Showing 1 words to 3000 words out of 52544 words

Chapter 1 - MAKAUNIYA CE BOOK COMPLETE BY Jidda s Mapi.txt

13 Oct 2025

185

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*Written by*
Jiddah S Mapi


*بسم الله الرحمن الرحيم*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*

*Assalamu Alaikum wannan littafi nayishi ne akan yanda mutane suke nuna kyamarsu ga nakasassu, ayau abinda yazama ruwan dare a duniya shine nuna kyama da ake ga nakasassu, musani fa su wanda suke da nakasan bada son ransu bane ba! Allah ne yaɗaura musu, muma bamufi karfin Allah ya jarrabemu da nakasa ba,wasu idan kaji sanadin da suka samu nakasa saika yi kukan Tausayi, jama'a muji tsoron Allah mudaina nuna kyama ga nakasassu.*
*Ina fatan Allah yasa nagama wannan littafin lafiya*


*WATTPAD*
_Jiddah S Mapi_


*Page* 1

"Karamin gidane me ɗauke da ɗakuna biyu Ɗaki ɗaya babba ne sannan ɗan karami agefenshi,
Cikin gidan an zuba duwatsu kanana da Alama sabida yanayin da ake ciki na damuna akasa,
Katangar gidan tayi ɗan kasa kamar zata faɗo sabida yanda tagaji,
Langa langa ne kewaye da gidan wanda be gama rufe cikin gidan ba.
Mutumin dake waje ze iya hango mutanen gidan".

Da Alama wannan gidan na marasa karfi ne waɗanda suke neman ataimaka musu.

"wata matace nagani zaune abakin kofar babban ɗakin tana daka cikin turmi da Alama barkono take dakawa! Domin tana ta atishawa, matar bazata wuce shekaru 32 Zuwa 33 ba, daganin kayan jikinta zakasan tana cikin matsin rayuwa, riga ne dogo na Atamfa pink wanda tsabar koɗewa harya zama fari, farace sol kyakkyawa da ita duk da yanayin datake ciki hakan be hana kyaunta fitowa ba! gefenta kuma wata kyakkyawar yarinya ce me kama da ita saidai kawai yarinyan tafita haske, yarinyan bazata wuce shekara 15 ba, daganin fuskarta zakasan yarinya ce karama sai girman jiki da tsayi, ita yarinyan tana yanka albasa idon ta duk hawaye, Matarce tnaji tace "Minal meyasa bakya yin abu da karfinki ne iye tin ɗazu fa kike kan yanka Albasa Ama har yanzu ace baki gama ba so kike sai alalen tayi sanyi kafin kikai musu?"

"Yarinyan danaji ankira da Minal naga taɗago kanta tana goge idonta tace Umma wallahi albasar ce da zafi"
Umma tace ay Minal yakamata ayanzu ace kin saba da wahala, Umma ai ba'a sabo da wuya cewar Minal, hakane Amma ai akwai wahalan Daya zama dole Asaba dashi.. Bama wannan maganar ba meyasa kwana biyu naga kin daina karatu? Minal ce tace Agaskiya Umma nahakura da karatun, umma tace haba Minal meyasa zakice haka bayan kinsan mahaifinki tun kafin yarasu yaso kiyi karatu sosai meyasa zakiyi haka?
Minal tace Umma naga karatunnan cikin takura nakeyinta, kiduba mana kigani yanda muke shan wahala kafin musamu kuɗin time, aganina kuɗin da zamu kashe wajen karatu ba gara mukashe shi tahanyar cin abincinmu dakuma kayakin sawa tunda bamu dashi"

Umma ce tace "Minal bazan yadda karatunki yaɓaci ba insha Allah sai kinyi karatu, tinda Allah yasa kinada Ilimi,
Kici gaba dasayar da Alalenki tunda Allah yasa kina ɗan samu nikuma zanje na nemi aikin wanke wanke ko a inane"
Minal tace "to Umma"
Umma ce tace yanzu tashi kije kiyi wankanki kinji?
Minal tace to Umma.

"Wanka tayi tafito tashafa mai da turarenta na cikin kwalba wanda bazai wuce naira talatin ba, tashafa wani powder fari da aka kulla a leda taɗansa kwalli a idonta, tayi kyau sosai duk da bawani kwalliyan kirki tayi ba, wata koɗaɗɗiyar shadda taɗauko tasa wanda duk ta tsufa ta yayyage amma An ɗinka, tsugunawa nayi zata ɗauki Hijabi cikin riyon kayanta taji riganta ya yage tabayan, taɓawa tayi taga rigan ya yage har kusan cinyarta, tinawa tayi da zaren datake ɗinka kayanta dashi tabari agidansu Madina, kuka tafashe dashi na takaici, wannan wani irin rayuwa ne? ace mutum kullum yana cikin ɗinka kaya? Ya Allah kafitar damu daga cikin wannan talaucin"

Umma ce taji Minal shiru, taleka ɗakin tana tambaya wai ina kike ne Minal
Tin ɗazu kina kwalliya kamar wata Amarya?
Ganin Minal tayi tana kokarin goge hawayen fuskarta tace "Na'am Umma gani"
Umma ce ta tsaya shiru tana kallonta yanda take kokarin ɓoye damuwarta,
Tace "Minal meya faru kike kuka?"
Minal tajuya bayanta tana nunawa Umma inda rigan Ya yage tace "kigani Umma kullum ina kan ɗinka kayana da hannu?"
Umma tace "shine kika zauna kina kuka Minal? To indai wannan ne karki damu zan ɗinka miki akwai zare a ɗakina kinji ko 'yata?"
Minal tace nagode Umma na Allah yabarmu tare har karshen rayuwarmu,
Umma tace "Ameen"

Umma ce taɗauki kayan taje taɗinka mata, sawa Minal tayi ajikinta tace "Umma na nagode" Umma tace "Kidaina godemin Minal kefa 'yata ce, 'ya guda ɗaya wanda Allah yabani, idan banyi miki ba wazan yiwa?"

Hawayene yafara fita a idon Minal, jin kalaman Ummanta, azuciyarta tace lalle nayi sa'ar Uwa wacce take sona Ubangiji Allah ka kara mata nisan kwana.

Rungumarta Umma tayi tana share mata hawayen itama batasan lokacin da Hawaye yafara zubo mata ba, ahankali Minal take sharewa Ummanta hawayen, tace "Umma bara natafi kar nayi latti"
Umma ce tace "to Minal kikula da kanki, kitaimakawa wanda yake neman taimako, kada kina duban mutane nasama dake, kina kallon nakasa dake kinji ko Minal?"

Minal ce tagyaɗa kai tace to Umma nagode saina dawo.

Fita tayi a ɗakin tasa wani slifas da cikinshi duk ya ciccinye, takalmin yafi karfin kafarta, sawa tayi tana jan takalmin taɗauko kwanun Alalenta da wasu robobi tafita.

Tana fita tashiga wani gida dake makwabtaka dasu, kiran sunan Madina!! Naji tayi da karfi, wata yarinya ce sa'ar Minal naga taɗauko roban awara tace ganinan Minal tin ɗazu nashirya baki zo ba,
Minal ce tace "to fito mutafi tinda gani"

Fita sukayi agidan suna sauri, Minal ce tace "Madina Allah yasa musamu ciniki don ni inason insiyi kaya da ribana kayana duk sun tsufa, duba kiga takalmin kafana Dakyar nake iya tafiya dashi wannan wani irin rayuwa ce? Madina anya zamu fita a wannan talaucin?"

Madina ce tace "haba Minal meyasa zaki faɗi haka? Mutane nawa suke cikin talauci daga baya Allah yaciresu? Mutane nawa suke da kuɗi kaddara tafaɗo kansu kiga sun talauce? Kuma ai dukkan menema yana tare dasamu, mucigaba da Addu'a kawai"

Madina tace "to"

Daidai wani Babban company naga sun tsaya, Madina ce tace ina ganin yau anan Zan tsaya don nayi latti ma'aikatan duk sun karya nasani, Madina tace nimade gara nazauna dan bawani ciniki zanyi ba idan nashiga.

Wani Bakin mota kirar marsandi da baƙin glass naga ta tsaya akofar company ɗin, megadi ne yatashi dasauri yaje yabuɗewa me motar get nashiga companyn.

Madina ce naga tana mintsinin Minal, tace "Minal kalli kiga mutuminki shima yau yayi latti"

Minal ce takawar dakanta tace "Madina banason ko ganin motar wannan mutumin. Hasalima ban taɓa jin tsanar wani a rayuwata ba kamar yanda nakejin na tsaneshi, shima nasan duk duniya babu wanda yatsana kamar ni, shiyasa wani lokacin sai naji kamar kar in kawo talla anan sabida irin wulakancin dayake nunamin, hawaye ne yafara fita a idonta ahankali tasa gefen hijabinta ta goge"

Madina ce tafara bata hakuri.

Mutumin da megadi yabuɗewa kofa kuma sainaga yatsaya dab dasu yasauke glass na motar yaɗan leko kanshi kaɗan nan naganshi wani fari ne tass yasa bakin glass yanada dogon hanci gashin kanshi kuma baki ne siɗik
Wanda yasha gyara yana yalki,
Megadi ne ya iso wajen yace "yallabai kana bukatar wani abune?"

Mutumin ne naga yabuɗe baki ahankali kamar wanda bayason magana yace kiramin wancan dirty girl ɗin.

Megadi yace yallabai bansan abun ba.

Mutumin ne naga yayi tsawa wa megadin yacw " nace kakiramin wancan kazamar yarinyan"

Megadin ne jikinshi yafara rawa yace "to yallabai"

Yana zuwa wajensu Minal yace "Minal yallabai yana kiranki"

Minal ce tace kaje kace mishi bazan zoba! Idan magana yakeson yi dani shi yazo,
Megadi ne yace "kinga Minal kibi mutuminnan ahankali sabida kisamu kina sayar da abinki akofan companynsu, yau idan yakoreki zaki shiga cikin matsala"

Minal ce tace nagommace yakoreni a companynsu da irin wulakancin dayakemin kaje kace mishi nace bazan zoba!

Megadine yajuya yakoma wajen mutumin gudun karya rasa aikinshi.

Yace yallaɓai tace wai bazata zoba indan kanason magana da ita kaje kasameta,
Mutumin ne naga ya buɗe mota yafito da zafi yace who is she? Waye ubanta agarinnan? Metake takama dashi? Dahar zan kirata taki zuwa?.

Megadi ne jikinshi yafara rawa, yace yallabai ban sani ba wallahi... Ya isa cewar mutumin dasauri yakarasa wajen Minal, yana zuwa yayi ball da roban alalenta, alalen duk ya zube akasa, Minal ce tatsala ihu tarike kafarshi tana kukan saiya biyata alalenta.

Dasauri ya hankaɗeta yace "wacece ke dahar BILAL ze kiraki kice bazakizo ba? Waye ubanki agarinnan?

Minal ce tace ubana ba kowa bane agarinnan Amma ubana yasan darajar mutum shiyasa yakoyamin sanin darajar mutane, ba kamar naka uban ba! Kuma dakace ban isa in kiraka kazo ba ai gashinan kazo.. Kafin takarasa maganar ya wanketa da wani mahaukacin mari yana huci yace "Kin isa? Wallahi baki isa ba!.

Zuwa lolacin mutane sun cika wajen taf suna ganin yanda Bilal yake dukan Minal Amma babu wanda ya iso wajen gudun kar Bilal yakoresu a aikinsu.

Minal bakinta yaki shiru sai jan Allah ya isa take tayi mishi,
Madina ce taga yanda yake dukan kawarta sai kawai taɗauki marfin robar awarta tafara kwala mishi, wani matashi ne ya iso wajen shima bazai wuce sa'an Bilal ba, yafara janye Bilal daga wajen dakyar yasamu Bilal yadaina dukan Minal.

Mota yabuɗe mishi Bilal ne yashiga motar zuciyarshi tana mishi zafi, matashin ne naga yaje wajensu Minal.

Ɗago Minal yayi dataketa kuka yaciro tissue a aljihun rigarshi yagoge mata idonta yafara share mata jikinta, daya goge mata jikinta yaɗauko roban alalenta yace ɗaura akanki, Minal ce takarɓi roban tasa akanta, yaciro kuɗi 'yan dubu ɗaɗɗaya yabata yace gashi kitafi gida kinji ko?

Minal ce tace "Aa karike kuɗinka Ummana zatayimin faɗa idan taga kuɗin" yace Aa kikarɓa bazatayi miki komai ba kice mata yayanki ne yabaki sunana Latif,
Minal taki karɓan kuɗin duk yanda yayi Da ita taki karɓa, saida yahakura, yana kallonta ta ɗauko ɗayan takalminta tasa tacewa Madina nikam natafi sai kinzo, juyawatayi tagoge hawayenta tana ganin 'yar uwarta awajen sana'a Amma ita wannan mutumin yahanata sakat, azuciyarta tace "Allah ya isa tsakanina dashi"

Tafiya tayi tabar wajen tana share hawayent.

Latif ma juyawa yayi yakoma cikin motar Bilal.

Shikuma Bilal yana shiga motar ya kwantar dakanshi jikin staring yana mein baking ciki, jiyake dayana da bindiga ba abinda Ze hanashi harbe yarinyannan yau, yatsaneta kamarshi Bilal ace yakira yarinyan nan tace bazatazo ba! Lalle sai yayi maganinta,
Latif ne yadafashi yace "haba Bilal wannan wani irin rayuwace kana ganin irin talaucin da yarinyan nan take ciki amaikon. Kataimaka mata sai kuma kake kuntata mata?"

Ya isa Latif nalura yarinyan tanada rawan kai amma insha Allah saina gyara mata zama, zatasan Bilal taraina,
Yana faɗan haka yaja motarshi yashiga cikin companyn.


_pls ✅ote Comment and share_


✍🏻 *JIDDAH S MAPI*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*Written by*
Jiddah S Mapi


*بسم الله الرحمن الرحيم*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*

_wannan littafin sadaukarwane ga yayata Maryam S Mapi_


*WATTPAD*
_Jiddah S Mapi_


*Page* 2

"Minal tafiya take tana hawaye yanzu idan naje gida mezan faɗawa Umma na? Gashi yau ko abincin dazamuci babu, wannan mutumin yacuce ni, dana sani ma dana karɓi kuɗin wannan Latif ɗin, to Amma idan Ummana tagani mezan ce mata? Ita kaɗai taketa maganar, tana cikin tunani taga wani me keke saura kaɗan ya bugeta, da gudu tamatsa awajen, me keken ne yace ke wace irin wawiya ce? Ana tamiki magana kin share mutane kina tafiya yanzu idan nakaɗeki saiki janyo min matsala wawiyar banza,
Minal ganin yanata zaginta acikin mutane yana mata ihu yasa tace mishi Malam bana matsa maka ba? Yazaka tsaya kanamin ihu? Nifa ba 'yarka bace ba tamm, yace ko zaki dake nine? Matsiyaciyar banza kazama, ran Minal ne yaɓaci tace niba matsiyaciya bace, yace se waye? Tace sai kai... Ai kuwa kafin takarasa ya sauko akan keken yaɗaga hannu zai sauke mata mari wani mutum daga gefe yarike hanunshi yace haba bawan Allah tunda ta matsa ba shikenan ba?
Ke kuma kina mace zaki tsaya kina faɗa da namiji a titi?
Minal ce wanda tuni idonta yafara kawo ruwa tace Baba tinani nake shiyasa yayi tamin magana banji shi ba Amma tinda namatsa ai sai yayi min uzuri.
Mutumin ne yace to yanzu dai kowa yayi hakuri, Minal ce tajuya tayi tafoyarta tana me share hawayenta.
Azuciyarta tace nikam banida farin jini awajen kowa, haka harta isa gida,
Tana shiga gida Umma tace Meya dawo dake Minal? Hala kin manta yaji ko nasanki da mantuwa, Minal ce tafara kuka zuciyarta tana mata raɗaɗi, Umma tace haba Minal meyasa kike kuka? Koso kike nima in fara kuka ne? Minal tace Aa Umma dama Faɗuwa nayi damuke tafiya shine alalan ya zube,
Umma tace to dan Alale yazube shine zakiyi kuka? Wanima arana ɗaya yake rasa gidanshi da dukiyar shikuma wancan ya zeyi? Indai akan wannan ne kidaina kuka Allah yasan damu kinji ko? Minal tagiɗa kai"

_Washe gari_

"Minal ce tafita da Alalenta taje gidansu Madina sun fito tare, ahanya Minal take cewa Madina nifa inajin kamar in canza wajen saida alale Dan Ummana batasan meyake faruwa ba! Datasani bazata barni naci gaba da saidawa anan wajen ba. Madinace tace Aa Minal karki faɗa mata kici gaba dakai abunki karki kulashi kinji?
Minal tace tom amma bazan iya daure wulaƙancin shi ba,
Madina tace idan bakya kulashi zai daina.

Shikuma Bilal idan yatuna abinda wannan ƙazamar yarinyan tafaɗa mishi sai yaji kamar yakashe kanshi,
Kwance yake akan makeken gadonshi ya lulluɓa jikinshi da bargo me taushi, jiyake yau kamar kada yaje din bayason ganin yarinyan ko kaɗan.

Knocking na kofarshi aka fara, ahankali yace Who is that? Ba'a tsaya da buga kofarba yasake cewa i say who is that?
Muryan mace ne tace "Afrah ce"
Yace me kikazo yi?
Tace "Mom ce tace nazo naduba ka sabida yau kofita bakai ba"
Yace shine inyi miki me yanzu?
Tace "kabuɗe inason inga lafiyarka hankalina yakasa kwanciya"
Wani takici ne yakamashi yanzu yaji da abinda yake damunshi ne ko yaji da nacin Afrah?
Shifa gaskiya yarinyan tafara isanshi dolene yaɗau mataki akanta, can daga bakin kofan naji tasake cewa "wallahi idan baka buɗe naganka ba zan iya mutuwa"
Bilal ne yaji kamar yarufe idonshi yaganshi a lahira tsabar takaici.

Tashi yayi yaje bakin kofar yabuɗe mata,
Wata yarinya ce wanda zatakai shekara 22 naganta sanye da dogon riga roba roba kanta ba ɗankwali tayi kitson attach kamar ba gobe, farace ita amma ba sosai ba, idonta tayi fixing na eyelashes dogo dogo, tanada jiki kaɗan, rigan jikinta yakamata sosai, tauna cingum take yana kara kass kass kass, tsaya Bilal yayi yana kallonta.

Azuciyarshi yace "yanzu wannan Musulma? Meyasa 'ya'yan musulmai suke haka?..
Kafin yakarasa maganar yaji saukan hanunta a shoulder ɗinshi, tana cewa "Honey meya sameka kazama wani iri haka?"
Janye hanunta yayi daga jikinshi kafin yace "ke kinga banason raini, idan kika kara shigo side nawa da ire iren wannan dressing ɗin saina ɓata miki ranka, oya get out".

Afrah ce tace "haba yaya Bilal meyasa zakamin haka? Kasani fa duk kwalliyan danakeyi sabida kai nake, amma sam baka gani, ina laifin wanda yace yana sonka?"

Bilal ne wanda ranshi yafara ɓaci sosai yace "Afrah waike wace irin mayya ce? Nace banason kina cewa kina sona Amma meyasa bakyaji?"

Sabida inasanka! wallahi yaya inasanka! Kuma Aurena nakeson kayi.

Ɗago kanshi yayi wanda idanunshi sukayi jaa, yace "ke in zan Aura? Ai ko mata sun kare a duniya bazan Aureki ba! Afrah kicireni aranki niba sa'anki bane"

Afrah ce tace "me bani dashi wanda 'ya mace take takama dashi? Me narasa arayuwata? Menene aibuna? Kuɗi, kyau duk ina dasu kai kanka kasan kuɗin ubana,
Kasan zan iya kashe ko nawane akanka, sannan kasan yanda Babana yake sona, ko nawa zai iya kashewa dan nasamu farin ciki...... Ya isa cewar Bilal.

Kuɗi, Babana, kyau, kullum shine maganarki, nasan baki rasa waɗan nan ba, Amma kin rasa abu Ɗaya wanda yafi muhimmanci a rayuwar mace.

Afrah tace "kafaɗamin mena rasa? Saina nemoshi ayau ko nawa ake saidawa".

Bilal ne yace "kuɗin ubanki be isa yasiyo muki ba sannan kyaunki baze iya nemo miki ba"

Menene wannan Bilal? Kafaɗamin.

Bilal yace "Kunya"

itace abinda kika rasa,
Sam baki da ita.
Yana faɗin haka yawuce toilet, tara ruwa yayi acikin bathtub, yazauna aciki shower yakunna tasaman kanshi, lumshe idanunshi yayi me yana tunani acikin zuciyarshi, wannan wani irin rayuwace? Ace mace kwata kwata batada kunya? Nace bana santa amma ta nace, ko matan duniya sun kare yana ganin bazai iya auren Afrah ba!
Yarinyan da bata tsoron jikin niji kp kaɗan, kai ina daya Auri Afrah gara yamutu ba Aure.

Sabulu Me sanyin kamshi yaɗauka yana gogawa ajikinshi, idonshi a lumshe, Yana gama wankan yaɗauko towel babba da karami yaɗaura babban daidai konkosonshi goge kanshi yake da karamin, ahankali yabuɗe Kofar toilet ɗin.

Yana fita aɗakin yaga Afrah kwance akan gadonshi, mamaki ne da takaici suka kamashi alokaci ɗaya, wannan wace irin mayya ce?
Karasawa yayi inda take azuciy, saidai yana zuwa Jikinshi yayi sanyi, ganin yanda ta tattara riganshi tarungume tana bacci.

Tsaki yaɗanja kaɗan, yajuya yakarasa wajen kayan shafe shafenshi,
Mayuka masu kamshi yashafa ajikinahi tare da turare me kamshi da sanyaya zuciya,
Cumb yaɗauko yataje gashin kanshi me tsantsi da yalƙi, wajen wardrobe nashi yaje yaciro wani pink nariga da baƙin jins, hanyan toilet yanufa yaje yasa kayanshi, koda yafito saiya duba kanshi a madubi yaga yayi kyau.
Makullin mota yaɗauka yafice agidan.

Ita kuma Minal yau daɗi Takeji me takurata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login