Showing 192001 words to 195000 words out of 419207 words

Chapter 65 - Sarka Book Complete By Zainab Idris Makawa.doc

i not your wife Omar don haka ina da right din shiga maganan yan uwan ka idan ya taso.
Merry why are you disturbing me about dis isue na fada maki ra,ayina Muslim college na zaba mata final ya fada da karfi cikin anger yana wucewa.
Binshi tayi da kallo da jajayen idanuwan ta da suka rikide mata ta takowa nayi zuwa inda take tsaye sai lokacin ta ganni tayi kokarin saita kanta lokacin.
Fatema kina waje ashe kinji mu muna rigima da yayan ki kan ya kaiki makarantar da zaki waye ki san duniya.
Ban san may yasa ku musulmai kuke da akidan son addinin ku ba har cikin zuciyar ku baku duban goben ku sai abinda addini yace daku.
Wani kallo nake mata dan na kasa mata magana saboda ban san abinda zance da itaba wanan lokacin.
Ta kama hannun yarta tana fadin fita zamuyi nima zan koma bakin aiki na don kin san ba a nan nake aiki zuwa nakeyi in danyi kwanaki a nan.
Shima naji yana fadin ba a gidan nan zaki zauna ba zaki koma can central London don yafi maki kusa da school.
Daga haka tayi man sallama ta fice kitchen din su na nufa nan na samu masu masu abinci maza guda biyu na gaida su da aiki.
Suka amsa mi tare da tambayana idan ina son wani abune nace abincin gargajiya irin namu nazo dubawa idan akwai shi.
Da sauri bakan fatan yace min akwai su bari a duba maki idan basuyi expearing ba don su ka,idan su ne sai an duba abinci kafin amfani dashi.
Nayi mamakin ganin ledojin abincin dake can sako an ajesu dagani ba a amfani dasu ko yaushe.
Dubawa nayi daya bayan daya ina karantawa garin doya na dauka don sai naji sha,awan cin sakwara ranan duk daba cimana bane a gida.
Sosai na tsaya nayi aiki shi don naga yadda mamu take tukawa kawu idan yace yana son ci sai dai tasu baikai wanan laudi ba da haske.
Miyan ganye nayi don na samu ganye a cikin fridge din su nama daine sai dana tambaya wanan dan aikin bakar fata ya nuna min wanda ogo yake ci nan na gane naman halal ne naman tunda har ya ware na amfanin shi.
Kamshin girkin mu daban yake haka yasa gidan ya dauki kamshi na gama a daidai yamma yayi masu gidan sun dawo.
Sai da suka dauki lokaci kafin su fito nima wanka nayi nai sallah na dan saka wani riga mara nauyi tare da daura gyalen shi saman kaina.
Na fito da zuman cin abincin dana girka sai na samay shi zaune yana yankan loma hankalinshi kwance.
Da dan mamaki nake kallon shi kamar baisan ina tafe ba don baiko dago kai ba don jin tafiyan da yayi shawaran juyawa nayi in koma har ya gama don gaba daya ya juye min kamar ba ya umar din dana sani bane a yanzu tun zuwan mu kasan.
Muryan shi naji yana fadin ke zo nan na juya na dan kalli bayana koda wani yake magana ganin babu kowa a kusa yasani matsawa kusa dashi kadan.
Sannu da dawowa nayi mai yace ba tare da ya amsa gaisuwa naba merry ta gaya maki zuwa jibi zaki wuce makaranta.
Kamar ince bata fada min ba don ba ita ya dace ta fada min ba sai dai a yanzu tsoron shi nakeji sosai.
Kaina girgiza mai yace bakiji bane ana magana kin kyale mutane nace a cikin wani murya bata fada min ba kamar a shagwabe.
Yace zaki wuce an gama komai na tafiyan ki kamar yadda daddy ya bukata ai maki don haka har gidan da zaki zauna na tanadar maki shi a can da komai yadda ya dace.
Idan kinga wani abinda bai maki ba zaki iya magana a kawo maki daga baya do haka ki fara shirin tafiya ke nan.
Nagode Allah ya saka da alheri nace ya dan dago kai ya kalleni ya kawar da sauri yana fadin ki mayar da hankalin ki ki kuma tuna da matsayin ki a can saidai bai fadi wani matsayi zan kula dashi ba .
Shin matsayina na musulma ko matsayin matar aure dana zo dashi kasan zan kula ko may oho ?
Na kara yunkurin juyawa zan wuce yace ba abinci zakici ba zauna kici abinki nina gama cin nawa.
Ya mike tare da daukan tissue yana goge bakin shi ya bar wurin cikin tafiyan shi na izza da kamar sallo.
Aji???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?yan zuciya na sauke ina rayawa a raina wani lokaci kagan shi kamar mutumin kirki amma a zuciya baude yake ko iyalin shi bai raga masu ba ni yanzu ba zance ga halin shi na gaskiya ba.
Don wata rana nakan ji sanyi wata rana kuma ya juye min kamar mara imani haka yasa na kasa fahintar yaya halinsa yake na gaskiya.
Zama nayi na zuba abincin ina ci sai ga merry ta fito daga dakin su tun daga nesa na fahinci yanayin ta yau ba dadi.
Samu wuri tayi ta zauna tana kallo abincin da nake ci din take tambaya waya hada abincin nan haka ?
Nace nice na girka da kaina nunani tayi da baki tana fadin you will become mumu very soon.
Tana gwada yadda zan koma da hannayen ta abinda ya dan sani murmushi sosai ke nan.
Kara kallon abincin tayi tare da fadin naga alaman kinji dasin wanan abincin sosai yadda naga kina cinsa yau da yawa.
Kai na gyada ma ta fara bude kulan abincin su sai taga ba,a taba ba da mamaki a fuskanta take tambayana brother din ki baici abinci bane ?
Nace yaci sai ta kalli abincin nawa da ido ta kuma maida hankali ga plate din da yaci nasa tace i understand now wanan da kika girka yaci ke nan.
Nan suka fara adduan su na gwalanci ido rufe ita da yar ta danaji tana kira da paith.
Bayan sun gama ne ta fara diba zata ba yar sai yarinyar ta girgiza kai why paith ta tambayi yarinyar ?
Mum i dont want to eat dis ta nuna nawa da hannun ta tace wawoo you means wancan zakici ko may ?
Ba tare da nayi magana ba na jawo plate na dan zuba kadan na tura mata gaban su yarinyar ta fara murna tana nuna abincin da hannun ta.
Ina tsakuran abincin ina kallon yadda yarinyar ke amsan abinci a hannun uwarta tana ci.
Can merry ta dago kai tace brother din ki yace tafiyan ki next tomorrow ne zaki zauna a centeral London.
Naso ace ya barki gida tunda zaki iya zuwa daga nan kullun duk da dai wurin yana da nisa da nan inda muke.
Anyway hakan ma da yayi yana da kyau don zakifi maida hankalin ki ga karatun ki saidai banso wanan school daya zaba maki ba don komai su a addinence suke abinsu.
Naso ya kaiki inda kanki zai bude ki waye sosai ki koyi mu,amula da mutane kala kala a duniya .
Zakiji dadin rayuwan ki idan kin je gurin saidai shi har yanzu yana da wanan kishi na islama a zuciyar shi.
Ba laifi ko can zaki waye din don zaki koyi abubuwa da dama dangane da addin ku saidai ni ba hakan naso dake ba.
Yadda kike Queen din nan ya kamata ace idon ki yafi nan budewa sosai koda zaki koma gida suga kin canza daga yadda suka sanki a baya.
Dan murmushi na sakar mata kafin ince ko wanan ma nagode don yaga ya dace danine ya kaini can ban faye son abin wayewa ba kwarai tace see you.
Tunda naji zancen tafiyan na fara shirin a tsanake don dama har lokacin kayana suna a yadda mamu ta saka min su ban taba ba.
Ina kewan gida sosai a raina saidai ba yadda zanyi don ni nawa kaddaran auren a haka yazo min zama kadaici yana min yawa saidai in fita dan wani hili dake bayan tagana daga dakin zaka iya tsayawa kana kallon ko ina na garin.
Ina kwance a dakin da dare sai gasu sun shigo ita dashi ina ganin su nayi yunkurin mikewa zaune.
Gaida su nayi merry ta amsa min da kyat itama wani kati ya miko min nasa hannu na karba yace wanan Oyster din ki ne don saukin tafiya guraren da kike so zuwa katine na shiga jirgin kasa ta wanan kasan.
Duk wani sauran abinda zaki bukata yanzu akwaishi a gidan zakiyi registration idan kinje Aaliya Arnall ki maida hankalin ki kiyi abinda ya kawo ki nan ban son wasa ko hurda da abokan da basu dace ba ki tsare .
Kudi ba matsalan ki bane don a kwai komai da zaki bukata a wanan katin ya sake miko min wani karamin katin na kudi.
Gobe merry zata kaiki idan ta dawo zata wuce itama gidan zai koma ba kowa ke nan sai masu aiki.
Har ya juya na furta nagode Allah ya rufa asiri nasan dama ba zan samu amsa ba na dai fada ne saboda sabo da hakan.
Mikewa merry tayi ta bi bayan shi ba tare da taimin magana ba suna fita na sauke ajiyan zuciya ina bin katin da kallo tare da fadi a fili wai wanan kudine don Allah.
Alam din agogon dakin ya tayar dani daga barci hakan na nuna min asuba yayi ke nan tashi nayi na fada ban daki nayi wanka tare da dauro alwala na fito na tayar da sallah gari dip ba wani alaman lokacin sallah yayi saidai mutum ya ksatanta kawai.
Nockin din da naji anayine yasa na mike a raina na dauka merry ce koda na bude shine a tsaye da sauri nace dashi ina kwana yaya ?
Lafiya yace tare da fadi a lokaci daya kin shirya ko nace eh yace ga usman nan zai shigo ya daukar maki kayan ki ya fadi yana daure fuskan shi.
Juyawa nayi cikin dakin na karewa dakin kallo ba abinda na bari mallakina a dakin saidai nasu ban taba komai daga cikin abinda na samu a gidan ba.
Shiya ja motan kai tsaye zuwa unguwar dayace din tafiya ne mai nisa sosai a tsakani na yarda central London muke bayan nan kuma wai a acition town gidan yake (lahore).
Gidane mai bene daya kamar sauran yawancin gidaje unguwar dauke da dan get da garden da garge gidan nada dan girma dakuna hudu ne sai kitchen da dan hilin shan iska a waje da falo mai dan girma irin dai gidajen su na can komai na gidan neat.
Bayan ya gama nuna min komai mun fito daga gidan sai makaranta don yin registration ba wani nisa da gidan don koda kafa zan iya zuwa kuma in dawo.
Sai da yaga komai ya kammala ya dawo dani gidan tare da tambaya ko akwai wani matsala kuma ?
Cikin nuna alaman ya gaji shima da zirga zirgan da mukayi din lokacin .
Nayi raurau da idanu na fadi a sanyaye ba komai saidai yaya ni kadai zan zauna a wanan gidan kuma ?
Kina tsorone ya tsareni da idanuwa yana son jin amsa ban iya bashi amsa ba nayi kasa da kaina kawai.
Gyara tsayuwan shi yayi yana fadin ki saki ranki kiyi karatu yadda ya dace daddy ya fada min likita kike son zama.
Koba haka bane na gyada mai kai alaman eh yace to baga shi kin samu ba har zaki fara karatun ki .
Zan dinga zuwa ina dubaki idan ina gari abinda nake so dake kawai ki maida hankali ta yadda daddy da maimuna da sauran iyayyen ki zasuyi alfahari dake nan gaba.
Kinji ko wanan unguwa yana da tsaro sosai fiye da ko ina a cikin garin nan don kuna kusa da birnin sarauniyan kasan .
Ina kallo ya ja motar shi ya bar gurin har ya bace min da gani ajiyan zuciya na sauke nabi gidan da kallo ina mamaki a raina wai ni kadai zan zauna a cikin sa.
Tsoro yasa na rufo get din gidan a hankali naja kafana zuwa cikin falon kamar wace za a kama har nakai tsakiyan falon naja na tsaya wuri daya ina bin ko ina da kallo.
Komai akwai na more rayuwan dan adam a falon takawa nayi zuwa kitchen din daya nuna min din.
Fridge din kitchen din na nufa na bude ko zan samu wani abin sanyi koda ruwa ne in sha a cikin sa.
Tab yake da kayan shaye shaye da sauran tarkace na girki lemon gwangwani dana gani nakai hannuna dauka tare da rufe fridge din na fito.
Falo na dawo na zauna na bude lemun ina kurbawa a hankali cikina ya fara karan wahalan yunwa don samun dan wani abu daya shiga mai yanzu.
Ina gamawa na tuna banyi sallah ba ko a zahar ga la,asar ya nuna lokaci dakin daya nuna min shine matsayin bed room dina na nufa a hankali na haura saman nan ma na tsaya ina bin ko ina da kallo.
Alwala nayi na fito na tayar da sallah bayan na idar na dade zaune ina rokon Allah kariya daga duk wani masheran cin abun da zanyi karo dashi a cikin wanan kasan.
Bayan na idar na mike don gyara kayana cikin wardrobe din dana gani a dakin ina budewa sai da gabana ya fadi.
Tufafine ciki a jere wanda babu kalan da babu daga dogon rigar abaya zuwa english wear da pakistan komai a natse tsab.
Zaune nakai bakin gadon ina kallon kayan cikin mamaki da firgici a raina sai lokacin na kula da saman mirrow din dakin kuma,
Mayuyuka shafine da su turare da sauran kayan kwaliya irin na mata a saman table din mirrow din.
Mikewa nayi daga inda nake zaune da sauri na karasa wurin ina duban kayan a hankali.
Hatta su pad da duk wani abinda zan bukata an ajiye a gidan don bukatan mutum komai ke nan saida ya tanadar min shi kafin inzo.
Fitowa falon gidan nayi na zauna shiru ina faman tunane can dai na mike don samawa kaina mafita kitchen din na koma ina bude bude naga abubuwan bukata na abincin nodles na dauko irin hadin mu nayi na gama na zauna naci saida na koshi.
Wanka nayi tare da sallah na haye gado na kwanta don banson makara da safe don farkon zuwa nane ga dokin da nake faman yi a raina.
Ranan wednesday na fara shiga school kowa ya ganni yasan bakuwa nake farkon zuwa na ke nan don irin yarda nake nesa da mutane.
Sosai na mayar da hankalina ga karatu Alhamdullahi kuma ina fahinta da kyau shida saura na iso gida don takowa nayi da kafa don inkara garin da kyau duk da ashe akwai dan jawa kadan tsakanin mu dasu.
Tun ban saba ba har na saba da safe zan tafi a mota don gudun makara idan zan dawo kuma nakan tako da kafa don in dan motsa jikina.
Ranan da ba karatu kuma haka zan wuni da kewa gida a raina idan zama da tunane ya isheni nakan fito ina zagawa cikin unguwan don debe kewa.
Ban manta da karatuna na addini ba don nakan dan taba idan ban komai kuma makarantar suna da kula wajen koyar da ibada.
Saiko kallo dana koyi yi yanzu saboda zaman kadaicin da yake min yawa ni dai gani nan zaune a kasan mutane ba wanda na sani sai Allah sai ma,aikin sa.
Tun ranan daya kawo ni wanan gidan daga shi har merry ban kara jin durinyan kowa daga cikin su ba, har tsawon sati uku ni kadai ke rayuwa na tun ban saba ba har yakai na saba da hakan yanzu.
Zama ni kadai baya damuna sai dai rashin waya a tare dani yanzu ne nasan matsalace rashin waya a tare da mutum.
Gashi dai gidan babu abindana nema na rasa na rayuwa zan ci mai kyau in saka mai kyau in kwana wuri mai kyau.
Amma kadaici ya hanani jin dadin hakan sosai sai yazama har na fara yar rama saboda damuwan dana jefa kaina a ciki.
Yau ina shawan saka irin tufafin mu na hausa don haka na dauro zani da riga da sai hijab dina dana dora saman kayan.
Abin kallo na koma a wurin mutane wasu har waige na sukanyi idan na wuce su niko hakan bai damay ni ba don ban ma san sunayi ba.
Gurin sallah na fito ina sauri in koma lectures karshe da zamuyi ranan naji ance Am i dreaming ko gaskiya ne ?
Jin ana magana da hausa yasani dago kai inga ko waye nayi mamakin ganin wanan the guy din na makarantar dana kare a kano.
Rabo dana kara ganin sa tun suka kare karatu dasu salma ban kara jin duriyan shi ba sai wanan ganin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login