Showing 6001 words to 7605 words out of 7605 words
Chapter 3 - Sa Maza Gudu Book 3 Book by Madakin Gini.txt
cewa lallai zai
shiga wannan gasa,amma ba don kawai a bashi
wannan dukiya ta dinare ba.Rakuma gudu dubu
saboda in ya koma gida yayi amfani da ita wajen
cika wani babban buri nasa wanda ya gagare shi
cikawa tsawan shekaru.Kawai sai Aryan ya dubi
wannan Almajiri yace Abokina meye sunanka?
Almajirin yace Sunana Hibairu bin Usman.Koda
jin
haka sai Aryan ya mikawa almajiri Hibairu
hannunsa na dama shima ya bashi nasa hannun
suka gaisa.Aryan yace,ina fatan zamu hadu gobe
a fada muyi kallon wanna gasa tare.Hibairu yayi
murmushi yace,tabbasa zamu hadu,koda gama
fadin haka sai Aryan ya mike da sauri yaje ya
hau
dokinsa ya zabure shi da sauri domin ya riski su
Gimbiya Malika saboda sun bashi tazara mai dan
yawa.Da isar Aryan wajen gimbiya Malika sai ta
dubeshi cikin murmushi tace,me ka tsaya yi a
wajen wancan almajirin?Aryan ya maidawa
Malika
martanin murmushin cikin biyayya yace,na
tambaye shi dalilin wannan cikowa mai yawa a
garin nan shine ya labarta mini cewa Sarkin
garinne ya shirya gasar jarumtaka ta duniya.Koda
jin wannan batu sai farin ciki ya lullube Malika ta
dubi Aryan tace,da zarar mun sauka a
masaukinmu kaje ka nemi sarkin kasuwa ka gaya
masa cewa nima ina son na shiga wannan gasa
don haka yaje ya biya mini kudin shiga gasar tun
kafin na yazo gareshi muyi lissafin kudaden.Koda
jin wannan batu sai tsoro da mamaki suka kama
sadauki Aryan ya dubi Malika cikin alamun
tsananin dimuwa yace,Haba ya shugabata ai
girmanki da darajarki tafi gaban shiga wannan
gasa,saidai ki barmu mu wakilceki kada ki manta
cewa gaba dayan manyan sarakuna kina hulda
dasu kuma babu wanda ya san cewa kina da
wannan jarumtaka bai kamata ki tonawa kanki
sirri ba.Koda jin wannan batu sai gimbiya Malika
tayi murmushi tace,idan kida ya sauya dole ne
rawa ta sauya.Ya kai Aryan ka sani cewa ni
yanzu
tun dana baro gida neman yadda zan kare kasata
daga shirin abokan gaba na daina daukar kaina a
matsayin yar sarki,wannan gasa da zan shiga ta
jaruman duniya zata taimaka mini na kara sanin
iyakar jarumtakata da iya yakina.Kuma zata
samini azamar das zan kara dagewa don
fuskantar babban aikin dake gabana.Abinda nake
so da kai shine kaima ka shiga wannan gasa
kaga
idan kayi nasara koda ni banyu ba shike nan
daukaka dai tana hannunmu.Koda jin wannan
batu sai sadauki Aryan ya sake duban Malika
cikin
alamun tsananin damuwa da mamaki yace,Haba
ya shugabata ta yaya zan iya lashe gasar
jarumtaka alhalin kina cikinta kuma na tabbatar
da cewar kin fini karfin damtse da iya yaki?Koda
jin wannan tambaya sai Malika ta yi murmushi
tace,yakai Aryan ka sani cewa karfin damtse da
iya yaki basu ne kadai ke sawa a sami nasara ba
akwai sa'a da rabo.Koda gama fadin hakan sai
Malika ta karawa dokinta kaimi tayi gaba ta nufi
masarautar garin
[5/20, 9:00 AM] princeauwal3156: SA MAZA
GUDU
Littafi na Uku(3)
Part E
Koda gama fadin hakan sai Malika ta karawa
dokinta kaimi tayi gaba ta nufi masarautar
garin,sauran tawagar suka bita da sauri a lokacin
da sadauki Aryan ya bita da kallo kawai yana
tunanin wannan kama da ta gaya masa ta
karshe,ya tabbatar da cewa shifa a rayuwarsa
sa'a da rabo take kaishi ga nasara bisa duk
abinda ya a gabansa amma ba wai jarumtakarsa
bace da iya yakinsa.Kamar yadda gimbiya Malika
ta shirya haka al'amarin ya kasance wato suna
sauka a masaukinsu,sai sadauki Aryan ya tafi
izuwa gidan sarkin kasuwa ya isar da sakon
Gimbiya Malika.Koda sarkin kasuwa yaji cewar
gimbiya Malika zata shiga cikin wannan gasa sai
mamaki da tsoro suka kamashi yayi kamar yaki
zuwa ya biya musu kudin shiga gasar saboda
tsoron kada wani abu ya sami Gimbiya Malika
Sarki Sharkuf ya turo a kamashi,amma da ya
tuna
cewa sadauki Aryuan babban badakaren tane
kuma amintaccenta,lallai da yawunta yake
magana kuma idan yaki bin umarninta zata iya
kwace duk harkokin kasuwancinta dake
hannunsa.Sai ya mike tsaye zumbur ya kama
hannun Aryan yaja shi suka tafi izuwa fada.Da
zuwansu sarkin kasuwa ya biya dinare dubu dari
sannan ya bayar da sunan Gimbiya Malika da
Sadauki Aryan a matsayin jaruman da zasu shiga
gasar.Su kansu masu rubuta sunan sai da suka
dago kai suna yiwa sarkin kasuwa kallon
mahaukaci sabon kamu,amma da suka fuskanci
cewa a cikin hayyacinsa yake lafiyarsa kalau sai
suka kamu da tsananin mamaki.Kashe gari da
duku dukun safiya fadar birnin misra ya cika ta
batse da jama'a ya zamana cewa duk inda
mutum ya hanga babu abinda zai gani face
kawunan bil'adama fululu babu matsakar tsinke
duk wani sarki mai isa gami da koshin lafiya ya
halarci wannan taro haka ma dukkan bokaye da
hamshakan attajirai sun zo,masana tarihi da
masu bincike a wannan rana saida suka tabbatar
da cewa ba'a taba kashe makudan kudade ba a
duk tarukan da kayi a duniya sama dana wannan
rana.Attajiran caca kuwa saida suka kure taskar
kudadensu suka fito dasu gaba daya saboda basu
taba yin cacar data kai wannan daraja ba.Duk
wanda ya cinye gasar ya san cewa idan aka
lissafa
attajiran duniya sai ya sami shiga a cikin mutane
goma.Saida kowa ya gama hallara a cikin filin
gasar sannan aka ji an buga gangar sarauta
alamar cewa ga sarkin Misra nan ya fito zai
shigo
filin gasar.Nan fa kowa ya mike tsaye don
girmamawa a wannan lokaci gimbiya Malika da
sadauki Aryan suna cikin jaruman gasa a tsakiyar
filin sunyi shigar kayan yaki kuma gimbiya Malika
ta rufe fuskarta da hular karfe.Nan take sai ga
Sarkin Misra tare da 'yarsa Gimbiya Zuhura sun
shigo cikin filin gasar.Yaune ranar farko da
mutane suka fara ganin fuskar gimbiya Zuhura
saboda bata taba fitowa daga gidan sarautar ba
tunda aka haifeta.Koda mutane suka yi arba da
Gimbiya Zuhura suka ga irin tsananin kyawun da
Allah ya bata sai suka dimauce suka kama
surutai
da sambatu,da yawa daga cikin matasan dake
wajen kuka suka kama yi saboda nadamar rashin
shiga wanna gasa ta jarumtaka ko don suyo suna
ace sun taba neman auren wanna 'yar
sarki.Hatta
Gimbiya Malika wacce take ganin kamar babu
mace mai kyanta a gaba daya wannan fili saida
ta
raina kanta ta gamsu a cikin zuciyarta cewa ita
mummuna ce akan gimbiya Zuhura.Tun da
sadauki Aryan ya shigo cikin wannan filin gasar
yake ta ware idanu yana kalle kalle da waige
waige ko zaiga Almajiri Hibairu a cikin yan kallo
amma ko mai kama dashi bai iya ganiba.Koda
Aryan ya juya ya fara kallon 'yan uwansa
jaruman
gasar sai zuciyarsa ta buga da karfi ya kamu da
tsananin mamaki.Ba komai ne ya haddasa hakan
ba face ganin almajiri Hibairu a cikin shigar yaki
kuma a tsaye daram cikin koshin lafiya babu
tauyewar hannu ko kafa.Suna hada ido sai
Hibairu yayi masa murmushi kuma ya dago masa
hannu,cikin alamun takaici Aryan ya ciza yatsa
yace,lallai wancan almajirin ya raina mini
hankali,ashe ba nakasasshe bane amma na dauki
kudina mai yawa na bashi sadaka,ai kuwa sai ya
biya ni kudina,kuma Allah yasa mu hadu dashi a
cikin wannan gasa dukan tsiya zanyi masa nayi
masa lilis amaimakon kudi na daya ci.Aryan yana
cikin yin wannan tunani ne yaji alkalin gasa yayi
gyaran murya a lokacin da filin gasar yayi tsit
kamar mutuwa ta gifta.Kawai sai Alkalin gasar
yace,Jaruman gasa na farko sune Gimbiya Malika
daga Birnin Madinatul Zauwara zata kara da
Jarumi Hibairu daga Birnin Nurul Islam.Koda jin
haka sai mamaki ya turnuke sadauki Aryan kuma
ransa ya baci bisa jin cewar wai wannan
makaskancin jarumi kuma almajiri shine zai
fafata
da gimbiyarsa.Su kuwa 'yan kallo da sauran
manyan mutanen dake filin gasar zazzaro idanu
sukayi saboda bisa jin cewa Gimbiya Malika 'yar
sarki Sharkuf ta shiga wannan gasa.Nan take
Jarumi Hibairu da Gimbiya Malika suka fito
tsakiyar filin gasar suka fuskanci jina
kowannansu
na rike da takobi da garkuwa,kawai sai ji sukayi
an buga gangar fara gumurzu.Dukaninsu sai suka
rugo da gudu kan juna suka runguntsume da
azababben yaki mai mutukar ban al'ajabi da ban
tsoro.
WAYE ZAI SAMI NASARA A WANNAN GASAR
JARUMTAKA TSAKANIN JARUMI HIBAIRU DA
GIMBIYA MALIKA?
WANE IRIN GAGARUMIN KARFIN DAMTSE DANA
SIHIRIN TSAFI YARIMA LAHAMAN ZAI SAMU
KUMA
IDAN YA HADU DA MALIKA ME ZAI FARU?
SHIN MALIKA DA SARKI HILAIRU ZASU KARBI
SOYAYYAR JUNA?YAUSHE NE GIMBIYA MALIKA
ZATA CIKA ALKAWARINTA TA MAYAR DA SARKI
HILAIRU KASARSA YA KOMA KAN KARAGARSA
KUMA A GYARA BIRNINSA?
TSAKANIN GIMBIYA MALIKA DA YARIMA
LAHAMAN
WAYE ZAI HAU KAN KARAGAR BIRNIN
MADINATUL
ZAUWARA YA KASANCE YA GAJI GIDAN
SARAUTAR?
MU HADU A WANNAN LITTAFI SA MAZA GUDU
LITTAFI NA HUDU DON JIN YADDA ZATA KAYA.An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT