Showing 6001 words to 7064 words out of 7064 words
Chapter 3 - Sa Maza Gudu Book 2 Hausa Novels by Madakin Gini.txt
taji wani irin gagarumin karfi ya shigeta don
haka sai ta faki numfashin shugaban dakarun ta
daka tsalle sama a lokacin da ya kawo mata
wani
mummuna suka da adda tagoce a saman ta
gabza masa wasa naushi a fuska da dukkan
karfinta.Take hakorinsa guda daya daga cikin
bakinsa yayi fitar burgo gami da feshin jini
saboda
karfin naushin sai gashi ya ya fadi kasa dukda
girman nasa.A lokacin dayaji jiri ya kwashe
shi,kafin ya mike tsaye tuni Malika ta dako tsalle
sama ta dira akan kirjinsa kuma ta soka masa
takobi guda a cikin bakinsa.Aikuwa sai takobin ta
bullo ta keyarsa ta cake cikin kasa jini na
bulbulowa.Koda sauran dakarun sumamen suka
ga abinda ya faru ga shugabansu sai suka firgice
suka tarwatse izuwa cikin jejin da gudu domin su
tsira da rayukansu.Ita kuwa Malika sai ta bingire
kasa daga kan gawar shugaban dakarun ta kama
haki har tana furzar da gudan jini daga cikin
bakin nata saboda tasabar lugudan naushin da
tasha,saida ta huta sosai sannan ta iya mikewa
tsaye taje tayi nuni da hannunta izuwa ga
wannan yana data lullube kofar kogon
dutsen.Take yanar ta bace bat Malika ta kunna
kai cikin kogon dutsen tana tafe tana layi da
tangadi kamar zata fadi kasa ga jini na yoyo a
hancinta.Koda su sarki Hilairu hangota taho
garesu a cikin wannan hali sai suka firgice,Sarki
Hilairu bai san sa'adda ya mike tsaye ba zumbur
ya rugu gareta,kafin ya isa wajenta ta langabe
zata fadi kasa,amma sai yayi sauri ya cafota ta
sume akan kirjinsa.Nan da ya dauketa a dimauce
yazi ya kwantar da ita suka shiga kokarin ceto
rayuwarta saboda tuni a wannan lokacin
numfashinta ya dauke kuma ba komai ne ya
haddasa hakan ba face mugun naushin da
wannan shugaban dakaru ya jera mata akan
kirjinta ba,in badon ma ta kasanace
BASADAUKIYA
ba da tuniya ya karya kasusuwan kirjinta,duk da
haka jini ne ya kume mata daga cikin kirjin nata
shi yasa tashiga wannan mugun hali.Sa'ae da
akayi daga cikin matan dake wajen akwai
likita.Koda likitar tayi nazarin jikin Malika ta gane
cewa tasha naushi da bugu a kirjinta sai nan
take
tasa akaje aka tsinko mata wadansu ganyaye a
cikin daji da yan dabaru aka hada murhu aka
dora tukunya aka dafa ganyayen sannan bayan
ruwan maganin ya dan huce sai aka durawa
Malika a baki.Faruwar hakan ke da wuya sai ta
farfado ta kama aman bakin gudan jini,saida ta
amayar da jini mai yawa sannan ta dawo cikin
haiyacinta,a sannane ta iya bude idanunta tayi
arba da sarki Hilairu a zaune daf da ita idanunsa
na kallonta suna zubar da hawaye saboda
tausayin Halin da yaga ta shiga,suma sauran
jama'ar tasa duk sun zageta sunyi jugum jugum
kamar ana zaman makoki.Malika ta dubi sarki
Hilairu cikin matukar karfin hali tayi masa dan
guntun murmushi kuma ta budi baki da nufin yi
masa magana amma saita kasa.Koda ganin haka
sai wannan likitar ta dubi zarhus tace,dole ne ka
hanzarta mayar da gimbiya can gidan sarauta
domin likitanta ya kara taimaka mata saboda ni
anan banida magungunan da ya kamata acigaba
da bata.Koda jin haka sai Zarhus ya mike tsaye
da sauri yaje ya janyo keken shanunsa mai dauke
da akwatuna guda Arba'in da daya yazo gaban
gimbiya Malika ya dubi sarki Hilairu yace,kusa
Gimbiya a daya daga cikin wadannan
akwatunan.Batare da wata fargabar komai ba
kuwa suka kinkimeta suka sanyata a ciki tamkar
sun sanya gawa domin ko motsin kirki
batayi.Nan
take tsoho Zarhus ya zira hannunsa a cikin aljihu
ya dauko yar karamar kwalbar nan mai dauke da
maganin barci wacce kuyanga Lasmira ta bata
tasha,ya bude kwalbar ya diga wa gimbiya digo
hudu na maganin a cikin bakinta ta hadiye.Take
barci ya dauketa,koda ganin haka sai ya dauko
mushen kwarin nan ya kifa akanta sannan ya
dubi su Sarki Hilairu yace,ku cigaba da zama a
cikin wannan kogon dutse kada dayanku ya
kuskura ya fita waje nan da kamar sa'a uku
gimbiya
zata turo dakarunta su dauke ku izuwa inda zasu
tsira.Koda gama fadin haka sai tsoho Zarhus ya
zaburi keken shanunsa da gudu ya fice daga
cikin
kogon dutsen ya nufi hanyar dazata mayar dashi
cikin birnin Madinatul Zauwara.Su kuwa su Sarki
Hilairu sai hankalinsu ya DUGUNZUMA ainun
saboda
suna ganin cewa koda yaushe Yarima Lahaman
da
dakarunsa zasu iya zuwa wajen su kawo mus
hari
su kashe su ko su kame su.
MEYE A CIKIN LABARIN JARUMI SA MAZA
GUDU?
WANE IRIN MASIFA ZAIZO TA ITA?
SHIN SARKI SHARKUF ZAIBAR GIMBIYA MALIKA
TAYI
WANNAN TAFIYAR?
SHIN YARIMA LAHAMAN YANA SAKE KAWOWA
SU
SARKI HILAIRU HARI?
INA LABARIN SAURAN DAKARUN SUMAMEN
DASUKA GUDU?
SHIN INA SUKA TAFI?
Mu hadu a cikin littafi SA MAZA GUDU littafi na
uku
dan jin wadannan amsoshi.Amma mene
hasashen
ku?An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT