Showing 3001 words to 6000 words out of 7064 words

Chapter 2 - Sa Maza Gudu Book 2 Hausa Novels by Madakin Gini.txt

tsaya a gabansu dakarunsa
kuma suka yiwa bayin KAWANYA,nan take Malika
ta dubi Zarhus tace ina dukiyata?Zarhus na jin
wannan tambaya sai ya sauko daga keken
shanun
ya bude akwati ta biyu ya cire shimfidar sama
mai dauke da matattun kwari,sai ga lu'u lu'u
birjik a kasan mai yawan gaske wanda ya isa
Malika ta biya gaba daya kudin da aka siyar mata
da bayin gaba dayansu har sarki Hilairu
kuwa.Koda Yarima Lahaman da dakarunsa sukayi
arba da wannan duki mai yawa haka,sai suka
cika
da tsananin mamaki yadda akayi ta
mallaketa.Kawai sai Malika ta dubi Lahaman
tace,kasa yaranka amintattu su debi iyakar kudin
daka siyar mini da wadannan bayi duka su bar
mini ragowar.Cikin rawar jik Lahaman ya dubi
wasu mutum biyu daga ckin su yace,ku kirga
adadin dinare dubu dari biyar da kuma dinare
dubu hamsin sau dari.Nan taje kuwa dakarun
biyu suka shiga kirga lu'u lu'u suna zubawa a
cikin buhu saida suka shafe sa'a uku suna
wannan aiki sannan suka kammala amma duk da
haka sai da suka gama dibar iyakan adadin da
aka umarce su kuma suka rage kudade da
yawa.Bayan an dankawa yarima Lahaman ya
karba yana ta farin ciki da walwala sannan an
saki bayin sunzo bayan Malika sun tsaya.Sai
Malika ta bude ragowar akwatunan da hannunta
sai gashi kowacce akwati cike take da dinare da
lu'u lu'u fal wadanda in da za'a bawa mutum
guda daya jal to zai shafe shekaru dubu a
rayuwarsa yana cin abinci yana sa irin suturar
dayake so yana walwala batare da sun
kareba.
Koda Yarima Lahaman ya kyallara ido
yaga
wannan dukiya mai dumbin yawa sai kishi ya
turnukeshi gami da tsananin mamaki yadda akayi
Malika ta tara wannan dukiya.Shidai ya sani
cewa
babu yadda za'ayi sarki Sharkuf ya iya bata duk
irin tsananin son da yake mata saboda ya
kasance mutum mai kwatanta adalci a tsakanin
'ya'yansa.Bayan Malika ta gama nunwa Yarima
Lahaman wannan dukiya sai ta dubeshu tace,Ya
kai Yarima ashe burinka gajere ne ban sani ba.A
zatona zaka bukaci dukiya mai yawan da tafi
wannan danazo da ita,kuma tabbas dana baka na
sake baka wata ninkinta,saboda ina da ira ninkin
baninkin.Ina so ka sani cewa ni Gimbiya Malika
MURUCIN KAN DUTSE nake ban fito ba sai dana
shirya.Kabar ganin cewa babu kamarka a
harkokin cinikin bayi a wannan nahiyar har kayi
tunanin cewa kafi kowa kudi da arziki.,to ina mai
tabbatar maka da cewa ni Malika a halin yanzu
na tara dukiya da baka da kaso daya cikin
gomanta.Duk harkokin na cinikin abinci dana
kayan yaki da ake yi da manyan Kasashen duniya
a wannan zamani nice babbar dilar da babu
kamarta.Itama harkar cinikin bayin ka zauna
cikin
shiri kwanan nan zan karbeta na zama na ni ke
sarrafata a duniya,ba don komai ba sai domin
nayi maganin manyan azzalumai irinku.Yanzu dai
gani ni kadaice na zo babu wani badakare ko
guda daya daya rakoni don bani tsaro.Idan ka
gadama ka turo min gaba daya dakarun naka su
tare mini hanya kafin na isa cikin gari suce zasu
kwaci wannan dukiya da wadannan bayin dana
siya wajenka.Na rantse dabgemun Mahaifinmu
dayansu bazai tsira da rayuwarsa ba.Idan kuma
kana ganin cewa kai ne da kanka zaka tareni to
ina jiranka ai KAR TA SAN KAR ce kuma shege
ka
fasa.Koda Malika tazo nan a jawabinta sai ta
dubi
su sarki Hilairu tace,wuce gaba mu tafi izuwa
inda
zan ajiye ku.Cikin tsananin farin ciki su sarki
Hilairu suka wuce gaba sannan Malika ta hau kan
keken shanu Zarhus ya tuka suka bi bayan su
Hilairu.Dama tunda Gimbiya Malika ta fara
bayaninta ga Yarima Lahaman sai jikinsa ya
kama
tsuma,idanunsa suka kada sukayi jawur ya kamu
da tsananin bakin ciki kuma ya rinka ji kamar ya
zare takobinsa yaje ya afka mata da yaki,amma
sai ya daure ya hakura sa'adda ta fadi kalma
mai
zafi da muni a gareshi sai dakarunsa su yunkuro
zasu afka mata,amma sai ya dannesu,saboda
yasan cewa AJALIN su zasu gaiyata kuma shi
kansa bazai iya karesu ba da komai.Har Saida
Malika tayi nisa da barin kofar wannan gidan
nasa
har ya daina hangosu ita da dukan bayin data
siya a hannunsa,sannan ya takarkare ya kwarar
uban ihu mai tsananin ban tsoro sannan kuma ya
durkushe kasa bisa guiwowinsa ya fashe da
matsanancin kuka na bakin ciki.Adaidai wannan
lokaci ne hadari ya gangamo aka fara tafka
walkiya da tsawo amma saboda tsananin bakin
ciki sai Yarima Lahaman yaki tashi ya shiga cikin
wannan gida nasa.Aikuwa take aka tsuge da
ruwan sama kamar da bakin kwarya,koda ganin
yadda ruwa yake dukan Yarima Lahaman kuma
gashi ruwa ne mai karfin gaske dauke da iska,sai
daya daga cikin wannan dakarun nasa ya matsa
daf dashi yace,ya shugabana zaifi kyau ka tashi
daga cikin ruwan nan domin zai iya cutar da
lafiyar...Kafin badakaren ya gama rufe bakinsa
tuni Yarima Lahaman ya shammaceshi cikin
bakin
ZAFIN NAMA ya zare takobinsa ya share masa
makogwaro,kawai sai gani akayi jini yayi feshi
daga cikin wuyan badakaren sannan ya fadi
matacce.A sannanne Yarima Lahaman ya mike
tsaye ya goge jinin dake jikin takobinsa akan
gawar badakaren sannan ya mayar da takobin
cikin kufe ya daga kansa sama yayi KURURUWA
mai razanarwa tamkar zaki yayi GUNJI a
dawa.Nan take duk wani abu mai rai dake kusa
ya dimauce,hatta ragowar dakarunsa dake tsaye
a
wajen da wanda ke cikin gidan saida suka firgice
suka rikirkice suna neman su cika wandonsu da
iska,amma sabida tsoro sai suka kasa guduwa
izuwa ko ina.A sannanne Yarima Lahaman yayi
rantsuwa da darajar uwarsa yace,daga yau
Malika
baza ta sake yi masa wulakanci ba,kuma komai
dadewa sai ya kasheta da hannayensa ya huce
takaicinta,koda samun nasarar yin hakan na nufin
mutuwar duk wani abu mai rai dake cikin kasar
nan.Yana gama fadin hakan sai ya mike tsaye ya
shige izuwa cikin wannan gida nasa.
Al'amarin Gimbiya Malika kuwa lokacin da suka
yi
dan nisa ga barin gidan Yarima Lahaman tare
dasu sarki Hilairu itana bisa keken shaun su
kuma
suna tafiya a kasa bisa kafafunsu kuma taga
hadari ua gangamo an fara walkiya,sai ta bayar
da umarni aka rugu cikin wani kogon dutse domin
a fake.Ai kuwa suna gama shiga cikin kogon
dutsen nan ruwan saman ya tsuge,nan fa
kowannansu maza da mata ya sami wuri ya
zauna,aikuwa aka fara ruwan saman mai dauke
da iska mai sanyi ya addabi kowa.Koda ganin
haka sai Malika tayi amfani da karfin sihirinta na
tsafi ta kunna wutar jin dumi har guda uku.Daya
sai gaba dayan matan suka kewayeta dayar
kuma
sai mazan suka kewayeta,ya zamana cewa zaura
wutar guda daya babu kowa a gabanta,shi kansa
Zarhus tuni ya zaro bargo a cikin keken
shanunsa
ya kwanta ya lullube jikinsa gaba daya.Nan fa ya
rage saura Gimbiya Malika da sarki Hilairu a
tsaye
a can gefe daban daban suna kallon juna,kuma
suna kallon wannan wuta guda daya data rage
wacce babu kowa a gabanta,kamar hadin baki
sai
duk su biyun suka taho izuwa gaban wutar a
lokaci guda suka zauna suna jin dumin kuma
suna
fuskantar juna.Tsawon 'yan dakiku dayansu bece
uffan ba kawunansu na sunkuye suna kallon
kasa.Kawai sai suka dago kai a tare kuma
kowannasu ya bude baki da nufin yace wani
abu,koda muryoyinsu suka sarke a lokaci guda
sai
suka kyalkyale da dariya saboda mamakin yadda
al'amarin ya kasance haka.A sannane Gimbiya
Malika ta dubi Sarki Hilairu cikin murmushi mai
taushi tace,ya kawai wannan saurayi Ma'abocin
kyau da kwarjini waye kai kuma yaya akayi ka
tsinci
kanka a cikin wannan rayuwa ta bauta?Kasani
cewa
a karon farko dana ganka jikina ya bani cewa ka
fito
daga babban gida kuma asalinka baka kasance
bawa ba.Koda Malika tazo nan a zancenta sai
taga
hawaye a zubowa sarki Hilairu,al'amarin daya
karya
zuciyar kenan taji ta kara kamuwa da tsananin
tausayinsa.Ta dubi Sarki Hilairu cike da tsananin
tausayi tace,yakai wannan sarki me yasa kake
zubar
da hawayenka alhalin ka tsira daga hannun dan
uwana kuma kasan cewa bazan taba cutar dakai
ba,kayi sani cewar bana kubutar dakai bane don
cutarwa,na kubuto daku ne domin tsirar daku
daga
cikin kangin da dan uwana zai saka ku a
ciki.Koda
Sarki Hilairu yaji wannan gada Gimbiya
Malika,saiya
girgiza kai ya saka hannu wansa ya share
hawayensa ya dubeta duba na tsanake sannan
yace,yake wannan gimbiya kiyi sani cewa ba ina
kuka bane don shiga halin dana kasance a ciki
ba,kuma banajin shakkar komai daga gareki na
tabbata kin kasance mace mai tausayin na kasa
dake.Wannan kuka da kikaga inayi inayinsa ne
kawai don rasa matata danayi sannan kuma ina
mutukar tausaya miki dake da mahaifinki da
kuma
sauran al"ummar wannan birni gaba daya.Koda
dayazo nan adaidai zancensa sai Gimbiya Malika
ta
dago kai a cikin kidima ta dubeshi domin batasan
wane irin tausayi ne Hilairu yake musu ba alhalin
sun kasance basu da wata lalura data
addabesu,babu fari bare wata cuta data kunno
kai
cikin kasarsu.Don haka cikin azama ta dubeshi
tace,yakai wannan sarki sanar dani dalilin dayasa
kake jin tausayinmu,meya faru haka da har ka
kasance cikin tausaya mana alhalin da
idanuwankan
kaga ni babu rashin ci da sha a cikin birninmu
sannan babu wata rashin lafiya uwa uba kasarmu
tana dauke da mayakan da a kaf nahiyar nan ba
a
isa a zo aga bayansu ba.Tana zuwa nan a
zancenta
sai Hilairu ya tareta dacewa,ko kina da labarin
SA
MAZA GUDU?Gimbiya Malika tayi shiru tana
tunani a
cikin ranta ta girgiza kai alamar batada
labarinsa.Sarki Hilairu yace,dakina da labarin SA
MAZA GUDU dana sanar dake dalilin dayasa nake
tausaya muku,amma idan kin koma cikin gidan
sarauta ki tambayi mahaifinki wanene SA MAZA
GUDU,in har ya sanar dake kadan daga cikin
labarinsa ni kuma zan sanar dake dalilin da yasa
nake tausayinku nake jin kanku badon komai ba
sai
don kyautatawa dakika yimin.Gimbiya Malika
takara
zuba masa idanu tana mamakin maganganunsa
gareta tace,yakai wannan sarki ina bukatar ka
sanar
dani. ko kadan daga ciki kafin naje ga mahaifina
na
tambaye shi wanene SA MAZA GUDU,inason
kafara
sanar dani ko yaya ne sannan ka sanar dani
dalilin
dayasa kake tausaya mana.Kodajin haka sai sarki
Hilairu ya daga kai yace zan sanar dake kadan
daga
cikin alakarmu dashi,amma labarinsa sai idan
kinje
kin tambayi mahaifinki ya karasa miki sani
akansa.Dajin haka sai takara gyara zama tana
mai
sauraronsa shi kuma ya ciga da cewa................
SA MAZA GUDU
Littafi na biyu(2)
Part B
Dajin haka sai ta kara gyara zama tana mai
sauraronsa shi kuma ya ci gaba da cewa:
SA MAZA GUDU guguwa ce wadda batada abin
tarewa a duk sa'ilin data nufo kasa ko
nahiya,bata tsawaita,sannan masiface babba a
cikin rayuwar duk wani mai rai dake doron
duniya,ba'a fatansa ba'a kuma marmarin
ganinsa.Duhu ne shi mai mamaye duk wani
haske,masiface shi mai tattare da dukkanin
masifa yake wannan Gimbiya,ki sani cewa
wannan runduna ta SA MAZA GUDU bata da kula
kan duk abinda ta sako shi a gaba,tana da ta'adi
ga duk wanda ta fuskanta bata barinsa sai taga
ta bata cikin kasarsa da jini,tayi masa ado da
naman sassan bil'adama.Ina son ki sani cewa
wannan sadauki da ake kira SA MAZA GUDU dan
uwa ne a gareni wanda muka fito ciki daya,kuma
a duniya bashi da wanda yake so sama dani don
haka yabar ni akan mulkin kasar mu ya fita
duniya.Zan cigaba da baki labarinsa a lokacin da
kika samu saninsa daga mahaifinki.Sann
an kuma
ya cigaba da sanar da ita yadda Yarima Lahaman
ya kashe masa matarsa a daren farkon
amarcinsu
bayan yayi mata fyade,wacce ta kasance tana
tsananin kama da ita.Da yadda Yarima Lahaman
tare da dakarunsa suka yita kashe mutane a
birninsa suka kwashe dukiyoyinsu suka kone
gidajensu kuma suka maishe dasu bayinsu.Koda
Sarki Hilairu ya gama baiwa Gimbiya Malika
wannan labari sai taji ta kamu da tsananin
tausayinsa dana jama'ar sa fiye da koyaushe
kuma taji sonsa ya karu ninki baninkin a cikin
ranta don haka bata san sa'adda hawaye ya zubo
mata ba,ta dubi Sarki Hilairu ta kwashe nata
labarin ta zaiyana masa har duk irin kiyayyar
dake tsakaninta da dan'uwanta Yarima
Lahaman,da irin GWAGWARMAYAR data sha a
rayuwa domin ta kare kanta daga sharrin
Lahaman da kuma kokarin kawo rugujewar
dukkan mugun nufinsa a nahiyar gaba daya.Daga
karshe sai ta dube shi tace,yakai wannan sarki
mai daraja kayi sani cewa ban siyeka ba a
matsayin bawa na,na saye kune domin kubutar
daku daga sharrin dan uwana Yarima Lahaman
saboda nasan cewa sai ya tarwatsaku ya siyar
daku ga mutanen daza su rarrabaku izuwa
sassan
duniya yanda har abada da yawanku bazasu sake
ganin juna ba.Nayi muku alkawari indai ina raye
kuma ina da koshin lafiya saina taimaka muku
kun fita daga wannan nahiyar lafiya kun koma
izuwa kasarku ta haihuwa kun sake gina birninku
kunci gana da rayuwarku kamar yadda kuka
saba.Duk abinda kuke bukata na kudi zan
taimaka
muku dashi,kuyi sani cewa yau saura kwana uku
kacal nayi shiri na bar kasar nan saboda haka
kuma saiku zauna cikin shiri domin tare zamu
bar
kasar nan.Lokacin da Malika tazo nan a
jawabinta
sai farin ciki ya lullube sarki Hilairu da dukkan
jama'arsa.Suka kama yi mata godiya da jinjina
suna shewa daga can sai sarki Hilairu ya dubeta
cikin alamun damuwa da fargaba yace,yake
wannan yar Sarki mai adalci yanzu bakya tunanin
cewa wannan dan uwa naki bazai shirya tuggun
da zai raba mu dake ba ba,bare har kin sami
damar taimakonmu?Koda jin wannan tambaya sai
Gimbiya Malika tayi murmushi sannan tace,idan
har kaga wani tsautsayi ya sameku to tabbas
nima ya sameni,idan har kayi imani cewa ni mai
kaunace a gareku ba mai cutarwa ba to tabbas
zaku tsira da mutuncinku,rayuwarku
daafiyarku.Abinda nake bukata daku kawai shine
kuyi duk irin umarnin dana baku,kada ku kuskura
kuyi wani abu daban bisa yin kanku face bisa
izinina da umarnina.Koda Gimbiya Malika tazo
daidai nan a zancenta sai suka ji an dauke ruwan
saman dake ta tafkawa yayi dif tamkar ba ayiba
har wasu daga cikin jama'ar sarki Hilairu sun
yunkura zasu fita daga cikin kogon dutsen sai
Malika ta daka musu tsawa tace,ku koma ku
zauna ashe bana gaya muku cewa kada kuyi
komai ba sai bisa umarnina.Koda jin haka sai
kowa ya koma inda yake ya zauna suka shiga
taitayinsu,Malika ta mike tsaye tsam ta fito waje
daga cikin kogon dutsen,tana fitowa saita tsaya
cak ta kasa kunnuwanta sosai tana sauraran duk
wani sauti dake cikin dajin kuma ta dubi gabas
da
yamma,kudu da arewa kawai sai taji a jikinta
cewar akwai sauyin yanayi a cikin dajin wanda
bata gamsu dashi ba,don haka sai kawai tayi nuni
da hannunta izuwa kofar wannan kogon dutsen
wanda su sarki Hilairu ke ciki.Nan take wata irin
yanar tsafi mai kauri ta lullube kofar yadda babu
wani abi da zai iya ratsawa ta cikinta.Faruwar
hakan ke da wuya kuwa sai taji takun sawaye da
yawa a saman kan duwatsu ana gudu alamar
cewa akwai mutane da yawa kewaye da wannan
kogon dutse,kwatsam saitaji hucin kibiya ta taho
da gudu zata soketa a kirji,cikin ZAFIN NAMA
tasa
hannunta ta cafe kibiyar kuma ta cillata izuwa
saitin inda aka harbota kawai sai tajiyo ihun
kato,saiga wanda kibiyar ta caka ya sallamo daga
can saman dutsen dake gabanta ya fado kasa
tim
a gabanta ya zama gawa alokacin da jini ke
kulbulowa daga cikin kirjinsa sakamon kibiyar
data cake masa da hannunta tayi masa KAIKAYI
KOMA KAN MASHEKIYA.Faruw
ar hakan keda wuya
saiga dakarun sumame a cikin shigar bakaken
tufafi kuma sun rufe fuskokinsu su da yawa suka
baiyana akan duwatsun a saman Malika kuma
dukkaninsu sun dana kibiya akan bakansu sun
saitota.Ba tare da wata alama ta fargaba ba ko
tsoro sai Gimbiya Malika ta gyara tsayuwarta
tana
kallonsu kawai.Nan take shugaban dakarun
sumamen ya daga hannunsa sama yama mai
bayar da umarnin a sakar mata harbi,aikuwa sai
gaba dayan dakarun sumamen suka harbowa
Malika kibiyoyin,nanfa suka ga abin Al'ajabi
saboda duk kibiyar data durfafeta take take
ruburbushewa tazama gari.Koda ganin abinda ya
faru sai shugaban dakarun ya zare takobinsa
take
sauran yaran nasa sukayi koyi dashi suka dako
tsalle kasa suna masu dira bisa kafafunsu suka
rutsa ta da makamansu alhalin ko tsinke babu a
hannunta da sunan makami wanda zata kare
kanta.Lokaci guda suka afka mata gaba dayansu
da nufin suyi mata rubdugu su daddatsa sassan
jikinta.Cikin wani bakin zafin nama Malika tayi
wani irin katantanwa a kasa ta buge kafafun
dakarun sumamen dake gabanta duk suka zube
kasa.Kuma ta taso sama kamar an harbota tayi
fanka da kafafunta akan fuskokin dakarun
sumamen dake samanta ta tarwatsa su da karfin
tsiya kuma tayi wuf ta cafe takobin daya daga
cikinsu.Kafin ta duro kasa ta hausu da SARA DA
SUKA,nanfa wurin ya hargitse aka ruguntsume da
AZABABBEN YAKI yazama cewa duk inda Malika
tasa gabanta saidai kaga maza na zubewa kasa
tamkar ana sassabe gona.Nanfa ihun mazaje ya
cika dodon kunne jini ya rinka feshi da
fantsama,karafkiyar karafa ta cika dodon kunne
yazama cewa yawan dakarun sumamen yazama
na banza amma saboda suna da bakin naci da
kuma taurin rai sai gashi indai ba kawunansu
Malika ta sara ba bata samun nasara.Aka cigaba
da gumurzu sannan kuma sai suka rinka rugowa
da gudu izuwa kofar wannan kogon dutse domin
su shiga ciki su hallaka su sarki Hilairu,amma
duk wanda ya sari wannan yana mai kauri wacce
ta lullube kofar kogon sai yaji kamar dutse ya
sara domin kuwa tarwatsin wutane ke tashi
tamkar karfe da karfe ne suka hadu kuma
takobin nasu ke dakushewa.Saida aka shafe
sama da sa'a hudu ana yin wannan masiffafen
yakin tsakanin Gimbiya Malika da wadannan
dakarun sumamen yazama cewa ita bata karar
dasu ba,su kuma sun kasa koda lakutar jikinta
kuma sun kasa shiga cikin wannan kogon
dutsen.Koda shugaban dakarun ya lura da cewa
Gimbiya Malika tayi musu mummunar barna don
ta kashe masa yara sama da guda dubu daya,sai
yayi sauri ya zaro wani karamin kaho ya
busa,take gaba dayan dakarun nasa suka dira
akan saman duwatsu sukabar Malika a tsaye ita
kadai jini na diga a jikin takobinta,kawai sai
shugaban dakarun ya diro kasa kusa da ita suka
fara kallon kallo.Shidai wannan shugaban
dakarun sumamen ya kasance narkeken kato mai
kira irinta mutanen farko domin tsayinsa ya ninka
na gimbiya Malika sau biyu kuma ya kasance
kakkaura mai fadin kirji gami da lafta kaftan
hannaye.Koda ya tsaya a gaban Malika sai ta
zama yar kankanuwa tamkar an ajiye dan tsako a
gaban shirwa,duk dacewar Malika ta yarda da
kanta tasan cewa ita jaruma ce ta kwarai saida
ta dan razana ta dan ja da baya.Nan take
shugaban dakarun ya kama rigarsa da hannu ya
tsarge ta daga sama har kasa,yayi wurgi da ita
saiga damatsan sa da kwanjinsa sun baiyana kai
kace duwatsu aka cuccura aka lika masa ajikin
nasa ga kuma tarin jijiyoyi sun tashi sunyi burdin
burdin kai da gani kasan cewa dole ne a sami
gagarumin karfi a tare dashi.Kawai sai ya zare
wadansu tagwayen adduna daga jikin guibin
cinyoyinsa dama da hagu.Addunan sun kasance
masu fadi da tsananin kaifi.Shugaban dakarun ya
gyara tsayuwa yana mai bude hannayensa
alamar cewa a shirye yake a fara kafsawa.Koda
ganin haka sai itama Malika tayi wuf ta suri wata
takobi dake kasa wato ta hada gud biyu
hannunta ta gyara tsayuwarta tana mai
fuskantarsa.Bayan sunyi kallon kallo na tsawo
dakiku sai suka rugo da gudu izuwa kan juna a
tare suka kacame da azababben yaki.
Wohoho idan jarumta ta hadu da jarumta kuma
gwaninta tayi karo da takwaranta tofa dan kallo
ya shigo tashin hankali bare wata halitta mai rai
data ra'bi kusa da inda ake gumurzun.Koda
Malika da shugaban dakarun suka fara kawai
junansu sara da suka cikin zafin nama,juriya da
bajinta sai nan da nan suka tashi hankalin
bishiyoyin da dukkan duwatsun dake wajen domin
kakkaryewa da farfashewa suka
kamayi,sakamakon masifar kaifin addunan
shugaban dakarun da kuma nauyin saransu.Nan
fa tarwatsin wuta da hayaki ya cika wajen ya
addabi sauran dakarun sumamen dake sama bisa
duwatsu suna kallon wannan bakin artabu.Nanfa
Malika ta gane cewa ta gamu da gamonta domin
bata taba jin mutum mai nauyin sara da iya yaki
ba kamar wannan shugaban dakarun face
mahaifinta sarki Sharkuf.Duk sa'adda ya kawo
mata sara ta kare da takubban hannayenta biyu
saita durkushe kasa bisa guiwarta guda ko duka
biyun ma saboda nauyin saransa.Badan ma tana
da mutukar zafin nama ba gami da juriya da naci
da tuni ya zargeta gida biyu.Duk da haka wani
lokacin yana samin nasarar gabza mata naushi
ko
bugu da hannu da kafa ta kife kasa amma sai
tayi
wuf ta mike tsaye su cigaba da fafatawa.Lokacin
da Malika ta fahimci cewa idan fa suka cigaba
da
gumurzu a wannan yanayi zai sami nasarar
galabaitar da ita,idan kuwa ta galabaita take zai
hallakata,nan take ranta ya baci ta tuna cewa
wadannan dakarun sumame Yarima Lahaman ne
ya turosu domin su hallakata kuma su hallaka su
sarki Hilairu,idan kuwa hakan ta faru karshen
adalci da zamam lafiya yazo karshe a nahiyar
gaba daya tunda dai shi ma Sarki Sharkuf girma
ya kama shi,a kodayaushe ajali zai iya riskarsa
ya
zama cewa babu wanda zai iya takawa Lahaman
birki.Koda gama aiyana hakan a cikin ranta sai
zuciyarta ta kama tafarfasa kamar zata kone nan
taje

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login