Showing 3001 words to 6000 words out of 6504 words

Chapter 2 - BAKIN ARTABU 3 Cigaban Jaruma Yazila by Madakin Gini.txt

" Sa'adda dabira tazo nan a zancenta sai sarki uhaisu ya kamu da tsananin bakin ciki gami da takaici har ya daga hannu zai mangareta sai ya kasa ya kura mata idanu kawai a lokacinda kwallar ta kaici tazo masa ya tuna cewa tunda uwarsa ta haifeshi yazo duniya ba a aba tofa masa yawu a fuskaba sai yau. Shin dama haka soyayya take, kana son mutum amma kuma shi ya tsaneka?". Sarki uhaisu ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa. Lokacin da Dabira taga sarki uhaisu ya kura mata idanu har kwallar takaici ta cika masa idanuwa sai tausayinsa ya kamata taji kamar ta gaya masa gaskiya cewar ba ita bace gimbiya yazila wacce ya kamu da tsananin sonta amma sai wata zuciyar ta haneta sarki Uhaisu ya mike tsaye ya koma gefe daya ya tsaya yana tunanin abin da zai fishsheshi. Kawai sai yaji dabira tace, "Nifa kishirwa nakeji". Koda jin wannan batu sai hankalinsa ya dugunzuma domin ya fashimci cewar babu ruwa a kusa kuma gashi dare ne sosai ga tsananin duhu a cikin dajin amma kuma sai yaji cewar ba zai iya barinta da kishirwa ba dole ne ya je ya samo mata ruwan. Kawai sai ya taho gareta da nufin ya kamata ya goyata a bayansa su tafi neman ruwan amma sai ta dakatar dashi da hannayenta tana mai daka masa tsawa tace, "Kai mufa a addininmu haramunne na mijin da ba muharraminka ba ya taba jikinka. Daga yau kada ka sake kusantata, kawai ka kwance mini hannayena na taka da kafafuna mu tafi neman ruwan tunda yanzu ko ka kyaleni kayi bazan iya komawa birninmu ba domin kaina ya juye ban ma gane a ina nake ba yanzu kuma ga tsananin duhu a wannan daji zan iya fadawa cikin wani wurin dazan iya cutuwa ko na hallaka". Sarki Uhaisu ya dubi dabira cikin alamun rashin yarda yace, "Menene tabbacin cewar idan na kwanceki bazaki cutar dani ba kuma bazaki gudu ba?" Dabira tayi dan guntun murmushi a gareshi tace, "Na rantse da girman ubangijina bazan guduba kuma bazanyi yunkurin cutar dakaiba bisa sharadi guda sharadin kuma shine ba zamu rinka kwanciya a waje daya ba daga nan har muje birninka kuma zaka kyaleni na rinka yin ibadata". Koda jin haka sai sarki Uhaisu yayi murmushi yace, "Ai wannan mai saukine, na yi alkawari duk zan yi kamar yadda kika bukata". Koda gama fadin hakan sai sarki Uhaisu ya kwance hannayen Dabira daga daurin da yayi mata ya dubeta ya ce, "Na san cewa kuna kiyaye darajar Ubangijinku da girmansa don haka na yi imanin baza ku rantse da shi ba kuma ku saba alkawarin, shi yasa na amince na kwanceki yanzu sai kizo mu tafi neman ruwa". Koda gama fadin hakan sai ya dauki ice daya daga cikin kiraren nan daya kunna wuta sannan ya nannadeshi da yankin nan na damararsa ya cinna wuta ya rikeshi a matsayin fitila dazata. Haska musu hanya ka wai sai ya nausa daji take dabira ta bishi a baya da sauri, sai da suka shafe kusan rabin sa'a suna neman ruwa basu samu ba sannan suka riski wata korama wacce ruwanta ke zubowa ta kan saman wadansu duwatsu. Ruwane garai-garai har wani irin kamshi yake mai dadi. Cikin matukar farinciki Dabira da Uhaisu suka ruga izuwa bakin kooramar suka tsugunna suka sha sannan suka dawo gefe suka zauna. A sannan ne wata irin iska mai tsananin sanyi ta fara kadawa wacce tasa jikinsu ya kama karkarwa kawai sai dabira ta dubi sarki Uhaisu a fusace tace, "Ya za a yi ka baroni da gidanmu inda na saba kwanciya a cikin daki kuma akan shimfida mai taushi kakawoni nan cikin daji inda sanyi ma zai iya lahantani? Hakika ka zalunceni kuma ka cutar da ni. Haka ake yin SOYaYYA ka cutar da masoyinka?" Koda jin wannan batu sai hankalin sarki Uhaisu ya dugunzuma ainun ya dubi dabira cikin alamun tsananin da muwa yace, "KI gafarceni ya masoyiyata yanzun nan zan magance miki wannan sanyi da ya dameki". Yana gama fadin hakan ya mike tsaye yaje ya kama saran bishiya sai da ya karyo rassa dogaye da masu kauri da yawa sannan yazo ya shiga aikin gina daki. Har ya kammala ginin dakin da itatuwa ya lullubeshi da ganye Dabira na zaune tana kallonsa kawai tana mamaki. A zuciyarta tana cewa, "yanzu kawai saboda ya kamu da soyayya yake ta wahala yake ta wahalar da kansa haka? Lallai kuwa ashe gaskiyar masu iya magana da suka ce "SOYAYYA dafice wacce in ta shiga jikin mutum bata fita har ajali" Bayan sarki Uhaisu ya gama gina dakin ice har da kofarsa ta shiga sai kuma yaje ya nemo ganyaye masu fadi da taushi yazo ya yiwa Dabira shinfida dasu a cikin dakin sannan yace ta shiga cikin dakin ta kwanta shi zai tsaya. A waje yayi gadin ta don kada wata dabbar daji tazo ta cutar da ita". Ba tare da gardamar komai ba kuwa dabira ta shiga cikin dakin ta turo kofa ta rufe tayi kwanciyarta ba tare da ta sake jin wani sanyi ba. A sannan ne fa taji tausayin sarki Uhaisu ya kamata domin ta san cewa ba karamar wuya zai shaba idan ya kwana a filin allah cikin wannan tsananin sanyin. Saukinsa daya ya hura wuta wacce zai rinka jin dumi, kuma koda wutar barci dai bazai yiwuba a wajensa kuma wannan sanyin zai iya cutar dashi.dabira taji kamar ta tashi ta bude masa dakin tace ya shigo amma data tuna cewa abune mai hadarin gaske a addinance ta kwanta da. Wani da namiji a cikin dakin sai ta fasa. A suba nayi Dabira ta farka daga barci ta bude dakin ta fito waje domin tayi alwala. Tana fitowa taga sarki Uhaisu zaune a gaban wuta yana jin dumi amma jikinsa na ta karkarwar dari kuma idanunsa sunyi jawur sakamakon rashin samun barci. Nan take taji tausayinsa amma sai ta murtuke fuska ta kau da kai ga barin kallonsa taje bakin wannan korama ta tsugunna tayi alwala sannan ta mike tsaye ta fuskanci alkibla ta tayar da sallah. Bayan ta idar da sallar ne ta shiga yin addu'o'I bata gushe ba tana yin addu'o'in har sai da alfijir ya keto gari ya fara haske sannan ta shafa addu'ar ta waigo ta dubi sarki Uhaisu tace, "Menene abin yi yanzu? Zaka nemo mini abincin kalaci ne ko kuma zamu ci gaba da tafiya ne?" Uhaisu ya dubeta cikin alamun damuwa yace, "Ki gafarceni ya masoyiyata bai kamata mu tsaya yin kalaciba anan domin ina zargin cewa mutanenku sun biyo sawummu, gwara mu kara gaba muyi nisa tukunna sai mu yada zango na nemo mana abincin kalaci". Ba tare da gardamar komaiba Dabira tace, "Na amince da hakan". Nan take suka hada nasu-inasu suka bar wannan daji suka kara gaba. Babban kuskuren da sarki Uhaisu yayi shine da bai rushe wannan daki daya gina ba kuma bai batar da ragowar wutar daya kunna ba domin sun zamo alama ta cewar suna cikin wannan daji shida gimbiya Dabira. Wannan shine abinda ya faru tsakanin sarki Uhaisu da gimbiya Dabira bayan ya satota daga gidan sarutar sarki Raihan a matsayin masoyiyarsa Jaruma YAZILA wacce ya kamu da tsananin kaunarta kuma yake son ta zamo abokiyar rayuwarsa ta har abada.
A CAN KOFAR BIRNIN MISRA KUWA, Lokacin da gari ya waye sai suka sake yin gagarumin shirin yaki suka fito filin daga. Da fitowarsu suka cika da mamakin domin gani suka yi babu kowa kuma babu komai a sansanin abokan gabar domin sun kwashe komai sun kara gaba. Al'amarin daya dugunzuma hankalin sarki Raihan, Yazila da sauran jama'arsu kenan musamman ma Humaira wacce taci gaba da kuka domin tana ganin cewa shi kenan har abada baza ta sake ganin 'yartaba Dabira. Nan take sarki raihan ya zauna da 'yan majalissarsa suka shiga taro na gaggawa don yanke hukuncin daya kamata akan bacewar abokan gaba. Sai da aka shafe kusan rabin sa'a ana ta kace-nake kowa na fadin shawararsa sannan aka yanke hukuncin abi sawun abokan gaba ataresu ahanya tun gabanninsu isa birninsu domin gara AYITA-TA-KARE yazamana cewa wannan shine yakin karshe daza a yi a tsakanin garuruwan biyu koda za a kwana ana yin BAKIN ARTABU". Nan take kuwa sarki raihan, jaruma Yazila da sauran zakwakwuran mayakan na birnin misra suka sukwani da wakansu suka nausa izuwa cikin daji da gudu domin su cimma abokan gaba. AL-AMARIN su sarki Daksur kuwa tun a daren jiya labari yazo musu cewa ai sarki Uhaisu ya shiga har birnin misra ya kai kansa bisa kamuwa da son Jaruma yazila amma an kamashi an tsare shi a kurkuku, a karshe ya gudu daga kurkukun ya kuma sace gimbiya Yazila ya tafi da ita". Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube su sarki Daksur domin sun fashimci cewar sarki Uhaisu bai karbi musulunci ba, kuma gashi ya sace Yazila ya kara karfin gabarsa da su sarki Raihan don haka har yanzu shi babban makiyi ne nasu sarki Raihan dole ne ya ci gaba da yin yaki dasu. Batare da bata wani lokaci ba su sarki Daksur suka hada nasu-inasu suka bar sansanin yakin suka durfafi birnin. Sarki Uhaisu domin suje su tayashi murnar bikin aurensa da jaruma yazila. Tabbas sun san cewa ma sai sun riga sarki sarki Uhaisu zuwa birninsa tunda shi a kasa yake ba akan doki ba don haka sai sun zaman jiransa. *** *** *** A CAN cikin daji kuwa sai da sarki Uhaisu da Dabira suka shafe sa'a bakwai suna tafiya sannan sai dabira ta ja ta tsaya cikin mamaki Uhaisu ya juyo ya dubeta yace. "Lafiya kika tsaya kokuwa kin gaji ne?" Dabira ta gyada kai tace, "Lokacin yin ibadata ne yayi" koda jin haka sai Uhaisu ya cika da tsananin mamaki bisa ganin yadda dabira bata wasa da addininta da kuma yadda tayi imani da Ubangijinta dari bisa Dari. Nan take dabira ta sami wuri mai kyau ta tayar da sallah Uhaisu ya koma gefe daya ya zuba mata idanu yana kallon yadda take yin ibadar tata. Abin da ya daure masa kai shine, ganin yadda yanayin ibadar tata yazo irin daya a ko yaushe acikin nutsuwa. Sarki Uhaisu bai daina kallon dabira ba yana sha'awar addininta har ta idar da sallar tayi addu'a ta shafa a dai-dai wannan lokaci ne hadari ya gangamo aka fara walkiya da tsawa. Al'amarin daya razana sarki Uhaisu ke nan ya dubi dabira cikin alamun damuwa yace, "Ya ke abar kaunata, yanzu idan mukace zamu tsaya mu fakewa wannan ruwa mutanenku zasu iya riskemu anan su tarwatsa dukkan shirina koda jin haka sai dabira tayi murmushi tace, "kada kadamu zan roki Ubangijina daya ki sauko da wannan ruwa har sai mun yi nisa sosai mun kusa isa birninka". Cikin alamun rashin yarda da kallon raini ya dubi Dabira yace, "Kada ki raina mini hankali mana, yanzu kina nufin zaki iya rokon Ubangijinki bukata a yanzu take kuma ya biya miki ita?" Dabira tace, "Ai ubangijina yafi gaban haka". Nan take dabira daga kanta da hannayenta sama ta kama addu'o'I. Ai kuwa tana sauke hannayenta sai hadarin ya fara dushashewa kuma nan take aka daina tsawa da walkiya da ake yi. Al'amarin da yai matukar girgiza sarki Uhaisu kenan ya kamu da tsananin mamaki fiye da ko yaushe. Take yaji kaunar addinin musulunci ta darsu a cikin zuciyarsa. Ita kanta dabira sai da ta fashinci cewar Uhaisu yaji wani abu a cikin ransa domin gaba daya jikinsa yai sanyi tamkar bashi da laka. Tafiya ma kasa yiyayi sai data yafitoshi da hannu sannan ya bita a baya suka sake nausawa a cikin daji. Hakika allah shine maiyin yadda yaso. Lokacin da Dabira ta roki allah akan ya tsaida wannan ruwan sama dake shirin saukowa sai ya amsa addu'arta kuma ya nuna ikonsa ya tsayar da ruwan a dai-dai inda suke, amma a sauran wurare a nashiyar gaba daya sai aka tsuge da ruwa kamar da bakin kwarya. Haka dai sarki uhaisu da da bira suka ci gaba da tafiya. Duk sa'adda dabira taji yunwa sai ta cije ta fadawa Uhaisu irin kalar tsuntsun da take sha'awar ci. Dole sai yaje ya farauto irin wannan tsuntsu ya kawo mata kuma shi zai yanka tsuntsun ya fige shi ya gasa mata ya bata taci. Komai kankantar aiki baza ta yishi da kantaba sai dai ta umarceshi dayi, kuma bai taba nuna gajiyawarsa ba. A cikin wannan tafiya tasu ne Uhaisu yayi ta ganin abubuwan al'ajabi atare da dabira wadanda suka shallake tunaninsa domin sau uku suna yin arba da mugayen bakaken aljanu amma da zarar dabira ta fara ambatar sunan ubangijin musulunci sai yaga aljanun sun kama da wuta sun kone kurmus ko kuma suyi sauri su bace. Haka dai suka ci gaba da tafiya har ya zamana cewa suna hango kofar birnin sarki Uhaisu, yazamana cewa ta zarar dake tsakaninsu bata wuce zira'I a shirin ba. Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai dabira taga sarki Uhaisu ya yi turjiya ya tsaya cak. A wannan lokaci suna iya hango su sarki daksur tsaitsaye a bakin kofar birnin bisa da wakai cikin matukar farinciki suna daga tutoci alamar cewa suna shirin tarbarsa. Cikin tsananin mamaki dabira ta dubi sarki Uhaisu tace, "Yaya naga ka tsaya, mai makon ka karasa da sauri tun da ga sauran 'yan uwanka can sarakai abokan gabata suna sauraron isowarka domin su tayaka murnar zuwa dani?" Koda jiin wannan tambaya sai sarki Uhaisu ya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan ya dubeta a lokacin da kwalla ta cika masa idanu yace, "Ya ke masoyiyata kiyi sani cewa ba komai ne yasa kika ga na turjeba anan ba face na sauya ra'ayina ne bisa abinda da nake shirin zartarwa akanki. Ba komai ne dalili ba face ganin tsantsar alkawari irin naku na ma'abota addinin musulunci saboda kafin mu fara wannan tafiya sai da kika rantse da girman ubangijinki cewar bazaki yi yunkurin cutar dani ba kuma bazaki gudu ba, gashi kin cika alkawarinki tunda mun iso har birnina baki saba ba. Abu na biyu har a cikin zuciyata naji na gamsu kuma nayi imani cewar babu abin bautawa da gaskiya face ubangijin musulunci, tunda agaban idanuna kin roki ubangijin musulunci a kalla sau hudu bisa bukatarki kuma ya biya miki ita nan take. Ubangijin musulunci ya karemu daga sharrin mugayen bakaken aljanu guda uku wadanda ni kaina ban isa na karemu ba da karfin sihirina ko na damtsena. Tabbas babu abin da yafi cancanta a bautawa sama da ubangijin musulunci. Inaso yanzu ki shigar dani izuwa cikin wannan addini naku mai daraja. " Koda sarki Uhaisu yazo nan azancensa sai hawayen farin ciki yazubowa Dabira, ta dubi sarki uhaisu cikin tsananin murna tace, "Hakika ka sami babban rabo. Ya kai wannan sarki ma'abocin karamci da jin kai tunda har ka karbi addinina to yanzu zan sanar da kai wani babban sirri wanda na boye maka.
BAKIN ARTABU Littafi na uku 3 Na Abdul'aziz sani madakin gini Typing:- bashir tokarawa Post:- Shuraih Usman @shuraih 99% Part D Kasani cewa ni sunana Dabira, wacce ka kamu da tsananin sonta kuwa 'yar uwata ce gimbiya Yazila wacce da itane ka fafata yaki har ka kaita kasa da nufin ka hallakata amma sai hular karfe dake kanta ta cire kayi arba da fuskarta. Na boye. Maka wannan sirri ne domin na jarrabaka na ga iyakar irin son da kake yiwa yar uwata, shiyasa nayi ta maka wulakanci iri-iri amma sai ka jure wulakancin ka ci gaba da nuna mini soyayya. Tabbas ka cancanci ka auri 'yar uwta domin kaine irin namijin da kowacce 'ya mace ke fatansamu a rayuwarta. Baya ga wannan na auna halayenka gaba daya na gane cewa kai mutum ne mai hakuri, tausayi da amana kuma mai son gaskiya. Bisa wannan daliline ma dakaga gaskiya a zahiri ka karbeta. Yanzu sai ka maimaita abin da zan karanta ma ka domin ka zama dan uwana musulmi. " Nan take dabira ta biyawa sarki Uhaisu kalmar shahada shima ya maimaita. *** *** *** Koda su sarki daksur suka hango abin dake faruwa tsakanin sarki Uhaisu da dabira suka fahinci cewa addinin musulunci ya karba sai suka kamu da tsananin bakin ciki suka kama ihu har da kuka. Kwatsam! Sai ga rundunar su sarki Raihan sun iso wajen a sukwane bisa dawakansu. Koda. Hangosu sai dabira taruga garesu ta tsaida su kuma tayi musu albishir da cewat a halin yanzu fa sarki uhaisu ya karbi addinin musulunci. Nan take farin ciki ya lullube sarki Raihan, yazila da Humaira suka sauko daga kan dawakansu suka rungume Dabira cikin tsananin murna bisa ganinta araye cikin koshin lafiya. Nan take Dabira ta kama hannun jaruma Yazila taja ta takaita har gaban sarki Uhaisu ta dubeshi tace, "Wannan ita ce masoyiyarka ta kwarai wacce zuciyarka ta kamu da tsananin sonta". Kawai sai yazila da Uhaisu suka kurawa juna idanu suna murmushi cikin farin ciki mara misaltuwa. A dai-dai wannan lokaci ne sarki Raihan ma ya sauko daga kan dokinsa ya ruga wajen sarki Uhaisu. Yana riskarsa suka rungume juna. Sarki Raihan ya kankame Uhaisu yana cewa, "Da ga yau kazama dan uwana na jini kuma na ba ka YAZILA" Cikin tsananin murna sarki Uhaisu ya durkusa bisa gwuiwowinsa da nufin yayi godiya amma sai sarki Raihan ya kama kafadunsa ya tasoshi sama sannan ya dubeshi yace, "Yanzu ga abokan gabarmu can akofar birninka suna kuka da bakin ciki bisa karbar addininmu dakayi, yanzu wana irin hukunci kake ganin yakamata muyanke musu?". Koda jin wannan tambaya sai sarki Uhaisu yayi murmushi yace, "kwantar da hankalinka ya kai sirikina kasani kura tasan gidan mai babban sanda, zabi biyu zanbasu yanzu, bani doki kagani" Batare da gardamar komai ba sarki Raihan yasa akakawowa sarki Uhaisu wani ingarmar doki ya hau, ka wai sai ya zaburi dokin da gudu ya nufi kofar birninsa. Saida ya rage bai fi tazarar kamu goma ba a tsakaninsa dasu sarki Daksur, kawai sai Uhaisu ya zare takobinsa sama ya daga murya yace, "Yaku wadannan sarakai kuyi sani cewa ni yanzu bana daga cikinku na karbi addininsu mai daraja wanda shine addinin

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login