Showing 21001 words to 21740 words out of 21740 words

Chapter 8 - MIJIN BABATA NE Book Complete by Ummu Jafar.txt

ya barta, sosai take sonshi , dan haka dole tayi haƙuri ta nuna kamar ba komai ba ne.

Tundaga ranar bai sake zama gidaba kullum yana can shida abokanshi da ƴan uwanshi ana shiri-shirin aure, ana gobe ɗauren aure shine bai shigo gida ba sai ƙarfe biyu saura na dare.

Har wannnan lokacin zaune take sai tunani take haɗi da tunanin Hansa'u shikenan tunda ta koma gidan kakarta ta barta ko, to ko ita bazata nemeta ba, taje can wajan dangin ubanta ta zauna, tana cikin haka yashigo tashi tayi ta tarɓoshi, abinci ta kawo masa amma yace ya ƙoshi, wanka yayi ya kwanta batare da ya kalleta ba, taso susha soyayya ta bankwana, dan tasan ita dashi sai bayan kwana biyu amma yace shi yagaji ko ruwan jiki bashi da yanzu dan haka ta saurara masa .

Tashi yayi daga kwanciyar ya kai dubanshi gareta yace,

" Saboda kina baƙin ciki zanyi aure shine baki je komai na biki ba bare kije kiyiwa iyayena Allah ya sanya alhairi ko?".

"A'a daman nace bari sai gobe sai naje da safe inyaso sai dare zan dawo".

Tsaki yaje ya koma ya kwanta ya barta zaune tana ta gumi, ahaka bacci yayi auwon gaba da ita.

***********

Hanyar da suka bi ya bi da kallo yana tunanin maganar da iyayenshi suka faɗar masa, to miyayi zafi haka da zasu yanke masa wannan huƙunci, ko wani abu aka zo akace yayi?.

Ahankali take taka ƙafarta cikin shigar da tayi riga da sikt na atamfa, sosai tayi kyau, kwanan biyu da tayi gidan har haskinta ya fito ta kuma wata ƴar lokota sosai tayi kyau ba kaɗan ba, mutsin da yaji ne yasa shi ɗaga ido a tunaninshi Mumy ce ta dawo, idonshi ne ya faɗa kan fuskar ta, lokaci ɗaya ya mike tsaye sai yanzu ya fara tunan yarinyar da yarufe gidanshi, bata kula dashi ba har ta ɗau abinda zata ɗauka ta koma ɗaki, ido ya kifa mata har ya daina ganinta sannan ya fita cikin tashin hankali.

Kai tsaye mota yashiga ya fige ta bai tsaya ko ina ba sai gidanshi, Baba mai gida tunda ya buɗe masa get yake ta gaisheshi amma ko kallonshi baiyi ba bare yasa ran zai karɓa masa, bedroom ɗinsa yashiga wayam yagani bai ganta ba, gabanshi ne yayi masifar faɗuwa, lokaci ɗaya ya ƙara tuna yarinyar da yagani gidan iyayenshi.

Cikin zafin nama yafita zuwa wajan mai gadi, ko gaisuwa bai tsaya sunyi ba ya tambayeshi waya shigo gidannan da baya nan? kai tsaye mai gida yace ba wanda yashigo, wuyan Baba mai gida ya cinkomu ya matse haɗi da zari ido yace,

" Wallahi ko ka gaya min ko yanzu nayi maka yankan rago wajannan".

Irin yadda yaga idonshi sun sauya sun koma kalar ja lokaci ɗaya yasa Baba mai gida cikin rawar ɗari yace,

" Alhaji ne yazo shida Hajiya suka.....kasa ƙarasawa yayi......tsawa ya daga masa yace,

" Suka yi me!".

Hanyar bedroom ɗinsa ya nuna masa da hannu yace,

" Suka shiga".

Hannu ya ɗaga zai wanke tsohon mutane da mari, kuma miya tuna sai ya fasa.

Tunkuɗe shi yayi sai da ya faɗi ƙasa kana yashiga mota ranshi a matuƙar ɓace, to waya gayawa Dady da Mumy ya kawo wata gidan? tabbas in ba abokansa ba to wannan tsohon mai gadi, dan yasan suna shiri da Dady kuma asali ma Dady ya kawoshi gidan dan yayi masa gadi.

Kai tsaye gidan iyayen nashi ya koma.
==========
Hawaye ne suka fara zubar masa kana ya dube Ahamd baki na rawa yace,

" Amma ba abinda ya haɗaku da Yayar taka ko?".

Ya faɗi haka a ɗan tsorace.

Ahamd bai samu damar buɗa bakinsa ba ya fito ɗakin da Baban nasu yaki ciki da tashin hankali, kai tsaye gidan Babarshi ya isa, koda yaje tana ɗaki ita da mijinta.

Ko sallama baiyi ba ya faɗa ɗakin, da sauri ta tashi tasaka hijab ɗinta haɗi da rufe mijin nata da zanin gado kana tace,

" Ahmad wai yaushe ka lalace! ashe zaka iya shigowa ɗakin nan batare da neman izini ba, kasan halin da zaka tarar damu? ai ko ba komai yana da kyau kayi sallama"......hannu ya ɗaga mata yace,

" Ni bashi nazo ji ba, yau ina so ki sanar dani waye mahaifina, kuma ya muke da wancan dakike cewa shine mahaifina".

Hannu ta ɗaura akai tace,

Yau minake shirin ji ko gani, Ahmad yau ni zaka zo kacewa haka!?".

Ta kai ƙarshin zanci tana kuka.....



*Comment and share*


*SUMMY M NA'IGE✍️*

6
7
8

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login