Showing 1 words to 3000 words out of 7605 words
Chapter 1 - Sa Maza Gudu Book 3 Book by Madakin Gini.txt
SA MAZA GUDU
Littafi na uku (3)
Part AAn dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
Tsoho Zarhus ya sami nasarar mayar da Gimbiya
Malika gida lafiya kuma aka shigar da ita har
cikin
turakarta a asirrance batare da wani ya
ganiba,ana kwantar da ita akan gado sai Zarhus
ya sanar da kuyanga Lasmira duk abinda ya faru
bayan barinsa gida.Koda jin haka sai Lasmira ta
ruga taje ta kirawo Likitan Gimbiya yazo ya hada
magunguna na musamman yace da zarar ta farka
daga barci a bata su ta shanye,aikuwa haka
akayi
sa'a uku na cika maganin barcin ya saki Malika
ta
farka.Tana bude idanunta bata ambaci komai ba
sai sunan Sarki Hilairu,koda jin haka sai kuyanga
Lasmira ta dubeta tace,ya shugabata idan har
kinason ki kara ganin sarki Hilairu dole sai kin
shanye magungunan da likita ya hada
miki.Batare
da wata gardama ba kuwa Malika ta karbi
magungunan ta shanyesu,faruwar hakan ke da
wuya sai taji karfin jikinta ya dawo sosai tamkar
babu wani abu daya sameta,kawai sai ta mike
zaune zumbur ta sauko daga kan gadon nata ta
dubu kuyanga Lasmira tace,Maza kije ki kirawo
min Sadauki Aryan.Lasmira ta ruga waje domin
cika umarnin,tabar Gimbiya a tsaye tana kai
kawo
cikin alamun tsananin damuwa da tashin
hankali.Sadauki Aryan ya kasance daya daga
cikin
dakarun Yakin birnin Madinatul Zauwara wadanda
ake takama dasu a filin daga domin kuwa zarto
ne mai TARWATSA MAZA,kuma shekarunsa bazu
haura Ashirin da biyar ba.Aryan yana da mutukar
farin jini wajen sarki Sharkuf kuma ya aminta da
shi ainun,sannan tun Malikat nada shekara shida
a duniya yazamo mai tsaron lafiyarta,don haka ya
shaku da Malika ainum kuma akwai yarda da
amana sosai a tsakaninsu.Bisa wannan dalili ne
Gimbiya Malika take shirya komai nata na sirri
tare dashi.Kai hatta kogon data boye wannan
dukiya tata mai yawan gaske Aryan ya
sanshi.Saidai bai taba zuwa ba,kuma baisan a
inda yake ba.Saboda kusancin da Aryan ya samu
da Malika har ya zamana cewa tun tana Yarinya
karama shike kwana acikin turakarta yana tsaron
lafiyarta.sai ta zamo kawarsa suyi wasa
tare,hakanne ya haddasa kauna a tsakaninsu.Yaji
tsananin begenta a cikin zuciyarsa har izuwa
lokacin data cika budurwa Sarki yasa hijjabi a
tsakaninsu.Yazamana cewa bai isa ya kwana a
turakarta ba saidai ya tsaya a kofar falonta yayi
aikinsa bazai kusanceta ba face zatayi dogon
zango domin bata kariya.Bisa wannan dalili ne
ma sa'adda ta fita wannan farauta daji ba'a fita
tare dashi ba.Tun Gimbiya Malika bata cika
budurwa ba Sadauki Aryan ya kamu da tsananin
sonta kuma yake fama da begenta da tunaninta
a
cikin zuciyarsa.Amma da yake yasan cewa
wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa kuma kwarya
tabi kwarya,bai taba nuna mata soyayyarsa
ba,sai
ya danne son a cikin ransa ya rungimi
kaddara.Lokacin da Sadauki Aryan ya gabata
wajen Gimbiya Malika a cikin falonta sai ya zube
kasa bisa guiwarsa guda ya kwashi gaisuwa
sannan ya dago kai ya dubeta cikin biyayya
yace,ya shugabata gani na amsa kiranki mekike
da bukata?Cikin yanayi na damuwa ta dubeshi
tace,Ina da wadansu bayi dana siya a wajen
Yarima Lahaman,kuma na boyesu a cikin Kogon
dutsen Barzu dake bayan gari,amma na fuskanci
cewa rayuwarsu na cikin hadari saboda haka ina
son ka debi dakaru na sirri ka tafi dasu izuwa
can
domin ku kwashe bayin daga cikin kogon ku
kaisu
can gidan gonata dake kauyen Himas,idan kun
kaisu can ba aikin wahala za'a sasu suyi ba.A
kai
shugabansu izuwa dakina inda nake hutwa ayi
masa irin hidimar da ake mini.sauran bayin ma a
basu masauki da abinci mai kyau sannan ka
dawo
ka sanar dani abinda ake ciki.Koda jin wannan
umarni sai fuskar Sadauki Aryan ta fadada da
murmushi yace,an gama ya shugabata,ina mai
tabbatar miki dacewa za'a kammala wannan aiki
cikin tsafta da nasara kamar yadda kike
bukata,kuma zanje na dawo gareki kafin gari ya
waye.Koda gama fadin haka sai sadauki Aryan
ya
mike tsaye ya juya ya fice daga cikin falon da
sauri.Sannanne Gimbiya Malika ta kawo gwauron
numfashi ta ajiye kuma ta sami nutsuwa da
kwanciyar hankali domin ta yarda da Sadauki
Aryan ainun kuma tasan cewa shi mutum ne mai
tsananin sa'a da nasara bisa duk abinda yasa a
gabansa.Bisa wannan dalile ne ma akeyi masa
kirari da dan baiwa.A tarihin jarumai da mayakan
kasar shine kadai Mayakin da ba'a taba ji masa
ciwo a filin yaki ko filin gasa na jarumtaka,komai
hadarin daji da irin masifun dake cikinsa sai ya
ratsa shi ya wuce lafiya bai taba samun wani
tsautsayi ba,kowa na kasar yana mamakin
wannan baiwa ta Sadauki Aryan kuma hakanne
yasa kowa yake shakkarsa.Babu yadda Yarima
Lahaman baiyi ba akan ya siye Sadauki Aryan
yabar bangaren Gimbiya Malika ya dawo wajensa
amma yaki yarda.Hakan ya jefa Lahaman cikin
tsananin bakin ciki gami da kiyayyar Aryan
saboda yasan cewa idan Ya mallaki Aryan tamkar
ya sami nasara akan duk abubuwan dayasa a
gabansa.Sau bakwai Lahaman yana danawa
Aryan
Tarkon dazai Hallaka shi amma yana kasawa
kuma kiri kiri Aryan din ya gane cewa Lahaman
ne keson Hallaka shi.Bisa wannan dalili ne
Lahaman ya koma tsoron Aryan ya daina shiga
harkarsa saidai suyi kallon kallo.
Cikin dare su Sarki Hilairu na zaune a cikin
wannan kogon dutse sai kawai suka jiyo sukuwar
dawakai an tunkarosu.Nan take suka firgice suka
mimmike tsaye saboda fargabar kosu Yarima
Lahaman ne suka kawo mus hari,nan fa aka rasa
wanda ma zai leko wajen kogon dutsen domin
yaga masu zuwa.Kawai sai Sarki Hilairu ya mike
tsaye ya fito waje ya tsaya a kofar kogon,take ya
hango mahaya kimanin mutum dari ruke da
fitulun itatuwa kuma a cikin shigar fararen tufafi
kuma babu dayansu wanda ya boye
fuskarsa.Koda ganin haka sai sai hankalin Sarki
Hilairu ya kwanta ya cigaba da jiran isowar
mahayan.Ai kuwa suna isowa sai sukaja Linzami
sukai cirko cirko agaban sarki Hilairu.Take
shugaban mahayan ya haska fuskar sarki Hilairu
da fitilar dake hannunsa.Koda yaga kamanninsa
saiya sauko da sauri daga kan dokinsa ya zube
kasa ya gaishe shi,saboda dama tuni tsoho
Zarhus ya kwatanta masa kamanninsa dakuma
matsayinsa a wajen Gimbiya Malika.Sadauki
Aryan ya dago kai ya dubi Sarki Hilairu cikin
girmamawa yace,suna na Sadauki Aryan kuma na
kasance babban yaron Gimbiya Malika.Nazo
nanne bisa umarninta akan cewar na kaiku izuwa
can inda rayuwarku zata sami tsaro da
nutsuwa.Koda jin wannan batu sai farin ciki ya
lullube Sarki Hilairu.Nan take ya kirawo gaba
daya jama'ar tasa suka firfito daga cikin kogon
dutsen mazansu da matansu.Batare da wani bata
lokaci ba kowane mahayi ya goya mutum a
bayan dokinsa.Suka zura da gudu izuwa cikin daji
suka nufi hanyar dazata kaisu kauyen da gidan
gonar Gimbiya Malika take.
Al'amarin Yarima Lahaman kuwa a cikin wannan
daren yana can cikin wannan gida nasa na bayan
gari ya kishingida akan wata karaga yanata
dirkar giya.Wani makadi na buga ganga,wata
shaidaniyar mace a cikin shigar banza tanata
faman tikar rawa a gabansa.Shi kuma Yarima
Lahaman yanata kyalkyala dariyar murna.Kallo
daya zakayiwa Yarima Lahaman kagane cewa
yana cikin farin ciki.Kuma ba komai bane ya jefa
shi cikin farin cikin ba face ganin cewa ya tura
manyan dakarun sumamen da babu kamarsu a
nahiyar domin su kashe bayin da Gimbiya Malika
ta siya a gunsa tare da ita kanta.Kuma yanada
yakinin cewa sai sun samu nasarar cika wannan
aiki daya sasu domin ya yarda da
jarumtakarsu.Lahaman na cikin wannan
Sharholiya ne daya daga cikin dakarun sumamen
ya shigo cikin gidan da gudu a firgice ya zube
kasa a gaban Lahaman yana haki.Cikin kaduwa
da fusata Lahaman ya dubi badakaren
yace,menene ya faru na ganka a birkice haka!
Cikin rawar murya yace,ai Gimbiya ta kashe
shugabanmu dukmun tarwatse bamu samu
nasarar cika umarnin kaba.Kafin badakaren ya
gama rufe bakinsa tuni Lahaman ya zabga masa
wawan naushi a ciki.Take wani gudan jini ya
furzo waje daga bakinsa ya baje a kasa matacce
ko shurawa baiyiba.A sannanne Yarima Lahaman
ya takarkare ya kwarara wani uban ihu.Ihun nasa
ya cika gidan da wajen gidan gaba daya.Kuma
ya firgita duk wani abu mai rai dake kusa domin
kuwa tsuntsaye ma tashi suka rinkayi suna sauya
sheka babu shiri.Yana gama wannan ihu ne ya
fashe da kukan bakin ciki yana mai cewa saboda
mene na kasa cika buri na akan makiya na?Shin
nayiwa abin bautarmu wani laifi ne?Idan har
ubangijin namu yadaina jibantar lamari na nima
daga yau nadaina bauta masa.Haka dai Yarima
Lahaman ya kama sambatu da surutai irin
wadanda basu da ma'ana da kan gado har yagaji
likis ya fadi kasa ya kama barci.Sai dauke shi
akai aka shigar dashi cikin wani dakin
shakatawarsa aka kwantar dashi.
SA MAZA GUDU
Littafi na uku(3)
Part B
Kamar yadda Gimbiya Malika ta tsara haka
al'amarin ya kasance wato Sadauki Aryan ya
sami
nasarar kaisu sarki Hilairu can gidan gonarta
kuma sun isa,aka baiwa jama'ar sarki Hilairu
masauki mai kyau,gami da abinci mai
daraja.Dayake da yawansu suturunsu sun
yayyage
kuma sunyi bakin kirin kamar almajirai,sai aka
kaisu kewaye sukayii wanka,sannan aka kawo
musu sababbun suturu masu kyau aka basu,suka
sanya sai gashi sun tsinci kansu a cikin farin ciki
mara misaltuwa,sukaji tamkar a cikin tsohon
birninsu suke,bambancin kawai shine basa tare
da sauran 'yan'uwansu,wasunsu kuma sun rasa
iyayensu,wasu yan'uwa wasu mataye,yayye da
kanne,hakanne ya tuno musu da rashin da sukayi
suka kama kuka.Shi kuwa sarki Hilairu da aka kai
shi dakin da Gimbiya Malika ke hutawa yaga irin
daular da aka shirya a cikinsa kuma har da
kuyangi guda hudu kyawawa masu yi masa
hidima,sai ya fashe da kukan bakin ciki saboda
tunowa da yayi da daularsa da aka rushe da
kuma matarsa marigayiya.Bayan yayi wanka an
kawo masa abinci na alfarma ya kimtsa cikinsa
sai
yaje ya kwanta yana kallon wani kyakkyawan
tsuntsu dake cikin keji a rataye.Nan take zuciyar
Sarki Hilairu ta tafi izuwa duniyar soyayya ya
runtse idanuwansa.Take ya tsinci kansa acikin
wani kayataccen lambu cike da furannin
kyawawa
gami da kayan marmari iri iri,ya tsinki inibi kenan
zai kai bakinsa sai ya hango Gimbiya Malika ta
nufo gareshi a cikin ado na kasaita,fuskarta cike
da annuri tana tayi masa murmushi,wani haske
ya baibaye jikinta gaba daya.Koda ya hangota
saishi ma ya nufeta yanamai bude
hannayensa,itama sai ta bude hannayenta suna
shirin su rungume juna kenan sai yaji ana
kwankwasa masa kofar daki.Sarki Hilairu yayi
firgigit kamar wanda ya farka daga bacci ya dubi
bakin kofar shigowa a fusace saboda bai so aka
yanke masa wannan tunani ba mai kama da
mafarki,kawai sai yaga ashe sadauki Aryan ne ya
shigo.Cikin hanzari Sarki Hilairu ya sake fuskarsa
ya sauko daga kan gadon ya taho wajen
Aryan.Shi
kuwa Aryan sai ya sake dukawa a gabansa a
karo
na biyu yace,ya shugabana mun gama cika
umarnin Gimbiya don haka yanzu a cikin wannan
dare zamu koma gareta domin mu sanar da ita
halin da ake ciki.Koda jin wannan batu sai Sarki
Hilairu ya sunkuya ya kama kafadun Sadauki
Aryan ya tashe shi tsaye sannan ya dubeshi cikin
murmushi yace,idan ka isa wajen Gimbiya ka
gaya
mata cewa ina godiya a gareta mara adadi,domin
kuwa bani da abinda zan iya saka mata dashi ba
face fatan alheri ga rayuwarta da kuma fatan
Allah yasa ta zamo mai gadon mahaifinta.Ya kai
wannan jarumi ma'abocin adalci yanzu haka idan
ka tafi ka barmu a wannan kauyen cikin wannan
gidan gonar baka zaton cewa mutanen Yarima
Lahaman zasu iya sake kawo mana wani harin
ba?Koda jin wannan tambaya sai Sadauki Aryan
yayi murmushi yace,ya kai wannan sarki
ma'abocin kyawu da kwarjini ka kwantar da
hankalinka,ka sani cewa kazo tudun tsira domin
kuwa wannan kauye yana karkashin tsaron
amintattun dakarun sarki guda dubu dari
biyar.Komai yawan runduna ta mayaka kafin su
shigo garin nan su cishi da yaki tuni labari ya
iske
mu a can babban birni mun kawo muku
dauki.Kuma ko Yarima Lahaman yazo nan da
kansa baza a barshi ya shigo ba saboda fiye da
shekaru goma baya sarki ya haramta masa zuwa
wannan kauye bisa sharadi mai tsauri.Koda
sadauki Aryan yazo nan a jawabinsa sai hankalin
sarki Hilairu ya kwanta.Nan take dai ya sake yi
masa godiya sukayi sallama.Ba tare da bata wani
lokaci ba sadauki Aryan ya kwashi dakarunsa
suka
fice daga cikin gidan gonar suka tasamma birnin
Madinatul Zauwara.
Gimbiya Malika ta farka daga barci sakamakon
tsamin jikinta datake fama dashi na gumurzun
yakin da tayi da dakarun sumame a jiya da
daddare.Koda ta bude idanunta taga yadda rana
ta kwalle sai ta kurma ihu saboda sanin cewa
tayi
laifin makara izuwa fada.Cikin hanzari ta
kwalawa
kuyanginta kira suka shigo cikin turakar da gudu
suka dauketa suka shigar da ita cikin kewaye
suka
tsala mata wanka.Kafin a gama wankan kuyanga
Lasmira ta kawo mata abincin kalacinta ta ajiye
akan tebur kusa da gadonta na barci.A tsaitsaye
Malika ta yiwa abincin loma uku sannan ta fice
da
gudu ta nufi fada.Kuyanginta sama dasu arba'in
suna take mata baya.Suna ruke da doguwar rigar
dake jikinta wacce ke fama sharar kasa,mai
siffar
bindin dawisu.Wasu daga cikin kuyangin kuwa
wucewa sukayi gaban Gimbiya suna watsa wani
irin fure mai kamshi kuma mai launin shudi kalar
rigar jikinta tana takesu da kafafunta.A haka
suka
iso cikon fadar,da shigar Gimbiya Malika sai sarki
Sharkuf ya mike tsaye cikin murna ya taryeta
cikin
murna,fuskarsa cike da annuri ya taryeta.A
wannan lokaci Yarima Lahaman na zaune a can
gefe daya cikin yan majalisa ya murtuke fuskarsa
tamkar wanda aka aiko wa da sakon
mutuwa.Koda sarki Sharkif ya rungume Gimbiya
Malika sai ta hada ido da Yarima
Lahaman,maimakon ita ma ta daure fuska sai
tayi
masa murmushin mugunta mai nuna alamun ta
sami nasara akansa.Al'amarin daya kara fusata
Yarima Lahaman kenan bai san sa'adda ya matse
hannun kujerar da yake zaune a kaiba,abinka da
al'amarin Sadauki take hannun kujerar ya
ruburbushe duk da cewa anyi tane da katako mai
kwari.Karar karyewar kujerarce ta janyo hankalin
yan majalisar dake zaune kusa dashi,suka kama
kallonsa suna kallon kujerar.Kuwa sai ya kama
yake yana nunawa kamar tsautsayine ya janyo
karyewar kujerar.Nan take fadar ya rude da
shewa bisa ganin shigowar Gimbiya Malika
maroka suka kama yi mata kirari a lokacin da
sarki Sharkuf ya kama hannunta ya jata izuwa
can
inda karagar mulkinsa take domin su zauna tare
a waje daya,yayin daya rage saura
baifi taku biyar ba su isa kan karagar sai Malika
ta
janye hannunta daga cikin na sarki ta dubeshi
tace,Ina mai neman alfarma ka barni naje na
zauna a kusa da yan uwana yayanka a yau rana
daya jal.Koda jin wannan batu sai mamaki da
farin ciki ya turnuke sarki Sharkuf domin bai taba
jin Malika ta ambaci kalmar yan uwanta ba,sai a
yau,hatta ragowar yayyanta maza su bakwai
babu
ruwanta da su kamar yadda suma babu ruwansu
da ita.Asalima dukkaninsu sun tsaneta kamar
yadda suka tsani mutuwarsu,saboda ganin yadda
uban nasu ya fifita ta akansu kuma yake nuna
mata tsananin SO DA KAUNA.Cikin fara'a Sarki
Sharkuf ya dubi Gimbiya Malika yace,nayi miki
alfarma jeki ki zauna a cikin yan uwanki kamar
yadda kika bukata.Koda jin haka sai Malika ta
nufi
inda su Yarima Lahaman ke zaune fuskarta cike
da murmushi.Al'amarin da ya baiwa kowa
mamaki kenan cikin fadar domin bata taba zuwa
cikin yan uwanta ta zauna ba.Kai tsaye Malika
taje
ta zauna akan kujerar dake daf data Yarima
Lahaman suka hada idanu a karo ba biyu sai ta
sake yi masa murmushi,sannan ta dubi ragowar
yan uwanta maza su bakwai dake zaune a
gefensu suma tayi musu murmushi a karo na
farko a rayuwar zamantakewarta dasu.Take su
duka hankalinsu ya DUGUNZUMA,kuma tsoro ya
shigesu,suka fara tunanin ko wata mugunta
Gimbiya Malika take shirin yi musu shi yasa ta
kusancesu a wannan rana.Ba tare da bata lokaci
ba aka fara zartar da harkokin fada kamar yadda
aka saba.Fadawa daManyan yan majalisa suka
fara fitowa gaban sarki suna kwasar gaisuwa
dogarai na amsa musu.Ana cikin wannan hali ne
Malika ta dubi Lahaman ta budi baki cikin
karamar murya kamar mai rada tace dashi,na
sayi bayi a wajenka kuma na biyaka
kudinka,saboda me ka aiko a kashe su?Ka sani
cewa ka tsokano tsuliyar dodon daya shekara a
kwance yana barci,kuma ka haifar da yakin da
bashi da karshe face dayanmu yakai dan uwansa
kushewa.Jibi zan bar kasan nan domin gabatar
da
tafiyar dana sabayi a duk karshen shekara,idan
ka
isa ka debo dukkan dakarunka da kake takama
dasu ka tareni a daji muyi yakin karshe domin mu
warware kiyayyar dake tsakaninmu ta tsawon
shekaru.Idan kuma baza ka iyaba to ka bazama
a
cikin duniya domin kayi sabon shiri na nemo
makaman yakata,ka sani har abada tsakanina da
makiya babu gudu babu ja da baya,yau zan gaya
maka sirrin da ban taba gaya maka ba,ka waccan
karagar Mulkin da mahaifinmu ke zaune a
kanta,ko gawarka bazata hau kai ba ballan tana
kai,nice zan hau kan waccan karagar kuma kanaji
kana gani da ranka da lafiyarka.Tun kafin
Gimbiya
Malika ta gama wannan jawabi nata fuskar
Yarima
Lahaman ta kama gatsinewa saboda tsananin
fushi fa kiyayya kai har saida ma ya dunkule
hannayensa biyu da nufin ya gabza mata naushi
amma daya tuna cewa a cikin zuciyarsa kar yayi
haka,sai ya cigaba da kallonta kawai har ta
gama
suruntunta ta mike tsaye tabar wajen ta tafi
izuwa wajen sarki tayi masa rada a kunne sannan
ta fice daga cikin fadar gaba daya.
Da kwanaki biyu suka cika ranar tafiyar Malika
tazo lokacin da
tazo yin bankwana da iyayanta Sarki Sharkuf da
Sulaira sai suka rungumeta suka fashe da kuka.
SA MAZA GUDU
Littafi na uku(3)
Part C
Al'amarin daya karya zuciyar Malika kenan ta
janye jikinta daga cikin nasu ta dubesu a alokacin
da hawaye ke kwarara bisa kumatunta
tace,saboda me kuke yin kukan rabuwa
dani,alhalin ba wannan ne karo na farko dana
fara yin wannan tafiya ba,ban taba ganin kunyi
kuka ba idan nazo yi muk sallama sai a wannan
karon,shin ko zaku iya gaya mini dalili?Koda jin
wannan tambaya sai mahaifiyar Malika ta sunkui
da kanta kas,ta kasa cewa komai.Shi Kuwa sarki
Sharkuf sai ya kama kafadun Malika ya ruke a
lokacin da hawaye ya subuto masa ya dubeta
yace,yake yata ki sani cewa bokana wanda na
aminta dashi ainun wanda duk abinda ya fada
mini sai ya faru a gaske,shine ya sanar dani
cewa
wannan rabuwa da zamuyi dake a yanzu itace ta
karshe a gareni,ma'ana ba zaki dawo ki riskeni a
rayeba.Koda jin wannan batu sai Malika ta firgita
ainun idanunta suka zazzaro kuma hawaye ya
sake zubo mata sannan ta sake rungume sarki
Sharkuf ta kankameshi a jikinta tana mai
fashewa
da matsanancin kuka.Itama mahaifiyartata saita
rungumesu