jikinsa, k'in karasawa tayi ta ajiye abincin hannunta tana kirkiran murmushi tace "Uhm gashi na kawo ma, xan wuce...." Mikewa xaune yayi yana kallonta, can ya mike ya isa Inda take, ta sunkuyar da kai kamar munafuka, ya fi minti daya yana kallonta, snn a hankali ya kai hannu ya tsinke Rosary din wuyarta, ta dago da sauri mamaki dauke fuskarta tana kallonsa sai dai ta kasa cewa komai, ganin yanda ya tsareta da brown eyes dinsa still yasa ta sauke idonta a hankali, dago kanta yayi xae yi magana suna hada ido ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login