Showing 6001 words to 6997 words out of 6997 words

Chapter 3 - BAKIN ARTABU Book 1 Cigaban Jaruma Yazila by Madakin Gini.txt

zamu bullowa wannan yaki. Yanzu ne muka yanke shawarar mu tafi izuwa yakin amma sai gashi mutum daya yazo ya tsaida komai. Yanzu shikenan sai dai mujira har sai sa'adda yayi barci ya tashi sannan zamu tafi?"
Lokacin da sauran sarakai suka ji wannan batu sai duk ™Nasiru Muhammad™ suka goyi bayan sarki ma'aruf, fadar ta rude da hayaniya.
Shi kuwa sarki Daksur sai ya kama murmushi. Daga can sai ya daga hannu sama akayi tsit sannan yai kyaran murya yace, 'yan uwana ina so ku sani cewa sarki Uhaisu ne zai jagoranci wannan yaki da zamu je kuma dukkan nasararmu na tare da shi, idan muka kuskura muka tafi yakin babu shi tabbas baza sami nasaraba ".
Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke gaba dayan jama'ar dake cikin fadar sarkin yaki ya dubi satki daksur cikin biyayya yace, "haba ya shugabana, yanzu duk yawannan namu amma ka ce ba zamu sami nasara ba face Uhaisu ya jagorancemu? Kai da bakinka kace damu yawanmu ya ninka na abokan gaba sau dari ba. Ai kuwa ina ganin cewa koda Uhaisu ko babu shi dole ne mu sami nasara a wannan yaki. "
Sa'adda sarki daksur yaji wannan batu sai ya mike tsaye ya dubi kowa dake cikin fadar, sannan yayi ajiyar zuciya yace, "yaku 'yan uwa ina so kusani cewa ni nasan abinda babu wanda ya sanshi a cikinku nan gaba daya A halin yanzu sarkin yakimmu ta da, wato JARUMA YAZILA tana can birnin misra kuma ta karbi addininsu, don haka ita da 'yar uwarta JARUMA DABIRA zasu hada KARFI DA KARFE su yakemu.
Tabbbas su biyu kacal sun isa su iya yi mana mummunat barna a wannan yakin, domin a duk fadin wannan nashiya babu wani sadauki ko mayaki wanda wanda ya isa ya taresu face sarki Uhaisu. Ina tabbatar muku da cewa ahalin yanzu babu wani sadauki mai karfin damtse irin na Uhaisu a duk fadin duniyarnan kuma shine mutumin da baya tsafi, kuma tsafi baya tasiri a kansa domin ku gasgata zancena yanzun nan zan nuna muku ku gani da idanunku ".
Koda gama fadin haka sai sarki Daksur yayi nuni da hannunsa izuwa ga saman bangon fadar saiga hoton irin gwagwarmayar da sarki Uhaisu yayi da 'yan fashi da masu yawan gaske wadanda adadinsu ya kai dubu ™Nasiru Muhammad™ ashirin da doriya sun yiwa sarki uhaisu kawanya 'yan fashin sun kasance gabza-gabza masu kirar mutanen farko kuma kowannensu na dauke da muggan makamia lokaci guda suka yiwa sarki uhaisu rubdugu shi kuwa sai ya wanzu yana mai gididdigasu cikin tsananin zafin nama irin wanda ido bai taba ganiba.
Cikin sa'a daya jal ya ragargazasu duka dayansu bai tsira da rayuwarsa ba, sai gashi filin dajin gaba daya ya cika da gawarwakin 'yan fashin, duk inda mutum ya duba sai dai yaga jini na malala da kwaranya tamkar ruwan sama akeyi.
Babban abinda ya baiwa kowa mamaki shine ganin sarki uhaisu a tsaye bisa dokinsa cikin koshin lafiya babu inda jikinsa ya sami rauni koda kwarzanewa kuwa, kai ba ma shiba, hatta dokinsa ma babu abinda ya taba lafiyarsa.
Bayan wannan gwagwarmaya sai kuma aka ga wani azababben yaki da sarki uhaisu yayi da wadansu dodanni wadanda yawansu ya wuce misali domin ninka na wadannan 'yan fashi sau biyar. Sai da sarki Uhaisu ya shafe kwana guda da yini daya yana yaki da dodannin bai gajiba kuma bai guduba sai ragargazarsu kawai yake yi, suna zubewa kasa matattu. Yawan dodannin sai ya zama na banza ya yin da bala'I yakai bala'I da kansu suka rinka guduwa suna neman maboya.
Nan take sarki daksur ya sake nuni da hannunsa izuwa ga bangon fadar hoton komai ya bace. A sannan ne gaba dayan jama'ar dake fadar suka yi ajiyar zuciya a lokaci guda saboda tsananin mamakin ganin irin wannan a zababbiyar jarumtaka ta sarki Uhaisu wacce ko a tarihi basu taba jin taba kuma gashi jarumtaka ce ta zahiri wacce babu sihiri ko tsafi acikinta.
Nan take kowa ya sallama ya gamsu cewa lallai sarki uhaisu nezai jagoranci wannan gagarumin yaki da za a tafi izuwa birnin misra.
Sai da rana ta fadi sannan sarki uhaisu ya farka daga barci domin huce gajiyar shi. A sannan ne kuyangi suka ™Nasiru Muhammad™ kai shi kewaye suka yi masa wanka a cikin bahon zinare mai cike da ruwan kamshi na turaren miski da furanni iri-iri.
Bayan angama yimasa wanka an shafeshi da mai sai aka kawo masa kayan yakinsa ya sake sanya su ya mayar da hular karfensa yasa a kansa sannan ya taho fada yana zuwa cikin fada sai kowa ya mike tsaye don girmamawa, hatta sarki daksur kuwa. Maimakon sarki uhaisu yaje ya zauna sai dubi sarki Daksur yace, "a kawo mini dokina yanzu zamu kama hanya mu durfafi Birnin MISRA.
Batare da gardamar komai ba kuwa sarki Daksur yasa aka kawowa sarki Uhaisu dokinsa ya hau kawai sai ya kada linzamin dokinsa ya juya da baya ya fice daga cikin fadar.
Cikin hanzari sarki Daksur ya bayar da umarni ga dukkan sauran mayaka da a fita ayi hawa abi bayan sarki Uhaisu. Nan da nan kuwa aka bi wannan umarni.
Kaico! Tashin han kali ba a samasa rana.
Inda ace mutun yana wannan wuri idan yaga irin tsananin yawan wadannan mayaka da kuma irin maggan makaman da suka debo dole ne ya firgita domin gani zaiyi kamar zasu iya tashin duniya gaba dayanta a cikin rabin sa'a.
Gaba dayan mayakan da suka fito wannan yakin babu abinda suke son gani face fuskar sarki Uhaisu da kuma irin kirar jikinsa amma sai gashi har yanzu bai cire hular karfen dake kansaba kuma bai kwabe kayan yakin da suka rufe jikinsa ba su kansu kuyangin nan da suka yi masa wanka dukkansu dimaucewa sukai suka fita haiyacinsu saboda ganin irin tsananin kyawun surar da allah ya baiwa sarki Uhaisu.
MENENE ZAI FARU A WANNAN GAGARUMiN YAKI DA ZA A YI A BIRNI MISRA?
WACE CE MATAR DA SARKI UHAISU ZAI AURA? Mu hadu a BAKIN ARTABU na biyu domin jin cigaban wannan kasaitaccen labari.
==============
Domin SAMUN WASU LITTAFAN YAKU YA MANA MAGANA TA WHATSAPP 09064179602

Tags:
Littatafai (Novels)

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login