Showing 9001 words to 12000 words out of 23330 words

Chapter 4 - Dakarun Musulunci Book 3 By Abdulaziz Sani M Gini.txt

wancan ya danne wannan, sukayi busu busu da kasa.
A bangaren sazirat da lafirat ma kuwa irin abinda ke faruwa da su uzaifat suma shi sukeyi, wato karfi yazo daya sun ragargazar juna, fuskokinsu duk sun kumbura saboda tsabar naushin juna, kuma kowaccensu jikinta yayi tsami har suma sun fara kokawa a kasa.
Lokacin da uwar mayu ta dawo cikin haiyacinta ta mike tsaye zumbur ta hango sarki shaaran rike da wuyan hirama ya shaketa tamau har kumfar wuya ta fara fita daga cikin bakinta.
Sai ta sake mikewa tsaye ta ruga kansa ta rufeshi da duka da dukan karfita.
Ai tamkar yarone ke dukansa ko juyowa baiyi ba ya kalleta, kawai sai yaci gaba da kyalkyala dariyar mugunta, kuma ya dada shake wuyan hirama da karfi, ya zamana cewa hirama da kyar take iya motsa kafarta guda, ta wuce mutuwa sai dai ace suma suma.
Koda uwar mayu taga haka sai ta daga hannayenta sama ta kwala kabbara da karfin tsiya tana mai neman taimakon Allah, kawai sai ta karci bayan sarki shaaran da faratanta. Take wajen ya dare gida takwas jini yayi tsartuwa.
Sarki shaaran ya kwala ihu ya dimauce.
Bai san saadda ya saki hirama ta fadi kasa ba.
Shima sai tsugunna kasa bisa gwiwoyinsa ya rintse idanunsa ya fara karanta wadansu dalasiman tsafi.
Nan take wannan rauni na bayansa ya fara warkewa da kansa da kadan kadan, daga ya na sama raunin na bacewa tamkar bai taba wanzuba a wajen.
Cikin hanzari uwar mayu ta ruga da gudu izuwa inda hirama ke kwance ta fara yi mata firfita da hannayenta domin ta farfado daga dogon suman da tayi.
Kafin sarki shaaran ya mike tsaye daga inda yake durkushe ya sake kawo musu wani harin.
Ai kuwa a dai dai wannan lokacin da saunin sarki shaaran ya gama bacewa ne hirama ta farfado daga sogon suman da tayi.
Cikin zafin nama uwar mayu ta sunkuceta ta goya a bayanta ta daureta tamau da jelar jikinta sannan ta juya ta fuskanci sarki shaaran a lokacin da ya mike tsaye ya juya suka dubi juna.
Kawai sai sarki shaaran ya rugo da gudu izuwa kan uwar mayu cikin mugun mufi.
Kafin uwar mayu ta budi baki tayi wata addua ka ta nemi taimakon Allah sai kawai ta ga sarki shaaran ya baiyana a gabanta tsulum kawai sai ya sa hannunsa UA gabza mata nashi a fuska.
Saboda karfin naushin sai da ta yi katantanwa sau uku a tsaye sannan ta sukale kasa a sume. Hirama ta subuce daga bayanta itama ta baje a kasa.
Sarki shaaran ya sunkuyo da nufin ya kama kan uwar mayu da na hirama ya murde, kawai sai ya juyo ihun dakarunsa dake saman tsaunin.
Nan take yaga ana jeho dakarun nasa daga kan dawakansu suna gangarowa kasan tsaunin.
Wasunsu da kibiyoyi ake harbosu, wasu kuwa sai dai kaga an fille kawunansu.
Nan da nan saman tsaunin ya kacame da azababben yaki.
Ba wani bane yake wannan barnar ba face sarki uwaisul karni da dakarunsa na yaki wadanda suma adadinsu ya kai miliyan uku da dubu dari bakwai.
Da karfin tsiya sarki uwaisul karni ya tarwatsa dakarun sarki shaaran dake gabanta yana ragargazarsu har ya iso karshe tsaunin ya leka kasa.
Nan take yayi arba da sarki shaaran, suka kalli juna sannan taga yayansa uzaifat da ukashat suna ta tumurmusar juna.
Kuma ya hango lafirat da sazirat suna kwamarzuwa.
Kana ya hango gawar Abul shajaa a can gefe daya a kwance.
Koda ganin wannan alamari sai sarki uwaisul karni ya fusata ainun, zuciyar sa ta kama tafarfasa kamar zata kone.
**DAKARUN MUSULUNCI**
LITTAFI NA 3
PART D✍️✍️

NA;ABDUL'AZIZ
SANI MADAKIN GINI
TYPING UMAR FAROUQ ZANGO.
POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷🥷

Bai san saadda yayi kundunbala ba ya dako tsalle daga saman tsaunin ya duro izuwa kasansa yana mai kwala kabbara duk da cewa nisan kasan tsaunin ya kai zirai arbain.
Ai kuwa kafafunsa na dira bisa kasa sai ya ruga izuwa kan sarki shaaran rike da takobinsa a sama.
Koda sarki shaaran ya hangoshi sai yayi alkafira a kasa izuwa inda ya watsar da wasu gajerun addunansa guda biyu ya suresu sannan ya tari sarki uwaisul karni suka kacame da sanin masifaffen yaki.
Sai gashi ana yaki a saman tsaunin a kasa ma anayi.
Yanzu dai gashi manyan kuraye biyu ne a kasa suke fafatawa wadanda suka kasance tsofaffin abokan gaba da suka zamana cewa KAR TA SAN KAR, kuma a shekara da shekaru kowannensu na son ganin bayan kowa amma lamarin ya taazzara.
Sarki shaaran da sarki uwaisul karni suka wanzu suna kaiwa junansu sara da suka cikin nuna kwarewa da sanin makama har tsawon sa'a daya da rabi, amma dayansu bai sami nasarar komai ba.
Sarki shaaran ya fara amfani da karfin sihirinsa domin ya hallaka sarki uwaisul karni amma sai abu ya gagara.
Haka dai suka ci gaba da artabu har wata rabin sa'ar ta sake shudewa ya zamana cewa duk sun gaji.
Da kansu suka rabu suka ja da baya sukayi cirko cirko suna haki da kallon juna kamar zakaru.
A sannane sarki shaaran ya dubi uwaisul karni ya bushe da dariyar mugunta sannan ya murtuke fuska yace, ya kai abokin gabata kayi sani cewa kk yanzu rasuwa tatashi dan koli ya ci riba.
Na haddasa rashin kwanciyar hankali a gareka da jamaarka.
Na raba zumuncin dake tsakanin yayanka.
Kuma na sa dankara guda daya akan mugun TAFARKI na sabawa ubangijin ku.
Kuma ina tabbatar maka da cewa babu yadda za'ayi ku sami nasara a wannan yaki da mukeyi.
Kodai mu musami nasara akanku ko kuma ayi RAGAS.
saadda sarki shaaran yazo nan a zancensa sai sarki uwaisul karni ya yi murmushi yace,ya kai abokin gabanta kayi sami cewa zuciyata a wanke take tas babu wani takaici a cikinta bisa illar da kaimin.
Dana da ya bijire min ya hada kai da ku domin aga bayanmu yayi hakance saboda kwadayin duniya kawai domin baya son dan uwansa ya samu mulkin birnina.
Nayi sani cewa ya aikata babban laifi huda biyu na karya dokokin ubangijina.
Kuma akwai hukuncinsu da ya dace da wadannan laifuka.
Na sani cewa yanzu baka da wani buri wanda yafi kai da jamaarka kun dangana izuwa birnina har ukashat ya sami damar tono wadannan layu guda gudu da aka binne a karkashin katangunhudu na birnina.
To ina Tabbatar maka dacewa kaine abin tausayi a ganina tunda gashi yar cikinka bata d wani buri wanda yafi ta kasheka da hannunta.
Ina tabbatar maka dacewa ko yanzu ka umarci dana ukashat ya kasheni da hannunsa ba zai iya ba duk da cewa baya kaunata a zuciyar sa. Idan kuma kana musu ne to ka jarraba ka gani.
Saadda sarki uwaisul karni yazo nan a zancensa ne ukashat da uzaifat suka baje a kasa suka daina gadan saboda tsananin gajiya suka kama haki da numfashi kamar tansu zai fita.
Sazirat da lafirat ma haka alamarin y kasance a garesu.
Koda ganin abinda ya faru sai sarki uwaisul karni ya daga hannunsa yana mai nuni ga jamaarsa da su janye daga filin yakin.
Nan take kuwa aka Busa kahon tsaida yaki sai dakarun suka fara guduwa daga filin yakin suna barin gawarwakin yan uwansu suka nufi can bakin wani kogin.
Har dakarun sarki uwaisul karni sun fara binsu suna rafkewa sai sarki uwaisul karni ya daka musu tsawa suka daina.
Shikuwa sarki shaaran sai yayi nuni da hannunsa izuwa ga ukashat da sazirat da kuma gawar sarkin yakinsa. Nan take suka bace daga filin yakin.
Har uzaifat ya yi yunkurin yin addua domin Allah ya baiyana su, sai sarki uwaisul karni ya hanashi ya dubi lafirat yace, tashi kuzo muje can kusa da inda su mahaifinki suka tsaya muma mu kafa namu san sanin wannan yaki bai kare ba sharar fage kawai akayi.
Ba tare da fargabar komai ba kuwa uzaifat da lafirat ta mike tsaye tazo kusa da uzaifat ta tsaya.
Sarki uwaisul karni ya kama hawa kan wannan tsaunin uzaifat da lafirat na biye dashi.
A sannane uwar mayu ta mike tsaye da kyar dama ta dade da farfado sannan taje ta dauki hirama ta sake goya ta a bayanta tabi su uzaifat.
Koda suka hau kan tsaunin gaba dayansu inda sauran dakarun yaki suke sai sarki uwaisul karni yasa aka baiwa uzaifat da lafirat dawakai suka hau.
A sannane hankalinsu ya kai kan uwar mayu da hirama.
Har uzaifat ya bude baki zai ambaci wani abu sai yaji uwar mayu ta ambaci sunan Allah kuma tayi godiya a gareshi bisa ceto rayuwar su da yayi ita da hirama daga hannun azzalumin sarki shaaran.
Kod jin haka sai sarki uwaisul karni yayi shiru baice komai ba.
Su kuwa sauran dakarun koda suka hango uwar mayu goye da hirama ta durfafo inda suke sai suka firgice suka hau dana kibiyoyi akan baka suka saitata.
Take uzaifat ya daka musu tsawa yace, akul dayanku ya harbeta domin yar uwarmu ce musulma.
Koda jin haka sai dakarun suka sauke bakansu kas suka cika da tsananin mamakin yadda wannan shirgegiyar aljanar ta karbi musulunci.
Ba tare da bata lokaci ba sarki uwaisul karni ya bada umarni a tafi can kusa da inda wannan kogin ya ke inda su sarki shaaran suka je suka tsaitsaya yace, ake a kafa tantuna. Amma a sami tazara ta a kalla zirai sabain a tsakani yadda dai suna iya hangosu suma haka.
Nan take kuwa aka bi umarni. Da izuwa aka iske tuni jamaar sarki shaaran sun gama kafa nasu tantunan.
Don haka suma dakarun sarki uwaisul karni sai suka hau aikin kafa nasu tantunan. Cikin kankanin lokaci suka kammal.
Gashi dai kowacce runduna tana hango kowanne bangare an zuba dakarun tsaro sun kewaye sansaninsu don gudun kada akawo farmakin sumame na bazato.
Lokacin da sarki shaaran ya shiga tantinsa ya zauna ya huta aka kawo masa abinci da giya yayi hanian sai ya tura aka kirawo masa ukashat da sazirat amma kafin su zo tuni yayi bincike a cikin hallarar tsafinsa.
Da shigowar ukashat da sazirat sai suka zauna a gefe daya suka fuskanceshi sukayi shiru. Sarki shaaran ya dubesu cikin nutsuwa tamkar bai sha wani abu na maye ba yace, abinda nakeso da ku shine ku saurara da kyau kiji abinda zan gaya muku domin idan kukayi kuskure guda daya a cikin aikin da zan baku yanzu shikenan dukkanin shirin mu ya ruguje babu wanda burimsa zai cika daa cikinmu.
Da farko dai ina so ku sani cewa ba wani abu bane yasa na tsaida wannan yaki ba face gano cewa idan aka ci gaba dashi bamu da nasara.
Domin sai an kasheni gaba dayanmu a wannan karon.
A yanzu haka daa cikin dakaruna mutum miliyan gudu an kashe mutum miliyan daya da dabi saura miliyan uku cif.
Ba komaine yasa suka sami wannan nasara ba face farmakin sumamen da suka kawo mana lokacin da jamaata ke bisa kan wannan tsauni ashe tuntuni suna labe a cikin dajin a kwance cikin duhuwa suna kallon mu sai bayan mun hau kan tsaunin sannan suka sadado suka afka mana.
A cikin binciken da nayi yanzu na ga duk wannan alamari a mudubin tsafina. Idan har muna son mu cisu da yaki kuma muje har can birnin Darul husuf mu karya katangarasu ya zamana cewa ki ukashat ka hau karagar mulki dole ne muyi abu uku.
Abu ma farko dolene muyi abinda zai dauke musu hankali anan dajin sannan mu sulale basu sani ba mu tafi izuwa birninsu koda kuwa mu ukun nanne Jal domin mu kadai zamu iya cin garin da yaki.
Abu na biyu dole ne mu sati yata gimbiya lafirat daa sansanin su domin idan har tana tare dasu zata iya musu jagora izuwa can birninmu suje su kubutar da rayuwar dakarun nan nasu wadanda muka tsare da kuma luhaira yar likita abu sharhaz a cikin gidan gonata inda aka killaceta tsawon shekara da shekaru.
Kun sani cewa bani da wani buri wanda yafi na tara da wannan yarinya luhaira amma ba zan taba samun damar hakan na sai bayan kunci birnin Darul husuf da yaki mun Kawar da musulunci mun shimfida kafirci da addininmu na tsafi.
Lokacin da sarki shaaran yazo nana a zancensa sai hankalin ukashat da sazirat ya dugunzuma ainun. Ukashat ya dubi sarki shaaran cikin damuwa yace, ya kai wannan babban sarki yanzu ta ya ya kake ganin zamu iya sato lafirat da daga cikin wancan sansanin na su uzaifat? Tayaya kake ganin zamu sulale mu tafi izuwa can birnin Darul husuf ba tare da su sarki uwaisul karni sun sani ba? Wane abune na uku wanda dolene muyi shi idan har munason musami wannan nasara akan abokan gabanmu? Domin baka baiyana mana shi ba. Saadda sarki shaaran yaji wadannan tambayoyi sai ya bushe da mahaukaciyar dariya harda bingirewa kasa tamkar nazai daina ba. Daga can sai ya tsuke bakinsa ya hade fuska yace, dangane da abu na uku wanda ban baiyan muku shiba, abune wanda bakune zaku aikatashi ba. Ba komai bane wannan abu face sato muzaira matar sarki uwaisul karni mahaifiyarka wadda yanzu haka antsareta a kurkuku sakamakon yunkurin kashe sarki uwaisul karni da tayi.
Dole ne mu satota kafin ma ka tono wadannan layu guda gudu domin itace kadai zata iya sanar dani abinda zanyi na iya hallaka sarki uwaisul karni a filin yaki.
Lallai ni da kaina zam sulale naje birnin Darul Husuf na sato muzaura.
Yanzu sai ku sake nutsuwa kiji bayanin da zan ya muku akan yadda zaku sami nasarar yin abubuwan biyu.
Na farko wato sato lafirat da tafiya izuwa birnin Darul husuf wanda a rana daya zamuyi su.
Dafarko a gobe idan gari ya waye zamu fito filin yaki na bukaci da aci gaba da yaki, amma ta hanyar zabar gwanayen sadaukanmu da nasu guda goma shabibbiyu su kara.
A gobe kuma sai a zabi mutum dari dari. A jibi kuma sai a zabi mutum dari biyar biyar. A rana ta gudu kuma mutum dubu dubu muyi yarjejeniya akan cewa haka zaaci gaba da yakin har mu karar dasu ko su sukarar da mu.
***********************
Najibullah Muhammad 🥷🥷🥷
************************

A wannan rana ta uku da za'ayi yakin mutum dari biyar daya daga cikinmu zai yi bad kama ya shiga yakin yadda ba zaa ganeshi ba.
Abinda nake bukata kawai shine ya yi iya kokarinsa ya sato gawar daya daga cikin abokam gabar ya kawo ta sansanin mu a boye ba tare da wani ya ganshi ba.
Tufafin badakaren muke so zamuyi amfani da shi idan dare yayi.
Wannan tufafi shi daya daga cikinku zai sanya a cikin daren yaje har sansanin nasu ya sato gimbiya lafirat ta kowanne hali ta hanyar amfani da dukan hikimarsa domin tsafi bazaiyo tasiri ba a cikin wannan alamari.
Idan har aka sami wannan nasara to a daren zan kirawo wani aljanina wanda zai daukemu yayi sama damu ya keta tacikin samaniya ba tare da makiya sun ganmu ba ya kaimu hat can kusa da kofar birnin Darul husuf.
A cikin daren zamu afkawa mutanen birnin mu cisu da yaki da karfin tsiya mu kafa gwamantain mu.
Su kuwa su sarki uwaisul suna nan filin yaki suna jira gari ya waye a ci gaba da yaki basu san tabargazara da muka tafka musu ba.
Yanzu a cikinku wane zai iya samo mana gawar badakaren abokan gaba kuma ya sati lafirat?
Koda jin wannan tambaya sai gardama tasarke tsakanin sazirat da ukashat kowannensu na cewa shine zai iya wannan aiki cikin nasara ba tare d an sami kuskure ba.
Koda ganin haka sai sarki shaaran ya shiga tsakanin suka yi shiru sannan ya dubi sazirat yace, ke mecece hujjarki ta ganin cewa lallai zaki fi ukashat samun nasara yin wannan aiki?
Sazirat ta yi gyaran murya tac, ya kai abbana kasani cewa ni ya mace ce saboda haka mata sunfi maza iya makirci da iya shirya tuggu.
Koda jin haka sai sarki shaaran yayi murmushi yace, naji taki hikimar. Kai kuma fa?
Ukashat yayi gyaran murya yace, ya shugabana ni babbar hujjata itace ni na fito ne daba cikin wadannan mutane don haka ni nafi sanin dukkan dakarunsu na tsaro kuma ni ne nasan dukkan sirrin su na dana tarkon kama abokan gaba. A takai ce dai da dan gari akanci gari.
Koda jin wannan batu sai sarki shaaran ya bushe da dariya tace, Tabbasa nafi samun nutsuwa d naka jawabi don haka kaine zaka yi wannan aiki nan da cikar kwana uku.

* * * * * *

A can tantin sarki uwaisul karni kuwa, kamar yadda sarki shaaran ya zauna ya gana da sazirat da ukashat haka Shima sarki uwaisul karni ya zauna tare da uzaifat da lafirat domin su tattauna danagane da yadda zasu bullowa wannan yaki domin basu san manufar sarki shaaran bisa dalilin tsayar da yakin ba, kuma idan gari ya waye basu san abinda zai zo dashi ba.
Sarki uwaisul karni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login