Showing 87001 words to 90000 words out of 155363 words
Chapter 30 - SARAUNIYAR KYAU_Takun Farko _cmplt. By The Nainarh Kd -2-1.txt
ga shahararren mutumin da duniya ke damawa dashi AL_HAJI SAMEER LAMIƊO Jigawa State.
Gaba ɗaya ɓangarori biyun shiri suke ba kama hannun yaro, ba ga dangin amare ba, haka zalika baga dangin angwaye ba, shirin shan shagalin biki ake sosai waɗannan suna nunawa waɗancan wane ku ta fannin mutunta juna da nuna abin Alkhairi ga juna.
Lokaci naja sosai har aka wayi gari a ranar wata laraba, an ɗaura Auren Sagir Samir Lamiɗo, da zankaɗeɗiyar amaryarsa Suwaiba Saleh Sama'ila a Birnin Kano ƙarfe sha ɗaya na safe, Auren da ya sama hallartar duban jama'a na fa ɗin Nigeria dama wajenta.
Sai kuma Sameen Samir Lamiɗo, shima da tashi gwanar a Babban masallacin jumma'a na Birnin Gombe State, misalin ƙarfe biyu da rabi na rana.
Sannan Yusuf Samir Lamiɗo, shima a Kaduna State ƙofar gidan mahaifin amaryar sa Yusra, Alhaji Nazir Sani Sidi, misalin ƙarfe huɗu da rabi na yamma aka ɗaura Auren.
Daganan kuma ƴan ɗaurin Aure da kuma matan da sukazo tare, aka wuce da amarya Yusra Jigawa State wurin dangin ango, kafin daga baya ita da angonta su wuce Borno State wurin da yake zaune.
Sun isa Jigawa State can cikin dare wajajen ƙarfe sha ɗaya, dan haka ba'a tsaya jiran komai ba, aka musu tarba na ban girma sannan aka saukesu a masauki ɓangarena musamman.
Washe gari da ta kama Alhamis sannan kuma ranar cikan biki, aka tashi da sabon shagali wanda aka nuna ainihin al'adar mutan garin, ansha shagulgulan biki sosai kuma jama'a da dangin amare sun ƙayatu matuƙa.
Sai da aka kwashe kwanaki uku ana shan shagulgulan biki sannan komai ya lafa.
Zuwa rana ta biyar da bikin, gaba ɗaya jama'a sun watse gida ya rage daga amare da angwayen su sai kuma surukai iyayen angwaye.
Zuwa dare bayan isha'i Alhaji Samir Lamiɗo, da matan shi Hajiya Harirah da Dr_Raheemah da kuma da Hajiya Zuwairiya.
Gaba ɗaya suna zazzaune a ƙaton palon gidan, wanda ya gaji haɗuwa yasha kayan more rayuwa kala kala abin ba'a magana sai wanda ya gani.
Sai ga Yusuf ya shigo amaryar shi na take mishi baya, fuskar ta lulluɓe da lufaya mai shigen kayan jikinta, wuri suka samu daga can gefe a ƙasa, suka zazzauna, sai ga Sameen shima da tashi amaryar sanye cikin shiga kala ɗaya suke, ita himar ne dogo har ƙasa a jikinta, wuri suma suka samu suka zazzauna Sameen kusa da Yusuf yayin da da amaryar shi ta zauna kusa da Yusra matar Yusuf suma suka gaggaisa dasu Hajiya Zuwairiya.
Can sai ga Auta Sagir da kyakyawar amaryar sa Suwaiba suma sun shigo bakinsu ɗauke da sallama cikin shiga iri ɗaya, suka shigo sai faman baza ƙamshi da gyalli irinna amare sabbin suke.🥰
Kusa da Alhaji Samir Lamiɗo Sagir ya ƙarisa ya zauna, ganin hakan yasa Suwaiba ita ma ta ƙarisa wajen su Sadeeyah ta zauna tana Suna sakarwa juna murmushin yaƙe na rashin sabo.
Buɗe taro akayi da addu'a sannan AL_HAJI SAMEER da matansa suka shiga jero nasihohi akan zaman Aure da ladan dake ciki, muddin za'a daure ayi haƙuri to akwai riba a gaba, domin shi Aure akwai farin ciki a ciki sannan kuma akwai akasin hakan, daga ƙarshe dai aka kuma rufe taro da addu'o'i sannan aka sallami kowa.
WASH£ GARI
Gaba ɗaya amare da angwaye duk suka watse yayin da Yusuf ya yi Borno State da matar shi.
Sameen kuma ya yi Lagos da nashi matar, su kuma Sagir da Suwaiba amarya sai wajen ƙarfe shida na yamma sannan suka bi jirgi izuwa London domin su a can ɗin zasu ƙarishe karatun su.
Gida ya rage daga Abubakar wanda shi sai zuwa gobe zai wuce Abuja, sai kuma sauran jama'ar ciki suma dai su Zuwaira, Jawaheer, Jummai, Sakeenah waɗanda sukazo rakiya ga angwaye sai zuwa dare duk suka koma gidajen su cike da kewar ƴan uwansu.
*AURE KENAN*
*WASH£ GARI*
Shima Abubakar mai kyau 😁
Yabi jirgin Safe izuwa Babban Birnin Nigeria Abuja City.
Da isarsa Abuja ya ɗaura da harkokinsa daga inda ya tsaya, sam baya ma saka maganar Aure a ranshi, domin kuwa ba shine a gabanshi ba, a halin yanzu Babban abin da ke gabanshi, shine gudanar da Aikin shi cikin nasara da kuma kyautatawa na ƙasa dashi.
_*
Rayuwa ta ci-gaba da tafiya tana lulawa da mutane cikin sauri sauri lokaci ke wucewa.
Har aka kwashe tsawon watanni biyar gaba, cikin lokacin harkoki sun ƙara buɗewa Abubakar Mai Kyau ta ko'ina kuɗaɗe shigowa suke yi gare shi, dama kuma akwai su waɗanda ba'asan a dadi ba ma, sunan Abubakar Mai Kyau ba iyaka family da Abokan shi waɗanda suka saka mishi sunan ya tsaya ba, a'a sunan Abubakar Mai Kyau ya zagaye gaba ɗaya ƙasa, harma da wajen ta.
Abubakar Mai Kyau shi sam yama manta da wata Agreement dake a tsakanin shi dasu Alhaji Yahya akan batun Aure, gaba ɗaya yafi mayar da hankalinshi akan gina gobenshi.
Wata Ranar Saturday da ta kasance weekend yana kwance saman 3sieter a dake ƙaton palon shi, yana tunanin yanayin Rayuwa ya yi nisa sosai.
Yaji ƙarar ringtone na wayar shi dake saman center table, cike da kasalar da baisan ta miye ba, ya miƙa hannun shi na dama ya ɗauki wayar, ba tare da ya duba mai kiran ba, domin kuwa idanun shi a rufe suke ruf ya yi picking call din, Sannan ya yi sallama a kasalance.
Bai san lokacin da ya miƙe daga zaune ba, ƴan sauran baccin da yakeji da kasala, gaba ɗaya ya nemesu ya rasa.
Cikin tsananin girmamawa da ladabi yake gaisar da mahaifin shi da ya kira wayar. Tamkar yana a gaban shi, cike da ladabi ya amsa da
"To Abbhee Insha Allah nanda gobe ina hanya."
Yana faɗan hakan sukayi sallama ya kashe wayar.
Aje wayar ya yi gefe sannan ya yi tsuru, yana tunanin abin da zaisa mahaifinsa ya mishi irin wannan kiran na gaggawa, Amma duk iya tunanin shi bai hasaso komai ba, dan haka miƙewa ya yi ya koma Bedroom tun a lokacin ya fara shirya shirye domin zuwa gobe ya wuce Jigawa State.
__WASHE GARI
JIGAWA STATE__
Ƙarfe ɗaya na rana tayi mishi a ƙofar gate na gidansu, horn driver ya yi, gate man ya wangale gate sannan slowly jerin motocin suka shiga cikin gidan.
Sai da driver ya daidaita zaman motar a filin ajiye motoci na gidan, sannan Abubakar ya fito jikin shi sanye da suit Ash color, ciki ya shiga yayin da escort ɗinshi suka tsaya a waje.
Wurin Hajiya Harirah ya fara zuwa mariƙiyar sa, bayan sun gaisa sannan ya wuce gurin mahaifiyarsa Dr_Raheemah, nanma sai da ya daɗe kana ya wuce Wurin Hajiya Zuwairiya, ita kam sunsha fira sosai, sannan daga ƙarshe ya wuce ɓangaren shi a gidan, domin ya huta kafin lokacin dawowar Alhaji Samir Lamiɗo ya yi.
*_*
Da yamma wuraren ƙarfe biyar Abubakar Mai Kyau yana zaune saman lallausar carpet, ya yi zaman cin tuwo yayin da ya yi tsit ya mayar da gaba ɗaya hankalin shi yana sauraron nasihar da mahaifinshi ke mishi.
Sai yanzu ma da Abbhee ya ɗauko mishi wannan maganar sannan ya tuna dalilin kiran da aka mishi zancen dai ɗaya ne shine maganar Aure.!
Ɗan ɗagowa ya yi ya saci kallon mahaifinsu jin tambayar da ya yi masa
"Wai ina matar Aure?."
Sai kace matan a rami ake samowa, cikin ƙasa da murya yace "A'a Abbhee har yanzu dai bansamu ba, ina dai lalube cikin duhu ne."
Murmushin manya Alhaji Samir Lamiɗo, ya yi sannan yace "Abubakar kenan to ai ita mace rufe ido kawai ake a lalubo, idan ba haka ba sai dai ka ƙare a tuzuru baka sani ba."
Ƴar dariyar da bayyi shirin yi ba ne ta kufce masa kana ya amsa da faɗar "Abbhee da gaske nake, ko budurwa ban taɓa yi ba."🙃
AL_HAJI SAMEER yace "Kenan dai kana nufin kace ka amince ni na zaɓa maka wacca ta cancanta, da kai ko?."
Cike da ladabi Abubakar ya amsa da "To shikenan Abbhee na amince, Allah ya zaɓa mana abin da yafi alkhairi a garemu."
Cike da alfahari Alhaji Samir Lamiɗo, yake kallon yaron nashi kana ya amsa mishi da "Ameen.!"
To daga nan dai maganar tasu ta tsaya, dama ita ce mussababin haɗuwar tasu a ranar zuwa bayan isha'i Abubakar ya bar Jigawa State ya dawo Abuja City, ya ci gaba da harkokin sa, cike da nasara, maganar Aure da mace kuma ya Aje a gefe ɗaya, domin kuwa shi a nashi ra'ayin har yanzu bai ga macen da ta masa ba, duk da dai akwai su kala kala da masu bibiyanshi, amma ko kallon kirki basu isheshi ba, abin da ya saka a gaba shine dai gina gobenshi a farko.
A yi maganar koma miye daga baya a cewar shi...
Ranar ta kasance Litini a gajiye ya dawo daga company dan haka bayan ya yi wanka ya huta, palo ya sauko ya zauna saman 3sieter yana karanta wani £nglish Book 'Nigerian Poverty.'
Wayar shi dake ajiye gefe ce, tayi ƙara alamar shigowar saƙo, ɗaukar wayar ya yi yana dubawa, saƙo ne daga Abbhee abin da ke cikin saƙon.
Da farko dai pictures ne guda biyu na wata kyakyawar matashiyar budurwa, ɗaya tana sanye cikin shigar Likitoci ta ɗaura Lab coat a saman kayan jikinta, babu hijabi a jikinta, sai wani Farin scarf da tayi rolling kanta dashi, tana murmushi.
Na biyun kuma tana a ɗakin kula da yara ne, cikin Asibitin da alama likitar yara ce, shima dai tana murmushi akayi hoton, sannan shima ba hijabi a jikinta, sai mayafi da tayi rolling dashi.
Kyakyawa ce Ajin farko, dan kuwa ta mallaki dukkan wani abu da ya kamata ace mace wacca ta amsa sunanta mace tana da shi, kuma da alama zatayi fara'a da kirki tunda gashi duka murmushi take lokacin da aka ɗauka pictures ɗin...😘
Murmushi ya yi yana shafa sumar kanshi mai tarin yawa, bawai yana murmushin kyawunta bane, a'a yana murmushin Abbhee ne, wato harda pictures dan karma daga baya yace "Ba ya yi, to wai yaushe ne Abbhee yasan ra'ayin sa, nason Auran mace Likita?.
Murmushi ya kuma yi sannan ya ɗauko wayar ya fara karanta rubutun dake a ƙasan pictures ɗin..
"Sunanta Rafi'atu Rafiq Rayyan.
Ta kammala karatun likitanci fanin pediatrics.
Yanzu ta kasance cikakkiyar likitar Yara sannan🩺.
Shekarun ta Ashirin da biyu, ita da Ahalinta suna zaune anan garin Abuja.
Mahaifin ta Alhaji Rafiq Rayyan, ya kasance Amini ne a gareni🤼.
Ga address na gidansu daga ƙasa 💒.
Zuwa gobe nakeso kaje ku haɗu da ita, bayan kun haɗun, idan kun dai dai ta, sai ayi tunanin shafa fahita. Domin kuwa ta mi ƙe za'ayi.
Ba batun wani saka rana da waye waye.
Ga Number ɗin ta, shima daga ƙasa.
Da Fatan zaɓinnawa zayyi maka. Ya ka Abubakar🤗
Saƙo daga Mahaifin ka mai ƙaunar farin cikin Ƴaƴan shi, a kullum💝.
Good look🙏."
Ya karanta wannan saƙo yafi a ƙirga, ba abin da yakeyi sai murmushi, wato dai iyaye iyaye ne, babu kamar su a kaf faɗin duniya, wanda ya kyautata musu ya huta.
To Allah yasa mu rabu da namu iyayen lafiya Ameen.🙏
WASHE GARI
Bayan ya dawo daga company, kamar yadda Abbhee ya buƙata shiryawa ya yi cikin shigar hausawa wanda ba ƙaramin kyau ya yi ba, sannan ya ɗauki mota shi kaɗai, ba tare da securities ba, ya nufa Address ɗin da ya gani, a saƙon.
Isar sa gidan keda wuya gate man ya wangale masa gate da alama ansan da zuwan sa.
Shigar da motar shi ya yi ciki sai da ya daidaita zaman motar a filin ajiye motoci na gidan, sannan ya fito yana ƙarewa ƙaton gidan kallo.
Gidan Babba ne sosai, mai ɓangarori uku, ga ma'aikata sai faman zirga zirga sukeyi.
Tunani yake shin ya lalubo wannan saƙon da Abbhee ya turo masa ne, don ya duba lambarta ya kira ta, ko kuwa ya tsaya jiran tsammani?.
Yana nan tsaye jin gine da mota, bai san abinyi ba, sai ga wasu kyawawan yara maza biyu mace ɗaya su uku waɗanda ba zasu wuce shekaru biyu a duniya ba, da alama Triple ne, ga wata kyakyawar budurwa tana binsu a baya yayin da su kuma suke faman gudu sunƙi bari ta kama su.
Hango mutum suka yi jikin mota, aikuwa ba tare da sun tsaya duba ko waye ba gaba ɗaya suka Ɗafalfale shi, suna dariya, bayan sun ƙarisa wurin.
Tsugunawa ya yi yana musu wasa shima domin kuwa akwai shi da son yara sosai.
Qarisowa wurin budurwar da ke binsu a baya tayi tana sauke haki, ta kira sunan ɗaya daga cikin yaran.
"Kai.! Aleem ƙariso wurina, kunga baƙone wannan, kar ku ɓata masa kaya ko.?"
Tayi maganar tana marairaice wa Yaran yayin da su kuma suketa faman ɓuya a wayanshi, suna ƙara ɗafal fale shi, suna dariya, ɗaya daga cikin yaran macen ta ce cikin gwarancinta
"Lah lah siz jaki jekemu e, idan ukazo urin ki."
Ita ma yarinyar ta bata amsa tana kuma ɗafalfale shi.
Ganin Yaran ba zuwa zasuyi ba, yasa budurwar ta kalla baƙon dake tsaye gabanta, yana ta wasa da yaran abin shi gunin burgewa, cikin faɗuwar gaba mara dalili ta ce
"Barka dai Mister Mai Kyau, dan Allah ka shigo daga ciki, Auntie Rafi'at ɗin tana ciki fa."
Tayi maganar tana yunƙurin kamo Yarinyar amma ta kasa.
Murmushi Abubakar Mai Kyau ya yi sannan Yace
"Barta kawai, ba zuwa wurin ki zatayi ba, tunda tayi sabon Yaya a yau."
Ita ma tana murmushi ta kuma cewa "Am sorry Mister mai kyau, Yaran duk sunbi sun ɓata maka kaya, akwai su da ƙiriniya sosai."
Maganar take cikin kulawa da kuma nuna girmamawa a gare shi.
Abubakar Yace "Ai Yaran kenan, karki damu kinji 'precioso'."
Da sauri ta ɗago tana kallon sa duk da ba jin yaren Spanish take sosai ba, amma ta fahimci sunan da ya kira ta dashi yanzu wato *KYAKKYAWA*
Murmushi tayi da ya bayyana kyakyawan dimples ɗin ta sannan ta ce "Shigo ciki please, na barka a rana kayi haƙuri fa."
Gaba tayi yabi bayanta, du ka hannayen shi riƙe dana Ƴan uku sunƙi bari ya yi ko nesa dasu, kamar dama can sun saba dashi ne.
Palon baƙi ta kai shi sannan ta fita, bata daɗe ba, ta dawo da Tray a hannunta saman Tray ɗin, an rufe da wani ƙayataccen gyalle Like a Indian People.🤔
Saman center table ta aje sannan ta kamo hannun Yarinyar suma sauran ta kamo da wayau da dabara, kana ta kalle shi cikin murmushi take faɗin "Am sorry Mister Mai Kyau ga Auntie Rafi'at ɗin nan ta kusa ƙarisowa."
Ah maimakon ya bata amsa, sai ya tsinci kanshi da faɗin "Por favor! cuàl esta vuestra nombre.?"
Ma'ana { "Please! what is your name?."
"Dan Allah! Menene sunan ki?." Da Hausa kenan, shi kuma da Spanish ya ma ta maganar.
Kallon sa tayi da kyau, tana mamakin abin da zai sa ya dinga ma ta harshen Spanish bayan kuma Hausa take masa.
"To kodai yasan a ƙasar Spain nayi karatu ne?."
Ta tambaya kanta sai kuma ta share, bata kawo komai ba a ranta cikin sakin fuska ita ma ta bashi amsa da
"I'm Haleesat Rashid Rayyan."
Tana faɗin haka ta nufa ƙofa zata fita, sai kuma ta tsaya a hankali ta juyo zata saci kallon sa, aikuwa karaf suka haɗa ido, ai a tamanin ta ƙarishe fi cewa daga palon hartana buge kanta da ƙofa.
Ajiyar zuciya Abubakar ya sauke yana jin bugewar da tayi kamar shi ne ya buge, shafa sumar kanshi ya yi yana sakin murmushin da bai san dalili ba.
"A ah kai Mister Mai Kyau.! dakata mana da wannan Nonsense tunanin, wai wannan 'Babe" ɗin ba ƙanwa bace a wurin Yarinyar da kazo gani bane?."
"Eh mana haka ƙanwar Yarinyar da nazo gani ce."
"To me yasa kake ɗarsa wa zuciyar ka tunanin ta bayan ta kasance ƙanwa ce, ga Yarinyar da ake shirin Aura maka?."
"Ni ma dai bansani ba."😞
"To dakata, tukunna wai ma, me yasa naji ita wancan Yarinyar da nazo wurinta an kira ta da Rafi'at Rafiq Rayyan. Ita kuma wannan ta kira kanta da 'Haleesat Rashid Rayyan'. Toh yanzu wacece ta kasance Asalin Ƴar gidan kenan?."🤨
Duk wannan uban surutun shikaɗai yake abin shi, a can cikin zuciyar shi, shi da zuciyar ta sa.🤣🤣
Ajiyar zuciya ya kuma saukewa sannan a fili yace
"Ooho dai."
Ciro tsadar diyyar wayarsa ya yi a aljihun doguwar Rigar shaddar dake jikin sa, ya fara latsawa a hankali.
Wani ƙayataccen ƙamshi ne ya fara baƙuntar hancin sa, sannan wacca ta kasance mamallakiyar ƙamshi ta bayyana.
Shigowa palon tayi bakinta ɗauke da sallama.
Amsa ma ta ya yi ba tare da ya ɗago kansa daga kan phone dake a hannun sa ba.
Wuri ta samu a kujerar dake fuskantar sa, ta zauna sannan cikin kashe murya ko kuwa dama can haka muryar take ohoo ta ce "Good afternoon Mister Mine Mai Kyau."🤓
Bai amsa ma ta gaisuwar da take antayo masa ba, sai kallon da yake ƙare ma ta ta ƙasan idanu.
"Yes she is so very Beautiful, domin kuwa ganin ta a fili yafi ganin ta a pictures, kyakyawa ce sosai fi ye da tunanin mai tunani, ba za'a kira ta da siririya ba, haka zalika bata da ƙiba na azo a gani, tana tsaka tsaki ne. Yanayin fuskar ta kuma is normalcy circle, domin kuwa bata da fa ɗin fuska, haka ma fuskar ta ba tsayi, tana nan dai ba yabo balle kuma 🤫.
https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20
*SARAUNIYAR KYAU*💓
_(The Glam Queen)_ 👑
```Takun Farko```
Story & Written By:
*_The Nainarh KD_*
____________________________________________👑
*THE ONGOING BOOK'S*
1. *SONKI NE ƘADDARA TA*
MALLAKAR
FATIMA ABDULLAHI
_Batool Kamba_
2. *ZAN JIRA KA*
MALLAKAR
A'ISHA ALƘALI
_Mrs Aysib_
___________________________________________👑
Page *51&52*
Tana sanye ne cikin doguwar riga ƙirar Saudiya, fara mai adon stones ash color, tayi rolling kanta da veil fari, fuskarta kuwa tasha light make-up, ta fito sak Shilpa Shetty Indian Actress, sai faman baza ƙamshi takeyi.
Ganin da tayi kamar bai ji abin da take faɗa ba. Yasa ta kuma kashe murya cike da kwarkwasa da kisisina ta ce
"Mister Mai Kyau good afternoon."
"Barkan ki, ya kike, ya gida?."
Ya tambaya ba tare da yana kallon ta ba.
Qara kashe murya tayi cike da yanga ta amsa da "Ina lafiya ina. Fatan kaima hakan?."
Ah maimakon ya Biye ma ta