Showing 57001 words to 60000 words out of 98763 words

Chapter 20 - ANA MALIK HAUSA NOVELS BY HUMAYRA BULAMA .doc

ku!
Sam Dogarin nan bai damu ba haka ya fara k ok arin shiga wajen dan ko a mutu ko a yi rai farin cikin ubangidan nasa shine a gabansa, dukda kuwa ya san wacece Gimbiya Mariya kuma ya san me shallake umarninta ka iya janyowa.
Wambai d in ne ya dakatar da shi sannan cikin b acin rai ya kalleta ya ce
 Saboda ba ki d auki rai a bakin komai ba?& .
Hala kin manta wacece wannan d in ko kuwa dai kan ki ne ya juye.

Takowa ta yi ta zo gabansa ta tsaya ta ce  hattara dai Wambai! Ba kowacce magana ce idan ta taho maka za ka Furtata ga Gimbiya Mariya ba!
Zan yi maka uzuri a matsayin mistake amma idan ka kuskura ka maimaita hakan a karo na biyu to zan hukunta ka hukunci mai tsanani dan ya zama ganganci, kuma Gimbiya Mariya ba ta d aukar wargi.
A fusace Waziri ya yunk uro zai yi magana Wambai d in ya rik e masa hannu da sauri.
Sai da ya d an daidaita fushinsa kafin ya ce  Mai ya faru? .

 Ba ni da lokacin da zan tsaya yi muku bayani!
Sakina ta yi
Laifi kuma zan hukuntata, that s final!

Da kyar ya iya janyo numfashi ya fesar da bakinsa ya sake controlling kansa tukunna ya kalli Nuradden ya ce  mai ya faru?

A hankali ya jinjina masa kai sannan ya matso ya ce  bayan dogon bincike da nazari mun gano ita ce ta saka kayan tsafi a k ark ashin gadon mai martaba shekaru biyu da suka wuce, ga videon ta nan lokacin da take bawa Hadiminsa wanda aka kama da laifin dumu-dumu& .
A take ya kunna ya mik a musu wayar.

Karb a suka yi jikinsu har wani b ari yake yi tsabar tashin hankali, gata nan tarr da murya da komai, dukda kuwa video d in a karkace yake kuma dishi-dishi
alamun an sha wahala wajen d auka da nemosa amma kowa yana gani ya san Gimbiya Sakina ce.
Turk ashi!! Tabbas ko a cikin rami idan ka yi abu a cikin masarautar nan to sai ya fito! Duk wani abu na Makirci da zaka yi in dai ka barr wanda kuka yi tare da shi to sai ya fito, kai ko ka kashe ma tabbas sai an samu leakage daga wani d an uwan wanda ya yi abun ko
wani wanda ya sanshi! Dan da taimakon Oga kwata-kwata, k ungiyar masu bincike ta masarautar take amfani shiyasa duk k ank antar evidence sai sun ganota sun yi amfani da ita ko da kuwa bata kai girman kwayar shinkafa ba. Tabbas shima yanzu ya sake tabbatar da  Oga kwata-kwata ba gaibu bane ba! Kamar yadda ake cewa (Astaghfirullah!!!)& .
Wambai ya aiyyana hakan a cikin zuciyarsa hannuwansa suna karkawa!
Ba su da ikon kub utar da ita dama chan to yanzu kuma ga evidence! He really can t believe wai yau shine zai nad e hannu ya zauna a gaban idanunsa a jefe Gimbiya y ar d an uwansa!
Dan ya san ko da ace Gimbiya Mariya bata da evidence to ba su Isa su hana ba ballantana kuma ga evidence.

A hankali ya mik awa Mai Babban D aki videon d in wadda ta matso kusa da su da kyar dan da kyar take iya jan numfashi ma& ..
Ta na gama gani duk wani k ok arinta na son ganin ta ci gaba da tsayuwa a kan kafafuwanta ta ceci y artata ya sire!
A take ta tafi ta sulale a wajen jinta ganinta tare da kuzarinta duk suka d auke d iff.

A hankali Wambai ya matso ya ce  Tabbas maganar ki dutse! Amma duba da matsayin Gimbiya inaga wannan hukuncin ya yi mata tsauri& 
Juyowa ta yi ta wani kallesa daga k asa ta d ebosa ta kai sama ta watsar, kamar baza ta ce komai ba sai kuma ta magantu ta ce  Inaga baka san matsayi da girman wanda ta yiwa laifin ba! Kuma ni a yadda na san tsarin masarautar nan in dai ba Sarki mace ta tab a aura ba to tabbas hukuncin jifa bai sauk a daga kanta ba!

A hankali Waziri shima ya matso ya ce  mun ji kuma mun sani amma inaga gara a sakata a  kurkukun ban kwana ta mutu a chan a kan dai a jefeta! Gimbiya ce fa!!
Sannan a gani na wannan hukuncin da kika yanke hukunci ne wanda ya kamata a ce an zauna an tattauna shi a Fada tukunna, tun da na san ba daga Sarki hukuncin nan ya taho kai tsaye ba!
Idan kina yanke hukunci da kanki kai tsaye haka to mu meye amfanin mu? Kuma fa ki duba girman al amarin a ganina ya kamata a tsaya a tattauna& .
Shiru ta yi kawai ta na bin motar da ta shigo d aukar Uwar Marayu, sai da aka zo aka d auketa aka sakata a ciki aka wuce da ita tukunna ta kalli Fadawanta maza ta ce  su rufe mata gates d in filin kar su bar kowa ya shigo! Dan ta san yanzu za a taru!
Sannan ta juyo ta kalle sa ido cikin ido ta ce  Saifuddeen! Wallahi ko kaine ka aikata laifin yunk urin tab a mini Sarki to sai na kaika lahira at the very moment da na yi finding out tun kafin a shiga meeting a wanke ka ko kuma a kaika gidan Yarin da na san za a iya fito da kai daga baya.

Daga haka ta d auke kai ta kalli bayin da suke wajen durk ushe cikin tsawa ta ce
 Ku jefe min ita na ce!!
Ko sai raina ya b aci? .

A hankali suka mimmik e suka je suka tsaya a gaban uban tulin dutsunan suka fara d auka suna jifanta da shi& &

Sai da kanta ya fara lilo yana shirin barin gangar jikinta tukunna suka tsayar wanda abunda ba su sani ba tun a jifan farko da wani bafade ya yi mata yanzun zuciyarta ta bugu ta mutu!
Barori ne ta koina zagaye da filin ta waje a durk ushe suna kuka, hatta barorin da suka yi jifan suma akwai masu kukan a cikinsu, Barorin Gimbiya Mariya ne kawai suke farin cikin cika aikin uwargijiyar tasu da kuma wasu a cikin barori waenda Gimbiya Sakinar ta tarewa rawar gaban hantsi da kuma waenda suke jin haushinta& .
Suna gama aikinsu suka bar wajen suka koma chan nesa suka zube a k asa.

Jikin Waziri har wani irin karkarwa yake yi! Tabbas ba su da amfani a masarautar nan he really can t believe he s this powerless da har ba zai iya sakawa a yi ba ko kuma ya hana a hanu ba.
Kallon Nuraddeen kawai yake yi wanda ya matsa kusa da Gimbiya Mariya suna wani k us-k us, sosai ya k ura masa ido yana mamakin sa kamar ba shine Gimbiya Mariyar ta disga a Fada satin da ya gabata ba!  Kalli fa hatta Ubansa Mahaifi bai sanarwa abunda take shirin aikatawa ba bayan gashi ga dukkan alamu shine ma a gaban komai, sai kawai gani Wambai d in ya yi tare da kowa.
Wanne irin kusanci ne haka a tsakaninsu sannan what are they up to?
Dan tabbas Nuraddeen wanda ko a wajen Ubansa ba ya juyuwa bai kamata a ce ya tsaya suna had in kai da Mariya ba ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.
Tabbas akwai wata a k asa, ko kuma a tsakaninsu wani yana cin dunduniyar wani ne& 
Ya aiyyana hakan a ransa& ..

Kai kana ganin fuskar Gimbiya Mariya ka san cewa she s relax ta sauk e wani nauyi.
Ana gamawa ta gama magana da Nuraddeen d in ta wuce bayan ta tamke fuska saboda kar ma wani ya ga rangwame a tare da ita.
Bayanta kawai ya bi da kallo yana wani irin murmushi&
 Tabbas matar nan sai na yi da gaske dan ta wuce tunani na!
& Gimbiya Sakina yanzu haka shekarunta sun fi arba in kuma ita ce za a ce Babba-Babba a cikin y ay a matan masarautar dan ko Giwar Mata maza ta dinga Haifa haka itama Mai Babban D aki y ay a maza ta yi ta Haifa da farko-farko wannan dalili ya sanya da ta haifi Sakina sai duk ta girmewa ragowar y ay an matan Giwar Mata kuma bayan ita sai da ta haifi mata goma sha uku tukunna ta haifi maza biyu amma da ikon Allah yadda ya tsara mata ba ta tab a ko auren fari ba! Wanda mutanen da basu gama yarda da k addara ba suke cewa asiri ne aka yi mata.
Masarautar ta KHAK IL tana da collaborations da dayawan k asashen nahiyoyin duniya wadda ita ce a sama-sama saboda girma da arzik in k asar wanda a yanzu haka power su take rawa sabida rashin capable leader! Dan kwata-kwata ko magana da iya tafiyar sarakuna Sarki ZainulAbiddeen bai gama iyawa ba ballantana azo kan mahimman aiyyuka, rannan da jirgin wasa d an k arami ya tafi fada ya manta yana mik ewa jirgin ya fad o kowa ya gani, da ikon Allah duk da girma ya riskesa amma har yanzun ya gagara ko da kamanta yi musu d aya daga cikin abubuwan da suka kamata ne, dan ko baya ga k arancin shekarunsa ma haka nan yake yin wasu abubuwan k asa da shekarunsa.
Wannan ya sanya ake tunanin nad a Gimbiya Sakina a wasu fannukan kafin ya gama girma ta dinga wakiltar k asar tunda ita ta yi karatu har PhD a k asashe mabambanta kuma ta sassan mutane sannan she s very social shiyasa aka bayar da shawarar a nad a ta ko kuma su dinga wasu abubuwan tare kafin ya gama mallakar hankalin kansa, duk da kuwa ba a hakan amma a fara a kanta tunda ba su da yadda za su yi dan matan Sarkin sai da suka san yadda suka yi suka haramtawa Waziri da Wambai sarautar k asar KHAK IL.
Nuraddeen ya je mata da tayin Soyayyarsa dukda kuwa ta girme masa sai dai shi sam bai damu ba dan a yadda ya ga ana shirin yi musu raba dai-dai ita da Sarki tabbas idan ta amince masa to kamar ta yi masa rabin aikin da ya tisa a gaba ne, amma sai ta yi fatali da shi har kusan sau uku wannan dalili ya sanya ya koma b angaren Uwar Marayu wadda tunda aka fara batun ta rikice ta gigice dan ta san in dai aka fara hakan to suna iya janyowa sarautar ta bar hannun d anta dad in d ad awa ta fi so ta samu full control da power bata k aunar sharing ko da d igon girman kujerar ne da kowa.
Wannan dalilin ya sanya ta had a mata gadar zare ita kuma ta afka ba tare da ta sani ba! Wanda daga ita sai Nuraddeen d in ne suka san kuma suka fusatata suka k ulla mata abunda ya sanya dole sai da ta kai ga yunk urin kashe k anin nata!
*****************
Jiya cikin dare har su Dije sun kwanta ta ji ana tab a k ofar d akinsu dan Inna ta tafi d akin Mallan.
Tana bud e k ofar ta ga Sumayya da wasu k awayenta y an islamiyyar su a bayanta.
Murmushi ta yi cikin sanyin da ba d abiarta ba ta ce  Ashe da gaske kike
Daga haka ta bud e musu k ofar suka shigo ciki& ..
Dama Sumayya ta iya k unshi sana arta kenan, dan haka suna zama ta shiga zana mata jaa na gargajiya.
Sai da ya yi ta cire ta saka mahallabiyya tukunna ta zana mata bak i shima hannu da k afa mai masifar kyau.

Zuwan nasu ya taimaki Dije kam dukda babu abunda ya ragu na game da damuwar da take a ciki amma ta yi raha dan duk su ukun akwaisu da barkwanci.
Ba su kwanta ba sai k arfe uku dan haka suka d an makara sallar asuba wanda kururuwa da koke-koken Kaka ne ma ya tashe su.


BULAMA
'?
0806 402 1951
ANA MALIK!!
Book 01.
Page 17.

Humairah Bulama.
Mikiya writers Association.

Cikin gigita duk suka yo waje wanda hakan ya yi dai-dai da k arasa cikar tsakar gidan.

Idanun Kaka suna sauk a a kanta ta k araso gareta ta na zuwa ta sa hannu ta shak eta wanda ko yunk urin kirki idan Dijen ta yi tsaff sai ta zubar da ita a wajen sakamokon rashin k arfin jiki na tsufa da take fama da shi& .
 Shegiya marar mutunci marar Imani!!!!
Dama na san wallahi ke da d an iskan kwarton kin nan ba za ku hak ura ba! Yanzu ke kin fi son d an daba akan mutum mai mutunci?? Da kika san ba zaki auresa ba ai da kin fito kin fad a an hak ura ba wai ki tura shi ya kashesa ba!
Salati tsakar gidan nasu ya d auka yayinda yuuuuuu!! Wani irin jiri ya d ebi Dije ta tafi zata zube a wajen su Sumayya suka ruk o su ita da Kaka wadda ta biyo ta luu za ta fad i itama.
Da sauri Mallan ya k araso wajen ya rik e Kaka idanunsa jazir alamun ya ci kuka.

A karo na ba adadi daga fitowar Kaka zuwa yanzu Asabe ta sake cewa  Kaka mai ya faru? Ya rasu fa kika ce, Yusufan ne ya rasu.

Cikin kuka mai cin rai Kaka ta ce  Wallahi Yusufa ya rasu Asabe ya riga mu gidan gaskiya sun kashe mini jikana!!
Sai kuma a fusace ta sake yin kan Dije Mallan ya yi saurin sake ruk ota amma cha take  shegiya y ar iska muguwa! Saboda son ranku gashi yanzu kin mayarda Y ay a takwas marayu mata biyu zawarawa, wannan wacce iriyar Annoba ce Allah ya sako min ita a cikin zuriata?? Mallan ka rabani da Yarinyar nan ta b ace mini daga gani kafin zuciyata ta buga!
Sosai Kaka take kuka wanda tsaff idan ka ganta dole ta baka tausayi.
 Shi kad ai iyayensa suka haifa amma tsabar rashin imani saboda bin son zuciyarki ke da d an iskan kwartonki d an daba kun yi musu yankan k auna& 

A hankali Iyya ta matso ta ce  ki daina aibantata sannan kar ki d aura zargi a mazaunin tabbataccen abu tunda baki da tabbas.

Cikin kuka Kaka ta kalleta idanunta jazir ta ce  Wallahi tallahi ba ni da tantama shi ne ya kashesa&
A bud e aka tarar da k ofar gidan nasa da aka shiga kowa bacci yake yi mai masifar nauyi baccin da har yanzu da muke maganar nan da ke basu farka ba! Kinga kenan abu aka shak a musu! Kuma aka tarar da shi da wuk a chake a k ahon zuciya da wata a yashe a kusa da matarsa inaga itama so ya yi ya kasheta watak il ya ji motsi shine ya gudu! Ki gaya min wannan aika-aikar kisan gillar dana wa ya yi miki kama???
Wallahi wallahi bani da tantama shine! Kuma wannan
Ta yi maganar ta na mai nuna Dije kafin ta ce  da saninta aka yi komai.
Ai ko Sagir shima na san k are mata kallon da ya yi ne ya sanya data gaya masa aka kashe sa! In ba haka ba ai kaff samarin gidan nan duk sun fita mai yasa su bai kashesu ba sai shi?
Ta yi maganar har yanzun tana kallon Dije da rinannun idanunta da suke baiyyana tsana da tsantsar tashin hankali da b acin rai.
Basu ga k arasowar Mahaifiyar Sagir ba sai sauk ar ruwan dukan da ta shiga sauk ewa Dije ne ya sanya aka ganta.
Fad i take  shegiya tsinanniya y ar iska wallahi yau mai raba ni da ke sai Allah sai na kasheki in sha Allahu
Tashi d aya matar ta sake hargitsa tsakar gidan ta sake gigita kowa gashi sai wani irin kuka take yi kamar ranta zai fita, sauk inta d aya ma Kubra bata ji ba dan an yi mata allurar bacci mai nauyi ne.

Da kyar su Gwaggo suka janyeta Iyya ta ce  Ashe ba ki san k addara ba? Ita har ta Isa ta kashe ko ta saka a kashe ba tare da izinin Allah ba?
Daga an fad i magana haka nan kawai tashi d aya har kin hau kin zauna kin fara aiki da ita kina hauka ne???
Cikin kuka Maman Sagir ta ce  ai dan ba Kamal bane ba shiyasa kike da bakin magana! Na rok i Ubangiji da  ya d aura masa Irin k addarar da kike ambatowa d in .

Duk da Iyya ta ji zafin maganar kuma abun ya yi mata ciwo amma sai kawai ta girgiza kai bata ce mata komai ba ta juya ta wuce d aki.

Abunda Kaka take yi bai gigita Dije ba kamar yadda Baba ya titsiyeta akan  sai ta gaya masa gaskiyar sun yi maganar Yusufa da Ma a! Dan in ba haka ba to a Ina ya san har hanyar gidansa ba, A gaban mutane.
Shiyasa ba ta san lokacin da ta durk ushe a wajen kawai ta fashe masa da kuka ba.

Wani irin kuka Dije take yi kamar ranta zai fita dan har wani shishshid ewa take yi gashi ta k i jin rarrashi, wanda hakan ya sanya jikinsa ya d an yi sanyi kafin ya juya kawai ya bar wajen k irjinsa yana dukan uku-uku.

A hankali Inna ta k araso ta mik ar da ita suka wuce ciki Kaka tana zaginsu ta uwa ta uba kamar ba tsohuwa ba.


Ba a yi minti ashirin ba suka shirya chap suka d auki hanyar Getso har da Asabe da Zainab, ita Inna bama ta sani ba sai a bakin Minu ta ji wanda bai dad e da dawowa daga asibiti ba.
Bayan tafiyarsu ta gwada kiran Mahaifiyar Yusufa a waya ta yi mata ta aziyya amma sai ta k i d agawa k arshema sai ta dinga rejecting dan haka ta hak

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login