Showing 6001 words to 9000 words out of 23330 words
Chapter 3 - Dakarun Musulunci Book 3 By Abdulaziz Sani M Gini.txt
ku kyaleni da hirama da uwar mayu zanyi maganin su.
Koda jin wannan umarni sai ukashat sazirat da sarkin yaki suka saki linzami dawakansu suka fara saukowa kasa dgaga kan tsaunin sannayan shima sarki shaaran ya biyo bayan su ya juya ya dubi sauran miliyoyin dakarunsa yace, kada dayan ku ya sauko nan kasa ba tare da kunji umarni daga gareni ba.
A dai dai wannan lokacine uzaifat, lafirat da Abul shajaa da hirama da uwar mayu suka dunkuke guri daya suna masu hada bayansu suna kallon kowanne gefe nasu.
Cikin alamun karayar zuciya hirama ta dubi uzaifat tace, ya kai wannan jarumi tayaya kake zaton zamu iya ceto kanmu a wajen sarki shaaran?
Ka dubi miliyoyin dakarunsa dake tsaitsaye a saman mu. Su kansu su sarki shaaran din sun ishemu balai da masifa.
Saada uzaifat yaji wannan tambaya sai ya dubi hirama yace, kash inda ace kema kin yi imani da ubangijina da ko kadan ba zaki ji shakkar kimai ba a zuciyar ki.
Kuma ina tabbatar miki da cewa albarkacin ubangijina a yau si mun ga bayan wadannan majiya namu.
Kedai abinda nake so dake shine kada ki yarda kiyi nisa da ni ko lafirat ko uwar mayu domin duk saadda kika shiga halin kaka ni kayi zamu iya baki kariya da maimakon ubangijina.
Wannan shine abinda su uzaifat suka tattauna.
Alamarin su sarki shaaran kiwa, lokacin da suke sakkowa kasan daga kan tsaunin kiwa sai sarki shaaran ya dubi ukashat yace duk yadda zakayi ka tabbata ka kashe danuwanka a wannan lokaci tunda yanzu kana da abinda shi bashi da shi.
Ka sani cewa dukan burina akanka yake. Kai kadai ne zaka iya zuwa ka tono wadannan layu guda hudu wadanda aka binne a kasan katangun birninku kuma idan har baka tono wadannan layu ba har abada ba zamu iya cin birnin da yaki ba, kaga kenan har abada ba zaka zami sarkin Darul husuf ba.
Shirina shine da zarar mun ci birnin da yaki sai a daura maka Aure da yata sazirat ka co gaba da mulkin kasar ya zamana cewa mun rushe dakunan bautarsu mun Kawar da addinin nasu.
Wanda duk ya bijirewa umarnin mu daga cikin talakawansu mu take wuyansa muyi masa yankan rago. Ina son ka sani cewa dan uwanka uzaifat ne kadai zai iya ruguza mana wannan lissafi ta hanyar hanaka zuwa hako wadannan layu amma idan ka sami nasarar hallakashi a yanzu shikenan.
Idan ka kasa hallakashi lallai ni da kaina zan kawo maka dauki mu gama dashi.
Lallai wannan karon sun fado hannun mu kuma vasu da mafita gaba da baya dole ne su dandana mutuwa. Tabbasa lokacin cikar burina yazo.
Sarki shaaran ya dubi sazirat yace, ke kuma ta kowanne hali ki tabbatar dacewa kin kashe yar uwarki lafirat domin itace kadai ta san sirrin mu da sirrin birnumu.
Idan har kika bari ta rayu zata iya giwa abokan gabarmu jagora su shiga har cikin birnjnmu su cimu da yaki.
Tabbas kema yanzu kina da abinda ba ta da shi,don haka ina da yakinin cewa zaki iya gamawa da ita cikin kankanin lokaci.
Gama wannan jawabi ke da wuya suka gama sauko wa daga kan dogon tsaunin su hudu suka tsaya cak a gabanku uzaifat aka ci gaba da kallon kallon ya zamana cewa tazara dake tsakaninsu bata wuce taku goma ba.
Daga can sai sazirat ta zare takobinta ta sauko daga kan dokin ta ta fuskanci lafirat tace da ita, ke nake jira mu raba gardama. Yauce ranar karshen tina tiki tsakanina dake.
Na rantse da karagar mahaifina yau sai na cire miki kai da wannan takobin tawa.
Koda jin wannan batu sai lafirat ta fusata ainun ta daga tata takobin da hannu biyu ta riketa da kyua tana mai fuskantar ta tace, ai ranar wanka ba a boye cibi.
Ya ke yar uwata kiyi sani cewa bani da sauran buri wanda yafi na gana kasheku d a hannuna ke da mahifinmu.
Tabbas naji a jikina cewa lokacin cika wannan buri nawa yazo.
Da jin haka sai sazirat ta tuntsire da dariyar mugunta tace, hakika wannan sambatu da kike dai dai yake da mafarkin karya.
Kafin lafirat ta sake budar baki tace wani abu sai sazirat tayi kukan kura ta ruga kanta suka kacame da azababben yaki.
A bangaren uzaiat da ukashat kuwa dayan su baice uffan ba, kawai dai sun kurawa juna idone suna giwa kansu kallon KAR TA SAN KAR
Ukashat ya tuntsire da dariya yace, ya kai dan uwana kayi sani cewa karshnku yazo kai da sarki, domin dole ne wannan karon katangar Darul husuf ta fadi, dole ne a zubar da jini a cikin birnin kuma nine zvgan yau karagar mulki.
Saadda ukashat yazo nan a zancensa sai takaici ya kama uzaifat har kwalla tazo masa ya dakawa ukashat tsawa yana mai cewa, tur da wannan mugun hali naka.
Hakika ka cuci rayuwarka da ka baiwa makiya Allah hadinkai don ganin an Kawar da dan uwanka musulmi.
Ka sank cewa ni yanzu bana san nayi yaki da kai a cikin duhu.
Maana ina son na san matsayinka shin kai musulmine ko kafiri? Ina da labarin kayi zina kuma ka sha giya.
Wadannan duk manyan kaifuka ne a wajen Allah wadanda suna da hukunci, amma ka aikatasu duk da cewa hakan baya nufin wai ka fita daga addinin musulunci, face ka aikata babban laifi a matsayinka na musulmi.
Ina mai yin umarni gareka da ka gaggauta sanar da ni matsayinka na sani.
Koda jin wannan batu sai ukashat yayi murmushi yace, ina nan a cikin addinina kawai dai na saki hanya ne domin na sami biyan bukatata.
Shawarar da zan baka itace, ka san hanyar da zakabi ka sulale ka bar wajen nan domin ni bazan iya kashe ka ba amma duk yadda zan yi bukatata ta biya sai nayi. Ya kamata ka mika domin bazaku taba samun nasara ba.
Koda jin haka sai uzaifat ya daga takobinsa sama yace, tsakanina da makiya Allah babu gudu kuma babu ja dabaya.
Nima bazaniya kashe ka ba amma zan iya illataka.
Kuma da izinin Allah sai na kamaka da hannuna na damkaka ga mahaifinmu anyi maka hukunci dai dai da binda ka aikata.
Gama fadin hakan ke dawuya sai uzaifat ya afkawa ukashat suma suka kacame da azababbane yaki ya zamana cewa suka kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama juriya da zafin nama da bajinta.
Kai da gani babu tambaya ka san cewa sadukantaka ce ta hadi da takwarar ta kuma kowanne na ji dan kansa.
Shikuwa sarki shaaran sai yaki saukowa daga kan cikinsa ya dubi uwar mayu da hirama a fusace ya daka musu tsawa yace, tur da wannan aiki da kuka aikata.
Ke uwar mayu hakika kin bani kunya kuma kimin bani mamaki yadda kananan yara sauya miki raayi cikin kankanin lokaci.
Ki tuna cewa shekara da shekaru kina zaune lafiya da yayanki a cikin gidanki ba a taba kashe miki kiwa ba, yau gashi an wayi gari kin rasa gaba dayan yayanki face guda daya JAL wanda ke goye a bayanki.
Yanzu wacce tina kika samu bisa karbar wannan addini na musulunci face kin rasa gidan ki mai kama da aljannar duniya kuma kin rasa yayanki, ina Zakije ki cigaba da rayuwa ma dadi a duniya.
Uwar mayu tayi murmuahi tace gaba dayan duniyar na ta ubangijin musulunci ce, don haka duk inda yaso zanje nayi rayuwata domin shine zai bani tsaro da kariya.
Babbar ribar dana samu bisa karbar addinin musulunci itace, na gane gakiya na saki karya.
Na fahimci cewa tsafi karya ne kuma zalunci haramune.
Abu ma biyu shine, na sani cewa idan na mutu anan duniya ubangijin musulunci zai kasheni nan gaba a Wata rayuwar daban, kuma zai yi min sakayya da gidan aljanna, idan har na bishi na kiyaye cikinsa.
Kaifa wane tanadi ne da a ban rayuwa ta nan duniya?
Kodajin wannan batu sai sarki shaaran ya bushe da dariyar mugunta yace, kece kika yi imani da wannan batu amma ni banyi ba kuma tabbas zan nuna miki kuskurenki kuma zan ga ta yadda ubangijin naku zai iya tserar daku daga masifata.
Shaaran ya dubi hirama yace, ke kuma kinyi babban gori ga rayuwar ki tunda har kika guji iyayenki kika jefa su cikin matsanaicin bakin ciki na har abada.
Koda jin haka sai hirama tayi murmushi tace, ai ba nice na fara yin abin gori ba yarka ce ta lafirat tafara tunda ta gujeka kuma ta tsaneka harma bata da burin da yafi ta kashe ka da hannunta, shin akwai abin da yafi wannan abin kunya da takaici.
Saadda sarki shaaran yaji wannan batu sai jikinsa ya kama tsuma zuciyarsa ta kufula. Cikin tsananin shammata ya daka tsalle sama daga kan dokinsa tamkar daga cikin baka aka cillashi.
Ya na a saman ya zare takobinsa ya kawai hirama mummunan sara a wuya da nufin ya filke nata kai.
Cikin tsananin zafin nama uwar mayu ta sure hirama daga inda taje tsaye, takobin sarki shaaran ta sari iska.
Uwar mayu ta ajiye hirama a bayanta ta ce da ita duk gumurzun da za'ayi kada ki sake ki ce zakiyi gaba da gaba da sarki shaaran.
Ban hanaki taimako na ba wajen yakarsa, amma dai kiyi taka tsantsan, nima zan tunkareahine da taimakon ubangijina, amma bani da karfin da zan iya tunkararsa.
Nan take uwar mayu ta daga kanta sama tace, ya ubangijin komai da kiwa ka sani cewa ni mai raunice akan sarki shaaran saboda haka ina mai neman taimakon ka da saarka akan wannan azzalumi mai sabonka a doronkasa.
A dai dai wannan lokacine sarki shaaran ya juyo ya sake fuskantar su cikin murmushi kuma ya kara rike takobinsa da hannu Baiyi yace, na gaisheki uwar mayu.
Tabbas kina da zafin nama, domin ban tana kai hari ba an tsallake sai wannan karon. Yanzu zan yakeku da dukan karfina da dukka dabarata sai na ga ta yadda zaku kubuta.
Kafin uwar mayu ta budi baki tace wani abu sai sarki shaaran ya sake afka musu ya rinka kai musu sara da suka cikin zafin nama da karfin. Uwar mayu ta wanzu ta mai karewa da hannayenta.
Duk saadda takobin sarki shaaran ta hadu da hannun nata sai kaji kamar karfe da karfe ne suka hadi, har tartsatsin wutane ke tashi.
Alamarin da ya mutukar baiwa sarki shaaran mamaki kenan domin ya san cewa babu wani abu da zai sara da wannan takobi bai rabe biyu ba ko da kuwa karfe ne ko dutse.
*********************
Najibullah Muhammad 🥷🥷
************************
Haka kuma ya san cewa a halin yanzu gaba daya sihirin tsafin uwar mayu ya karye tunda ta karbi addinin musulunci yaya akayi yanzu takobinsa ta kasa yi mata illa.
Haka dai suka ci gaba da gumurzu su sazirat da nasu sarki shaaran.
Kura ta turnuke sararin samaniya.
Karafkiyar karafa ta cika dodon kunne su kuwa sauran dakarun sarki shaaran suna sama kan tsauni sunyi cirko cirko suna more kallo kawai, kuma sun giwa filin yakin kawanya dayansu baiyi yunkurin sauko wa kasa ba.
Sazirat da lafirat sai da suka shafe kusan rabin sa'a suna kaiwa junansu sara da suka, dayansu bai sami nasarar komai ba.
Koda ganin haka sai sazirat ta fara amfani da karfin sihirinta ta rinka watsa mata kibiyoyim tsafi masu da wuta.
Amma duk abinda ya doshi lafirat sai ka ga ya narke ya zama ruwa.
Ita kanta sazirat sai abin ya bata mamaki domin a saninta lafirat bata da karfin sihirin da zata iya kare kanta daga wadannan miganyen makamai.
Abinda bata sani ba shine, karfin addua ne yaje aiki.
Haka dai suka ci gaba da gumurzu har tsawon wata rabin saar ya zamana cewa duk takubbansu sun dakushe, Shima sarki shaaran sai tsafaffiyar takobin nasa ta karye.
Cikin fushi yayi wurgi da takobin tasa.
Uzaifat da ukashat ma nasu takubban duk sun kakkarye sukayi watsi dasu. Nanfa akayi cirko cirko ana kallon juna.
Daga can sai sarki shaaran ya koma kusa da ukashat da sazirat ya tsaya.
A wannan lokaci Abul shajaa ne da sarkin yaki ne kadai ya rage suna fafatawa har ma kowannesu yayi nasarar yankar jikin dan uwansa.
Shidai Abul shajaa a kirjinsa aka sareshi wajen ya dare jini na zuba.
Amma saboda juriya sai yayi sauri ya daure kirjin da rawaninsa ya gyara tsayuwa.
Shikuwa sarkin yaki a cinyarsa aka dankara masa saran.
Shima wajen yayi rami sosai jini na shatata amma sai yayi sauri ya yage rigarsa ya daure cinyar tamu ya tsaya yana dingishi cikin juriya da bajinta.
Kawai sai suka sake kacamewa da sanin artabu. Ya zamana cewa wannan karon yaki suke mai ban tsoro domin kowa iya karfinsa yake yi. Kuma suna neman rayuwar junane.
Har ukashat ya yunkura zai kai masa dauki sai sarki shaaran ya tareshi yace, ai abin kunyane mutum biyu su rufarwa mutu daya shiyasa ma na hana dakaruna tayamu wannan yaki.
Yanzu mu zuba ido muga waye zai nasara namune ko nasu. Bayan an kashe daya daga cikinsu sai kuma mu gwanda yar kashi tsakanin mu da abokan gwaminmu, tunda makami da tsafi yaki yayi tasiri.
Tabbas yanzu ne na gane sai munyi da gaske zamu iya samun nasara akan wadannan mutane domin sihirinsu yana da matukar karfi.
Koda gama fadin haka sai sarki shaaran yayi shiru ya zuba ido akan gumurzun da su Abul shajaa suke.
Filin yakin yayi tsit bakajin komai face ihun Abul shajaa da na sarki yaki da kuma karar haduwar takubbansu.
Nan fa suka ci gaba da mugun artabu ya zamana cewa karfi yazo daya suka ci gaba da yiwa junan su muggan raunika.
Babu abinda zai baiwa mutum mamaki face yadda yanayin yakin nasu yake kasancewa. Da zarar daya yasamu nasarar yankan daya sai kaga dayan ma ya samu.
Nan da nan jikinsu yai kaca kaca da raunika, jini ya rinka zuba a jikinsu.
Tun suna tsaye sai da suka durkusa kasa suna ci gaba da saran juna. A karshe sai kowannensu ya cakawa kowa takobi a ciki. Takubbansu suka faso ta bayan su.
Sarkin yaki ya tsandara uban ihu ya fara kakarin mutuwa. Shikuwa Abul shajaa sai ya fara Kalmar shahada.
Cikin gudu uzaifat ya ruga ya dora Abul shajaa akan cinyarsa.
A hannunsa ya karasa cikawa ya rasu.
Nan take hawaye ya zubowa uzaifat ya rungume gawar Abul shajaa a kirjinsa.
A wannan lokaci ne shima sarki shaaran ya rugo fa gudu izuwa wajen sarkin yakinsa ya kankameshi yana girgizashi amma sai ya ga ko motsi bayayi. Harshensa ya zazzago kasa, idanunsa suka Kafe.
Koda ganin haka sai sarki shaaran ya takarkare ya kwada uban ihu mai tsananin firgitarwa. Ihun nasa ya cika dajin gaba daura yana mai amsa kuwwa.
Nan take uzaifat ya dauke Abul shajaa ya koma can da baya ya ajiyeshi sannan ya dawo ya tsaya kusa da lafirat.
Shima sarki shaaran sai ya dauke gawar sarkin yaki ya kaita can gefe daya ya ajiyeta sannan ya dawo filin daga ya kanannade rigar hannunsa sannan ya cire dukan sauran makaman dake jikinsa ya watsar dasu gefe daya, kawai sai ya dunkule hannunsa biyu ya dagasu sama ya fuskanci uwar mayu da hirama yace, yanzu sai kuzo mu fidda raini ko.
Koda uwar mayu da hirama suka ga yadda kwanjin sarki shaaran ya kumbura kuma suka ga kirare jikinsa, suka ga duk jijiyoyin jikinsa sun kumbura, sai suka razana, jikinsu yayi sanyi zuciyar su ta karaya domin sun tabbatar da cewa ruwa ba saan kwando bane.
Shima ukashat sai ya dunkule hannunsa ya fuskanci uzaifat.
Sazirat ma ta dunkule nata hannun ta fuskanci lafirat.
Sarki shaaran ya dubi uzaifat yace, yanzu ne zami yakin gakiya da gakiya.
Na rantse da girman karagata dayanku ba zai tsira da rayuwar sa ba.
Gama fadin hakan ke da wuya sai shima sarki shaaran ya ruga kan uwar mayu da hirama ya rufesu da duka.
Naushin farko da yayiwa uwar mayu a fuska sai da gudan jini yayi fitar burgu daga bakinta, idanunta suka lumshe taga taurarin wuya. Tayi baya taga taga ta baje a kasa.
Ita kuwa hirama da kafa sarki shaaran ya nausheta a ciki, sai da tayi tsalle sama da baya ta fado kasa tana aman jini ta baki da hanci.
Kafin uwar mayu ta mike tsaye sai sarki shaaran ya ruga inda hirama ke kwance ya cafi wuyanta ya daga ta sama da hannu daya ya shaketa.
Nan da nan idanunta suka yi lubu lubu suka kada sukayi jawur, kafafunta suka kama wutsil wutsil.
A wannan lokaci uzaifat da ukashat suna mugun gumurzu suna ta naushin juna da bugun juna,duk sun hadawa junan su jini da majina.
Wani lokacin ma sai kaga sun kacame da kokawa sun rukunkume juna.
Wani lokacin kaga sun fadi kasa suna birgima wannan ya danne wancan