Showing 3001 words to 6000 words out of 7605 words

Chapter 2 - Sa Maza Gudu Book 3 Book by Madakin Gini.txt

sannan Malika ta janye jikinta daga
nasu ta sake fuskantar sarki tace,ai kuwa in har
bazan dawo na riske ka raye ba banga amfanin
yin wannan tafiya tawaba,tunda kafin na dawo
Yarima Lahaman ya hau kan karagar ka,ka
sanicewa idan har ya hau kan wannan karaga
talaka sun shiga uku,kuma mulkin zalunci da
murdiya za'a ciga da gudanarwa a cikin wannan
kasa tamu mai albarka,duk kokarin dakayi na
ganin an sami zaman lafiya da yalwar arziki a
kasar nan tsawon shekaru ya zama na banza
kenan.Koda gimbiya Malika tazo nan a zancenta
sai Sarki Sharkuf ya tari numfashinta
yace,kwantar da hankalinki yake yata,kiyi sani
cewa kamar yadda zaki bar gari yanzu bayan
kwana biyu da tafiyarki shima Yarima Lahaman
zaiyi shiri ya tafi neman karin Horon yaki gami da
ilmin tsafi.Kuma ba zai dawo ba sai bayan cikar
watanni shida,kinga ke nan saima kin riga shi
dawowa da tazarar wata uku.Bokana bai sanar
dani anihin sauran kwanakina a duniya ba,zan iya
kaiwa wannan lokaci na dawowarki wata kila
kuma bazan kaiba.A cikin binciken da bokana
yayi
zaki sami gagarumar daukaka a cikin wannan tafi
taki,kuma zaki hadu da wani mutum mai darajar
gaske wanda shine sanadin daukakar taki,amma
kada ki kuskura kice zaki yaki wannan mutum
saboda zaku banbanta a addini da ra'ayi.Ki bishi
a hankali kuma ki lallaba shi ki sami karin Ilmin
yaki a wajensa,zaki kiyi yake yake tare dashi
kuma zaki shaku dashi ainun,amma kada ki
kuskura ki kamu da sonsa ko kuma ki karbi
addininsa.Sai kinyi hakanne kadai zaki iya
dawowa gida ki iya fuskantar dan'uwanki Yarima
Lahaman domin a sannan shima ya zamo
gagarumin sadauki kuma gawurtaccen matsafi
abin tsoro a duniya.A sannan ne zakuyi gasar
hawa karagata ta mulki a samin wanda zai
gadona a cikinku.Lallai saikin kiyaye wadannan
dokoki dana zaiyana miki a yanzu sannan zaki
iya
samun nasara akan dan'uwanki.Koda sarki
Sharkuf yazo nan a zancensa sai Gimbiya Malika
ta sake rungumeshi ta fashe da kuka.A cikin
zuciyarta kuma tana tunanin tayi masa maganar
Dan'uwan sarki Hilairu wato SA MAZA GUDU,tana
jin tsoro don kada ya tambayeta a inda ta san
wannan sunan har ta jawo ya gano abinda take
na sirri.Nan dai ta juya ta nufi dokinta da nufin
ta
hau su nausa sai taji muryar Mahaifinta yana mai
cewa,yake 'yata kiyi sani cewa a wannan fita da
zaki yi lallai kiyi kokarin kiyaye irin mayakan
dazakiyi yaki dasu.Domin a cikin wannan tafiya
taku zaki iya haduwa da GUGUWAR ANNOBA
wacce batada magani,Ruwa mai tafiya da duk
abinda yasha masa gaba,lallai ki kula sosai
domin SA MAZA GUDU yana bisa cikin wannan
nahiya
mai albarka.Koda jin haka sai ta waigo ta dubi
mahaifinta a nutse tace,ya Abbana shin waye
wannan wanda ban taba jin sunansa ba,alhalin
naga a cikin batunka kana kuranta
jarumtakarsa.Koda Sarki Sharkuf yaji wannan
tambaya sai yace,Labarin Sa Maza gudu yana da
tsayi,saidai kawai na sanar dake cewa babbar
masifa ce shi a cikin duniya MURUCIN KAN
DUTSE ne shi bai fito ba saida ya shirya.Asalinsa
an haife
shi a cikin wannan nahiyar saidai bai rayu a
wannan nahiya ba,yake 'yata kiyi sani cewa shi
wannan jarumi bai kasance azzalumi akan wanda
bai masa laifi ba,amma ya kasance azzalumu
akan duk wanda ya taboshi,baya ragawa kowa
face kaifin takobi ta shiga tsakaninsu.Don haka
ina mai miki gargadi akan ki kiyaye shiga sabgar
duk wanda bai shiga harkarkiba,kada kiyi yaki da
kowa sai in har shi ya neme ki da yaki.Wannan
kadai idan ki kiyaye zaki fita daga ukubar SA
MAZA GUDU,da wannan nake miki bankwana.
Nan Gimbiya Malika ta juya cike da tunani a cikin
ranta
ta haye dokinta Sadauki Aryan ya jera tare da
ita,Dakaru dubu uku da kuyangi arba'in suka rufa
musu baya,suka fice daga cikin gidan
sarautar.Tun Sarki da Mahaifiyar Malika na
hangosu har suka bace musu da gani.Nan take
sarki ya kama hannun matarsa suka juya suka
koma cikin gidan sarautar rungume da juna suna
zubar da zazzafan hawaye na bakin cikin rabuwa
da gimbiya Malika.Da fitowar su Gimbiya Malika
daga cikin Birnin Madinatul Zauwara sai ta dubi
Sadauki Aryan tace,gidan gonata zamu fara zuwa
domin na gana da su sarki Hilairu sannan nasan
abinda ya kamata nayi dasu.Koda jin haka sai
Aryan ya baiwa sauran dakarun umarni,kowa ya
kada linzamin dokinsa aka nufi hanyar da zata je
wannan kauye inda gidan gonar gimbiya Malika
take.Tafiyar 'yan Sa'o'i kadan sukayi suka iso
kauyen,tun daga nesa masu gadin kofar garin
suka hango tutar mulki ta birnin Madinatul Zauwa
suka busa algaita alamar cewa gimbiya Malika ta
iso.Nan da na jama'ar kauyen suka rinka
tururuwa suna fitowa taryar gimbiya Malika cikin
mutukar farin ciki saboda kaunar dasu ke yi
mata.Dakarun kauyen kuwa sukayi sahu biyu
suna mika gaisuwa,maroka da mawaka suka
kama yiwa gimbiya Malika jinjina da kirari,kai
hatta kananan yara da tsofaffi,matasa samari da
'yan mata fitowa suke daga cikin gidajensu a
guje
suna zuwa bakin hanya suna mika
gaisuwarsu.Bawai a wannan kauye bane kadai
ake
yiwa gimbiya Malika irin wannan tarba ba,duk
garin da taje a cikin kasar haka ake bikin murnar
zuwanta,kuma ayita kawo mata kyaututtuka iri
iri.Ita kuwa Gimbiya Malika duk garin da taje sai
ta bincika taji matsalar data damesu tayi musu
maganinta,idan ta fara yiwa mutane kyautar kudi
kuwa har sai anga a bin ya wuce na hankali
sannan kuyangi suke janyeta daga wajen.Ko
kadan
Gimbiya Malika bata kyamar Talakawa kuma bata
gudunsu.Har ziyarar gidaje takeyi cikin dare a
sirrance tana ganin matsalolinsu tana magance
musu.Kananan yara kuwa da matsa kamar sa
hadiyeta saboda kaunar dasukeyi mata.Wannan
dalili ne yasa a cikin gaba dayan 'ya'yan sarki
Sharkuf a kasar Madinatul Zauwara Gimbiya
Malika tafi farin jini kuma kowa ita yake so tagaji
sarki saboda tana da irin adalcinsa da jin
kansa.Saida Gimbiya Malika ta batwa wajen Sa'a
uku a cikin garin tana karbar gaisuwar jama'a da
kyaututtuka kansu sami damar isa gonarta.Da
yake dama ansan da zuwanta tuni gaba dayan
ma'aikatan gidan gonar da dakaru masu tsaro da
kuma su sarki Hilairu da jama'arsa sun fito sun
jera layi a cikin harabar gidan gonar domin yi
mata barka da zuwa.Koda Gimbiya Malika ta
shigo cikin harabar gidan gonar jama'a suka fara
miko gaisuwa da jinjina sai ta hango sarki Hilairu
tare da jama'arsa sun zube kasa suna
gaisheta,cikin hanzali Malika ta tsaida dokinta ta
sauko kasa sannan taje wajen Hilairu ta kama
kafadunsa a karon farko kenan da ta taba jikin
wani 'da namiji inba mahaifinta ba da kuma "dan
uwanta Azzalumi Yarima Lahaman wanda shima
a
lokacin dasuke gumurzun yaki ta tabashi.Bayan
Malika ta tayar da Hilairu tsaye sai ta dubeshi
ciki
alamun damuwa tace,Haba yakai wannan sarki
mai daraja,shin ka manta ne cewa kai ma sarki
ne?Koda jin wannan tambaya sai Hilairu yayi
murmushi cikin yake yace,tabbas a da ni sarki
ne,amma a yanzu na kasance bawa na yar sarki
tunda siyo ni akayi daga hannun wani.Koda jin
wanna batu sai tausayin Hilairu ya kama kowa a
wajen musamman ita kanta
GimbiyaMalikan,kawai sai ta sake dubansa ta
girgiza kai tace,ai ni ban fanso ka ba domin ka
zama bawana ba,sai domin na 'yantaka tare da
dukkan jama'rka,yanzu mu karasa cikin dakin
shakatawa ta saboda ina da magana mai
muhimmanci dakai.Koda jin wannan batu sai
Farin ciki ya lullube gaba dayan mutane sarki
Hilairu bisa jin cewa an 'yanta su,nan fa suka
kama tsalle da murna suna yiwa gimbiya Malika
Godiya.Bayan Malika ta zauna ta huta tareda da
Sadauki Aryan a cikin dakinta na hutun.An kawo
musu abinci da abin sha na alfarma sun ci sun
gyatse,sai ta tura aka kirawo Hilairu.Da
shigowarsa cikin dakin sai Malika ta dubi Aryan
tayi masa inkiya ya tashi ya basu wuri.Nan take
Aryan ya mike ya fice daga cikin dakin zuciyarsa
cike da kishi domin a rayuwarsa babu abinda ya
tsana sama da yaga wani 'da namiji ya kusanci
Gimbiya Malika.Fitar Aryan ke da wuya sai
Malika
ta dubi Sarki Hilairu cikin murna tayi masa izinin
ya zauna akan kujerar da take fuskantar tata
sannan ta dubeshi tace,yakai wanna sarki,kayi
sani cewa tun daga ranar danaji labarinka bisa
mugun abinda dan'uwana Yarima Lahaman yayi
maka a birninka naji na kamu da tsananin
tausayinka,babu wani abu dazaisa zuciyarka tayi
sanyi face na mayar da kai da jama'arka izuwa
kasarku ka koma kan kragarka ta mulki.Kuma na
taimaka maka da kudi a sake gina birnin a
kawata
shi ainun tunda an kone gidajenku,kayi sani cewa
na dauki alkawarin yin hakan acikin zuciyata
tuntuni,amma a halin yanzu bani da ikon cika
wannan alkawari saboda ina kan hanyata ne ta
zuwa manyan kasashen duniya guda uku domin
gabar da harkokina na kasuwanci kamar yadda
na
saba a duk karshen shekara.Shin zaku bini ne
izuwa wannan tafiya kuyi min rakiya idan na
gama sabgata na dawo gida sai mu sake shiri mu
tafi?Lokacin da Gimbiya Malika tazo nan a
zancenta sai Sarki Hilairu yayi ajiyar numfashi
yayi
shiru yana tunani har izuwa tsawon yan dakiki
daga can sai ya dago kai ya dubeta yace,yake
wannan yar sarki kiyi sani cewa zamana a nan ko
a can birnina acikin daula da kwanciyar hankali
bazasu taba dawo min da abinda na rasa ba,na
sani cewa kina da labarin matata wacce
dan'uwanki yayi mata fyade kuma ya kasheta a
gaban idanuna wacce take tsananin kama dake
tamkar an tsaga kara.To kiyi sani cewa dawowar
wannan masoyita tawa shine kadai zai yaye mini
damuwata da bakin cikin zuciyata.Koda sarki
Hilairu yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubo
masa ya fashe da kuka,nan take Malika taji da
kamu da tsananin tausayinsa fiye da koyaushe
har ta budi baki zatace dashi a shirye take ta
maye masa gurbin matarsa sai ta kasa,Ta sunkui
da kanta kasa tayi sauri ta goge hawayenta don
kada ya gani.Saida taga ya nutsuwa ya daina
kuka
sannan ta dubeshi tace,yanzu mene zabinka?
zaka
bini ne ko zaka zauna anan din?Koda jin wannan
tambaya sai Sarki Hilairu ya dago kai ya dubi
Malika yace,na zabi na biki tare da jama'ta.Dajin
Haka sai farin ciki ya lullubeta,Gimbiya Malika
nan
take ta sallame shi ya tafi izuwa can wajen
mutanensa.Ita kuma sai ta shiga can cikin kuryar
dakin ta kwanta akan gado domin tayi barci
amma sai barcin ya gagara sakamakon tunanin
al'amura biyu da suka fado mata.Al'amari na
farko shine tunowa da abubuwan da mahaifinta
Sarki Sharkuf ya gaya mata dangane da bakon
jarumin daya bata labarin cewa zata hadu dashi a
wannan fitowa da tayi.Take ta tambayi kanta a
cikin zuciyarta tace,wai shin yaya kamanin
wannan jarumi zai kasance bare da zarar ta hadu
dashi ta gane shi,kuma aina ma zata hadu dashi?
To yaya zan ribaci wannan jarumi har na karo
horon yaki daga wajensa,alhalin mun banbanta a
addini da ra'ayi?Koda Malika tazo na a tunaninta
sai ta kasa baiwa kanta amsa,a sannan ne kuma
tunanin dan uwanta Yarima Lahaman dana SA
MAZA GUDU suka fado mata a rai.Ta shiga
Tunanin yadda za'ayi Lahaman ya zama
gawurtaceen jarumi kuma matsafi a cikin
watannin shida kacal.Nan hankalin Malika ya
DUGUNZUMA ta gane cewa lallai aikin dake
gabanta ba karami bane,kuma Allah ne kadai
yasan irin gwagwarmayar da zata sha da bakar
wahalar daza ta fuskanta kafin ta sami nasarar
zama sarauniyar birnin Madinatul Zauwara.Haka
dai Malika taci gaba da wannan tunani tana so ta
huta sosai domin idan sun ci gaba da tafiyar
Sarki
Hilairu ya bata Labarin Jarumtakar SA MAZA
GUDU,da haka har barci ya saceta bata saniba.A
wannan rana Sadauki Aryan ne yayi gadin
Gimbiya Malika kuma bai bari sarki Hilairu ya
sake
shiga wajenta ba har gari ya waye.Tun da duku
dukun safiya Gimbiya Malika tare da jama'arta da
jama'ar sarki Hilairu sukayi shirin aka kawo mata
dokinta aka dunguma gaba daya aka fice daga
cikin yankin kasar Madinatul Zauwara.Koda aka
iso wani wuri inda hanya ta rabu gida uku,sai aka
tsaitsaya.Kawai sai Sadauki Aryan ya dubi
Gimbiya
Malika yace,ya shugabata yanzu wace kasa
zamu
fara zuwa Tsakanin Misra,Yemen da kuma
Kisra.Koda jin wanna tambya sai Malika tayi
shiru
tana tunani kamar bazatace komai ba,daga can
kuma sai ta dubi Sadauki Aryan tace,mu tunkari
birnin Misra domin shine birnin da muka dade
rabonmu dashi.Koda jin haka sai Aryan ya kada
dokinsa ya nufi gabas take Malika da sauran
jama'ar gaba daya suka rufa masa baya.Haka dai
su Gimbiya Malika sukayi ta tafiya suna ratsa
dazuzzuka,birane da kauyuka har tsawon
kwanaki
goma sha shida sannan suka iso birnin Misra.
Part D
Haka dai su Malika sukayi ta tafiya suna masu
ratsa dazuzzuka,birane da kauyuka har tsawon
kwana goma sha shida sannan suka iso Birnin
Misra.A cikin wannan tafiya sun sha haduwa da
'yan fashi mugayen aljanu da mugayen dabbobin
daji amma dukansu farat daya suke yi
musu,sannan gimbiya Malika ta rike wasiyar
mahaifinta bata taba kulasu wasu yan fashi ba
sai
sai in sun kula su,suna kula su kuwa saidai su
gama dasu su bar gawarwakin a yashe a wajen
su
kara gaba.Da shigowar su Gimbiya Malika cikin
birnin Misra sai suka iske garin ya cika makil fiye
da koyaushe a duk lokutan da suke zuwa a
baya.Fatake,bokaye da yan kasuwa iri iri da kuma
masu fataucin bayi sun cika garin.Al'amarin daya
baiwa su Gimbiya Malika Mamaki kenan har suka
kasa hakuri.nan take sadauki Aryan yaga wani
almajiri a zaune a gefen hanya rike da dan
'ko'kon yana bara.Shidai wannan almajiri ya
kasance saurayi mai kirar sadaukai,amma kuma
kafarsa guda ta hagu da hannunsa na hagu duk a
shanye suke ko sarrafasu baya iyawa.Aryan ya
zura hannu a cikin aljihunsa ya dauko dinare
guda
daya a lokacin daya tsaida dokinsa daf da
almajirin ya jefo masa wannan dinare a cikin
kokon sannan ya dubeshi yace,ba sadaka na
baka
ba,labari nake nema,mene dalilin wannan cikowa
mai yawa a cikin wannan birni?Koda jin wannan
tambya sai almajirin yayi murmushi yace,da
wannan dan kudin kake son kaji babban labari ai
sunyi kadan.Koda jin haka sai Aryan yayi
murmushi ya sake zura hannu cikin aljihunsa ya
dauko dinare guda ya jefa cikin kokon
yace,yanzu
fah?Almajirin yace da saura domin kuwa labarin
da zan baka zai amfaneku a matsayinku na
manyan jarumai daga babbar kasa.Koda jin
wannan batu sai mamaki ya turnuke sadauki
Aryan yace,A cikin ransa anya kuwa wannan
almajiri ba boka bane,yaya akayi yasan cewa mu
jarumai ne daga babbar kasa,kuma menene zai
amfane mu akan labarin da zai bamu.Koda gama
wannan zancen zucin sai Aryan ya sake fidda
dinare uku ya sauko daga kan dokinsa yazo ya
tsuguna a gaban almajirin ya zuba masa dinaren
a cikin kokonsa ya zama guda biyar sannan ya
dafa kafadarsa yace,Abokina bani labari me yake
faruwa a cikin wannan gari?Almajirin ya sanya
hannunsa mai kyan cikin kokon ya kwashi
dinaren
ya zuba su a cikin aljihunsa na wando sannan ya
dubi Aryan cikin nutsuwa yace,Ai sarkin garin
nan
ne ya shirya gasar jarumtaka ta duniya don haka
jarumai da yawan gaske sunzo daga manynan
kasashe,sarakuna sun zo,kuma attajirai yan caca
sun taru domin baje kolunsu a goben da safe a
gidan sarauta.Duk wanda ya lashe wannan gasa
za'a bashi zabin abubuwa guda uku ya dauki
daya ko dai ya auri yar sarki kokuma a bashi
dinare da rakuma dubu ko a bashi mulkin babbar
jaha daga cikin jahohin kasar nan.Koda jin
wannan batu sai Sadauki Aryan ya kamu da farin
ciki nan take ya aiyana a ransa cewa lallai zai
shiga wannan gasa,amma ba don kawai a bashi
wannan dukiya ta dinare ba.Rakuma gudu dubu
saboda in ya koma gida yayi amfani da ita wajen
cika wani babban buri nasa wanda ya gagare shi
cikawa tsawan shekaru.Kawai sai Aryan ya dubi
wannan Almajiri yace Abokina meye sunanka?
Almajirin yace Sunana Hibairu bin Usman.Koda
jin
haka sai Aryan ya mikawa almajiri Hibairu
hannunsa na dama shima ya bashi nasa hannun
suka gaisa.Aryan yace,ina fatan zamu hadu gobe
a fada muyi kallon wanna gasa tare.Hibairu yayi
murmushi yace,tabbas zamu hadu,koda gama
fadin haka sai Aryan ya mike da sauri yaje ya
hau
dokinsa ya zabure shi da sauri domin ya riski su
Gimbiya Malika saboda sun bashi tazara mai dan
yawa.Da isar Aryan wajen gimbiya Malika sai ta
dubeshi cikin murmushi tace,me ka tsaya yi a
wajen wancan almajirin?Aryan ya maidawa
Malika
martanin murmushin cikin biyayya yace,na
tambaye shi dalilin wannan cikowa mai yawa a
garin nan shine ya labarta mini cewa Sarkin
garinne ya shirya gasar jarumtaka ta duniya.Koda
jin wannan batu sai farin ciki ya lullube Malika ta
dubi Aryan tace,da zarar mun sauka a
masaukinmu kaje ka nemi sarkin kasuwa ka gaya
masa cewa nima ina son na shiga wannan gasa
don haka yaje ya biya mini kudin shiga gasar tun
kafin na yazo gareshi muyi lissafin kudaden.Koda
jin wannan batu sai tsoro da mamaki suka kama
sadauki Aryan ya dubi Malika cikin alamun
tsananin dimuwa yace,Haba ya shugabata ai
girmanki da darajarki tafi gaban shiga wannan
gasa,saidai ki barmu mu wakilceki kada ki manta
cewa gaba dayan manyan sarakuna kina hulda
dasu kuma babu wanda ya san cewa kina da
wannan jarumtaka bai kamata ki tonawa kanki
sirri ba.Koda jin wannan batu sai gimbiya Malika
tayi murmushi tace,idan kida ya sauya dole ne
rawa ta sauya.Ya kai Aryan ka sani cewa ni
yanzu
tun dana baro gida neman yadda zan kare kasata
daga shirin abokan gaba na daina daukar kaina a
matsayin yar sarki,wannan gasa da zan shiga ta
jaruman duniya zata taimaka mini na kara sanin
iyakar jarumtakata da iya yakina.Kuma zata
samini azamar das zan kara dagewa don
fuskantar babban aikin dake gabana.Abinda nake
so da kai shine kaima ka shiga wannan gasa
kaga
idan kayi nasara koda ni banyu ba shike nan
daukaka dai tana hannunmu.Koda jin wannan
batu sai sadauki Aryan ya sake duban Malika
cikin
alamun tsananin damuwa da mamaki yace,Haba
ya shugabata ta yaya zan iya lashe gasar
jarumtaka alhalin kina cikinta kuma na tabbatar
da cewar kin fini karfin damtse da iya yaki?Koda
jin wannan tambaya sai Malika ta yi murmushi
tace,yakai Aryan ka sani cewa karfin damtse da
iya yaki basu ne kadai ke sawa a sami nasara ba
akwai sa'a da rabo.Koda gama fadin hakan sai
Malika ta karawa dokinta kaimi tayi gaba ta nufi
masarautar garin..

SA MAZA
GUDU
Littafi na uku(3)
Part D
Haka dai su Malika sukayi ta tafiya suna masu
ratsa dazuzzuka,birane da kauyuka har tsawon
kwana goma sha shida sannan suka iso Birnin
Misra.A cikin wannan tafiya sun sha haduwa da
'yan fashi mugayen aljanu da mugayen dabbobin
daji amma dukansu farat daya suke yi
musu,sannan gimbiya Malika ta rike wasiyar
mahaifinta bata taba kulasu wasu yan fashi ba
sai
sai in sun kula su,suna kula su kuwa saidai su
gama dasu su bar gawarwakin a yashe a wajen
su
kara gaba.Da shigowar su Gimbiya Malika cikin
birnin Misra sai suka iske garin ya cika makil fiye
da koyaushe a duk lokutan da suke zuwa a
baya.Fatake,bokaye da yan kasuwa iri iri da kuma
masu fataucin bayi sun cika garin.Al'amarin daya
baiwa su Gimbiya Malika Mamaki kenan har suka
kasa hakuri.nan take sadauki Aryan yaga wani
almajiri a zaune a gefen hanya rike da dan
'ko'kon yana bara.Shidai wannan almajiri ya
kasance saurayi mai kirar sadaukai,amma kuma
kafarsa guda ta hagu da hannunsa na hagu duk a
shanye suke ko sarrafasu baya iyawa.Aryan ya
zura hannu a cikin aljihunsa ya dauko dinare
guda
daya a lokacin daya tsaida dokinsa daf da
almajirin ya jefo masa wannan dinare a cikin
kokon sannan ya dubeshi yace,ba sadaka na
baka
ba,labari nake nema,mene dalilin wannan cikowa
mai yawa a cikin wannan birni?Koda jin wannan
tambya sai almajirin yayi murmushi yace,da
wannan dan kudin kake son kaji babban labari sai
sunyi kadan.Koda jin haka sai Aryan yayi
murmushi ya sake zura hannu cikin aljihunsa ya
dauko dinare guda ya jefa cikin kokon
yace,yanzu
fah?Almajirin yace da saura domin kuwa labarin
da zan baka zai amfaneku a matsayinku na
manyan jarumai daga babbar kasa.Koda jin
wannan batu sai mamaki ya turnuke sadauki
Aryan yace,A cikin ransa anya kuwa wannan
almajiri ba boka bane,yaya akayi yasan cewa mu
jarumai ne daga babbar kasa,kuma menene zai
amfane mu akan labarin da zai bamu.Koda gama
wannan zancen zucin sai Aryan ya sake fidda
dinare uku ya sauko daga kan dokinsa yazo ya
tsuguna a gaban almajirin ya zuba masa dinaren
a cikin kokonsa ya zama guda biyar sannan ya
dafa kafadarsa yace,Abokina bani labari me yake
faruwa a cikin wannan gari?Almajirin ya sanya
hannunsa mai kyan cikin kokon ya kwashi
dinaren
ya zuba su a cikin aljihunsa na wando sannan ya
dubi Aryan cikin nutsuwa yace,Ai sarkin garin
nan
ne ya shirya gasar jarumtaka ta duniya don haka
jarumai da yawan gaske sunzo daga manynan
kasashe,sarakuna sun zo,kuma attajirai yan caca
sun taru domin baje kolunsu a goben da safe a
gidan sarauta.Duk wanda ya lashe wannan gasa
za'a bashi zabin abubuwa guda uku ya dauki
daya ko dai ya auri yar sarki kokuma a bashi
dinare da rakuma dubu ko a bashi mulkin babbar
jaha daga cikin jahohin kasar nan.Koda jin
wannan batu sai Sadauki Aryan ya kamu da farin
ciki nan take ya aiyana a ransa

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login