Showing 6001 words to 6504 words out of 6504 words

Chapter 3 - BAKIN ARTABU 3 Cigaban Jaruma Yazila by Madakin Gini.txt

gaskiya. Ina mai kira a gareku daku tuba ku daina bautar gumaka da aljanu kuzo ku rungumi addinin gaskiya, idan kuma kunki sai mu gwabza yakin karshe muda ku yanzu a ga wanda zai rinjayi wani. Ni kam na tabbata da cewa ko yaushe gaskiya ce akan karya. " Yana gama fadin hakan sai ya kada linzamin dokinsa ya juya da baya da gudu a sukwane ya koma can inda rundunar su sarki Raihan take ya juya yana kallon su sarki Daksur yana sauraron yaji hukuncin da suka yankewa kansu. Kawai sai sarki Daksur ya shiga cikin tsakiyar 'yan uwansa sarakai suka yi kus-kus suna gama tattaunawa ne suka zare makamansu suka sakarwa dawakansu linzami suka taho da gudun tsiya izuwa inda rundunar su sarki Raihan. Koda ganin haka sai sarki Uhaisu ya daga takobinsa sama yana mai yiwa su sarki Raihan nuni da a tari abokan gaba. Nan take kowa ya zare takofinsa ya sakarwa dokinsa kaimi aka tari abokan gaba. Musulmi suna kabbara, kafirai suna ihu aka hadu a tsakiya aka cakude. Nan fa aka ruguntsume da azababben yaki mai ban tsoro. Kura ta turnuke wajen gaba daya, ihun mazaje, haniniyar dawakai da karafkiyar karafa ta cika dodon kunne sai da rana ta fadi magariba ta doso kai ana ta yin wannan BAKIN ARTABU sannan aka karar da gaba dayan wadannan kafirai. Duk wanda ka duba a cikin musulmi sai kaga jikinsa ya rine gaba daya da jini, kuma kusan kowa ya sami rauni a jikinsa. Tabbas allah ya Nuna ikonsa a wannan yaki tunda kafirai sun ninka musulman yawa sau kamar goma amma sai gashi musulman ne dai suka yi nasara. Nan dai aka bude birnin, sarki Uhaisu ya yiwa su sarki raihan jagora suka shige ciki gaba daya. Nan take. Wannan lokaci sarki Uhaisu ya kaddamar da ADDININ MUSULUNCI a birnin nasa kowa ya musulunta sannan aka yiwa mutane magani bisa raunikan jikinsu. Kashe gari aka sake dunguma aka koma birnin misra inda acan ne aka daura auren sarki UHAISU da jaruma YAZILA ita kuma jaruma DABIRA ta auri wani sadaukin jarumi mai suna BASHER IBINI ISHAQ a she sun dade suna soyayya a boye batare da kowa ya saniba a garin. Nan dai sarki Uhaisu yayi sallama gasu sarki raihan ya dauki amaryarsa JARUMA YAZILA ya tafi da ita izuwa birninsa cikin tsananin farin ciki. Can birnin sarki Daksur kuwa da sauran biranen da aka ci sarakunansu da yaki duk sai da sarki Raihan ya taka da kafarsa tare da dumbin dakaru masu take masa baya suka je kowanne birni suka kafa tutar musulunci, kuma suka nada shugabanni masu adalci da tsoron ALLAH. Har yau har gobe gaba dayan kasashen dake wannan nashiya sun zama birane na MUSULUNCI, kuma duk gumakan dake nahiyar sai da aka konesu gaba daya. TAMMAT BIHAMBULLAH. KARSHE. Alhamdudila muna godiya ga allah madaukakin sarki da ya bani ikon kawo muku wannan littafi JARUMA YAZILA da cigabansa BAKIN ARTABU lafiya allah ya kara daukaka musulunci da musulmai. TAMBAYA ME KAFASHIMTA DANGANE DA WANNAN LITTAFIN?

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login